18.





Karfe tara da rabi Khalid ya isa garin Kano. Rabon shi da garin an kwana biyu, yaga chanje chanje da yawa.

Daga tasha ya dauki abun hawa zuwa gidan Ya Ramlah da ke Hotoro. Yasan faɗa za ta yi mai akan rashin wucewa Rijiyan Zaki. Amma dole ta yi haƙuri, dan saura ƙiris ya shiga motar da zata koma Zaria.

Jakar baya kawai ya dauko dan ba zama ya zo ba. Idan da hali gobe ya ke so ya koma. Amma ya san Ya Ramlah zata cinye shi danye dan haka kwana biyu ze yi.

A ƙofar gidanta me mashin din ya ajiye shi. Bayan ya sallame shi ya shiga ciki. Babu mota a harabar gidan, wannan ya nuna mijinta baya nan.

Ya kai minti biyar yana ƙwanƙwasa ƙofar kafin ta buɗe. Da hijabi a jikanta daga gani daga barci ta taso. Fuskarta a ɗaure an katse mata barci amma tana ganin ƙaninta ta wartsake.

"Khalid!"

Da murna ta rungume shi. Ba ta yi tsammanin ganinsa ba dan bai faɗa mata yau ze taho ba, ya dai ce gashinan zuwa.

Khalid ya yi murmushi ya rungume ʼyar uwarsa. Tabbas ya yi kewarta. Sai yanzu ya ƙara jaddada hakan.

"Shine baka faɗa mun da wuri zaka taho ba. Ya Allah! Ban tanadar ma komai ba."

"Ya Ramlah." Ya yi dariya. "Ni ba sai kin tanadar mun da komai ba."

"Dole mana. Inaga rabon ka da gidana tun Ammar na jariri."

"Kai! Banda sharri. So nawa ina zuwa bayan nan."

Hannunsa ta janyo suka ƙarasa falo. Ta kalla jakarsa ta girigiza kai amma bata ce komai ba. Tunda ta samu ya zo garin ai shikenan.

Kicin ta shiga ta ɗaura mai a wuta. Tana da sauran dankalin da ta ferewa Baban Ammar. Shi ta soya, sannan ta soya kwai. Ta haɗo da kayan shayi ta ajiye mai kan dining table.

Yana cin abinci suna hira. Kukan Ammar ta jiyo, da sauri ta je ta dauko shi.

Girman yaro babu wuya. Da mamaki Khalid ke kallon yaron da ya bari a zani ya zama ɗan saurayi.

Ashe daɗewarsa har ta kai haka?

Hannu ya miƙa Ammar ya noƙe kafaɗa ya fara kuka.

"Be san ka ba." Ya Ramlah ta ce tana girgiza Ammar.

Khalid ya san da biyu ta faɗa haka. Abincin shi ya cigaba da ci, Ya Ramlah kuma ta haɗawa Ammar na shi abincin.

Bayan sun kammala ta koma ɗaki shi kuma ya dawo falo. Nas ya kira ya faɗa mai ya iso.

"Masha Allah. Ka gaida su Hajiya. Yaushe zaka dawo?"

"Za ta ji in sha Allah. Gobe da safe na ke sa ran dawowa."

"Sai nan da kwana huɗu ze dawo Nasir!" Ya Ramlah ta ce da ƙarfi daga uwar ɗaka. "Khalid ka daina zancen banza, ba gobe zaka tafi ba."

Nas ya yi dariya daga ɗayan gefen. "Toh Yaya babba ta yi magana. Sai mun ga kenan MK."

"Kai rabu da ita. Idan na daɗe in kai jibi."

"Za mu gani Khalid. Ka raina ni ko?"

Sallama ya yi wa Nas. "Ya Ramlah ni ban raina ki ba. Amma me zan zauna in yi har kwana huɗu. Ya kamata ina haɗa kan project ɗina ne fa."

