23.



Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuh

Ku yi hakuri kun ji ni shiru. Har nagama typing na ji babin be yi ba sam. Shiyasa na yi tambaya a IG story dina.

This chapter is dedicated to all that took their time to respond. Jazakumullahu khairan.

I lost my grandma💔 Dan Allah ku sakata a addu'a.









JUNE 2010.

"Maryam fa ki ka fara waya da MK babu ranar gamawa kaman a kan ku a ka fara soyayya. Dan Allah ni ki faɗa mun inda ya ke sauri na ke yi." Hamida ta ce cike da ƙosawa.

Maryam ta gyara kwanciyarta a kan gado tana nunawa Hamida inda abun ya ke da yatsa. "Ba tun jiya na ce naka ba ka ƙi yarda. Had it been you listened to me da an yi avoiding haka amma ka nuna ka ƙware. Gashi nan ka yi asara ai kuma ka zauna da yunwa."

"Na ji, na ji. Moral of the story shine in riƙa jin maganar ki Your Highness." Khalid ya amsa ta ɗayan ɓangaren.

"Maryam!" Hamida ta ce da ƙarfi. "Ni fa ban gani ba. Dan Allah ki tashi ki ɗauko mun ke kika yi amfani da shi ƙarshe. Kin san ina da class, wallahi na yi latti daga ke har MK din zan haɗa."

"Tashi Babe ki ba Hamida abunda ta ke so kafin ta cinye mun ke." Khalid ya ce yana dariya. "Ina da aikin da zan ƙarasa. Za mu yi magana anjima. Love you."

"Love you too." Maryam ta ce tana murmushi.

Hamida ta juya idanu. "ʼYan love youn bura uba. Dallah malama ban cal ina da Physics class. Wannan shegen course din Allah dai Ya bani ikon gyara shi kar ya sani spill."

"In sha Allah ba za ki yi spilling ba Hamida." Maryam ta ce daga gaban locker inda ta ke neman scientific calculator.

A inda ta cewa Hamida ta duba tun farko a nan ta gan shi amma tana magana Hamida zata hayayyaƙo mata yanda ta ke a wuyan nan dama ƙaɗan ta ke jira.

"Ki kwantar da hankalinki, ki yi ta addu'a. Nima ina tayaki da ita. Yanda mu ka shigo makarantar nan tare haka zamu barta tare da yardar Allah."

Hamida ta yi ajiyar zuciya. "Allah Ya sa Maryam. Ba ki ji yanda gabana ke faɗuwa ba. Da na faɗi fa spill ne kuma second semester. Kuma course ɗin da wahala wallahi ban iya ba. Shi yasa ma da ya dawo ban yi mamaki ba."

"Be optimistic mana Meeda. Ki yi kyakyawan zato."

"Ina yi amma..."

"Amma nothing. Ki yi karatu sannan ki dage da addu'a dan ba sanin mu ko wayon mu ke sawa mu wuce ba, Allah ne ke bamu sa'a."

Hamida ta rausaya kai. "Hakane. Allah Ya bamu sa'a. Carryover a final year yafi tashin hankali. Kin samu supervisor ɗin ta ki?"

"Bata ɗauka wayar ba. Tun jiya na ke kiranta. Ofis ɗinta a rufe. Inaga gidanta ta ke so in bita."

Supervisor ɗin ta yarda da topic dinma ta san halin da ta ke ciki ya gagara. Hamida har ta fara labwork ɗinta, Sumy ma wani satin zata fara ita tana nan ko topic bata da shi.

"Da alama. Bari in tafi kar in yi latti. Ban ma san ina ne venue ɗin class din ba. Shima class rep ɗin ʼyan 200 level ɗin dan iska ka yi ta kiranshi ba ze dauka ba."

"Yanzu in kin je sai ki amsa lambar wani dan ajin."

"Dole." Hamida ta ɗauki jakarta. "Sai na dawo."

"Toh sai kin dawo."

