2.
















Ranar ta kasance assabar babu makaranta. Maryam da wuri ta tashi ta taya Umma wankin wake, Idris kuma ya kai niƙa.

"Safiya idan ba ki shiga kin yi wanka ba sai na gamu da ke. Yarinya sai ƙazanta." Inji Umma. Safiya na ƙunƙuni ta dauko bokiti ta nufa ɗaki. "Saura kuma kada ki yi wankann da kyau ki shiga ki watsa ruwa kawai ki fito.

Maryam ta gimtse dariyarta dan yanzu za su yi faɗa in Safiya ta ganta tana yi mata dariya. Tun ɗazu Umman ke bin kanta har ƙarfe uku ta yi.

Sallamar Abba ya sa ta ɗaga kanta daga inda ta ke zaune kan tabarma tana wasa da kayan kicin ɗinta. Ta yi mai sannu da zuwa, ya ce ta kawo mai ruwa.

Abba a gajiye ya ke, dawowar shi kenan daga tudun wada inda gidan mahaifiyar shi ya ke. Sam bai ji daɗin halin da ya samu mahaifiyarsa a ciki ba. Zama kan kujera ya yi zuciyarsa a cunkushe. Bai ji shigowar Maryam ba sai da ta taɓa shi.

"Abba ga ruwan."

Ya karɓa kofin ya kurɓi kaɗan ya maida mata. "Ina Umman ku?"

Maryam ta kalli ƙofar ɗakin Umma. "Inaga ta shiga bayi, in kirata ne?"

"A'a kyaleta. Mai ku ka dafa?"

"Shinkafa da miya sai salak da aka yanka."

Fuska Abba ya yamutsa. "Kawo mun salad ɗin kawai, idan akwai lemun tsami ki kawo mun."

Umma ta fito sanda Abba ke ba Maryam umarni. Gefen shi ta zauna kan kujera. "Lafiya ba za ka ci abinci ba? Ko baka jin dadi ne?" Ta tambaya  saboda yanayin shi ya nuna babu lafiya.

Arc. Ahmad ya karkata kai ya kalleta kan shi har yanzu jingine jikin kujera. "Yaushe rabon da ki ga Inna a asibiti?"

Umma ta ɗan yi jim tana tunani. "Gaskiya an kwana biyu."

Ido Arc. Ahmad ya runtse, fuskar shi ta nuna ba amsar da ya so ta bada ba kenan. "Sa'adah, akwai matsala. Musa baya kai Inna asibiti."

Gaban Umma ya faɗi. "Me yasa ka ce haka?"

"Gashi ba kya ganin su, ce mun ya yi fa duk sati likita ya ce su riƙa komawa check up. Da suna zuwa ko yane ai zaki gan su. Allah na tuba, kuma yanayin jikinta ya nuna, da tana samun kulawan da ya kamata da tafi haka lafiya. Sa'adah na yi sakaci."

Umma ta kamo hannunsa kenan Maryam ta shigo. Itama ta ji a jikinta kaman ta katse wata muhimmiyar magana. Da sauri ta ajiye kwanon salad ɗin ta koma. Umma ta sake kamo hannun mijinta.

"Ban taɓa zaton haka daga Musa ba," Abba ya ce yana girgiza kai. "Lokacin da na ce zan dawo da Inna nan shi ya ƙiƙiye ya ce in barta a chan saboda iyalin shi na kusa, za su kula da ita, har 'yar shi ta koma gidan duk dan in yarda. Na ce to ba zai yi komai shi kadai ba,  duk wani abu da ya shafi ci da sha, da asibiti duka ni zan kula da shi. Duk wata na ke tura mai kuɗi, idan bai isa ba zai sanar da ni in ƙara. Ashe dama ba dan neman albarka ya ke yi ba, da wata manufar a ran shi."

Magana Arc.Ahmad ya ke ran shi na ƙuna. Babu abunda ya fi ciwo ka gano mutumin da ka yarda da shi yana munafuntar ka, mutumin ma ɗan uwan ka da kuka fito ciki ɗaya wanda baka taɓa haɗa shi da kowa ba.

