22.
Zuciyarta na duka kaman zata tsaka ƙirjinta ta fito. Bata taɓa shiga fargaba irin wannan ba. Ya zata yi idan sakamakonta be yi kyau ba? Da wani ido zata kalli Umma bayan duk kuɗin da ta kashe a kanta?
Maryam ta dafe ƙirji tana kiran sunan Allah ko zata samu ƙarfin gwiwar duba result ɗin su da aka manna a notice board yau da safe.
Suna cikin lecture hall wani ya zo yana cewa ga exam officer chan ya saka a yi mai clearing notice board. Tun lokacin gabanta ya yanke ya faɗi. Jikinta har karkarwa ya fara yi. Daga nan ta daina fahimtar karatun har malamin ya fita wani ya shigo. Tun ƙarfe takwas ta ke zaune wuri ɗaya har sai ƙarfe ɗaya ta tashi.
Tana fita ta wuce ɗaki dukda ba haka ta so ba amma gaban notice board ɗin cike ya ke da mutane. Tana isa ɗaki ta dau buta ta yo arwala. Ta roƙi Allah sosai a sujada. Bayan ta idar ta kira Umma.
"Maryam lafiya na ji muryar ki na rawa?"
"Umma," ta ce kwalla na taruwa a idonta. "Umma result ɗin mu ya fito."
"Toh yaya? Kin faɗi ne?"
"Ban sani ba, ban duba ba. Umma ina tsoro. Idan na samu carry over fa?"
Umma ta yi dariya. "Ke carry over ne damuwar ki ba ma GP din ba. A gaishe ki Yaya Maryam."
Tun tana ss3 ta ke jin yanda malamai su ke kiran carry over kaman wata annoba. Da ka yi abu sai a ce haka zaka je jami'a kana daƙikanci ka samo carry over. Tun lokacin ta ke tsoronta.
GP kuma bata ma san shi ba sai da MK ya yi musu bayani farko-farkon fara karantun su.
"Ina tsoran harda shi mana Umma. Amma dai na fi tsoron carry over."
"Kina da shirme Maryam. Carry over ba ƙarshen duniya bane. Ko kin faɗi za ki iya gyarawa. Kina ina yanzu?"
"Ina ɗaki. Ba a daɗe da sakawa ba mutane sun yi yawa."
Dandazon mutanen da ke wurin ba zata iya kutsawa ba kuma ita bata iya ture-ture ba.
"Dama ai dole wurin ya cika. Anjima ko bayan la'asar sai ki je ki duba. Kin ci abinci?"
"Umma intestines ɗina sun harɗe ba zan iya cin komai ba."
Umma ta sake yin dariya. "Allah Ya shirye ki Maryam. Ki kwantar da hankalin ki. Ba dai kin yi karatu da kyau ba kuma kin amsa tambayoyin daidai gwargwadon ki ba?"
"Eh Umma," Maryam ta amsa tana tuna yanda ita, Hamida da Sumayya su ka yi ta karatu lokacin exam din. "Wallahi mun yi karatu sosai."
"Toh ki kwantar da hankalin ki. Kin yi karatu kuma kin yi addu'a, ai shikenan. Idan sakamakon ya yi kyau Alhamdulillahi, idan ma be yi ba wanda ba ma fatan haka, shima Alhamdulillahi you can always do better next time. Ki yi ta hasbunallu. Ki kirani idan kin duba."
"Toh Umma. Na gode, sai anjima."
A hankali bugun zuciyarta ya ragu. Ta yi murmushi. Uwa mai daɗi. Ita da ƙannenta sun yi ɗace da mahaifiya mai son su da ƙaunar su. A shirye ta ke ta sadaukar da komai domin su. Bata taɓa bari sun ji cewa yau sun rasa mahaifi ba. Duk abunda ta ke yi su ta san ko Abba na nan iyakar abunda ze yi musu kenan. Sai dai su yi kewarsa saboda sabo amma ba dan sun rasa wani abu na abun duniya ba.
Shi yasa ta yi kanta alƙawari zata dage. A fannin karatun ta da kuma sana'arta. Ba zata ba Umma kunya ba, ba zata bari duk ƙoƙarinta ya tafi a banza ba.
