14.
Daɗi kaman ya kasheta a lokacin da ta ga sunanta a list ɗin results da a ka yi pasting da makin da ta samu. Baƙinta har kunne ta kasa daina murmushi. Kutsawa ta yi ta cikin dandazon dalibai da suka zo ganin sakamakon su suma.
A yau ne Department Of Chemistry suka manna sakamon gwajin CHEM 101 da 121 da suka rubuta satin da ya wuce.
Ta fito siyan abu gaban hostel ta ji wasu na zancen an yi pasting har sun duba na su. Niyarta ta koma ɗaki sai ta dawo tare da su Hamida amma taga kai, bazata iya ba ta ƙosa taga mai ta ci.
Har yanzu murmushin fuskarta ya ƙi gushewa. Nata kaɗai ta duba bata yi karanbanin duba na sauran ba duk da kuwa ta san reg numba ɗin su.
Wuri ta samu ta zauna sannan ta ciro wayarta daga cikin jaka ta nemo sunan Ummanta. Bugu biyu aka ɗauka.
"Hello Umma." Ta ce murya cike da murna.
"Yaya Maryam!" Muryar Zee ta riske kunnenta.
"Na'am Zee. Ya kike? Ina Umma? Hala sato wayan kika yi bata sani ba."
Zee ta yi dariya da ya tabbatar da zancenta gaskiya ne. "Yaya yaushe zaki dawo? Tunda kika tafi ba ki zo ba ke da kika ce duk weekend za ki riƙa zuwa."
"Ƙarshen satin nan zan dawo in sha Allah. Ranan alhamis zamu gama test, amma sai juma'a zan taho."
Zee ta yi ta murna. "Yaya ki yi mun tsaraba idan za ki dawo."
"Toh Zee. Kaiwa Umma wayar."
Bayan minti biyu muryar Umma ta daki kunnenta. "Waye...hello?"
"Umma ni ce. Ina wuni?"
"Au wai da ke ce Maryam. Ina tambayar yarinyan nan ma ba ta tsaya ta saurareni ba bare ta ban amsa. Ya makaranta?"
"Lafiya lau. Umma yanzu naga result ɗin test ɗin da muka yi na chemistry."
"Sakamakon ya yi kyau dai ko?"
"Sosai! 101 na ci talatin da takwas, a 121 kuma na samu maki talatin da huɗu."
"Masha Allah! Alhamdulillah! Haka ake so Maryam. Allah Ya sa albarka ya cigaba da bada sa'a. I am so proud of you. A cigaba da dagewa kin ji?"
"In sha Allah Umma. Ina su Mama, a bata mu gaisa."
Ta faɗawa Mama da Baba Malam makin da ta samu suna ta saka mata albarka. Sai da ta gaisa da kowa a gidan tukun nan su ka yi sallama.
Ɗaki ta koma ta iske shi rufe. Mukullinta ta ciro daga jaka ta buɗe ta shiga. Ɗakin gaja gaja wanda ke nuna Hamida sauri take yi bata ma tsaya gyrawa ba. Tukunyan da ke ajiye saman tebur ɗin da suka girki ta buɗe. Jollof ɗin shinkafa da wake ne a ciki.
Abincin ta zuba ta zauna ci. Bayan ta gama ci ta sa hannu zata dauko ruwa ta ga wayam. Dole ta saka hijabinta ta sauƙa ƙasa ta siya a ɗaya daga cikin shagunan da ke hostel ɗin.
Daga nan kuma ta hau gyaran ɗakin. Harda mop suka siya, saboda haka ta gyara sannan ta share ta goge ta fesa turaren ƙamshi. Ta gama aikin nan kenan wayarta ta yi ƙara. Da sauri ta cirota a jaka sai dai kafin ta amsa kiran ta tsinke. Wani ya ƙara shigowa nan da nan.
Sunan MK ne baro baro a fuskar wayarta. Hakanan ta samu kanta da faɗuwar gaba har saida ta dafa ƙirji. Fargaban ko na meye? Oho.
"Salamu alaikum Maryam."
"Wa'alaikumus salam. Ina wuni?"
"Lafiya lau. Result ya fito ban san ko kina da labari ba."
"Eh, ai har ma na duba."
"To yaya?"
Bata san sanda murmushi ya kubce mata ba har MK na iya jiyo sautin ta ɗayan bangare. "Alhamdulillah, daga ji score ya yi kyau."