Su uku mahaifiyar su ta haifa. Shi ne babba, sai ƙanwarsa Badawiya da Allah Ya yi wa rasuwa da ɗaɗewa, ɗan ko aure bata yi ba, sai Musa. Inna ta haifi yara da dama kafin Ahmad sai dai duka basu yi tsawon rai ba. Allah Ya ƙaddara shi da sauran suna da tsawon rai har su ka kai haka. Akwai sauran ƴan uwa da suka haɗa uba amma tun bayan rasuwar mahaifin su shekaru goma da su ka wuce zumuncin su ya lalace. Dama zama ne a ke yi mara daɗi, wanda ya haɗa alakar na barin duniya kowa ya kama gabansa.

Babu abunda ya ke so a rayuwa sama da iyalinsa, mahaifiyarsa da ɗan uwan shi. Kullum tunanin shi ya zai kyautata musu. Amma a ce...kai! Ko a mafarki bai taɓa tsammanin Musa ze yi mai haka ba.

"Ka kwantar da hankalin ka ɗan Allah Baban Maryam," Umma ta furta a sanyaye tana murza mai hannu. Bata san wani hali zai shiga ba idan ya ji sauran abunda ɗan uwan shi ke yi ba.

"Inaga aikin Maidugurin ma ajiye shi zan yi, gwara in dawo gida kawai. Rashin zamana a garin shi ya janyo haka."

"A'a, Arc. Maganar ajiye aiki bata ta so ba. Kada ka yanke hukunci kana cikin fushi."

"Sa'adah nan da Bauchi ma ki kalla abunda ya ke yi. Ina ga idan na tafi Maiduguri. Kullum na ganta ina sha ciwo ne sai yau ramar da rashin lafiyar su ka fito ƙarara. Rabonta da abinci fa tun jiya Sa'adah. Jiya fa. Ina raye a ce Inna na yini bata ci abinci ba. Kenan bani da amfani."

Umma bata taba tsammanin abun Musa har ya kai haka ba. Amma ko da yake ba ta yi mamaki ba. Mutumin da za a haɗa baki a cuci ɗan uwan shi da ya ke tamkar uba a wurin shi komai zai iya yi. Amma bata yi zaton a rashin mutuncin na shi har mahaifiyar shi bata tsira ba.

"Yanzu wani hukunci ka yanke? Ka yi mai magana?"

Kai ya girgiza. "Baya gidan. Kawai zan dauko Inna in dawo da ita gabana. Kuɗin da ya ci ya je shi da Allah. Amma ba zan bar mahaifiyata a chan ba yana wahalar da ita ba."

Umma ta jinjina kai. Bata taɓa ganin mutum mai hakuri da kawaici irin Ahmad ba. Duk yanda zai yi dan kaucewa rigima zai yi dan an zauna lafiya. Mutum ne da bai hada son makusantansa da na kowa ba.

"Yaushe zaka taho da ita? Ka ga sai a gyara mata ɗakin su Maryam, alabashi su sai su dawo ɗaki na. Ko ya ka gani?"

"Hakan ma ya yi. Allah Ya yi miki albarka Sa'adah. Haƙiƙanin gaskiya ni mai sa'a ne. Allah Ya bani ikon faranta mi ki kaman yanda ki ke faranta mun."

"Duk mai ya kawo wannan Baban Maryam. Dan Allah ka bari."

Girgiza kai ya yi. Musa ya raunana mai zuciya. Bai ma san ta inda zai fara tunkarar shi ba. Ya ce mai me? Tunda ya iya wa mahaifiyar shi ƙeta kowa ma zai wa. Shi da ya zata Musa ko bayan ran shi zai kula da iyalin shi sai gashi ko Inna ya kasa rikewa ina ga a je kan wasu daban. Da ya buɗe baki ya ce mai yana da buƙatan kuɗi, zai bashi da ba sai ya cuce shi ba, ya cutar mai da mahaifiya ba.

"Sa'adah..."

"Ya isa," ta yi saurin katse shi. "Sauko ka ci abinci." Fita ta yi sai gata ta dawo da tray. Abba bai yi musu ba ya sauko sai dai abincin jin shi ya ke yi kaman magani.

