10.
Zagwaɗi bai bari Maryam ta fahimci mai tafiyarta makaranta ke nufi ba sai da taga zata shiga mota ʼyan uwanta na ɗaga mata hannu.
Yanzu ana nufin shikenan wani gari zata tafi baza ta riƙa ganin su kullum ba?
Tashin hankali!
Ita da ko sama da sati ɗaya bata taɓa yi a wani wuri ba. Anti Jamila da Anti Firdausi sun yi fushi har sun gaji akan rashin zuwanta hutu gidajen su. Sai dai Safiya da Zee su je, ita ko tana gida.
Tun ɗazu take maƙale jikin Umma ta ƙi sakinta. Tare da Hamida za su tafi Babanta ya bada mota a kai su. Umma ta ce ba sai ta yi rakiya ba tunda Maman Hamida zata je. Amma a zahiri bata so ta je ne dan ta san idan ta je abu ɗaya cikin biyu ne ze faru. Ko ta ƙi tahowa ko ta sa ʼyarta cikin mota su dawo tare.
"Maryam shiga mota haka nan kina bata mu ku lokaci." Mama ta ce tana kamo hannunta.
Da kyar aka janye Maryam daga jikin Umma. Idanuwan su duk sun yi ja jawur musamman na Maryam. ʼYan uwanta ta sake rungumewa. Idi yana wani cijewa amma daurewa ya ke yi kar ya yi kukan shima. Ɗan auta Bashir ko tun ɗazu ya ke sharar ƙwalla.
Jiya da dare Mama ta yi mata nasiha sosai dan haka ta ce mata, "Kar ki manta me na ce miki, kin ji?"
"Toh Mama."
A haka aka rabu rai babu daɗi. Har suka kai Jaji Maryam bata daina kuka ba. Hawaye kawai ke zuba tana gogewa da tissue. Babu wanda ya ce mata komai aka barta ta yi kukan mai isarta.
Da misalin sha ɗaya na safe su ka isa jami'ar Ahmadu Bello da ke Samaru a garin Zaria. Tunda ta hango ƙaton tambarin makarantan da ke bakin get zuciyarta ta fara dukan uku-uku.
Hamida ta kalleta ita kuwa murna da farin ciki ne su ka bayyana a fuskarta sabanin Maryam da tsoro ya kamata.
A gaban Ribadu hostel su ka tsaya. Gaban hostel din cike da dalibai mata da kaya niƙi-niƙi. Wasu sababbin zuwa ne kaman su, wasu kuma returning students ne wato 'yan aji biyu zuwa sama.
Motar dama daga Anti Nafisa a gaba sai Maman Hamida da yaran a baya. Anti Nafisa ta fara buɗe ƙofa ta sauka sauran su ka bita. Hamida na ta waige waige.
Mata ne suka rufe motar lokaci ɗaya, tsaffi da ʼyan matasa suna son ɗaukan kaya. Wata har ta kai hannu zata buɗe bayan motar dreban ya yi saurin dakatar da ita.
"Inna tsaya mana."
Anti Nafisa ta koma wurin kayan. "Mutane huɗu sun isa dan Allah."
Nan fa suka fara gardaman su waye zasu ɗauka. Wasu sun dage sune a kan layi sauran kuma sam sun ƙi yarda. Anti Nafisa ta nuna wasu su huɗu ta ce su matso sauran su yi haƙuri. Nan suka fara ƙunƙuni, wanda ta zaɓa ba su bane a kan layi.
"Ku dai abunda kuke yi wallahi ba ku kyautawa. Yanzu fa kuka dawo daga kai wasu kayan. Ni da Ladidi ya kamata mu fara ɗauka. Amma ku cigaba, in da rabon mu babu wanda ya isa ya hana."
Ɗaya a cikin su ta yi ta mita. Duk cikin su abun ya fi bata haushi. Wata motar na tsayawa su ka koma kanta aka saki babin ta su.
Akwatinan su da ghana-most-gos aka daurawa matan nan a kai. Maryam na gani kaman ba za su iya ba musamman wata da girma ya kamata sosai. Sauran kayan mara sa nauyi irin su bokiti Maryam da Hamida su ka ɗauka.