Maryam ta daga kai kaman yana gabanta. "Thirty eight a 101 sai thirty four a 121."
"Masha Allah! See, na ce miki za ki iya. Kin yi ƙoƙari sosai, keep it up."
"Nagode. It wouldn't have been possible without your help. Nagode."
Khalid ya gyara zamansa daga ɗayan bangaren. "Maryam," ya kira sunanta a sanyaye. "Taimakon da na yi kaɗan ne. It was all you."
Maryam ta yi murmushi amma bata ce komai ba.
"Ranan thursday za ki gama test ko?"
"Eh, in sha Allah."
"A ranan za ki tafi?"
"A'a. Da rana ne test ɗin, sai washegari idan Allah Ya kaimu."
"Okay. Allah Ya kaimu."
Daga nan su ka yi sallama. Babu daɗewa Hamida da Sumayya suka dawo. Maryam ta barsu ɗazu suna shirin zuwa saloon wankin kai. Itama kan nata ya yi datti amma sai ta je gida zata wanke.
"Maryam daga department mu ke. Test ya fito." Cewar Hamida
"Nima na biya ɗazu da na fita." A lokaci ɗaya su ka ce, "nawa kika ci?" Sai kuma suka kwashe da dariya.
Hamida ta ci maki talatin da huɗu a 101 sai maki talatin da ɗaya a 121. Sumayya kuma duka ta ci maki talatin da uku uku. Dukan su dai babu wanda ta ci ƙasa da maki talatin. Hakan ba ƙaramim daɗi ya yi musu ba suna ta sakawa MK albarka.
"Maryam da mun biye miki da shikenan kin ja mana asara."
Ai kuma ta bani wurin Hamida. "Toh! Ke wai abu baya wucewa a wurin ki ne? Haba."
"A'a wai dan in tuna miki. Ni hankalina ma tashi ya ke yi idan na tuna final year ya ke, wannan ce shekarar shi ta ƙarshe a makarantan. Dama wani three ya ke ko four, kai three ɗin ma. Yanda muna three yana final year kinga ina lefi mun more karatun shekara uku."
"Sai ki zaunar da shi a makaranta ai ya cigaba da koya miki karatu."
"Da zan iya da na yi. Tun bare ni da ke Sumy," Hamida ta juya ta kalla Sumayya dake zaune kan gadon Maryam. "Chemical engineering ya ke zai iya chemistry ɗin nan namu, dama Maryam ce sai ta nemo wanda zai riƙa mata Biochem."
"Ke kika sani."
Gaba ɗaya yinin ranan da murnan ganin sakamakon su ka yi. Shine result ɗin su na farko a ABU, kuma ya zo a daidai.
Fatan su Allah Ya sa hakan ya ɗore.
Washegari Zuby ta ce Maryam dan Allah ta rakata cafe zata yi abun ʼyan Kaduna State da yake da indigene din nan ta ke amfani. Maryam ganin babu abunta ta ke yi ta shirya ta samu Zuby a ɗakinta. Duka bai wuce so huɗu ta taɓa zuwa ɗakin ba. Ina ma Zubaida ke zaman bare a zo ɗakinta.
Zuby ta sha kwalliya kaman zata biki. Maryam ta kasa shiru sai da tambayeta idan akwai inda zata je.
"Idan mun gama zan haɗu da tutor na."
"Tutor kuma? Karatu ze miki? Ba test ɗin Biology kaɗai ya rage ba."
Biology kuwa mai ya haɗa shi da tutorials. Ka karanta ka fahimta ne sai kuma ka haddace.
"Eh, ba tutorial zai mun na. Zamu je wani wuri ne."
Babban magana. Wayaga ta sha kwalliya zata fita da MK. Bata san me zata ce ba dan haka ta ja baƙinta ta yi shiru. Ɗaya daga cikin cafes ɗin da ke cikin social centre suka je. Cafe ɗin cike ya ke da mutane ʼyan verification, da yake President ɗin student association ɗin Kaduna ya ce a yi wa ʼyan aji ɗaya kyauta.
Suna tsaye suna jiran layi ya zo kan ta Zuby ke tambayar Maryam batun score ɗinta na Chemistry. "Ni twenty eight na ci a 101, 121 kuma na shi twenty nine. Maki ɗaya ya hanani cin talatin wallahi."