"Ni kar ka dameni da maganan makaranta. Ba a kan ka aka fara ba. Ka gama makarantan ka koma kasuwa."

"Kasuwa? Ni na ce zan koma kasuwa?"

"Idan ba kasuwa ba toh ina zaka koma. Kasan dai yanda aikin gwamnati ke wahala. Duk cikin 'yan mazan gidan kafi su sanin kan kasuwa, kafi iya mu'amala da mutane."

Khalid be ce mata komai ba. Babban burnsa kan karatun da ya ke yi dan kar ya koma kasuwa wurin mahaifinsa. Shi be ga amfanin yin karatun ba in har zaka gama ka ajiye kwalin ƙarƙashin katifa. Ribar karatu ai a amfana da shi. Toh akan wani dalili zai gama wahala wurin kammala digiri ya ƙare a shago."

"Baka ce komai ba."

Idan ya faɗa abunda ke ransa faɗa za su yi da Ya Ramlah. Har yanzu babu wanda ya fahimce shi cikin yan uwansa. Gwara ma Ya Ramlah, ta kan fahimta wasu lokutan. Amma har yanzu ta kasa fahimta dalilinsa na ƙin komawa kasuwa.

"Yanzu dai bari in gama, in yi bautar ƙasa. Bayan nan sai in san me zan yi da rayuwata."

Allah Ya so shi Ammar ya fara kuka. A nan maganar ta tsaya.

Bayan Ya Ramlah ta yi wanka ta shirya suka nufa Rijiyan Zaki. Zuciyar Khalid ta harba lokacin da ya gansa tsaye ƙofar gidansu.

Allah Ya sa mai gidan bayanan.

Gidan shiru babu kowa. Ya Ramlah ce a gaba yana binta a baya gwiwa a sake, zuciyarsa na harbawa kama zata tsaga ƙirjinsa.

Wani bangare na zuciyarsa na farin cikin ganin mahaifiyarsa, ɗayan bangaren kuwa na fargaban haɗuwa da mahaifinsa.

Bangaren Mama su ka isa, ƙofar abokiyar zamanta a rufe da alama babu kowa.

"Ba su nan ne mutanen gidan?" Khalid ya tambaya.

Ya taso mahaifinsa na da mata huɗu, da girmansa da wayonsa biyu su ka yi yaji Alhaji ya bi su da takardunsu. Ya rage saura Mama da Anty. Bayan rabuwa da sauran matan ya auro mata sun fi a ƙirga amma duka babu wacce ta zauna. Wasu sun haihu wasu kuma ko wata biyar ba su yi ba su ka tattara kayan su.

A yanzu dai babu ko ɗaya amma ba abun mamaki bane ya sake dawowa ya samu an yi amarya.

"Ta yi tafiya."

"Ta yi tafiya ko ta gaji da zama da shi?"

"Khalid!"

Gaba ya yi yana taɓe baki. Daga faɗin gaskiya sai cibi ya zama ƙari. Palon Mama babu kowa sai telebijin da aka bari a kunne. Wuri ya samu kan kujera ya zauna sai ka ce baƙo. Ya Ramlah ta girgiza kai cike da takaici. Wani lokacin kaman ta kwaɗa mai mari. Ya fiye taurin kai. Kullum a son ya banbanta kansa da Abba bai san a wurinsa ya dauko zuciya, riƙo da taurin kai ba.

Saɓe da Ammar a kafaɗarta ta shiga uwar ɗakan Mama. Daga waje za'a zata mahaifiyarta ta haɗa komai. Miji mai kuɗi, ga danƙareren gida cike da motoci, ga sutura iya sutura. Amma sai ka matso kusa zaka gane sam ba haka bane.

Akwai dukiyar dan dukiya amma babu farin ciki da kwanciyan hankalin amfani da ita.

"Ramlah? Yaushe kika zo?"

