12.
Tun ɗazu take kallon takardun da ke gabanta amma ko abu ɗaya bata fahimta ba.
Tashin hankali! Akwai matsala!
Me ya sa bata fara karatun physics ba tuntuni sai yanzu da test ya kusa? Kullum ta tashi karatu sai ta dauko GENS ko Biology, sune masu saukin karantawa, sai Maths. Physics da Chemistry ta ajiye su gefe kai ka rantse bata yin courses ɗin.
Duka bai wuce saura sati biyu a fara test ba, gashi ido na nema ya raina fata. Rufe takardun ta yi ta ture su gefe. "Hamida ban iya komai ba." Ta ce murya kaman zata yi kuka.
"Nima ban iya ba Maryam. Anya ba zamu nemo wanda zai koya mana ba."
"Toh wa muka sani?" Ta ina zasu fara nemo mai koya musu karatu?
"Ba za'a rasa ba. Mu dai bincika. Dan muka zauna haka Allah carry over zamu kwaso."
Gaban Maryam ya tsinke jin an ambaci carry over. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya zama dole su nemo wanda zai koya musu. Tana tsoron Allah tana tsoron carry over.
Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Ko da ta sake buɗe littafin bayan ta huta bata fahimci komai ba, sai ma sake ruɗewa da ta yi. Dan kar ta yi asarar lokacinta ya tafi a banza sai ta dauko Biology ta fara dubawa. Shi da sauki tana fahimtar abunda take karantawa. Sannan karatun da ta yi a baya bai zube ba. Hakan ya sake ƙara mata ƙarfin gwiwar cigaba da karatun.Har sai sha ɗaya na dare ta kwanta.
Washegari da ta haɗu da Zuby wurin lectures ta ke tambayarta ko ta san wanda zai yi musu karatu.
"Ana tutorials fa a faculty na 'yan hundred level. Mazan engineering ke yi. Kuma sun iya koyarwa babu laifi."
"Haba? Shine ba ki faɗa mun ba."
"Ban san za ki so zuwa ba ai. Naga ba ki cika son fita bane shi yasa ma ban faɗa miki ba."
Maryam ta gyada kai. Da gaskiyarta kam. "Wannan ai tutorial ne Zuby. Zani mana. Physics da Chemistry dinnan ban san me ake yi ba."
"Nima ba'a daɗe da faɗa mun ba. A FSLT a ke yi. Jiya na je, an yi Physics, yau za'a yi Chemistry."
"Dole in je. Wannan courses din kaɗai su ke yi?"
"Duka courses din hundred level banda GENS da Biology. Bari zan taho miki da timetable din."
"Yauwa na gode sosai Zuby. Ƙarfe nawa ake fara tutorials din?"
"Ƙarfe takwas."
"Allah Ya kaimu."
A gaban Lab din suka rabu Zuby ta ce da inda zata je. Tunda Maryam ta lura Zubaida na da son yawo ta kama kanta. A da da ta ce "Maryam zo ki raka ni," zata kwashi ƙafa ta bita. Da taga abun ba mai ƙarewa bane ta dena. Ko ta nemi ta rakata sai ta ce a'a. Itama Zubyn da taga haka sai ta dena tambayarta.
A ƙofar hostel ta haɗu da Hamida. Nan take faɗa mata yanda ta yi da Zuby.
"Dole mu je kuwa. Bari in kira Sumayya in faɗa mata."
Takwas saura su ka fito daga hostel su uku. Kayan da ke jikinta ɗazu su ta maida. Riga da sket na atamfa sai gyale da ya hau da kayan. Ta rataye jakarta me dauke da takardu da calculator a kafaɗa.
Isar su FSLT II suka ga wurin cike dam da mutane. Maryam nata hangawa ko zata ga empty seat da zasu zauna.
"Anya akwai wurin zama kuwa?" Sumayya ta ce.
Hamida ta yi gaba. "Mu shiga mu gani." A bakin ƙofa suka tsaya jiran wasu da suka fito daga ciki su wuce. "Wannan sai ka ce an tara duka ʼyan hundred level ɗin makarantar."