Maryam ta yi dariya ta ce mata ta yi ƙoƙari.
"Ke nawa kika ci?" Zuby ta sake tambaya tana murmushi. Maryam na faɗa mata score ɗin da ta ci murmushin nan ya ɓace bat a fuskarta. Ta ɗaure fuskar nan tamau sai ka ce ba yanzu yanzun nan ta gama dariya ba. Daga ƙarshe ma cewa ta yi wai tutor ɗinta na jiranta ta fasa screening ɗin.
Su ka bar social centre ta ƙofar baya da ke bullo da mutum wurin Ribadu hostel. Ko sallama kirki Zubaida bata yi mata ba ta tafi har lokacin fuska a ɗaure.
Abunan ya tsayawa Maryam a rai har ta kasa daurewa sai da ta faɗawa Hamida da dare suna shirin kwanciya.
"Wallahi Hamida ina faɗa mata score ɗin fuskarta ta chanza completely, kamar kiftawar ido ta haɗa rai. Har muka rabu ko haƙoranta ban sake gani ba."
Hamida ta jinjina kai tana taɓe baki. "Ki ce kawai baƙin ciki ta nuna ƙarara."
"Baƙin ciki?" Maryam ta maimaita.
"Baƙin ciki mana Maryam. Idan ba ɓakin ciki ma mai zai sa annurin fuskar ki ya gushe ke da ba mummunan labari aka faɗa miki ba. Ni kawai yanda na fahimta shine ta so a ce kin ci ƙasa da score ɗinta, sai ta ji kin yi mata fintinkau. Irin mutanen nan ne da suke so kullum sune a gaba da kai ɗan su riƙa ji kaman kai baka kai su ba. Muddin wani abu naka ya fi na su basu iya boye baƙin cikin su."
"Kai Hamida."
"Dagaske Maryam. Duk wanda kika faɗawa haka abunda zai ce kenan. Sai ki fara ja baya da ita. Ni dama yarinya bata wani mun ba."
"Zubaida is nice Allah. Kawai dai wannan abun da ta yi ya bani mamaki."
"Niso ne ba nice ba. Sai ki dage ki riƙa cin less than her dan kar ki ɓata rai tunda she is nice."
"Hamiiiiiidaaaaa..."
Hamida ta yi dariya. Daga nan suka saki zancen Zuby su ka kama na tafiyar su gida da ke ta matsowa.
Ranan alhamis su ka rubuta paper ɗin su ta ƙarshe. Maryam ji take yi kaman ta gama semester ɗin. Sai dai bata ga komai ba dan test bai kamo ƙafar exams ba.
Suna dawowa ɗaki ita da Hamida su ka hau shirya kaya. Tun wancen satin su ke shiri sai ka ce idan sun tafi ba dawowa za su yi ba. Hutun Mid semester ɗin duka na sati ɗaya ne.
"Wai Maryam a ina ma zamu hau mota ne? Ni fa ban taɓa hawa motar haya ba."
"Kina magana kaman ni na taɓa hawa." Duk zirga zirgan post utme da admission da su ka yi Baban Hamida ke bada mota a kawo su. "Na ji an ce ana samun motocin Kaduna a gabam main gate."
"Toh sai goben mu je mu gani."
Da dare kiran MK ya shigo wayarta. Rabon da su ga juna tunda su ka rubuta Physics. Daga nan ba su sake fita karatu tare ba tunda sauran courses ɗin karantawa za ka yi ka fahimta.
"Gobe sai gida." Ya ce mata bayan sun gaisa.
"Yes. Na ƙosa gari ya waye mu kama hanya."
"Su Maryam za'a gida. Ba za ki zauna damu a makaranta ba?"
"Kai ba zaka je gidan ba?"
"Mmmm mmmm bazani ba, ina da abubuwa da yawa da zan yi. Nasan idan na je Kano kuma dole sai na ƙara sati ɗaya a sama."
Maryam ta tambaye shi dama a Kano gidan su ya ke.
"Eh Kanon Dabo ba. Kin taɓa zuwa?"
Ta yi dariya ta ce, "Ban taɓa zuwa ba."
"Ahh ahh. An barki a baya gaskiya ya kamata ki je ki ga Kano. Goben ta ya za ku tafi?"
"Main gate zamu. An ce ana samun mota a nan."
"Baku taɓa hawa mota ba?"