Ya Ramlah ta yi murmushi. "Ina kwana Mama. Tun ɗazu mu ke sallama. Ina sauran mutanen gidan?"

"Yaran sun tafi makaranta. Antin ku kuma..."

Bata dawo ba. Ramlah ta sani ba sai Mama ta ƙarasa ba. Wa ya sani ko Anti zata dawo. Ba wannan ne karonta na farko na yin yaji ba. Duk matan da Abba ya ke aurowa ita kadai ya ke biko. Sauran duk wacce ta yi yaji sai dai ya bita da takarda.

Mama ta miƙa hannu ta karɓa Ammar ta na yi mai wasa. "Tare da Khalid mu ke."

Da sauri ta dago cike da mamaki. "Khalid? Yaushe ya zo? Shine bai faɗa mun ba."

Ya Ramlah ta dunƙule hannu ganin yanda fuskarta ta chanza. "Ya na falo. Bari in kira shi."

"A'a, bari in fita." Kafin Ya Ramlah ta yi magana Mama ta miƙa mata Ammar ta fita.

Khalid na zaune ya na kallo ƙaton hoton da ke liƙe a bango. A hoton dukan su ne. Iyayen su mata na zaune sun saka Alhaji a tsakiya yaran sun zagaye su. A haka kaman duka kenan.

Su takwas Mama ta haifa. Biyar sun rasu, wasu tun kafin a haife shi. Saura Ya Ramla da babban wan su da ke aikin soja. Shi baka fiye ganinsa ba ma. Sai sauran da suka haɗa uba ɗaya. Wa'annan bai san adadin su ba. Wasu sun girme shi wasu kuma ƙannensa ne.

Dayawan su wurin Mama suka taso saboda iyayensu ba su daɗe a gidan ba. Duk matar da Alhaji ya saki idan akwai yara tsakanin su bai bari su tafi da su.

"Khalid?"

Da sauri ya miƙe. Wani abu ya tsaya mai a makogwaro da ya hana shi magana sai kallonta da ya ke yi har ta iso gare shi. Ta ƙara tsufa, fuskarta dauke da kuncin nan da kullum take ƙoƙarin boyewa.

"Yanzu auta har ka yi girman da ba za ka zo gani na ba sai na roƙa?"

Khalid ya runtse ido, ya haɗiye yawu da kyar. "Ina kwana Mama."

"Lafiya lau." Hannu ta sa ta tallabo fuskarsa. "Ba ka cin abinci ko? Ji yanda ka yi ƙasusuwa. Bari in shiga in dafa maka abinci. Me ka ke so ka ci?"

Idonsa ya fara zafi saboda hawayen da ya ke ƙoƙarin haɗiyewa. Mahaifiyarsa ta fi kowa kyaun zuciya. Sai dai da yawa mutane na amfani da haka su cutar da ita, musamman mahaifinsa.

"Mama ba sai kin dafa mun komai ba. Ya Ramlah ta bani abinci."

Kai ta gyada sannan ta zauna kan kujeran da Khalid ya miƙe. Shima zama ya yi. Mama ta fara tambayansa ya makaranta. Haka dai su ka yi ta hira. Duk da ita ke jansa shi sai dai ya bata amsa.

"Abban ku yau zai dawo."

Kaman ta buga mai guduma a kai. Abunda ya sa ya taho yau saboda ya san Alhaji baya nan kaman yands Ya Ramlah ta faɗa mai. Sam baya so ya haɗu da shi. Haɗuwarsu ta ƙarshe ba su wanye lafiya ba, kuma ya tabbatar su ka ƙara haɗuwa za'a maimaita ne.

"Khalid me yasa?" Mama ta ce murya a raunane. "Har yanzu baka huce ba? Ba ya wuce ba, shekara nawa amma har yanzu ka ƙi ka haƙura. Kasan yanda abun ke mun ciwo kuwa."

"Ki yi haƙuri." Abunda kawai zai iya cewa kenan.