Bayan fitar Hamida ta hau gyaran ɗaki. Da su ka fita aji da safe a hargitse su ka bar shi. Ƙaran wayarta ya ɗauke mata hankali daga sharar da ta ke yi. Da saurinta ta ɗauko wayar tunanin Khalid ne sai ta ga ba shi bane.

"Me ye?" Ta ce bayan ta amsa wayar.

"Yaya Maryam ID card ɗina cikin jaka dan Allah za ki miƙo mun, sun hana ni shiga."

"Ke ma ya a ka yi ba ki fita da shi ba. Kin san halin security ɗinnan sarai ba su da mutunci."

"Ina sha yana cikin wallet ɗina da na chanza jaka."

Hijab ta zura saman kayan barcinta, ta fita bayan ta ɗauko ID card ɗin. Wata sista ta miƙawa ta ce mata zata ga wata sanyen da baƙar after dress ta bata. Bayan minti uku sai gata ta shigo.

"Na gode Yaya. Kin yi abinci?"

Maryam ta galla mata harara. "Eh lallai Safiya. Tunda kin ajiye kuku ba dole ta yi mi ki abinci ba."

Safiyya ta karya wuya. "Kai Yaya wallahi yunwa na ke ji."

"Ai sai ki nema abunda za ki saka a ciki dan ko ruwan zafi ba zan dafa miki ba."

Safiyya na mata magiya har su ka shiga ɗaki. Tana shiga ta zare gyalen da ta yafa ja samar baƙar after dress ɗinta. Safiyya ba dai gayu ba. Idan ka ganta sai ka rantse final year ta ke nan ko ba su san aji ɗaya ta ke ba. Gata ta tsawo ta fi Maryam nesa ba kusa har girman jikin ma. Wanda bai san su ba tsab ze ce Safiyya ce babba saboda yanda Maryam ke komawa ʼyar ƙarama kusa da ita.

"Kar ki sa ke ki yarda mun kaya ko ina ban daɗe da gama gyara ɗakin ba."

Tunda su ka fara ABU ɗaki ɗaya a ke saman mu su ita da Hamida na mutane biyu a Ribaɗu. Yanzu ma da Safiyya ta zo irin shi a ka ba su tunda mutane uku za su iya zama ba su takura ba.

Safiyya ta samu matsala da JAMB ɗinta wanda ya sa ta yi shekara biyu a gida bata samu admission ba sai wannan karon.

"Ina Ya Hamida?"

Maryam ta bata amsa sannan ta haye gado tana janyo laptop ɗinta. Ita da ta siya laptop musamman saboda project har yau ko kalama ɗaya bata taɓa typing ba sai kallo. Fim ɗin ta fara kallo ta kunna, daga nan ya ɗauke mata hankali gaba ɗaya.

A kwana a tashi yau gata a final year za ta gama makaranta. Tana murna amma ƙasan ranta akwai fargaban sai me kuma. Daga makaranta sai me? Bautar ƙasa? Aiki? Aikin gwamnati ba garanti garesa ba dan haka ita bata wani saka rai ba. Tana da sana'arta mai zaman kanta 'Food by Maryam' wanda sai haɓaka yake yana bunƙasa. Tun lokacin nan da ta fara meatpie kamar wasa yanzu har abincin biki ta ke yi tana da ma'aikatan da ke taya ta. Dan ma makaranta bata barinta ta maida hankali. Amma dai yanzu ai an zo ƙarshe nan zata bada himma.

Wata zuciya ta ce mata, kin manta abu ɗaya da kowa ze fara tambayar ki ko yi miki magana a kai.

Aure.

Ita bata san haɗin gama karatu da aure ba. Tunda ta shiga final year dinnan Mama kullum sai ta yi mata maganar fiddo miji. Kaman ba su ke mata huɗubar babu ruwanta da maza ba da ta taho aji ɗaya.

"Saurayin ki sai ya fito a sa rana. Idan be shirya ba ya matsa ya ba wanda su ka shirya wuri."

