16.
Maryam ta ciro ƙaramin littafi da ke dauke da list din abubuwan da take buƙata. Daga kan filawa har zuwa kan gisihiri komai ta rubuta. Sun siya kusan komai na list.
"Saura nama Hamida, ina zamu samu niƙakƙe."
Hamida ta fita sanin kan kasuwa shi yasa ta janyo ta suka zo tare.
"Mu je wurin Haladu mai nama, nan Mama ke siya."
Hamida na tafe Maryam na biye da ita. Suna tafiya suna hira. A wurim mai naman Maryam ta faɗa adadin da take ganin zai isa a zuciya tana addu'a Allah Ya sa kar ya yi kaɗan.
"Nawa naman per kilo?"
Yana faɗa ta rubuta a littafinta. Daidai da gishiri sai ta rubutu na nawa ta siya bare su butter da filawa.
Ƙarfe biyu su ka koma gida. Jiya talata Umma ta zo mata da albishirin aikin da ta samo mata. Da farko ta ji kaman ba zata iya ba saida Umma ta kwantar mata da hankali. Yau da safe Baba Malam ya bata kuɗin da zata yo cefenen abunda zata buƙata tunda ranan juma'a ne taron sunan kaman yanda matan ta ce.
Umma night duty ne da ita yau dan haka tana gida. Suna kasuwa aka yi azahar. Sallah su ka fara yi kafin Maryam ta dauko dan littafinta. Lissafi ta yi taga adadin da ta kashe. Cikin kuɗin da Baba Malam ya bata harda chanji. Kaman yanda aka koyar da ita a makarantar koyan girki, ta yi lissafin komai harda ribarta. A ƙa'ida harda kuɗin gas da kuma kayan aiki irin su rolling pin din da zata yi amfani ya kamata ta saka toh su wannan bata san yanda zata su shi cikin lissafi ba. Bata da kayan aiki nata na kanta bare ayi maganan gas.
Bayan ta gama lissafi tare da Hamida ta kaiwa Umma ta gani. Umma ta karɓa ta jinjina kai. "Yaya Maryam ribar bata yi kaɗan ba?"
Haka Hamida ma ta ce. "Sai a ƙara Umma."
"Da dai an ƙara dan ba ƙaramin daɗi meat pie ɗinki ke da shi ba. Kin san nawa na ci wurin aiki da basu kai na ki daɗi ba sai tsaɗan tsiya."
Maryam ta yi dariya. Bayan ta ƙara kuɗin ribar Umma ta kira matar ta faɗa mata, bata yi jayayya ba ta ce toh. Ranan juma'a da safe su ke so zata aiko a karɓa.
Dayake a speaker Umma ta sa wayar, ta juya ta kalla Maryam. "To kin ji. Yaushe za ki yi?"
"Tunda da safe ta ke so, sai a yi rana alhamis da dare ko?"
Umma ta gyada kai. "Hakan ya yi."
Ta koma ɗaki ta samu Hamida na sa hijab. "Ina za ki je?"
"Yanzu Mama ta kirani, akwai aikin da zan yi mata. Mu gani," ta miƙa hannu ta karɓa littafin. "Ko ke fa. Da kin wani sa kuɗi kaɗan. Ko ranar da muka sha a kasuwa ai ya cinye kuɗin nan bare a zo kan aikin rolling da folding. Yaushe su ke so?"
"Ranan juma'a da sassafe."
"Ranan Alhamis da dare za ki yi kenan?" Maryam ta gyada kai. "Tun yau zan fara roƙon Baba, Allah Ya sa ya barni sai in kwana in taya ki."
"Ameen," Maryam ta yi murmushi tare da rungume babbar ƙawarta.
Hijabi ta saka ta raka Hamida har bakin titi ta hau ʼyar ƙurƙula. Tana dawowa ta hau neman kayan aikin da ta san zata buƙata gobe. Dayawa an daɗe ba'ayi amfani da su ba. Wanke su ta yi sannan ta kife a kwando. Tana ɗauraye hannunta wayarta ta yi ƙara.
Ba ƙaramin mamaki ta yi ba ganin sunan Zubaida a fuskar wayar. Tun ranan da ta faɗa mata makin da ta samu a Chemistry test Zuby ta daina kulata sosai. Toh dayake ma kanta ya dauki zafi tana ta karatu bata lura ba. Sai da ta dawo gida ne ta yi ta kiranta bata ɗauka ba. Sai gashi yanzu tana kiranta.