"Mu tsaya a nan tunda atleast mun ganin board." In ji Sumayya.
Maryam ta ce, "Zamu karewa wasu amma."
Tunda suka shigo hankalin shi ke kanta. Kaman an ce ya kalli ƙofa idanuwansa su ka yi tozali da kyakkyawar fuskarta. Tun ranan da suka haɗu ya ke ta waigawa ko zai sake ganinta Allah bai yi ba. Sai yau.
"Ta chan sama akwai wuri." Ɗaya daga cikin su ta ce.
"Hamida ba'a fahimtar komai a wurin. Ni ko board din bana hangowa idan na zauna a baya."
Khalid ya yi dariya. Rashin tsawonta na ɗaya daga cikin abubuwan da ya ja hankalinsa zuwa gareta. Yana zaune a bayan su a row din farko yana jin duk abunda su ke cewa.
"Kai zaka yi musu.....MK!" Wani ya zungure shi hakan ya sa ya dauke kai daga kan ta. "Tun dazu na ke maka magana, me kake kallo?"
"Babu komai. Sorry hankali na baya wurin, ya aka yi?"
"Presido ya ce kai zaka yi tutorials dinnan yau fa. Wakili ba zai samu daman zuwa ba."
Zai ba shi amsa, ya ga Maryam da ƙawayenta suna haurawa steps din da zai kai su seats din dake chan sama na theatre din. Wani yaro ya yi wa alama da hannu ya zo. "Kaga 'yan matan chan su uku, ka ce musu su zo ga seat, ka tabbata su suka zauna fah." Ya juya ya kalla abokin shi ya ce, "mu je waje ka yi mun bayani ni ban fahimta ba."
A waje abokin shi Nasir ke faɗa mai shi ze yi tutorial din CHEM 121 da za'a yi yanzu. "Ni karatu na zo yi, ban zo da shirin yin tutorial ba."
"Taimakawa zaka yi MK, idan ba kai ba babu wani da zai yarda a wurin nan. Gashi mun tara yaran nan babu daɗi mu ce musu an fasa."
"Kai me yasa ba za ka yi ba?"
Nasir ya yi dariya. "Kai ma ka san da kyar na sha course dinnan. In zaka kashe ni ba abunda zan iya tunawa a yanzu haka dai. Besides kune ʼyan Chemical ku kuka san kan course ɗin."
Tabbas Maryam tutorials ɗin ta zo idan ya yi la'akari da hirar su da ya ji. Ba zai so ta yi zuwan banza ba. Dalilin kadai da zai sa ya yarda ya yi tutorial din kenan.
"Shiga ka nutsar da su to. Sannan ina handout din kuma wani topic?"
"Ka fara daga farko kawai." Nasir ya bashi amsa sannan ya shiga ciki ya tsaya gaban theatre ya gabatar da kan shi. Daga nan ya yi musu bayanin asalin wanda ze yi tutorial ɗin ba zai samu daman zuwa ba amma MK zai maye gurbin shi. "Bismillah MK."
Khalid ya sa kai ya shiga ciki ya tsaya gefen Nasir. Ta wutsiyar idon shi ya tabbata Maryam da ƙawayenta na zaune a wurin sannan ya maida kallon shi gaba.
Bayan Nasir ya gama jawabinsa ya bar wurin. Khalid bai tsawaita bayani ba, kawai ya ce su kira shi da MK kaman yanda Nasir ya gabatar da shi.
MK ya samo asali daga sunan shi wato Khalid Muhammad. Dayake a makaranta surname yawanci ake fara rubutawa kafin first name sai ya zama Muhammad Khalid daga nan kuma abokai su ka mayar da shi MK. Tun hundred level sunansa ya bace idan ba MK ka ce ba babu mai ganewa.
Handout da marker da Nasir ya ajiye ya dauka daga kan teburin ya isa gaban board. Bismillah ya yi a zuciya sannan ya hau bayani.