Shekara ɗaya kenan da ta fara soyayya da Khalid. 'Officialy' in ji Hamida dan ta ce tun tuni abunda su ke yi kenan kawai ba su cewa 'I love you' ne.

Bayan gama makarantarsa ya yi bautan ƙasa a Kaduna. Kusan duk weekend sai ya zo Zaria. A nan ma har ya koyar da su abunda ba su gane ba. Bayan ya gama NYSC ma'aikatar ta riƙe shi ta bashi aiki. Da first class mai rai da lafiya ya gama, ga MK da hazaƙa a duk inda ya ke. Ya kwana biyu a Kaduna kafin su yi mai transfer zuwa Jigawa inda ya ke a yanzu.

Tunda ya yi mata maganar bashi dama a aji ɗaya bai sake tado zancen ba sai shekara ɗaya da ta wuce. A lokacin tana IT ɗinta a NAFDAC. Har Kaduna ya zo shi da amininsa Nas. Ya ce maganar nada muhimmanci bai kamata su yi ta a waya ba. Maryam bata taɓa zaton abunda zai kawo shi ba kenan. Dan da taga bai sake dago zancen ba ta sha ya chanza ra'ayi.

A wannan karon kam Maryam ta bashi amsar da ya ke so. Ko bayan ta amsa mai ba wani abu ya chanza sosai a tsakanin su ba. Dan tun barin shi makaranta sun saba sosai kusan kullum sai sun yi waya. Duk abunda ya ke ciki wajan aiki ta sani haka shima ya san abunda ke faruwa da ita a makaranta. Kamar dai yanda Hamida ta ce ne, ƙarin 'Love you' ne kawai a ka samu. Dan ko Zuby bata yarda sai lokacin su ka fara soyayya ba.

A gida kowa ya san Khalid dan haka Umma ba ta yi mamaki ba da ta faɗa mata.

Khalid na da dabi'un da ko wace mace ta ke so. Hankali da sanin ya kamata babu kamar shi. He is so attentive wani abu ma ta manta ta faɗa mai amma shi bai manta ba.

Hankalinta ya kwanta da shi haka zalika zuciyarta cike ta ke da son shi.

Ta gama kallon fim ɗin cikinta ya fara kiran ciroma. Safiyya indomie ta girka ta ce bata da ƙarfin yin wank girkin kuma yunwa na cinta ba zata iya jira ba ma. Itama indomie ɗin ta dafa, cikin locker ta ɗauko kwai guda uku ta ɗaura.

"Yaya kin yi waya da Umma yau?" Safiya ta tambaye ta.

Maryam na cikin ɓare kwai ta girgiza kai. "Wani abu ya faru ne?"

"A'a. Kawai dai ina ta kiranta bata ɗauka ba."

"Wata ƙila tana duty ko."

Safiyya ta gyada kai. "Hakane kuma."

Sallama a ka yi wata budurwa ta shigo tana neman Sophie. Safiyya ta shirya su ka fita tare. Ta zo fita Maryam ta ce, "su Sophie manya. Toh dai Safiyya sunan ki. Safiya, ehe."

"Kai Ya Maryam. Ni ki kyaleni. Abba kawai ya sa mun sunan tsaffi."

Maryam ta yi dariya, Safiyya ta yi gama. Inda su ka sha banban da ƙanwarta kenan. Har yau ƙawarta ɗaya tilo Zuby, sai wanda a ke gaisawar mutunci. Amma Safiyya da ta zo jiya-jiya adadin ƙawaye da mutanen da ta sani sun fi a irga.

Bayan ta gama cin indomie ɗin ta wanke kwanukan da ga ɓata ta kife su a kwando.

Daga nan kuma ta rasa me zata yi. Wannan semester ɗin bata da wani lectures sosai. Courses huɗu ta ke yi kawai. Kuma babu wani karatu a gabanta dan duk ta gama fahimtar abunda a ka koyar da ita.

Biochem mugun course ne ba dai wahala ba. Da ƙyar da suɗun goshi Allah Ya kawo su ƙarshe. Mutane da yawa da suka fara da su sun yi change of course. A da sun kai wurin su ɗari da ɗori amma yanzu ba su wuce ashirin da biyar ba. A haka ma wasu ba shekarar nan za su gama ba sai sun dawo spill.