"Hello Maryam."
"Na'am Zubaida, ya kike? Ya hutu?"
"Hutu Alhamdulillah. Ya KD? Kin tafi Kaduna har kin manta da ni."
Maryam ta yi dariya tana girgiza kai. Lallai ma. Kira nawa ta yi wa baiwar Allah nan bata ɗauka ba wai amma tana ce mata ta manta da ita.
"Ni na isa in manta da ke Zubaida. Ya Zaria?"
"Zaria lafiya lau. Yauwa Maryam kin tuna gayen nan da muka haɗu da shi ranan da kika raka ni comm market? Za ki iya tuna sunan shi, wallahi ya shige mun."
Maryam ta dan yi nazari. Tabbas rana wani ya yi mata magana amma idan ta ce ga sunan shi ko kaman nim shi ta yi ƙarya. "Ba zan iya tunawa ba Zuby."
"Wayyo! Na so a ce kin tun. Yau na shiga makaranta naga wani kaman shi toh na manta sunan shi ba daman in tsaida shi. Bai faɗa miki department ɗin da yake ba?"
"Zuby babu abunda zan iya tunawa, ranar a gajiye nake ban gane komai."
Zubaida ta ɗan yi tsaki. "Ban ji daɗi ba. Tun ranan ban manta da gayen nan ba, Allah bai sake haɗa mu ba sai yau, gashi ba'a samu wani cigaba ba. Da zan san department din da yake na san nemo shi ba zai mun wahala ba."
"Allah sarki," Maryam ta ce, bayan wannan bata san mai ya kamata ta ce ba. "Sai anjima Zubaida, Umma na kira na."
Nan su ka yi sallama Maryam ta ajiye wayar. Towel ɗin da ake goge kwanuka ta ɗauka ta goge kayan da ta wanke. Bata gama ba wayarta ta fara ƙara. Kaman ba zata ɗauka ba kuma sai ta fasa.
Ba tare da ta duba sunan dake rubuce ba ta amsa kiran ta sa wayar a kunneta da dama ta riƙe wayar da kafaɗarta. "Salamu alaikum."
"Wa'alaikumus Salam Maryam an wuni lafiya?"
Ba dauki muryan ba. Cire wayar ta yi daga kunne taga ashe Baba Zubairu ne. "Ina wuni Baba."
"Lafiya lau. Ya makaranta?"
"Alhamdulillahi mun yi hutun mid semester ma tun wun wancan satin."
"Semester har ta miƙa kenan, toh Allah Ya bada sa'a. Ya Ummanki da sauran 'yan uwanki?"
"Duka suna nan lafiya."
"Toh madallah. Duka ki gaishe su."
"Za su ji in sha Allah Baba."
Daga nan ya yi mata sallama. Wasu mutane akwai kirki. Shekaran Abbanta nawa da rasuwa amma har yau Baba Zubairu bai yarda su ba. Tabbas amini nagari ne, mai riƙe zumunci. Wanda suka fito ciki ɗaya da Abban ma bai yi musu abunda Baba Zubairu ya musu ba. Asali ma rabon su da Baba Musa tun dawowar su Kaduna. Shekera uku kenan.
Ta san yana turowa Umma saƙonni wani lokacin idan abun shi ya motsa. Ita da kanta ta yi blocking lambar a wayar ba tare da Umman ma ta sani ba. Ranan wayan na hannunta text ɗin ya shigo. Kasa kai ƙarshen text ɗin ta yi saboda munanan kalaman da ya yi amfani da su. Ba wannan ne karon farko da ya fara turo saƙonnin ba.
Lamarin Baba Musa na ɗaure mata kai yana bata tsoro. A ce ɗan uwanka da kuka fito ciki ɗaya shi ke wulaƙanta iyalinka bayan ran ka.
Kaman ita ce a ce ta kasa riƙe yaran Safiya ko Idi. Ba a nan abun ya tsaya ba ma, bayan ta kasa riƙe yaran ʼyan uwanta, dan gadon da aka bar musu take neman hambaɗewa.
Kai!
Allah kar Ya nuna mata ranan da zata iya kwatankwacin abunda Baba Musa ke yi. Allah kar Ya bar son abun duniya ya rufe mata ido ko na ʼyan uwanta har su so cinyewa marayu dukiyar su ko cutar da su.
Ta san da Baba Musa ne ya fara barin duniya Abbanta sai inda ƙarfin shi ya ƙare wurin kula da iyalan da ya bari.