Mama ta girgiza kai. "Kullum abunda ka ke cewa kenan amma banga chanji ba. Ni da kake fushin dan ni na yafe to kai me yasa ba za ka iya haƙuri ba komai ya dawo kaman da." 

Khalid ya yi murmushi mai cike da ciwo. Tabbas ba kowa ke da zuciya irin ta mahaifiyarsa ba. Baya fata Allah Ya ba shi irin zuciyarta. Cutar da ita kawai ake yi. Amma ko sau ɗaya bata taɓa buɗe baki ta ce an yi mata ba daidai ba.

Ita zata iya haƙuri har ta yafe amma shi kam baya jin zai iya. Dan babu yanda ze yi da ya raba aurenta tsakaninta da mahaifinsa.

Sai dai duk duniya babu abunda zuciyar Mama ke so sama da mijinta. Duk abunda ze yi bata ganin laifinsa. Son da take yi mai ya rufe mata ido bata ganin cutar da ita da ya ke yi.

"Khalid." Mama ta taɓa mai kafaɗa. "Ka ji abunda na ce maka?"

"Na ji Mama."

"Toh baka ce komai ba."

"Ki yi haƙuri."

Fuskarta ta nuna ba haka ta so ba. "Tashi ka je ka kai kayanka ɗaki."

Yasan ya kaita ƙarshe. Idan ya ce ze yi gardama ranta zai ƙara ɓaci. Gwiwa a sake ya fita daga falon. Ƙofar falon Anty ya kalla. Yana ji a jikinsa kaman ba zata dawo ba wannan karon.

Ɓangaren samarin gidan ya nufa. Da yawan su sun tafi kasuwa sai ʼyan tsirara. Ya gaisa da su ya shige ɗaki. Wayarsa ya ɗauko ba tare da dogon tunani ba ya kira Maryam. Bugawa uku ta ɗauka. Bai san lokacin da murmushi ya kubce masa ba tun kafin ya ji muryarta.

"Salamu alaikum Yaya Maryam." Tun lokacin da ya ji Zee na kiranta da sunan ya ke tsokanta da shi.

Dariya ta yi har cikin ransa. "Wa'alaikumus Salam Yaya MK. An isa lafiya? Ya ka samu yan gidan."

"Lafiya lau Alhamdulillah."

Hira su ka yi da ta warware mai duk wani bacin rai. Kaman kar su yi sallama amma dole ya ce mata sai anjima.

Yana tsoron yanda Maryam ta mamaye duka zuciyarsa a lokaci kaɗan. Har yanzu bai sanar da ita sirrin zuciyarsa ba. Sai ya ke gani kaman ya yi wuri dayawa. Kar ta zargesa ta ce ba dan Allah Ya ke taimakon su ba. Ga shi sun kusa fara jarabawa, baya so ya dauke mata hankali daga kan karatunta.

Kafin zangon karatun ya ƙare dole zai sanar da ita.

Takardunsa ya fito ya duba wasu abubuwan tunda baya da abun da ze yi.

"Abba ya dawo!"

Daga sama ya ji ɗaya daga cikin yaran gidan ya faɗa da ƙarfi. Yana ji ʼyan ƙananan cikin su su ka ruga a guje suna mai oyoyo.

Zuciyarsa ta harba da ƙarfi. Sam bai shirya haɗuwa da mahaifinsa ba. Ya so ya cigaba da karatun amma babu natsuwa a tattare da shi. Dole ya rufe ya maida jaka.

Hayaniyar yaran ya cika gidan. Murmushi ya yi mai ciwo yana tuna yarintarsa inda shima ya ke murna idan Abba ya dawo. Yana aji uku a sakandire ne ya gane ainihin waye Alhaji.

"Khalid?" Muryar Ya Ramlah ta kira tana buga ƙofa. "Ka fito Abba na neman ka."

Ya aka yi ya san ya zo?