Ita dai Allah Ya taimake ta tunda ta shigo makaranta course bai taɓa dawo mata ba. GP ɗinta kam kullum sama ya ke yi. Last semester ne ma ya tsaya chak, be yi sama ba, be yi ƙasa ba.

A yanzu haka tana cikin top 3 a department ɗin. Sai an gama gaba ɗaya za ta ga idan ta yi maintaining.

Wayarta ta yi ƙara ta ga Khalid ne. Tana amsawa ta ji muryarsa wani iri.

"Babe? Lafiya na ji ka haka?"

"Lafiya lau. Kawai gajiya ce."

Maryam ta ji kawai amma bata yarda ba. Abu ɗaya ne kawai ya ke ɓata mata rai cikin halayen Khalid.

Zurfin ciki.

Da wuya ya buɗe baki ya faɗa mata abunda ke damun shi. Zai faɗa mata komai amma muddin abu ya danganci wata matsala ba zai taɓa sanar da ita ba. Sai idan ta matsa sosai ko ta nuna bacin ranta. Ita bata ce sai ya faɗa mata komai dalla-dalla ba amma ya ce akwai matsalar ko addu'a ne ta taya shi.

Amma a'a, zai nuna komai lafiya lau ko da a gabar yana fuskantar abu me tsanani.

Akwai lokacin da ya samu matsala da ogar shi a wajen aiki, wanda ya so jan barin shi aikin ma gaba ɗaya, ba da dan gaskiya ta yi halinta da wuri ba a ka gano matar ce da laifi. Be faɗa mata ba sai da a ka warware komai.

Sai lokacin da mahaifiyarsa ta yi rashin lafiya. Shima suna waya ne ta ji shi kaman a asibiti, sai a sannan ya sanar da ita ai satin ta uku a kwance.

Ta san halin shi ko ta matsa ba faɗa ze yi ba har sai ya yi niya, dan haka ta kawar da maganan gefe. Koma menene tana roƙon Allah Ya yaye mai.

Sun daɗe suna waya a inda ta yi nasarar ƙawar da dukkan damuwar da ke tare da Khalid.

Tana cikin wayar Hamida da Sumayya su ka dawo. Hamida ta kalleta ta kalla wayar da ke maƙale jikin kunnenta.

"Oh ni Hamida. Ba dan da idona na ke gani da bazan taɓa yarda ba idan wani ya ce mun Maryam zata zama cingam ɗin waya saboda saurayi. Maryam ɗin da a da ta ke yi kaman bata san da halittun maza a duniya ba. Ko irin a ga saurayi dan hansam gaye dinnan a yaba halittar Ubangiji sai ku ga tana wani basarwa. Amma yau ita ce kusan kullum liƙe da waya tana hira da MK. Lallai MK, a gaishe ka."

Maryam ta girgiza kai. Ita dai ta shiga uku wurin Hamida. Khalid na jinta yana dariya. "Ai na cira tuta Hamida. Nima na sani."

Ta juya ido tana hararar Hamida. "Ni sai anjima."

Hamida ta yi wani shu'umin murmushi ta kalla Sumy. "Wai Sumy Kin tuna lokacin da Maryam ta sha Khalid nada budurwa harda kuka?"

Maryam bata kai ga katse wayar ba Khalid ya ji? "Mene? Kuka?"

Maryam ta zaro ido tana kallon Hamida da alamar ba ta kashe wayar ba. "Sai anjima." Ta ce da ƙarfi.

Sai dai kafin ta samu ta katse kiran Hamida ta yi saurin fizgewa daga hannunta. Ta kara wayar a kunne ta cigaba da cewa, "wai ba ka sani ba? Wallahi kuka wiwi da kyar muka samu ta yi shiru. Lokacin kana Kano ta yi tunanin wata abokiyar aikin ka soyayya ku ke yi." Me ya ce mata oho ta kyalkyale da dariya. "To shikenan. Sai ka ji ni."