Maryam ta ɗan yi shiru sannan ta ce mai eh. "Ƙarfe nawa za ku tafi zan zo in kai ku ku hau mota."
"A'a ba sai ka z—" Maryam ta fara cewa MK ya katse ta.
"Ƙarfe nawa Maryam?"
"Goma."
"Around nine thirty zan zo toh."
"Toh mun gode."
Daga nan su ka yi sallama Maryam ta tsurawa wayar ido. Kai ta ɗaga ta kalla Hamida wanda tun tuni hankalinta ke kan Maryam ɗin. Ganin tana shirin ɗagowa ne ya sa ta yi saurin kauda kai. Leɓenta na ƙasa ta ciza dan kar Maryam ta ga murmushin da ke fuskarta.
"Kin ji MK wai zai zo gobe ya samu a mota."
Hamida ta gimtse fuska dan kar asirinta ya tono. "Ai ko mun gode."
Daren ranan ba su yi barci ba sai ma hira da suka tsira har wurin ƙarfe biyu na dare. Washegari da sassafe su ka yi wanka su ka gyara ɗakin tas. Ƙarfe tara da rabi kaman yanda MK ya yi alƙawari ya iso.
Basu dauki kaya da yawa ba. ʼYan ƙananun jakunkuna irin na matafiya duka suka ɗauka sai jakar hannunsu. Duka dogayen hijabai su ka saka tunda ba motar gida zasu bi ba.
Khalid na tsaye na Nas yana jiran fitowar su. Yau dai burin Nas ya cika ya rako shi wurin Maryam. Jiya a kunnenshi ya ji yana cewa zai zo ya rakata. Bai nuna ya ji ba sai yau da safe Khalid zai fito Nas ya biyo shi ya ce su je.
Khalid ya tsaya yana mai kallon mamaki Nas ya ja hannunshi yana ce mai ya yi sauri kar su barta tana jira.
Khalid ya san ko me ze yi tunda Nas ya ce zai je to fa sai ya je dan haka be yi mai gardama ba su ka taho.
Tun ɗazu ya ke tsokanar shi wa ya kwantar da hankalin shi bata tafi ba.
"Kana da matsala wallahi Nasir. Saura su fito ka yi ta surutan banza da wanda aka tambaye ka da wanda ba'a tambaye ka ba."
Nas ya kyalkyale da dariya. "Abokina ka ce so kake yi in yi maintaining. Kar ka damu I will be the best wingman. Zan yi ta koɗa ka har sai Babe ɗin ta ka ta ji kai MK dinnan ya haɗu."
MK ya girgiza kai faɗawa Nasir abu bata lokaci ne wani sa'in. Babu daɗewa Maryam da Hamida su ka fito. Sanye ta ke da hijab cream color da ya haska fatarta. Khalid ya ja nannauyan numfashi ya saki a hankali.
"Shege MK, ka tafi wallahi." Nas ya ce ƙasa ƙasa.
Gaisawa su ka yi sannan ya gabatar da Nasir a matsayin abokin shi. Maryam da Hamida su ka sake gaishe shi. Su kam gaisuwa ba ta yi musu wahala. Yanda kasan ya haife su haka su ke gaishe shi duk sanda su ka haɗu.
"Hamida ina Sumayya?" Khalid ya tambaya.
"Tana ɗaki ita sai gobe zata tafi Abuja."
Nas ne ya ja Hamida da surutu. Dukan su dama zuba ne da su kaman aku. Gaba ma su ka yi suna hira kaman sun daɗe da sanin juna.
MK ya kalla Maryam. "Mu je." Ya ce yana miƙa mata hannu. Kallon shi ta tsaya yi ya nuna mata jakar hannunta.
"Na gode." Ta ce ta miƙa mai.
A hankali su riƙa tafiya. Nas da Hamida tuni sun yi gaba. Khalid ya riƙa jan akalar hirar. Duk da shima ba mai yawan surutu bane amma a nan dole ya buɗe baki ya yi magana dan ya ga Maryam ta fi shi rashin son magana. Idan ta ita ne har su kai main gate bara su ce komai ba.
Gaban Main gate sai ka ce tasha. Masu motoci na ta neman fasinjoji. "Kaduna one! Kaduna one! Kaduna! Abuja direct!"
Tunda Maman Hamida da Anti Nafee su ka kawo su basu sake leƙa waje ba sai yanzu. Gaban wata Golf su ka tsaya babu kowa a ciki booth a buɗe. Wani mutum ya karɓa jakunkunan su ya saka a ciki.