Kaman ta san abunda ke ransa ta ce, "Su Hashim su ka faɗa mai."

"Gani nan zuwa."

Bata jira shi ba ta yi gaba. Lumfashi ya furzar yana ambaton sunan Allah. Da ma ya yi zamansa a Zaria. Falon Abbba cike da yara ana ta mai sannu da zuwa. Yana ta musu dariya ya ciro tsaraba yana ba kowa na shi.

Alhaji na daga kai ya shigo. Da mamaki ya kalle shi. "Khalid."

"Na'am. Sannu da dawowa."

Ko zama be yi ba ya tsaya a bakin ƙofa. Mama ta kalle shi tana girgiza kai. Ya Ramlah ta galla mai harara.

"Yauwa. Samu wuri ka zauna mana. Ya makaranta?"

"Lafiya lau."

Alhaji ya kalla kayan da ke baje a ƙasa. "Gashi ban san kana nan ba, ban taho maka da komai ba."

"Babu damuwa. Nagode."

"Ka zauna mana Khalid, kai da ba baƙo ba."

Kai ya girgiza. "Akwai wanda ke jirana. Allah Ya huta gajiya."

Bai bari wani ya sake cewa komai ba ya fita ransa na ƙuna. Bai taɓa ganin mutum mai fuska biyu irin Alhaji ba.

"Khalid! Khalid!"

Ya Ramlah ce ta biyo shi. Da ƙarfi ta bankaɗa kofar ɗakin ta shiga.

"Ya Ramlah..."

"Me ye matsalan ka Khalid?" Ta ce cike da masifa. "Nasan mance abunda ya faru abu ne mai wuya amma Abba na iya baki ƙoƙarinsa wurin ganin ya gyara komai. Me ya sa ka ke haka? Ka ƙi ka ba shi dama."

"Ya isa haka!" Ran Khalid ya ɓaci. Ya gaji da kallon da ake yi mai kaman shi ne mara kirki. "Kina son sanin asalin dalilina na ƙin dawowa? Toh bari in faɗa miki yau. Mai gidan da kan shi ya ke cewa kar in zo mai gida."

Ya Ramlah ta buɗe ido. "Abba ba zai.."

"Ba zai ce ba ko?" Ya yi saurin taron lumfashinta. "Haka ki ke gani. Ni kaɗai na san asalin waye Alhaji. Duk abunda zan faɗa miki ba lallai ki yarda ba saboda master manipulator ne. Mama idonta ya rufe gaba ɗaya bata ganin abunda ya ke yi. Ya raba ta da kowa har ʼyan uwanta, ya killace ta ya sa ta dogara da shi saboda ya ji daɗin juyata. When was the last time Umma ta je Gaya? Har Baba Audu ya rasu bata je ba. Yana mata wasa da kwakwalwa yana neman haukata ta amma duk bata gani."

Ya Ramlah ta kasa cewa komai sai kallonsa da ta ke yi.

"Kin san bai dena ba ko?"

Ya Ramlah ta gyada kai. "Na sani. Na sani Khalid amma na rasa ya zan yi. Mama bata faɗa mun komai. Da na dauko maganar ta ke chanzawa."

Ba zai taɓa manta ranar da ya fara ganin Alhaji ya daga hannu ya daka Mama ba. Har abada wannan baƙar ranan ba zata taɓa gogewa daga kwakwalwarsa ba.

Babu abunda ya fi ciwo sama da ganin mahaifiyar ka a wannan yanayin kuma babu abunda za ka iya yi.

"Ya Ramlah a raba auren kafin ya kasheta."

Ya Ramlah ta runtse ido. "Ka manta ta ce idan mu ka sake mata maganar zata tsine mana?" Hawaye ne suka gangaro fuskarta.

Khalid bai taɓa tsintar kansa cikin tashin hankali irin na ranar ba. Suna son sun taimaki Mama sai dai ta saka musu takunkumin da babu daman cirewa.