Waya da Umma ba ƙaramin ƙarfafa mata gwiwa ya yi ba. Daidai gwargwado ta yi karatu kuma ta fahimta sannan ta amsa tambayoyi. Kuma duka test dinta ta yi ƙoƙari ba kaɗan ba, maki ƙalilan da ta samu shine ashirin da tara da ɗigo biyar, sauran daga talatin su ka fara. Subjects din da ba su saka sakamakon test ba su ma tana fata hakan ta ci. Ta kuma yi addu'a sosai, ta tashi da dare kamar yanda Umma ke kiranta a kai a kai tana tayar da ita. Wani lokaci tana ƙunkuni ta ke miƙewa daga kan gadon amma bata taɓa kin yi sallar da addu'a ba in har ta tashi. Sallar dare dabi'ar Abba da Umma ce.
Ƙarfe biyu da rabi Hamida da Sumayya su ka dawo.
"Maryam me ya same ki? Wani abu ya faru ne?" In ji Hamida tana buɗe robar ruwa.
"Me kika gani?"
"Na ga duk kin yi zuru-zuru ne ai kaman jira kike yi a ce ket ki ruga a guje."
"Result din mu ya fito."
Ruwan da Hamida ta sha be wuce bakinta ba ta dawo da shi. Da sauri ta ajiye robar. "Kin duba? Wayyo Allah!"
Maryam ta girgiza kai. "Wurin a cike ya ke. Umma ta ce in bari sai bayan la'asar."
"Toh. Za mu raka ki idan kina so. Wayyo Allah na, Allah Ya sa babu carry over."
Maryam ta yi dariya. Ba ƙaramin tsoratar da su a ka yi da carry over dinnan ba.
"Umma ta ce ko akwai za mu iya gyarawa."
"Allah Ya sa ma babu. Da mu ka yi Chem 101 fah na ga yan final year da yawa. Kenan tun suna hundred level su ka faɗi har lokacin ba su gyara ba. Ke da kawai Allah Ya raba mu da ita."
"Ameen."
"Ke kin ji daɗi Ummanki ta ce ko kin samu babu damuwa. Ni da Baba ya ce kar in sa ke in kawo mai ƙasa da 3.6 fa. Yayyuna su huɗu duka babu mai ƙasa da haka. Kin ga kuwa maganan carry over ma babu ita dan zan sani ne idan na samu."
"Ze yi miki faɗa sosai?" Maryam ta tambaya.
Sumy ta yi dariya. "Allah Ya sa a faɗa kawai ze tsaya."
Maryam ta amsa da Ameen tana jin wani iri a ranta. Yanzu tafi tsoranwa Sumy C.O a kan ta. Allah Ya sa bata da shi.
Jininta a akaifa ta kai la'asar. Suna idar da sallah su ka tafi. Ba zata iya zuwa ita kaɗai ba. Kar ta je ta faɗi.
Wurin babu mutane kaman ba ɗazu yake cike ba. A hankali ta taka zuwa gaban notice board ɗin zuciyarta na dukan uku-uku.
Da kyar ta iya nemo reg no ɗinta. A hankali idonta ya kai ƙarshe inda sakamakon ya ke.
Tana gani ta saki ajiyar zuciya sai a lokacin ta yi kwararren lumfashi. Nan da nan idonta ya cika da kwalla ta juya ta kalla su Hamida tana murmushi.
"Faɗa mun Yaya Maryam me kika samu." Nesa da notice board ɗin su ka tsaya.
Maryam na dariya ta ce, "3.46! Babu carry over!"
Hamida da Sumy su ka yi ihu su ka rungumeta.
"Kai Masha Allah! Muma Allah Ya sa namu ya yi kyau haka."
"Ameen."
"Kin duba na ƙawar ki?"
Sai a sannan ta tuna da Zuby. Bata dawo ba ma. "A'a. Babu ruwana. Idan ta dawo ta duba abunta. Bari in kira Umma."
Bakinta har kunne ta kira Umma sai dai bata ɗauka ba. Ganin haka su ka wuce ɗaki. Tana ta hamdalah a zuciya.
Chan sai ga kiran Umma. Waje gaban ɗaki kan kujerun kankare ta fita ta zauna sannan ta amsa.
"Kin kira ina meeting. Yaya? Kin duba?"
Maryam ta washe baki. "Umma 3.46!"
"Alhamdulillah! Wow! Maryam kin yi ƙoƙari sosai. Masha Allah. Saura ƙiris ki shiga two one. Kai Masha Allah. I am so proud of you."
Jumlar 'I am so proud of you' ya tuna mata da Abbanta. Duk lokacin da ta karɓo result ɗin makaranta abunda ya ke cewa kenan.
"Na gode Umma."
"Babu carry over kenan," Umma ta ce cike da zolaya.
Maryam ta yi dariya. "Babu."
"Sai a dage ko Yaya Maryam. A yi maintaing momentum ɗin kar a yi ƙasa."