"Wani block ne?" Ɗaya a cikin su ta tambaya.
"Block C, links amma, room 23," Anti Nafisa ta amsata. Dayake ita ta samo musu ɗakin. Su ko block din basu sani ba bare lambar ɗakin dan ko takardun sheda bata ba su ba, magana ta yi aka a basu ɗakin.
Ƙofar da zata sada su da cikin hostel din su ka nufa. Sai da matan nan suka sauke kayan security ɗin wurin su ka duba sannan su ka ƙara ɗaurawa a kai su ka yi gaba.
Yara mata nata kai kawo a cikin hostel. Maryam bata taɓa shiga hostel ba tunda ba ta yi makarantan kwana ba, saboda haka abun duk baƙo ne a wurinta. Wurin yafi yanda ta ke tsammani girma. Ga ʼyan mata na ta hada-hadar su, wasu ma wanki su ke yi.
"Anti Nafee wasu har sun fara wanki," Maryam ta ce cike da mamaki." Duka yaushe aka dawo?" Ko sati biyu ba'a yi da dawowa makarantan ba fa.
Anti Nafisa ta yi dariya. "Wata ƙila suna da nisa ne sun bar kayan a makaranta bayan an yi hutu. Kinga idan sun dawo dole su wanke su."
Sun iso block C inda Anti Nafee ce a gaba har su ka isa ɗakin a hawa na biyu. Matan nan huɗu suna tsaye a bakin ƙofa sun sauke kayan suna jiran isowar su.
Anti Nafee ta ciro key daga cikin jaka ta buɗe kofar. Ɗakin bai da girma sosai da gadaje guda biyu na kwanan mutum ɗaya. Ɗaya a gaban locker mai ƙofa uku ɗayan kuma na bayan ƙofa. Sai wani tebur da kuran da ke kai bai boye irin baƙin da saman ya yi ba.
Maman Hamida ta toshe hanci saboda kurar da ta taso. "Wai, dole sai an wanke ɗakin."
"Hajiya muna wanke ɗakin ma idan kuna so." Ɗaya daga cikin masu kawo kayan ta ce.
Maman Hamida ta ce to su yi sauri su share. Ƙasa suka koma akwai wurin zama su ka zauna. Maryam da Hamida nata ƙus-ƙus suna kalle kalle.
Anti Nafee ta miƙe. "Ni ba na manta ba ku yi clearance ba. Mama bari mu je mu dawo."
Chan hanyar shigowa hostel din su ka koma. A hannun dama akwai ofis inda dalibai su ka yi dogon layi. Anti Nafisa ta ce su jira a nan tana zuwa. Kutsawa ta yi ta shige bayan minti biyar sai gata ta dawo. Ta ce su biyota. Suna ƙoƙarin fara shiga matan da ke wurin su ka fara ƙorafi. Haka dai har su ka shiga cikin ofis din. Tebur uku ne ko wanne an yi layi a gaba. Na hannun dama su ka nufa matar na gamawa da yarinyan da ke gabanta ta ce su Hamida su matso.
Wani littafi ta ciro ta ce su nemo lambar ɗakin su. Suna nema matar na hira da Anti Nafee wanda daga gani akwai sanayya sosai a tsakanin su. Hamida ce ta nemo lambar ɗakin matan ta ce su rubata sunayen su. Ɗakin na mutum biyu ne suna rubutwa ta ja layi a ƙasa.
"Na baki mukullin ko Nafeesa?"
"Eh, har ma mun kai kaya."
"Madallah. ʼYan mat, welcome to ABU. Idan wani abu ya taso za ku iya zuwa ku same ni a nan ofis din kun ji."
Su ka gyada kai sannan su ka yi mata godiya. Wato komai a ƙasarnan in ka san wani shikenan. Da yanzu haka za su bi dogon layin nan da bai da rana ƙarewa. Ga shi sai kokowan shiga ake yi.
Gaban block C suka koma inda su ka bar Maman Hamida a zaune. "Har an yi clearance din?"
"Mama ai muna da Anti Nafee, ba mu da matsala." In ji Hamida.
Anti Nafisa ta dungure mata kai. "Za ki gane shayi ruwa ne yarinya. Bari mu tafi."