Maryam ta girgiza kai ta cigaba da aikin da take yi. Bata cika son irin wannan tunane-tunanen ba sabo wani irin ciwo da zuciyarta ke mata.
Duk wani abu da ta san zata buƙata na yin meatpie ɗin gobe ta haɗa kan su wuri ɗaya. Naman ta saka shi cikin freezer, dankalin kuma ta cire daga cikin leda ta baza a ƙasa.
Ƙarfe uku ʼyan makaranta suka dawo. Da gudu Zee ta shigo ta ɓoye bayan Maryam tana haki. Kafin ta tambayeta menene Idris ya shigo rai a ɓace ya yo kan Zee.
"Wayyo Allah Yaya! Ki kare ni!" Zee ta yi ihu ta riƙe rigar Maryam ta baya.
Shi kuma Idi ya sa hannu yana ƙoƙarin janyota. Sun sata tsakiya suna kokowa.
Maryam ta ma kasa magana. Sai juyi ake yi da ita. Tsawa ta daka musu sai da duka suka tsaya chak. "Me ye haka? Lafiyar ku ƙalau kuwa?"
Idris na haki kaman wanda ya ke shirin haɗiye Zee ga wani kallo da yake mata. "Idris me ta yi maka?"
"Wallahu Yaya babu abunda—"
"Yi mun shiru ban tambaye ki ba. Idris?"
Idon shi ya ɗauke daga kan Zee ya maida su kan Maryam. Ya buɗe baki zai yi magana ya rufe ya girgiza kai. Da yatsa ya nuna Zee. "Wallahi sai na karya ki wata rana."
Ɗaki ya wuce ba tare da ya sake cewa komai ba. Maryam ta juya ta kalla Zee da ke ta zare idanu kaman ta yi wa Sarki ƙarya. "Wata rana sai ya miki dukan da baza ki iya motsawa ba. Ki cigaba da neman tsokanan shi."
"Ni fa ban mai komai ba," ta ce tana turo baki gaba.
"Ni dai na faɗa miki. Idris da zuciyar tsiya wata rana sai ya ji miki ciwo."
Nan ta barta tana ta faman nishi kaman wanda ta yi wani aikin ƙarfi. Ɗaki ta ciga idan ta samu Safiya na chanza kaya.
"Yauwa Yaya, an ƙara bamu Chemistry assignment."
"Sai mai ya faru da aka baku Chemistry assignment?"
Safiya ta yaƙe hakora ta dawo kusa da Maryam a kan gado. "Ya MK za ki kira mun akwai abunda ban fahimta ba."
Ta wutsiyar ido Maryam ta yi mata wani kallo. Su Ya MK manya. "Safiya ki fita idona bana son shegantaka. Kar ki je malamin ku ya miki bayani ki tsaya nan kina jira in kira a yi miki explaining. Da chan wa ke miki idan baki gane ba."
"Ai dan kina nan Yaya shi yasa. Shi da kan shi ya ce fah in kira shi idan ina da tambaya."
"Sai ki kira shi da wayar ki ai."
"Kai Ya Maryam."
"Ki ma cire rai dan ba zan kira shi ba. Abun ai ba hauka bane. Daga kin samu ya yi miki assignment sai ki mayar da shi lesson teacher."
"Yaya Maryam mana. Dan Allah!"
"Kar ki isheni Safiya."
Ɗakin Maryam ta bar mata. Da wayarta ta tafi dan ta san tsab Safiya zata dauka ta kira shi. Ita bata san meye hadin ƙannenta da MK ba. Ba Safiya ba, ba Zee ba. Tun ranan da ya yi wa Safiya assignment kullum sai sun ɗago zancen shi kaman wa'inda aka yi wa asiri.
Wurin Mama ta tafi suka sha hira har sai da aka kira sallan la'asar. Ta baro ɓangaren Mama ta koma ɗaki. Bayan ta idar da sallah Bilkisu Kabir ta kirata.
Tunda ta karɓa lambarta wurin Sumayya basa kwana biyu ba su yi waya ba. Shekaru kusan huɗu da suka shafe ba su rage alaƙarsu ba. Sun daɗe suna hira kafin su ka yi sallama.
Washegari da la'asar Hamida ta iso. Babanta ya yarda ta kwana. Murna wurin Maryam ba'a cewa komai. Cikin gidan sai yaran kaɗai Umma da Mama sun fita, Baba Malam kuma na chan sashen shi.