Tunda mai tutorial din ya fara bayani Maryam bata dauke kai daga kan board din ba. Da yaron nan ya ce musu ga wurin zama ta zata kawai raina musu wayo ya ke yi. Da niyarta su yi banza da shi Hamida ce ta fizgo mata hannu tana ta yi mai godiya. A nan ya ke faɗa musu wani daban ne ya basu seat din ba shi ba. Da ta yi musu buƙulu suna chan sama basu ganin board.
Allah Ya sakawa wanda ya basu seat dinnan da alkhairi dan ba ƙaramin taimakon su ya yi ba. Tasan a saman chan ba lallai ta fahimci komai ba. Yanzu kuwa ji take yi kaman an buɗe kwakwalwarta ana zuba mata karatun. Komai shiga kawai yake yi. Ina ma shine lecturer din su ai da basu da matsala. Ya iya bayani filla-filla dole ka gane. Ashe haka course din ke da sauki bata sani ba.
Shi yasa da ya ce a nan zasu tsaya bata san lokacin da ta ce "No!" ba. Allah Ya so ta ba da ƙarfi ta yi magana ba. Hamida da ke kusa da ita kawai ta ji.
"Kema kamar kar ya daina ko? Ashe babu wahala."
"Wallahi. Kawai mu cigaba."
"In sha Allah Wakili zai cigaba gobe daga inda na tsaya." Ya ce da turanci. "Babu mai tambaya?"
Mutane uku su ka yi tambaya. Nan ma ya yi musu bayani har sai da suka ce sun gane.
"Assalamu alaikum," ya ce ya ɗauki marker da littafin ya fita. Daga nan aka fara tururuwar fita.
Sai da aka rage aka daina ture-ture sannan su ka fita daga theatre ɗin. Basu taɓa kaiwa ƙarfe goma a waje ba sai yau. Amma baza ka ce goman dare ne ba yanda dalibai ke ta hidimar su. Tun ɗazu ta ke ta waigawa ko zata ga Zubaida. Da zasu fito ta kirata wayar bata shiga ba.
"Mu tafi." Hamida ta ce.
Stairs suka nufa suna hirar tutorials ɗin. Kowaccen su mamaki ta ke yi ashe haka course ɗin ke da saukin fahimta.
"Da zamu same shi ya riƙa koya mana ai da mun huta." In ji Sumayya.
Maryam ta gyada kai. Tabbas, dan wallahi ya burgeta yanda ya ke bayani. Idan ya koya musu na sati ɗaya ai dole su fito da A a course ɗin.
"Ko numbar shi zamu nema." Hamida ta ce.
"To uwar azarbaɓi. Ina zamu samo numba din shi?"
"Abu mai sauki. Ba Engine boy ne ba, yanzu da mun tambaya wani mun ce number ɗin MK mu ke so tsab za'a samo mana. Ko shi muka samu mu ka roƙe shi ai ze mana. Kin gan shi chan tsaye kuwa. Ku zo muje."
Kafin Maryam ta yi motsi Hamida ta fara jan su wurin dandazon mazan da ke tsaye a ƙarshen stairs ɗin.
"Hamida!" Maryam ta je ce da ƙarfi tana ruƙota. "Tsaya mana!" Oh Hamida! Sai Allah! "Kawai sai mu je mu same shi. Gaskiya a'a."
"Toh me ye a ciki? Taƙarƙari ya ce ba ze yi ba mu nemi wani. Ko ba haka ba Sumayya?"
"Tabbas." Sumayya ta jinjina kai.
Maryam ta girgiza kai. Halin su ɗaya ai. "Gaskiya ku chanza shawara. Haka kawai bamu san shi ba sai mu same shi mu ce ya yi mana karatu."
"Banda ni da muka zo tare wa kika sani a makarantan nan Maryam? Ba a haka ake sanin mutanen ba."
"Na ji amma dai ba zamu tunkare shi haka ba."