"Sai dai sama in sha Allah."
"Haka na ke son ji. Allah Ya yi miki albarka."
Da murmushi a fuskarta ta amsa da "Ameen Ameen Umma."
"Su Hamida sun duba?"
"A'a. Na su be fito ba."
"Toh Ubangiji Allah Ya sa a ga alkhairi. Ki gaishe su. Ki kira su Baba Malam ki faɗa musu. Da Baba Zubairu."
"Toh Umma. Sai anjima. A gaida su Zee."
Bata bar wurin ba sai da ta kira su. Baba Malam da Mama sun yi ta saka mata albarka. Ba su wani daɗe ba ta kira Baba Zubairu. Shima ba ƙaramin murna ya yi ba daga jin muryarsa. Ya yi ta saka mata albarka.
"Brainbox ce ke kamar Abbanki."
Dariya ta yi tana jin daɗi har ranta. Da Abba na nan da ya ze ji? Tana fata shima ze yi murna.
"Abbanki was the best graduating student a set ɗin mu. Kowa na son ya zama abokinsa saboda yana koya karatu tsakanin shi da Allah babu ha'inci. Bai damu da wani ya wuce shi ba. Sun so retaining ɗin shi ya yi lecturing ya ce baya so."
Baba Zubairu ya bata labarin rayuwar jami'ar su tare da Abba kaman kar ya daina. Tana jin kusanci da mahaifinta idan ana bata labarin shi.
Suna gama waya da Baba Zubairu saƙo ya shigo wayarta. Tana dubawa ta ga ya turo mata dubu ashirin. Kallon wayar ta yi da kyau ko dai idonta ne baya gani.
Da sauri ta kira shi. "Baba..."
"Gashinan ki ƙara ko. Allah Ya bada sa'a."
"Na gode Baba. Allah Ya saka da alkhairi."
"Ameen Maryam."
Dan kar ta mance ta kira Umma ta faɗa mata. "A gaishe da Zubairu. Me za ki yi da kudi da yawa haka."
"Nima abunda na ce kenan Umma. Idan na zo sai in je banki in ciro in ba ki ki yi amfani da su."
"A'a na ki ne, riƙe abun ki. Ki adana su sai ki yi wani abun mai amfani da su."
Ita me zata yi da kuɗi har haka kuwa idan ba ta ƙara jari da su ba. Tun suna yara Umma bata koya musu kashe kuɗi ba shi yasa ko yanzu ma allowance ɗin da Umma ke bata ba ta iya kashe su gaba ɗaya. Toh me ma zata siya ita da ta ke da komai a locker.
Ranan ita ta yi girkin ɗare. Ta siyo musu gasasshiyar kaza da lemu su ka haɗa da abinci.
"Masha Allahu. Ni na muku alƙawarin tsire idan na mu ya fito." In ji Hamida.
"Toh Allah Ya kaimu."
"Kin faɗawa MK?" Sumayya ta tambaya.
"Shi ya kamata ki fara kira bayan Umma gaskiya dan ba ƙaramin ƙoƙari ya mana ba."
Maryam ta yi shiru tana kallon su. Ita yanzu tsakaninta da shi karatu ne kawai. Tun lokacin nan ko waya ba su sake yi ba. Yanzu ma idan ya zo Hamida ya ke kira ko Sumayya su fito, ko idan ba zai samu zuwa ba.
"Idan mun haɗu zan faɗa mai."
Hamida ta kalleta. "Ya je Kano fa. Ki kira shi mana."
"Ai ze dawo ko. Idan ya dawo zan faɗa mai. Ba zan kira ba."
Daga nan su ka maida hankalin su kan abincin da ke gaban su.
Bayan sati result ɗin Hamida da Sumayya ya fito. Hamida nada 3.0 daidai, Sumayya kuma 3.70. Ranan wuni su ka yi suna murna.
"Allah Ya sa result ɗin mu na ƙarshe ya fi haka kyau." Hamida ta ce tana matsar kwalla.
"Ameen!"
Fitowar result ɗin ba ƙaramin ƙarfin gwiwa ya bata ba. Kaman an buɗe mata kwakwalwa haka karatun ke shiga ya zauna.
"Ni ko MK lafiya bai dawo ba. Sati ɗaya ya ce ze yi fa." Hamida ta ce a hanyar su ta dawowa ɗaki da dare bayan sun gama karatu. "Ya Maryam ya kamata ki kirashi."
"In kira in ce me? Da ya tafi ya faɗa mun ne?"
Hamida ta kalla Sumayya su ka kwashe da dariya. "Yanzu dai haushi ki ke ji be faɗa miki ba."