Sama su ka koma inda su ka samu matan nan sun wanke ɗakin sun goge shi tas kaman ba shi ba. Mama ta sallame su suna ta godiya. Ko ina sun goge babu ha'inci. Har cikin lockers din sun goge tas.
"To ʼyan makaranta sai mu ce Allah Ya bada sa'an karatu," Anti Nafi ta ce daga bakin ƙofa. "Mama ya kamata mu kama hanya kar dare ya mana."
Mama ta yi dariya. Hamida ta waigo da sauri. "Kai Anti Nafi! Ko kaya fa ba mu shirya ba, kuma ba mu je mun karɓo admission letter ba."
"Wannan duk da kan ku za ku yi ai. Mu mun gama na mu, ko ba haka ba Mama."
"Hakane kam."
"Anti Nafi!" Hamida ta kira sunan yayarta cike da shagwaɓa. "Dan Allah ki bari, duka ƙarfe nawa ki ke cewa dare ya yi."
Sai da Mama da Anti Nafi su ka gama ja musu rai sannan aka hau shirya kaya cikin locker. Babbar mai murfi biyu su ka jera kayan sawan su, ɗayan kuma aka loda mata kayan abinci.
"Yara ʼyan gata, sai ka ce wanda aka turo cin abinci," Anti Nafi ta riƙe haɓa tana bin kayan dankallo, "wannan kayan ai zasu buɗe ƙaramin shago. Mu dai lokacin mu ba a haɗo mu da kaya haka ba."
"Kai Nafisa ki ji tsoron Allah," Mama ta yi dariya. "Ke da kullum kina hanyar gida diɓo kayan abinci."
Sun gama shirya komai. Akwatinan aka daura su saman locker din. An haɗa musu risho an saka lagwani sannan aka ɗura kananzir a ciki. Mama ta ce su yi amfani da risho ɗaya kawai ba sai an fasa wani ba. Anti Nafee da ta san kan makaranta ta siyo musu leda, aka shimfida a ɗakin ledar ta rufe simintin gaba ɗaya.
Ƙarfe biyu har sun kammala. Ɗaki ya fito tsab kaman ba shi ba. A gurguje Anti Nafi ta raka ko waccan su department dinta ta karɓa admission letter. Dayake an daɗe da fara karɓan admission letter din ba su samu layi ba, a department din su Hamida ne ma aka ɗan bata lokaci.
Anti Nafi ta nuna musu lecture halls din da yawanci a nan ʼyan aji ɗaya su ke classes.
Gaban Ribadu Hostel su ka dawo inda mota ke jiran su. Wasu sabbin hawaye ne su ka cikawa Maryam ido. Mama ta rungumeta. "Haba Maryam, kukan ya isa haka. Ko dai in maida ki wurin Umma?"
Maryam ta yi dariya tana share hawayenta. Mama da Anti Nafee su ka yi musu sallama haɗi da jan kunne sannan su ka shiga mota. Itama Mama sai ta ji tausayin yaran ya kamata. Girman kenan.
Basu koma ciki ba har sai da motar ta ɓacewa ganin su. Hamida ta kalla Maryam da ke ta matsar kwalla. "Haba Maryama, sai ka ce ke kaɗai ce, kina da ni fa ko kin manta. Yanzu mu zagaye makarantan ko mu bari sai gobe?"
"Mu bari sai goben."
Hostel su ka koma Hamida na ta ƙoƙarin kwantarwa da Maryam hankali. Ita ko a jikinta, murna ma ta ke yi. Ɗaya daga cikin matan da su ka kawo musu kaya zata riƙa dibo musu ruwa. Har ta cika musu drums da bokitan wanka. Ba su koma ɗaki ba sai da su ka zagaye hostel ɗin gaba ɗaya. Ashe hostel biyu ne a wuri ɗaya. Akwai wani chan ciki Alexandra Hall.
Bayan sun dawo Maryam ta ɗauki buta zata yi fitsari. Nan fa ake yinta. Dama haka bayin makaranta ya ke babu ƙofa? Wurin wankan buɗe ya ke. Da sauri ta kauda kai sakamakon wata da ta gani haihuwar uwarta tana wanka. Ita ko ko labule ai sai ta yi da zaninta, Maryam ta riƙa mita a zuciya.