"Naga alama Maryam kaman ba ki fahimci da zafi-zafi ake dukan ƙarfe ba. Idan wasu su ka rigamu fa? Kin ga idan baza ki iya zuwa ba ki bari ni da Summy mu je. Sumayya taho."
Maryam ta yi tsaye tana kallon ikon Allah. Hamida akwai ƙarfin hali. Magana Hamida ta yi sai shi MK ɗin ya bi su suka koma gefe. Ko me suke cewa Allah masani. Taga dai ya dago kai sau ɗaya ya kalleta.
Sun yi a ƙalla minti goma kafin Hamida da Sumayya su ka dawo. "Kin gani da mun biye miki da mun yi asara. Ya yarda. Dama ba shi ke tutorials din a nan ba. Gobe ya ce mu same shi a Faculty Of Engineering ƙarfe takwas. Har su Physics ma duk ya ce zai koya mana."
"To barka." Ta ji daɗi dan ya iya koyarwa amma ita har ga Allah tana fargaba. Kar wani abu ya zo ya same su.
Kaman Hamida ta san abunda ta ke tunani. "Ki kwantar da hankalin ki, ki yi fatan alkahairi. In sha Allah babu wata matsala."
"Allah Ya sa."
A ƙofar hostel su ka rabu da Sumayya. Itama Amina Hall ta ke. Suna isa ɗaki kowa ya bi lafiyar gado.
Washegari a aji Maryam ke tambayar Zuby ya bata ganta wurin tutorials ba.
"Har na fito na ji cikina na kartawa."
"Wayyo. Sannu, ya jikin yanzu?"
"Da sauƙi. Kin je tutorial ɗin kenan."
"Na je. Ya iya koyarwa sosai Zuby. Hamida ma ta yi mai magana ya ce zai yi mana karatu mu kaɗai. Ki zo muje, yau da dare zai fara mana."
"A'a, ni ina da mai koya mun."
Maryam bata san lokacin da ta juyo ta kalleta ba. "Kina da me koya miki?"
"Eh, wani friend ɗina ya haɗa ni da shi. Wurin sati biyu ma kenan."
Maryam ta jinjina kai. "Okay. Toh shikenan."
Daga nan bata sake ɗauko zancen karatu ba suka nufi ajin su na gaba.
Da dare ƙarfe takwas a Faculty Of Engineering ta musu. "Toh yanzu ina zamu gan shi?"
"Me kike ci na baka na zuba? Kiran shi zan yi ko Hajiya Maryam." Hamida ta ce tana ciro wayarta. "Hello? Gamu nan wurin Wolfson Theatre....okay toh... Gashi nan zuwa. Shikenan?"
Maryam bata ce mata komai ba sai murmushi da ta yi. Basu daɗe tsaye a wurin ba sai ga shi ya iso.
"Sorry na bar ku a tsaye."
Hamida ce ta amsa shi. "Babu komai. Ina wuni."
"Lafiya lau. Hamida ko?"
Hamida ta gyada mai kai. Sumayya da Maryam ma suka gaishe shi sannan ya ce su biyo shi. Wani aji suka je babu mutane sosai, kuma wurin shiru kowa ya maida hankali kan littafin da ke gaban shi. Mutane da yawa sun daga mai hannu da suka shiga. Daga gani wannan mai jama'a ne.
Khalid ya nuna musu dogon tebur ya ce su zauna. Maryam suka saka a tsakiya. Shi kuma ya dauko kujera ya sa a gaba yanda zai riƙa fuskantar su. A saitin Maryam ya saka kujeran, ya lura da yanda ta kauda kai da sauri dan kar su haɗa ido.
Dagaske bata gane shi ba ko tsabar kwarewa a shariya ce? Dan tun jiya bata nuna alamun ta san shi ko sun taɓa haɗuwa ba. In har bata gane shi lallai a gaisheta. Shi yana nan ya kasa mance fuskarta ito ko riƙe kamanninsa bata yi ba.
"Mu cigaba daga inda muka tsaya jiya ko a dawo daga farko?"