Ya Ramlah ta zauna ƙasa kan kafet dafe da kai. "Khalid ban san ya zan yi ba. Sometimes ina tunanin idan na yi kaman na mance komai zai daidaitu da kansa. Sai dai kawai yaudaran kaina na ke yi."

Khalid ya zauna kusa da yayarsa. Ya tsana halin da ya ke ciki. Yana ji yana gani amma babu abunda zai iya yi ya yaye mata abunda ke damunta.

Sun zauna shiru sai saƙa da warwara su ke yi a zuciya. Ya Ramlah ta miƙe. "Bari in shiga ciki."

Khalid bai tashi a wurin ba. Kansa har ya fara ciwo. Dalilinsa na ƙin san dawowa gida kenan. Turo ƙofar ɗakin aka yi sai ganin mutum ya yi tsaye a kansa. Yana daga kai ya haɗa ido da mahaifinsa yana mai wani irin kallo.

"Me kake yi a nan? Ban ce bana son ganinka ba!"

"Mama na zo gani."

"Ka manta abunda na ce maka kenan? Kai ke saka ta tana saɓa mun, bata tsallake umarni na sai kana nan, dan haka na baka nan da awa biyu ka bar mun gida kafin in wayi gari in rasa kan iyalina."

A fusace Alhaji ya fita. Khalid ya yi ajiyar zuciya. Shi kuma jarabawarsa kenan a rayuwa. Da ana iya chanza uba da tuni ya chanza. Duk cikin mazan gidan Khalid ne kaɗai ya ke iya ja da maganan Alhaji. Sauran suna tsoro wasu kuma sam ba su damu ba. Shi yasa Alhaji baya son zamansa a gidan.

Ya Ramlah ce kaɗai ke yunƙurin yin wani abu. Ita kuma tafi gane ta share abun kaman hakan zai sa komai ya daidaita.

Saidai matsalan gidansu ba abun da zai daidaitu da kansa bane.

Ya fi minti talatin yana tunanin me ya kamata ya yi. Idan ya ƙure Alhaji yana iya sauke fushinsa kan Mama. Khalid bai son abun ya kai ga haka.

Jakarsa ya goya ya shiga ciki. Ya Ramlah na ganinsa da jaka ta miƙe. Daga ganin idanuwanta ta sha kuka ba kaɗan ba.

"Khalid..."

Bai amsata ba ya shiga ciki. Mama na kicin tana faman girka mai abunda zai ci. Wani abu ya sokesa a ƙirji.

"Yunwa ko? Bari na kusa gamawa."Mama ta waigo ta kalle shi. "Khalid ya na ganka da jaka?"

Runtse ido ya yi. "Yanzu supervisor na ya kira yana neman mu gobe. Idan ban je ba kuma za'a samu matsala."

Babu matsalar da za'a samu ko da kuwa dagaske supervisor dinsa ke nemansa dan malamin na da kirki sosai.

Fuskar Mama ta nuna bata ji daɗi ba. "Wannan makaranta dai Allah Ya sa ka gamata lafiya. Ka bari to in gama abincin ko a hanya sai ka ci."

Idanuwan Khalid yaji su ke yi saboda hawayen da ke ƙoƙarin taruwa. "To Mama."

Yana ji yana gani dole zai tafi dan ya kareta.




I know! I know😪🥲 and I am so sorry. Bari in ara kalaman MK, "final year jama'a😩" After all the ASUU strike and the ABU wahala Allah Ya kawo mu. So please bare with me zuwa in gama hada kan digiri dina😂

A saka ni a addu'a🥹 whenever you remember Ya Maryam da MK a yi wa Maymunatu addu'a dan Allah.

Da fatan za ku fahimce ni

Nagode.

Na daɗe ina tantaman babin nan. For some reason, I am nervous. Amma dai gashinan. How was it?

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top