Ta yi fitsarinta ta koma ɗaki. Hamida ta cire atamfar da ta zo da ita ta saka rigar material mara nauyi. Itama chanza kayan ta yi sannan su ka ci abinci. Umma ta yi musu haɗadɗiyar miya da ta soyu sosai ta ji naman shanu da na kaza. Sun taho da farar shinkafa da aka dafa amma ita ʼyar kaɗan ce.
Bayan sun gama cin abinci Maryam ta yi waya da ʼyan gida. Sai da ta gaisa da kowa hankalinta ya kwanta. Zee na ta zuba sai da Umma ta ƙwace wayarta. Bayan ta yi gama waya da su, ta kira Anti Firdausi da Anti Jamila. Suma sun daɗe kafin su ka yi sallama. Tsintar kanta ta yi da kiran Baba Zubairu. Bugo ɗaya kuwa ya dauka.
Bata taɓa kiran shi da wayarta ba dan haka bai da lambarta. "Baba Maryam ce," ta ce bayan ta gaishe shi.
"ʼYar mitsila ke ce?"
Maryam ta yi dariya. "Ni ce Baba. Dama na kira in faɗa maka na tafi makaranta."
"Masha Allah har kin isa Zaria, Allah Ya bada sa'ar karatu."
"Ameen Baba. Sai anjima."
"Sai anjima Maryam. Nagode sosai. Wannan numbar ki ce?"
"Eh."
"To bari in yi saving. A maida hankali kin ji. Allah Ya bada sa'a."
Ta amsa da Ameen sannan su ka yi sallama. Bayan ajiye wayar ta yi ƙara alamar shigowar message. Kati aka saka mata har dubu biyu. Tasan aikin Baba Zubairu ne. Nan da nan ta kira ta yi mai godiya dan kar ta manta.
Farfajiyar ɗakin suka fito suna kallon mutane.
"Da kin bari mun zagaye makarantan."
"Saurin me kike yi? I am sure makarantan zata zo ta ishe ki. Gobe Sunday ba sai mu je ɗin ba. Ni yanzu jikina ma ciwo ya ke yi."
"Sannu. Sai mu duba time table daga nan. Wallahi na so course ɗin mu ɗaya. Kinga shikenan tare za mu riƙa fita lectures. Yanzu kuwa dole sai mun yi sababbin ƙawaye."
Maryam ta girgiza kai. "Ke kuma matsalar ki kenan. Sababbin ƙawaye?"
"Eh mana. To hakanan mutum zai riƙa zama a aji kaman maye. Dole sai kin samu ƙawa mana. Ke ce ma abun tausayi ai."
"Ban gane abun tausayi ba, ciwo na ke yi?"
Hamida ta yi dariya. "Ni ban ce ciwo ki ke yi ba. Amma Maryam tsakanin ki da Allah kina da wata ƙawa bayan ni da su Sofi?"
"Gori za ki mun saboda kina da ƙawaye Hamida Bello?"
Hamida ta sa hannu ta tureta. "Dalla chan. Amma maganar gaskiya, ke ma kin sani. Dole ki saki jiki ki yi mu'amala da mutane idan ba haka ba za ki zama loner.
"Na ji kar ki cinye ni." Maryam ta ce tana harararta.
Ita bata damu da sai ta yi ƙawance da duk mutumin da ta haɗu da shi ba. Hamida ce sarkin kwashe kwashe. Ita magana da mutane ma idan ba ya zama dole ba bata yi. Ta gwammace ta yi zamanta ita kaɗai.
Da dare Maryam ta kasa barci. Sun ci abinci sun wanke kwanuka sannan kowaccen su ta haye gado bayan an rufe ƙofa. Hamida irin mutanen nan ne da barci ke dauke su suna kwanciya. Tuni ta yi barci ta bar Maryam da zare ido cikin duhu.
Sai ta runtse ido sai ta ji kaman wani abu yana tunkaro ta. Gashi an ƙulla musu net da bata saba da shi ba. Da ya taɓa mata jiki sai ta firgita.