Babu islamiya Bashir da Zee na falo suna kallo. Idris kuma ya tafi kwallo. Safiya na ɗaki tare da su Maryam ana ta hira.
"Da zaman nan da mu ke yi da ba mun rage wani aikin ba. Ko dankali ne a fere a tafasa, a yi jajjage da ɓare maggi." Cewar Hamida.
"Hakane kuma," Maryam ta ce tana miƙewa. "Mu je toh, bari in ciro kayan."
Hamida da Safiya suka bita kitchen ɗin. Zee na ganin sun fita itama ta bi su. Zee na fere dankali Safiya na datsawa. Hamida kuma ta gyara kayan miya dan ta markaɗa su.
Maryam ta dauko fulawa da butter ta auna daidai wanda zai isheta. Sannan ta saka gishiri yanda ya kamata. Murza fulawan da buttet ɗin ta yi suka haɗe kaman burbuɗin biredi sannan ta zuba ruwan sanyi ta yi ta murzawa har ya haɗe jikin shi kaman kwabin chin-chin.
Bata taɓa kwaɓa mai yawan haka ba. Kafaɗunta sun riƙe suna zafi. Kowa ya gama aikin shi ya barta tana dambe da fulawa. Hamida ta karɓa rabi ta tayata.
Bayan dough ɗin ya kwabu ta saka shi cikin fridge ya ida haɗe jikin shi. Daga nan kuma ta fara yin filling ɗin.
Mai ta fara zubawa cikin kaskon sannan ta zuba tafarnuwa da albasa. Tun daga nan ƙamshi ya baɗe kitchen ɗin. Bata bari tafarnuwan da albasar suka ƙone ba ta zuba niƙakƙen naman tare da ɗan gishiri da rabin ɗanɗanon da zata saka. Wuta kaɗan ta saka, tana yi tana juyawa har naman ya fito da ruwan jikin shi ya kuma tsotse. Daga nan ta zuba saura spices ta zuba dafaffen dankali da karas da shima an dafa shi.
"Kin ji ƙamshi tun daga tsakar gida." Hamida ta shigo kicin ɗin. Bayan duk sun gama aikin su ciki suka koma sai ita kaɗai kitchen din. "In zo in yi miki ɗanɗanon gishiri?"
Maryam ta yi dariya. "Wannan dai ba na gida bane bare ki cinye filling ɗin tun a kan wuta."
Bayan naman ya yi ta kashe wutar. Idan ya hushe zata zo ta yi mai wuyar. Murzawa.
Falo ita da Hamida su ka koma. Safiya na jin su ta fito daga ɗaki. Kusa da Maryam ta zauna ta fara mata magiya. "Yanzu Yaya ba za ki kira mun shi ba?"
Hamida da ke gefe ta kalla Safiya. "Wa zata kira miki Safiya?"
"Ya MK. Yauwa! Ya Hamida na san kina da numban shi ai. Dan Allah kira mun shi."
Maryam ta harara Safiya. Lallai yarinyan nan ta raina ta. Laifinta ne ai, da tun farko bata kira ya yi wa Safiya assignment ba da duk hakan bai faru ba.
"Ni ko ke da lambar shi. Bari in kira mi ki shi."
"Dan Allah kar ki kira Hamida. Wannan ai rashin sanin ya kamata ne. Wa ya ce kar ta maida hankali a aji ta fahimta lokacin da malamin ke koyarwa." Maryam ta maida kallonta kan Safiya. "Zan haɗa ki da Umma idan kika sake kika ƙara tado zancen."
Tashi ta yi ta shiga ciki ta barsu a wurin. Safiya da taga da gaske Yayarta bata so sai ta bar zancen.
Bayan sallan maghrib duka ʼyan matan su ka shiga kitchen a ka hau murza dough. Hamida da Maryam ke aikin, ɗaya na murzawa, ɗaya na folding. Idan sun gaji su chanza. Zee na kamawa amma da ta ɗan yi ta ke ajiyewa wai ta gaji.
Hajiya Safiya kam ita aikinta yi musu hira ne. Tana game a wayar Maryam kiran MK ya shigo. "Yaya ana kiran ki."
"Dauka ki sa mun a speaker," Maryam ta ce tana barbaɗa fulawa a saman slab.
"Ke ko ba ki san waye ba za ki ce a saka a speaker." In ji Hamida.
"Ya MK ne." Safiya ta faɗa a hankali.