"Ahmad..." Umma ta kira kan ta a ƙasa. Bata cika kiran shi da sunan shi ba shi ya sa Arc ya tattaro duka hankali da nutuswar shi yana jiran abunda za ta ce. Lumfashi ta fitar har yanzu kan ta a ƙasa. "Ni ce mai sa'ar cikin mu. Ni da yaranka muna alfahari da kai, we are proud of you. Kuma muna ƙaunar ka sosai."

Arc. Ahmad ya saki ajiyar zuciya. Umma ta matsa gefen shi ta kwanta kan kafaɗar shi, shi kuma ya sa hannu ya rungumo ta jikin shi da kyau.

Umma addu'a ta ke yi Allah Ya kawo mata mafita yanda zata sanar da shi tsakanin ta da Musa. Amma ta ji daɗi da Arc ya fara fahimtar Musa wana irin mutum ne. Dan ta tabbata da ita ta same shi da zancen nan ba shi ya gani da idon shi ba zai taɓa yarda ba. Arc mutum ne da idan ya yarda da kai ya yarda kenan har sai in kai ne ka yi abun da zai sa ya fara tunanin akasin haka.

Washegari aka fara shirin dawowar Inna. Gadon da ke ɗakin Abba aka dawo da shi ɗakin su Maryam. Gadajen ɗakin su Maryam kuma su ka koma dakin Umma. Dayake gadon ɗakin Umma babba ne shi ya koma ɗakin Abba. Kafinta aka kira ya yi 'yan gyare gyare. Umma ta so a sake pentin ɗakin su Maryam ɗan duk sun zane shi Abba ya ce ba yanzu ba.

Da yaran Abba ya tafi dauko Inna. Suna ta wasa abun su a mota ana kalle-kalle ta window. Zee da Idi wai suna irga motocin da ke garin. Bashir ne kawai cingam ya likewa Umma ya ƙi biyo su. Motar na tsayawa Safiya, Zee da Idi su ka ruga da gudu babu wanda ya tsaya rufe ƙofar motar.

"Maryam, fito mu je mana."

Mayafinta ta gyara ta fito ta ƙofar da ƙannenta su ka fita. Doguwar riga ce a jikinta ta kanti sai ɓakin gyalen doguwar rigar Umma da ta dauko ta yafa.

Gidan Inna ba ya da banbanci da na su ta fanni gyara. Ko kwan fitila aka chanza a gidan su sai an zo an diba idan nan ma na da buƙata. Sai dai a maimakon gidan su da ya ke kullum tsaf-tsaf nan ɗin ya yi datti kai ka ce babu kowa a ciki. Wani wari da ya yi musu sallama dole Maryam ta toshe hancinta.

Inna na tsakar gida zaune yaran na gaisheta. Abba ya yi sallama. Tana jin sallamar shi ta hau murmushi. Abba kama ya ke sak da mahaifiyarsa, babu inda ya barota sai duhun fatar mahaifinshi kawai da ya ɗauko.

Maryam kamarta ɗaya da Abbanta. Fatarta ce kawai ta ɗan fi ta shi haske, amma daga kan madaidaitan idanuwan shi da dogon hancin shi zuwa kumatun shi da ke lotsawa in ya yi dariya duka ta ɗauko. Ƙaramin jikin dai wurin Umma ta dauko shi.

Bayan sun yi sallama Abba ya zauna kusa da Inna su ka gaisa, tana ta fara'a. Bata san da zancen komawarta gidan shi ba dan haka ya ce su Maryam su tafi gidan Baba Musa su gaisa da ƴan uwan su.

Maryam kaman ta ce mai ita dai bazata je ba amma ta kasa. Haka rai bai so ba ta ja su Zee su ka tafi gidan kawun na su da ya kasance jikin gidan Inna.

Inna da kanta ta kawo wa Abba ruwa. Ya tambaye ta ina Naja'atu 'yar gidan Musa.

"Wannan in ta fita ai sai dare na ke ganinta."

Abba ya gyada kai. "Batun asibiti fa, yaushe rabon da ku je?"