Maryam ta taɓe baki. "Haushin me zan ji? Ya daɗe be faɗa ba. Amma yanda be faɗa mun ba, ba zan wani ɗauki waya in kira shi ba."
Abu kaman wasa har a ka yi sati biyu MK bai dawo ba, kuma bai kira su ba.
"Allah Maryam ina ji kaman wani abu ne ya same shi. Dan Allah ki kira ki ji."
Maryam ta gallawa Hamida harara. "In kin damu ke ki kira mana."
"Toh shikenan ni bari in kira. Bani wayar ki banda kati." Kafin Maryam ta amsa ta dauki wayar sai dai rashin sa'a ba a ɗauka ba. "Idan ya ga missed call ze kira."
Bayan awa ɗaya sai ga kiran ya shigo. Hamidar da ta kira bata nan. Ita bata yi niyan kiran shi ba duk da ta damu da rashin dawowar shi amma kafin ya tafi ai shareta ya riƙa yi. Ita kuma bata ta tura kanta idan ba a so.
"Salamu alaikum?" Muryar Khalid ta isa a kunnenta a raunane da kyar ya ke iya magana.
Ido Maryam ta zaro jin muryar ta sa. "Wa'alaikumus salam. Khalid ba ka da lafiya ne? Me ya same ka?"
Yar dariya ya yi da ta zama tari. Bayan ya saita kansa ya ce, "banda lafiya ne Maryam. Haɗari na yi kan mashin."
"Inna lillahi wa inna ilahi raji'un! Yaushe a ina? Ba ka dai ji ciwo sosai ba ko? Me na ke cewa? Gashinan da kyar ka ke magana."
Khalid ya sake yin dariya. "Da sauƙi sosai. Mura na ke yi shi yasa ki ka ji muryata haka. Na samu targaɗe a ƙafa shi yasa ban dawo ba."
Take Maryam ta ji ba daɗi, bata kyauta ba. Tana nan tana fushi ashe be ma da lafiya.
"Allah Ya baka lafiya Ya ƙara sauƙi. Bamu sani ba da mun kira tuntuni."
"Ahh haba babu komai. Ina ta so in kira ki amma na kasa. Ki yi haƙuri na san ban kyauta ba kafin in taho."
Ashe ya san abun ya yi kenan.
"Ki yi haƙuri na ce miki babu abunda ze chanza and I ended up doing just that. Idan na dawo I will make it up to you I promise."
Maryam ta yi dariya. Ta ji daɗin haƙurin da ya bada saboda ba ta ji daɗin yanda ya mata ba.
"Result ɗin mu ya fito."
"Dan Allah? Toh yaya?"
Ta faɗa mai harda na su Hamida. Ya nuna farin ciki sosai. "Kai Masha Allah! Kun yi ƙoƙari sosai! Bari in dawo this calls for a celebration."
Maryam ɗin da ke fushi da ba zata kira shi ba sai gashi sun fi awa ɗaya suna magana.
Da Hamida ta dawo ta ke faɗa mata abunda ya faru da Khalid.
"Kin gani! Sai da na ce miki. Yanzu ya jikin na shi?"
"Da sauƙi Alhamdulillah."
"Allah sarki MK. Bari kuwa in kira shi."
****
Khalid ya ajiye wayar a gefe da ɗan ƙaramin murmushi a fuskarsa. Ƙafarsa ya kalla ta ke duk wani annuri ya ɓace bat! Ɗaure ta ke da farin cast. Matsar da ita ya yi kaɗan amma raɗaɗin har tsakar kansa.
Duk abunda ya samu ɗan Adam muƙadari ne amma akwai sila. Sun ja mai gashi yanzu ya tsinta kansa zaune cikin gidan da ya ƙi jini.
Kiran Ya Ramlah ya ɗaga mai hankali ba shiri ya kama hanyar Kano. Sam be ji daɗin halin da ya iske Mama a ciki ba. Ta rame ta yi baƙi. Sai a lokacin Ya Ramlah ke faɗa mai dalilin shigarta wannan halin.
Mijinta ya tarkata ta gefe ya ajiye, amarensa ne kawai a gabansa.
Khalid yana mamakin irin zuciyar da mahaifiyarsa ke da ita. Tsakaninta da Allah son shi ta ke yi har ta damu da shareta da ya yi. Farin ciki ya kamata ta yi ai shi a ganinsa.
"Ya Ramlah ban san me ya sa kika kirani na zo ba. Da na zo me zan yi mata?"