Ba dan ita ba ya san ba zai taɓa yarda ya koyar da wasu karatu ba. Abunda bai taɓa yi ba kenan tunda ya shigo makarantar. Abokanshi dai yana yi musu bayanin abunda ya shige musu, wannan in ka tambaya ba zai taɓa cewa a'a ba. Amma wai wasu su same shi ya zama tutor ɗin su musamman mata? Bai taɓa ba. Sai a kan Maryam. Dan albarkacinta su ka ci.
"Mu fara daga farko idan ba damuwa." Wacce ta ce mai sunanta Hamida ta ce.
"Ba damuwa. Duk abunda baku gane ba kar ku ji nauyin tambaya."
Kaman jiya dalla-dalla ya yi musu bayani. Bayan ya gama revision ɗin abunda ya yi musu jiya ya ɗaura daga nan. Bayan awa ɗaya ya ce bari ya barsu su ɗan huta sai su cigaba.
Bayan ya bar wurin Sumayya ta ce, "Wallahi mu riƙe shi hannu bibbiyu. Kun ga yanda ya ke kwararo bayani. Lecturer din mu ashe duk shirme ya ke yi."
Hamida ta zunguri Maryam da gwiwar hannunta. "Toh su Yaya Maryam ma su cewa kar ayi mai magana."
Ai kuma ta shiga uku wurin Hamida. "Ai na janye ko?"
Hamida ta kyalkyale da dariya. "Da kar ki janye mana."
Bayan minti goma sai gashi ya dawo ya ɗaura daga inda ya tsaya. Dukan su babu wanda ya lura lokaci ya ja sai da wayar MK ta yi ƙara. Bayan ya gama amsawa ya ga har sha ɗaya ta yi.
"Subhanallah! Ashe dare ya yi haka. Sha ɗaya. Karatu ya yi dadi ko?" Duka su ka yi dariya. "Zamu tsaya a nan sai gobe. A sati zamu riƙa karatu so uku sai ku zaba ranakun da suka yi muku. Sannan bayan Chemistry da Physics babu wani course da kuke so mu yi?"
"Sai Maths." Maryam ta ce. Tunda ya yi musu tayi ai ba sa ƙi karɓa ba.
MK ya gyada kai. "Toh shikenan. Wani Maths din kuke yi?"
"103 da 105 amma ni bana 105."
"Kin huta da calculus kenan. Zamu haɗa da Maths din in sha Allah. Wani hostel ku ke? Mu je in raka ku dare ya yi."
"Ba sai ka raka mu ba. Zamu iya komawa da kan mu." In ji Hamida.
MK ya girgiza kai. "No, it's not safe."
Aikuwa makarantar ta yi tsit. Faculty Of Engineering da ɗazu ya ke cike kamar kasuwa yanzu babu kowa. Ko a hanya ma mutane kwarara kawai su ka gani. A gaban hostel su ka yi sallama dayake Sumayya a ɗakin su zata kwana.
"Mun gode." Su ka ce a tare.
Khalid bai tafi ba sai da ya tabbata sun shiga ciki. Hanyar hostel ya ɗauka shi kaɗai tunanin Maryam ya yi mai rakiya har ɗaki. Tun haduwarsu ta farko ya san cewa she's a calm person. Yau ya sake tabbatar mai da hakan. Kuma ya lura bata da son hayaniya ba kaman ƙawayenta. Ya yi musu tambayoyi akan abunda ya koya musu, yanda muryarta ke fita a hankali yayin da take amsawa ya tsaya mai a zuciya. Bai ƙi ba ta yi ta magana shi kuma ya yi ta sauraronta.
"Khalid haka ka koma?" Ya tambaya kan sa a fili yana dariya.
Mace bata taɓa daukar mai hankali ba haka har ya tsinci kan shi da yawan tunaninta.
"Maryam." Ya kira sunanta a hankali.
Har ya ƙosa gobe ta yi.
•
•
•
•
•
ʼYar mitsilar Abba fa an yi kamu🤭😂
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top