"Amsa ki ce mai aiki na ke yi." Maryam ta ce tana cigaba da rolling ɗinta.
Safiya kuwa ta amsa ta saka a speaker. Sallamar MK ta karaɗe kitchen ɗin. Maryam ta zaro ido gashi ba daman yin magana saboda bata son ya ji tana kusa.
"Ya MK ina wuni Safiya ce."
A zuciya Maryam ta ce, ko yaushe sunan shi ya zama Ya MK ni ban sani ba. Safiya iyayinta ya yi mata yawa.
"Lafiya lau Safiya. Ya makaranta?"
"Alhamdulillah. Ya Maryam ɗin bata kusa."
"Oh. Toh idan ta dawo ki ce mata na kira."
"Toh in sha Allah. Sai da safe."
Safiya na ji na gani ta yi mai sallama ba tare da ta yi mai tambayar da take so ba. Yanda Mr. John ya yi musu bayani ya ruɗata shi yasa ta ke so ya yi mata dalla-dalla.
Hamida ta kalla Maryam da ke aikinta kaman ba tutor ɗin su bane ya kirata hakanan babu dalili. Hamida ta yi murmushi. Tuni ta harbo jikin MK dama, kallon shi kawai ta ke yi. Kai ta girgiza su ka cigaba da aiki.
Ƙarfe tara su ka kammala komai. Saboda tsabar tsayuwa tafin ƙafafunta ciwo su ke yi. Meatpies ɗin sun yi kyau sosai. Komai ya tafi yanda ya kamata. Ta tashi da pieces hamsin cif-cif. Ta siya irin fararen ledojin nan da ake packaging a ciki ta saka.
Umma na ta yi musu sannu. "Ku shiga ga ruwa chan an kai muku ku yi wanka. Hamida wannan da ke za'a raɓa kuɗin dai ko?"
Hamida ta yi dariya. Ita ta fara shiga wankan Maryam kuma ta faɗa gado. Daɗin su ɗaya, sun yi sallah. Wanka kawai za su yi.
Maryam ta gasa jikinta sosai da ruwan ɗumi. Tana saka kaya ta shige bargo sai dai duk gajiyan da ta yi bata jin barci.
"Ranan lahadi zamu koma makaranta?" Hamida ta tambaya daga ɗayan gefen.
Maryam ta ja tsaki. "I can't believe har satin ya ƙare. Dama sati biyu aka bamu wallahi."
"Sai ki zauna ki yi sati biyun ai." Hamida ta yi dariya.
"Wa? Rufa mun asiri. Muna komawa ʼyan kwanaki za'a yi za ki ji ana cewa exams. Allah dai Ya bamu sa'a."
"Ameen. Exams ai bai kamata ya ɗaga miki hankali ba. Ki cigaba da addu'a, kuma kina da MK ai."
Maryam ta gyada kai. Hamida ta murgina tana fuskantar ƙawarta. Ƙura mata ido ta yi har saida Maryam ta ce ta bar kallonta.
"Su Ya MK manya. Ahh ahhh! Yaya Maryam. Yaushe abu ya yi progressing haka bani da labari."
Maryam ta watsa mata harara. "Ba ki da lafiya Hamida. Safiya ce da iyayi daga ya yi mata assignment ta wani kwakwaba mai Yaya."
"Wato har ya fara sabawa da 'yan gida! Kai Masha Allahu."
"Allah Ya shirya ki. Ni daina kallona barci zan yi."
"Ai ba ki isa ba. Ya Maryam ki bada fili kawai bawan Allahn nan ya gabatar da kan shi. Na san ki san intentions din shi kawai kina yi kaman ba ki sani bane."
"Wasu intentions? Kawai dai yana da kirki ne kema kin sani."
Hamida ta ɗaka mata duka a cinya. "Kin manta ba kirki ba. Me ya sa tunda muka dawo ke kadai ya kira? Ni da Summy duk bai kira mu ba sai ke."
"Oho. Wannan shi ya sani kuma. Kin ga Hamida ni na gaji sai da safe."
Ta ja bargo ta rufe jikinta gaba ɗaya har kai. "Za ki gama noƙe-noƙen ki ne."
Bata amsa ta ba, ta runtse ido. Ita bata san wasu intentions din shi ba kuma ba zata taɓa sani ba.
Karatu ya kaita Zaria ba shirme ba.