"Bismillah, ku shiga" MK ya ce. Magana ya yi da dreban sannan ya dawo ya yi musu sallama. "Allah Ya kiyaye hanya, a gaida ʼyan gidan."
"Ameen. Za su ji Mun gode." Maryam ta ce.
Nas ma ya yi musu sallama kafin su ka juya su ka nufi get din makaranta.
Maryam da Hamida na jira su ga wasu mutanen sun shigo motar kaman yanda sauran motocin su ke a cike sai suka ga mutum ɗaya kawai ya shiga gaba dreba ya ja mota suka kama hanya.
"Malam ya naga baka amsa kuɗin mota ba?" Hamida ta tambaya.
"Ai wanda kuka zo tare da shi ya biya. Kuɗin mutum huɗu ya biya ma dan ku zauna ku kadai a baya."
Hamida ta kalla Maryam, Maryam ta kalla Hamida. Hamida ta jinjina kai. "Lallai MK. A gaishe shi. Yaya Maryam sai a kira shi a yi mai godiya."
"Ke me yasa baza ki kira shi ba sai ni?"
"A'a wai naga ke kike jaddada mana muhimmancin godiya shi yasa. Kuma dai wannan abu dan ke aka yi dan haka ke ya fi chanchanta ki yi godiya."
"Ba ki da lafiya." Maryam ta ce tana share zancen. Amma maganar Hamida ta ƙi barin kwakwalwarta. Kai ta girgiza. Kawai MK na da mutunci ne shi yasa. Hamida ta fiye shirme.
Ƙarfe sha ɗaya saura motar ta tsaya a tashar Kawo da ke Kaduna garin gwamna. ʼYar ƙurƙula suka hau aka ajiye su a sign board sannan su ka sake shiga wata bus ɗin ta shiga da su cikin unguwar dosa.
Maryam ta fara sauka dan layin su Hamida a gaba ya ke. "To Yaya Maryam Allah Ya huta gajiya ki gaida su Umma. Kar ki manta ki kira MK ki miƙa godiyar mu."
Maryam ta girgiza kai. Hamida ba lafiya wani lokacin. Amma dai zata kira ta yi mai godiya dan hakan shine daidai. Kaman ta ruga da gudu ta isa gida haka dai ta taka a hankali har ta isa. Da Bashir ta fara cin karo a ƙofar gida.
Yana ganinta ya taho da gudu yana ihun murna. Ya ƙara tsawo kaman ba shekaran shi takwas ba. Bayan ya rungumeta da gudu ya shiga gida yana ihu. "Yaya Maryam ta dawo! Yaya Maryam ta dawo!"
Dayake su ma midterm break su ke yi a makaranta duka suna gida. Zee da Safiya na ji su ka fito da gudu suma. Tun dazu su ke damun Mama ta basu waya su kirata su ji inda ta ke.
A tsakar gida su ka haɗe Maryam ta yarda jakarta suka rungume juna gwanin ban sha'awa. Tunda su ke basu taɓa tsawon lokacin nan basu ga juna ba. Bayan sun gama ihun su da tsalle tsallen su Zee ta karɓan mata jaka su ka shiga ciki.
Falon Mama su ka nufa Umma ta tafi wurin aiki. Idris na falo yana kallo Maryam ta dungure mai kai. "Ashe kana ciki."
Ya wani haɗe fuska amma da ka gani kasan murmushi ya ke so ya yi. Maryam kuwa ta rungume ɗan ƙanin nata bada damu da mazuran da ya ke yi ba duk da kuwa ta ji hannun shi a bayanta shima ya rungume shi.
Mama ce kaɗai a gidan sai yara. Baba Malam ma baya nan.
Ɗakin Mama ta shiga ta gaisheta. Mama ta amsa cike da fara'a. "Anya Maryam kina cin abinci kuwa kin ga yanda kika sake zama wata ʼyar mitsila."
Maryam ta yi dariya. "Ina ci mana Mama."
Mama dai bata yarda ba. "Ki riƙa cin abinci dan Allah. Je ki ma Zainab ta kawo miki abinci yanzu ki shi. Tuwon shinkafa da miyar taushd Umman ku ta yi kafin ta tafi wurin aiki."
"Toh Mama."