Inna ta yi murmushi. "Ai kwana biyu jikin bai motsa ba shi yasa na ce ba sai an je asibitin ba. A je ayi ta tsire ka da allura."

Arc. Ahmad ya san Inna kawai kokarin kare ɗanta ta ke yi. Miƙewa ya yi ya shiga uwar ɗakanta, shi da kan shi ya haɗa mata kayanta. Inna dai bata ce komai ba kallon shi kawai ta ke yi har ya gama kai kayan mota.

Dawowa ya zauna a gabanta. "Inna ina so ki dawo gida na."

Daga sama Musa ya faɗo gidan ko sallama babu. "Ban gane kana so ta koma gidan ka ba? Yaya wannan wace irin magana ce, nan ɗin wani abu a ke mata ne? Kuma gidan ka wai zai kula da ita kai da matarka ba zama ta ke yi ba tana asibiti kullum."

Arc. Ahmad ko daga kai ya kalli Musa be yi ba. Ran shi ƙuna ya ke yi kuma ya san muddun ya buɗe baki za a samu matsala wanda sam baya son hakan ya faru a gaban Inna.

"Inna..."

"Yaya babu fa inda zata je. Daga sama ba za ka zo ka dauke ta ba. Chan gidan ka wa ta sani wa ya santa, so ka ke yi ta je ta yi ta zaman kaɗaici."

Ba tare da ya kalli Musa ba ya ce, "ba shawarar ka na ke nema ba." Mayafin Inna ya dauko ya yafa mata sannan ya taya ta miƙewa.

Inna har yanzu ta gagara cewa komai har Abba ya kaita mota inda ya iske Maryam tsaye a jikin motar. Buɗewa ya yi Inna ta shiga ya ce Maryam ta je  ta kira sauran za su tafi.

Gidan ya koma ya manta jaka ɗaya Musa ya biyo shi. "Ahmad! Wai mai kake taƙama da shi ne? Ƴar dukiyar da ka tara ita ce ta rufe maka ido. Ka tuna fa Inna mahaifiya ta ce nima, ba kai kaɗai ta kawo duniya ba."

Rai a bace Arc. Ahmad ya juya ya kalle shi. "Ashe ka san mahaifiyar ka ce. Na zata ka manta ai tunda har ka iya cutar da ita kasa rayuwarta cikin haɗari."

Musa ya firgita da furucin Arc, har saida ya yi baya. "Wani munafikin ne ya zo ya yi maka ƙarya? Hala Sa'ad—"

"Musa!" Ahmad ya daka mai tsawar da ta razana shi. "Kar ka sake ko da wasa sunan matata ya fito daga bakin ka." Har ya matso gab da Musa muryar Maryam ta dakatar da shi.

"Abba?"

Musa na ganin haka ya juya ya fita da sauri zuciyar shi na harbawa.

Abba ya sauke ajiyar zuciya yana koƙarin danne bacin ran shi. "Maryam je ki mota gani nan zuwa."

Maryam ta juya ta kalli kofar da Baba Musa ya fita. Takawa ta yi zuwa inda Abba ke tsaye zuciyarta na duka a ƙirjinta kaman zata fito. Tuna zuwan Baba Musa gidan su sau biyu ta yi da kukan da ta samu Umma ta na yi. A nan kawai ta yanke shawarar faɗawa Abba.

"Abba," ta kira tare da riƙo rigar shi. "Abba..."

Abba ya juya ya kalle ta. Tsugunniya ya yi gabanta. "Lafiya Maryam? Mene ne?"

"Abba ranan nan da baka nan Baba Musa ya zo..." duka yanda a ka yi Maryam ta kwashe ta faɗa mai. "Amma kar ka cewa Umma ni na faɗa maka, za ta yi mun faɗa."

Kai kawai Abba ya iya gyadawa. Haka ya yi tuƙi ransa cike fal da tunani daban daban. Ko menene zai gano bakin zaren, sannan Musa zai yi nadamar taɓa mai iyali da ya yi. Da akan shi abun ya tsaya zai kyale shi amma tunda ya iya taka ƙafa ya shiga gidan shi har ya saka Sa'adah kuka tabbas sai ya ɗauki mataki a kan shi.











~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top