Washegari da safe dattijuwar nan ta aiko dreba ya amsar mata saƙon tare da kuɗin cikin farar envelope. Maryam ta leƙa taga kuɗin a ciki. Nan wai nata ne.
Umma ta kaiwa envelope din. "Masha Allah. Yaya Maryam Allah Ya sa albarka a ciki."
Maryam ta girgiza kai da Umma ta miƙa mata kuɗin. "Umma ki yi amfani da shi. Sai a siyanwa su Zee wani abu. Ki bani ɗari biyar in ba Hamida"
Umma ta kalleta ta yi dariya. "Kuɗin ki ne Maryam ai ba nawa ba. Jiya da kina ta dambe da fulawa ni ba ina ɗaki ba. Ansa abunki, ki je kiyi duk abunda kika ga ya ɗace."
Maryam ta so ƙiyawa sai da Umma ta yi mata jan ido. Tana karɓa ta cire wasu a ciki ta ajiyewa Umma ta fita da gudu. Sashen Baba Malam ta tafi inda ta same shi zaune falo da Mama.
Nan ma kuɗin ta bada Mama ko ta rufe ta da faɗa akan me zata kawo masu kuɗin aikin da ta yi. Baba Malam ya bata haƙuri ya kalla Maryam. "Ɗauki abun ki Yaya ki tafi kin ji. Allah Ya sa albarka."
Ta amsa da Ameen ta koma ɗaki. Ta san idan ta ba Hamida itama ƙin karɓa zata yi. Zata san yanda zata yi ta bata wani abu a ciki.
A bakin gado ta zauna ta ƙurawa envelope ɗin ido. Inama Abbanta na nan. Hawayen da suka tarun mata a ido ta yi saurin haɗiyewa. A wardrobe dinta ta ajiye kuɗin kafin ta san abunda ya kamata ta yi da su.
Da yamma sai ga kiran matar ya shigo. Umma ta saka a speaker. "Hajiya Sa'adatu gaskiya na ji daɗin meatpie dinnan sosai. Da na ɗanɗana na farkon ji na yi kaman in adana sauran kar a raba wurin taron. Ya yi daɗi sosai."
Bakin Maryam har kunne ta sauraronta.
"ʼYar ki ce ke yi ko?" Umma ta amsa da eh. "Zan samu wasu fifty pieces ɗin zuwa Monday?"
Umma ta kalla Maryam. Da sauri ta daga kai tana ce mata 'Sunday'."Eh toh, za ki samu ranan Sunday. Da yake tana karatu a ABU ta zo hutun mid-semester ne."
"ABU? Kai Masha Allah. Toh babu damuwa."
Umma na gama wayar Maryam ta ɗane ta. "Nagode Ummana."
Umma Sa'adah ta yi murmushi tana shafa bayan Maryam. "Wancan kuɗin sai ki cire kuɗin kayan da za ki siya ko? Sauran kuma ki adana su. In kin je kasuwa ki siyo asusu."
Umma bata ba yaranta tarbiyar kashe kuɗi ko yaya ba. Asalima bata cika basu kuɗi a hannu ba, ko kuɗin break bata basu sai once in a while. Duk abunda suke so zata siya da ɗan dama ta ajiye. Tun farko haka Abban su ya koya musu ba zata sa ƙafa ta shure tarbiyar shi ba.
Yanda Umma ta ce haka Maryam ta yi. Wannan karon ita kaɗai ta yi yawancin aikin sai dan abunda ba za'a rasa ba da Safiya da Zee su ka kama mata. Ashe ba ƙaramin taimako Hamida ta yi mata ba. Aiko ta ji a jikinta.
Kaman wancan karon, drebanta ya amsa sanna ta miƙa mata kuɗin. Ta yi mai godiya ta koma ciki fuska ɗauke da murmushi.
Farkon fara sana'ar Yaya Maryam kenan.
Ranan littinin da safe motar gidan su Hamida ta ajiye su a tashar Kawo domin komawa garin Zazzau.
•
•
•
•
•
Nima dai gani garin Zazzau banda lokacin kai na😩😂
Ina ta ganin comment din ku. Komai lafiya kawai dai boko ta taso ni gaba.
School has me on a chokehold sai an yi haƙuri da ni. And please, a sani a addu'a🥹 Allah Ya ba Maimunatu sa'ar karatu.
Thank you. I love hearing your thoughts so please drop them in the comment section. Mai kuke gani zai faru? Ina labarin ya dosa?💃🏻 Kwament below let's chat.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top