Ɗakin su ta nufa Zee da Safiya na biye da ita. Wanka ta fara yi kafin ta fito sun kawo mata abinci. Tana ci suna hirar yaushe gamo.
"Yaya ina tsarabar da na ce ki mun?" Zee ta tambaya.
Safiya ta yi tsaki. "Abunda ya zaunar da ke kenan."
Zee sarkin tsiwa ta ce, "toh ina ruwan ki?"
Maryam ta janyo jakarta ta ciro gurguru da ta siya mai ɗan karen daɗi da ake yi a gaban hostel ɗin su. Sai tarkacen su sweet da biscuit. Tun a makaranta ta ƙulla na kowa a leda. Ta ba Zee nata ta ba Safiya nata.
Irin masu tallan nan na cikin hostel taga suna saida ɗan kunne shima ta siyan ma Zee da Safiya. Aiko Hajiya Safiya da ke tashen gayu ta ji daɗin tsarabar ɗan kunne sama da kayan zaƙin.
Maryam ta ce a kira mata Bashir shima ta bashi na shi yana ta jin daɗi. Falon Mama ta kaiwa Idris na shi da kanta.
Ya yi murmushi ya karɓa. "Na gode Yaya."
Ɗaki ta koma saboda barci ne a idonta jiya ba su barci da wuri ba ita da Hamida.
Bata farka ba sai da ta ji muryar Ummanta sama sama. Tana buɗe ido ta ganga a ɗakin. Ai da sauri ta miƙe ta rungume mahaifiyarta. Umma ta yi dariya tana riƙe Maryam gam a jikinta.
Umma ta janyeta daga jikinta tana ƙare mata kallo. Itama irin ƙorafin Mama ta riƙayi wai Maryam bata cin abinci. Ita dai sai dai ta yi dariya.
Umma nata kallonta saboda kamannin Maryam da Abbanta da suka sake fitowa.
Tun yaushe Maryam ta manta da batun wani MK. Cikin ʼyan uwanta ta shiga ana ta hira. Sai wurin ƙarfe huɗu ta tuna da taga missed call ɗin shi. Tun wurin ƙarfe ɗaya ya kirata.
Bugu biyu ya ɗauka. "Su Maryam an ci tuwon Umma an manta da mu ko."
"Ba haka bane." Ta ce tana dariya.
"Ya kika isa gida? Ya ʼyan gidan da fatan suna lafiya."
"Lafiya lau Alhamdulillah. Mun zo biyan kuɗin mota dreba ya ce ka bada, Allah Ya saka da alkhairi."
"Ameen Ameen. Ki gaida Umma da su Zee. Allah Ya huta gajiya."
Tunda Zee ta dauki wayar Umma ta kirata suna karatu ya riƙe sunan. "Za su ji in sha Allah. Sai da safe."
Khalid ya tsurawa wayar ta shi ido kaman Maryam zata fito daga ciki.
"MK manya. An gama soyayyar kenan. Ko muryar ka ba'a ji fah."
Khalid ya yi banza da Nasir. In da sabo ya saba da halin Nas. Suma tunda su ka zo hundred level aka haɗa su ɗaki ɗaya. Sanadiyar abokantakan su kenan.
"Amma dagaske ba zaka je gida ba?" Nas ya chanza akalar zancen, fuskar shi ta chanza kaman ba shi ya gama tsokana ba.
"Kai ma ka sani zuwana baya da wani amfani. Gwara in yi zamana a nan kawai."
"Khalid..." Nasir ya kira sunan shi na asali. Da wuya ka ji Nasir ya kira shi da sunan, in ko ya kira magana ce ze yi mai muhimmanci. "Ya kamata ka je gida kaima ka sani. Ba'a fushi da iyaye. Ina tsoro kar ka je ka janyowa rayuwar ka masifa."
Khalid ya kauda kai gefe Nasir ya san ya yi hakane saboda baya son maganan. Nasir bai takura mai ba ya bar zancen amma kafin ya fita ya ce abun da ya tsayawa Khalid a zuciya.
"Iyaye matsayin su na nan a iyaye ko da kuwa shirka su ke yi. Wannan tsakanin su da Ubangijinsu ba shi zai hanaka ka yi musu biyayya ba."
•
•
•
•
•
•
Toh fah! Nasir🤔 Don't ask, nima ban sani ba😩😂 yanda kuka ji nima haka na ji.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top