"Ganin ka zai ɗauke mata hankali daga kan abunda ya ke damunta."
"Kin san dai ba zama zan yi ba ko? Kwana biyu zan iya yi gaskiya. Ina da sauran aikin project ɗin da ban gama ba."
Ya Ramlah ta girgiza kai cike da takaici. "For once ka bar maganan makaranta ka nuna damuwa kan mahaifiyar ka."
"Toh me kike so in yi?!" Ya tambaya rai a ɓace. "Me zan yi mata Ya Ramlah? Babu abunda zan iya yi! Me yasa kin ƙi ki gane hakan?"
Ya Ramlah bata bashi amsa ba ta girgiza kai ta fita.
A ranan da zai tafi Alhaji ya shigo sashe Mama yana faɗa. Be tsaya ya saurari faɗan me ya ke yi ba dan ya san ba wani abu bane. Ƙaramin abu sai ka ga yana faɗa kaman an yi mai sata a shago.
Ganin cikin faɗa ya yo kanta ga su a bakin ƙofa ya sa Khalid ya sha gabanta. Ƙofar falon Mama na da tudu ba ze iya cewa me ya faru bayan nan ba kawai ya ji azababben ciwo da be taɓa ji a rayuwarsa ba.
Sai gashi daga kwana biyu ya koma sati biyu. Yana da wani satin kafin ya fara tafiya da sanda (crutches) a yanda likitan ya ce.
Shigowa ɗakin da a ka yi ya dawo da shi daga tunanin da ya faɗa. Mama ce ɗauke da tray. Kan tebur ta ajiye sannan ta zauna a bakin gado.
"Sannu Khalid ya jikin?"
Muryarsa da mura ta dasher ya amsa, "Lafiya lau Mama. Ina wuni?"
"Lafiya lau. Ga abinci nan ka ɗaure ka ci. Na yi maka farfesu ko murar ta sake ka."
Ya yi murmushi. "Na gode."
"Anata karatu ko? Ka dai sanar da su abunda ya faru?"
"Eh na yi magana da supervisor ɗina, ya sanar da sauran malaman."
"Toh barka. Allah Ya taimaka."
"Ameen."
Mama ta miƙe kenan Alhaji ya shigo. Take yanayin ɗakin ya chanza. Mama ta yi murmushi. "Sannu da zuwa."
Alhaji ya kalleta da wani irin yanayi sai ka rantse duk duniya babu mai sonta sama da shi. A hankali ya amsata. "Yauwa. Ya mai jiki?"
"Da sauƙi Alhamdulillah. Murar ce dai har yanzu, amma itama ta fara sakin shi tunda yanzu har yana iya magana muryar ta dawo."
"Alhamdulillah. Alhamdulillah. Haka na ke son ji. Sannu ko Khalid."
Mama ta kalle shi ba dan ya so ba ya danne bacin ransa ya amsa. "Yauwa. Ina wuni? Ya aiki?"
"Lafiya lau. Kasuwa kuma Alhamdulillah. Yanzu na rabu da sabon abokin kasuwanci na Musa. Ban san ko Mamanka ta faɗa maka me ya faru ba."
Khalid ya cije ya ce, "ta faɗa mun. Allah Ya kiyaye gaba."
"Ameen. Ameen. Musa ba ƙaramin taimako ya mun ba. Bala ya cuce ni ban taɓa zaton haka daga gare shi ba."
"Haka mutane su ke Alhaji. Babu amana sai haƙuri."
"Tabbas kuwa. Da kowa zai zama kaman Musa ai da ba a riƙa samun matsala a kasuwa ba."
Khalid na sauraron su zuciyarsa na tafarfasa. Ya tashi ya fita babu dama ƙafa a ɗaure.
"Bari in shiga ciki. Khalid Allah Ya ƙara sauƙi."
Wannan karon bai amsa ba. Kaman ba shi ya ture shi ya faɗi ba. Amma babu wanda ya nuna hakan, gaba ɗaya an maida abun kaman tsautsayi bayan sarai sun san abunda ya faru.
"Bari in je Abbanku na san zai nema wani abun." Mama ta ce sannan ta fita.
Khalid ya girgiza kai. Toh. Ko ba komai ta dalilin targaɗen Mama ta samu abunda ta ke so.
•
•
•
•
Yawanci idan na fara rubutu I don't have the complete picture. A ʼyan kwanakin nan na yi ta tunanin ina littafin ya dosa.
I have found my answers🤭🌚 any guesses?
Ku yi haƙuri ban yi editing ba, ban da ƙarfin yi yanzu sai zuwa anjima🫠
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top