Tana gamawa ta miƙa mata wayarta. Ta fizge tana hararta. "Kina da matsala wallahi Hamida. Me ye na faɗa mai dan Allah! Kaii!"

Hamida ko a jikinta sai ma dariya da ta ke yi Sumy na taya ta. Maryam ta girgiza kai. "Allah Ya shirye ku."

Sam Maryam bata son tuna wai harda kukanta saboda ta yi zaton Khalid nada budurwa. Kai! Allah Ya kyauta.

Saƙo ya shigo wayarta daga Khalid. 'Za ki yi mun bayanin kukan da kika yi Maryam'

Hamida ta cuceta. Bata so ya ji zancen nan ba wallahi.

Babu daɗewa Umma ta kirata tana neman Safiyya saboda ta ga kiranta da  yawa. Maryam ta ce mata ta fita bata dawo ba.

"Lectures ta tafi?"

"Kai anya? Wata ƙawarta dai ta zo su ka fita tare."

"Ke ce babba Maryam na ce ki riƙa gyara mata ko. Ni bana son tarin ƙawayen nan na Safiyya wallahi. Yarinya sai kwashe-kwashen tsiya. Kin haɗu da supervisor ɗin ta ki ko har yanzu."

"Har yanzu fa Umma. Har na gaji da zuwa ofis dinta."

"Ai gajiya bata gan ki ba Maryam. Ba ki fara komai ba. Allah dai ya ɗaura ki a kanta."

"Ameen Umma."

Daga nan Zee ta amsa wayar su ka sha hira.

"Ina Idi da Bash?"

"Idi tun ɗazu ya fita, Bash kuma yana wurin Baba Malam."

"Toh duk ki gaishe su."

Daga nan su ka yi sallama.


***

Ƙarfe biyar na yamma Khalid ya tashi daga wurin aiki. Inda ya ke haya da ma'aikatar da ya ke aiki babu nisa, tafiyar minti goma ce a ƙafa. Amma ya kwaso gajiya haka ya tsare dan achaba.

Yana shiga wanka ya fara yi dama ya taho da takeaway ɗin abinci. Ɗakin ƙarami ne kuma babu tarkace. Daga katifa sai tebur da ya ke aiki da kujerar roba. Ko wardrobe babu kayansa na cikin akwati.

Bayan ya gama bautar ƙasa saura ƙiris a yi yaƙin duniya na uku a gidansu inda Alhaji ya dage a kan sai dai ya ƙi karban aikin da aka ba shi ya koma kasuwa.

Khalid ya nuna sam be yarda ba. Be yi shekara biyar a ABU ba ya fito da sakamako mai kyau wanda har a ka bashi kyautar best graduating student a duka Faculty of Engineering dan kawai ya koma kasuwa ba.  Idan ya yi haka ai ya ci zarafin digiri ɗin shi. Duk rashin barci da wahalar da ya sha sun tashi a tutar babu kenan.

Mama a son ta farantawa mijinta ta ce mai ya yarda alabashi daga baya sai ya nemi wani aikin.  Duk hanyar da ze bi ya nuna mata hakan ba shawara ba ce taƙi ta saurare shi. Harda cewa ai Alhajin ya biya mai kuɗin makarantar dan ya ce ya ajiye aiki ba laifi bane.

A lokacin Khalid ya sake sarewa da lamarin mahaifiyarsa.

Abu kaman wasa sai da iyayen Alhaji(ƙannen mahaifan shi da ke raye) da wan Mama wanda a hannun shi ta girma su ka shiga zancen.

Mama ta yi fushi da shi sosai wai a kan mai ze gayyato wasu cikin lamuransu. Khalid ya bata haƙuri kuma be yi yunƙurin kare kansa ba. Rashin faɗawa magabata ya sa ta cikin mawuyacin halin da ta ke fuskanta.

Da tun lokacin da Alhaji ya fara ɗaga hannu a kanta ta bari an kwatar mata ʼyancinta ai da ba haka ba. Sai ta nuna tafi son mijinta har gaba ta fara da yayanta lokacin da ya so raba auren.

Shi kam ba ze yi abunda ta yi ba. Dole ya kwatarwa kan sa ʼyanci. Ba zai ƙare rayuwarsa a ƙarƙashin Alhaji ba dukda kuwa mahaifinshi ne. Ya fi so ya tsaya da ƙafafuwansa. Yana da ra'ayin kasuwancin ba wai be da shi ba amma sai ya fara gina kan sa tukun, sannan ba ya so ya kasance ƙarƙashin wani.

Da ƙyar dai magana ta wuce ya fara aiki a Kaduna kafin ya dawo Jigawa. Dawowarsa Jigawa Ya Ramlah ta ce tunda ya dawo kusa sai ta riƙa leƙawa kasuwan. Be ce mata eh ba kuma be ce mata a'a ba. Ya dai ji ta kawai. Tun tana magana a kai a kai har ta yi fushi ta watsar wanda shi a daɗinshi. Saboda har yanzu Ya Ramlah bata gama fahimtar waye Alhaji ba. Kuma baya tunanin zata taɓa fahimta.

Son ya koma kasuwa ba wai dan yana alfahari ko sha'awar aiki da shi bane. A'a, wata hanyar da zai durkusar da shi ne ya nemo. Amma duk ʼyan gidansu sun kasa fahimta. Gani su ke yi kawai Khalid taurin kai gare shi ko kuma ya raina Alhaji.

Ya ji kuma ya yarda. Tunda Allah na sane ba da niyar raini ko taurin kai ya yi ba ai shikenan.

Yana zuwa gida ba laifi yanzu tunda ya dawo kusa. Idan be je ba ma Ya Ramlah zata cinye shi ɗanye.

Har yau Alhaji bai ƙara ɗauko zancen kasuwar ba, ko na dena zuwa gidan ma be sa ke yi ba. Shirun shi na bawa Khalid tsoro. Ya san ba zai kyale ba, akwai wani abu da ya ke shiryawa.

Kafin ya kwanta ya kira abar ƙaunarsa Maryam. Sun sha hira sosai inda ya riƙa tsokanarta a kan kukan da Hamida ta ce ta yi. Ta ƙi faɗa mai me ya faru.

"Ki kwantar da hankalin ki Maryam. Zuciyata ke kaɗai ta ke so."

Maryam na ɗaya daga cikin rahamomin da Ubangiji ya mai. Idan yana tare da ita jin sa ya ke a sama. Yana mamakin son da ya ke mata.

Idan Allah Ya yarda Maryam matarsa ce, uwar ʼyaʼyansa. Da ita ya ke son gina rayuwar da ta sha banban da ta iyayensa.

"Babe yaushe zan turo a saka mana rana?" Jin ta yi shiru ya sake maimaitawa.

"Rana kuma?"

"Rana mana ko ba za ki aure ni ba?" Da wasa ya yi tambayar amma zuciyarsa duka ta ke yi.

"Me zai hana ni auren ka? Babu shi ai."

"Maryam dagaske na ke yi. Na san su Baba Malam sun sanni but I want to make things official."

"Nima ai ba wasa na ke yi ba."

Khalid ya miƙe zaune daga kwanciyar da ya yi. "Kin yarda gobe gobe in tura magabata na."

"Na yarda."

Ajiyar zuciya ya saki, farin ciki ya mamaye illahirin jikinsa. Ya daɗe yana tunanin ya zai tunkareta da maganar, har ƙasan ransa aure ya ke so. Bai damu ba ko a shekaran nan ne a saka musu rana ba. Ya tabbatar yana son Maryam, yana son kasancewa da ita. Babu amfanin jira.

"Maryam ina son ki. And I can't wait to marry you."






Mhmmmm🌚 su yar mitsila fa an girma jama'a. Harda su I love you.

Auren nan zai yiyu ko kuwa????🤔🤔🤔

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top