Addu'a babu wanda bata karanto ba. Har kai ta rufe da bargo, gashi sai zufa ta ke yi. Daga ƙarshe dai fitilar wayarta ta kunna cikin bargon. Shine ta samu har barcin ya ɗauketa. Sai dai ko minti talatin bata jin ta yi da fara barcin Hamida ta tasheta lokacin sallah ya yi. Kaman ta ƙwala ihu. Dole ta haƙura ta yi sallah. Tana idarwa ta haye gado ko adhkar bata tsaya yi ba. Ta ci sa'a wannan karon tana kwanciya barci ya yi awon gaba da ita.
Ba ita ta farka ba sai ƙarfe sha biyu saura. Hamida har ta yi wanka abunta. "Sannu sleeping beauty kin tashi."
Maryam ta yi miƙa tana salati. "Ke jiya kasa barci na yi."
"Na manta ke fa matsoraciya ce kaman farar kura. Me ye abun kasa barci a nan? Ni kam harda munshari."
Maryam ta sauko daga kan gado ta zura slippers. Hularta da ta faɗi garin barci ta dauka ta maida. "Na ji ki ai. Kina barci kaman kasa, da sace ki za'a yi da tuni an yi."
Hamida ta fashe da dariya. "Ke kika sani. Ga abinci nan na rage miki, sai ruwan zafi cikin flask. Ki yi sauri dai ki yi wanka kafin ayi gaja-gaja da bayin."
Kaya ta cire ta ɗaura towel sannan ta saka wani ƙaramin hijabi a sama. Yau ga Maryam zata yi wanka a bayin makaranta. Ta cika bokitin fam da ruwa sannan ta dauko jakar da ke dauke da soso da sabulu. Da towel ɗinta ta yi labule duk da bai wani sitirceta yanda ya kamata ba. Dukda haka dai da babu gwara babu daɗi.
Bayan sallar azahar su ka fita zagaye makaranta. Hamida ce ʼyar jagoran tafiyar. Maryam binta kawai ta ke yi. Department din su Hamida su ka fara zuwa ta kwafo time table ɗin sannan su ka nufi department of biochemistry. Ginin department ɗin su Maryam ya sha banban da sauran.
A hawa na biyu ne su ka ga notice board me dauke da time table din. Maryam itama ta kwafa. Ta gama tana shirin maida littafin jaka ta ji an taɓata. Ta firgita tunda tasan ba Hamida ba ce, ta sauka siyan ruwa.
"Yi haƙuri na tsorata ki,"yarinyar ta ce. "Dan Allah ke ma fresher ce? Biochem?"
"Eh," Maryam ta gyada mata kai.
"Ko kin san inda zan karɓa admission letter?"
"Yau lahadi ai, sai gobe."
"Oh," yarinyar ta ce tana gyara gyalenta da yake ta faɗuwa. "Amma ki nuna mun wurin, gobe sai in dawo."
Maryam ta nuna mata ofis din sannan ta sauka inda Hamida ke jiranta. Ranan dai a titin makaranta su ka ƙare. Su je chan, su je chan. Siye siye kuwa ba'a magana. Kai da ka gan su ka san Jambitos ne.
Ranan Monday dukan su ƙarfe bakwai su ke da aji. Tunda asuba su ka yi wanka. Bayin ba'a wanke ba ya yi datti ga wari amma haka su ka toshe hanci su ka yi wanka. Jiya da dare sun dafa taliya. Ita suka ɗumama.
Hamida CHEM 101, Maryam kuma nada BIOL 111. A gaban department of Biological Science su ka yi sallama. Hamida venue ɗinta FSLT ne babu nisa, Maryam kuwa sai ta je chan da nisa OBL.
Ita kaɗai ta ke tafiyarta ta goya jakarta a baya. Ko da ta isa wurin ta same shi cike da daliba. Gaban babu wuri dole ta shige chan ciki. Maryam ba tsawo ba tunda ta zauna ko kallan malamin bata gani ba har ya gama lecture na awa biyu. Wasu nata rubutu itama ta fara hayaniya ya yi yawa ta daina jin abunda malamin ke cewa. Tunda ta shiga makarantar boko bata taɓa zaman baya ba sai yau. A takaice de zaman banza ta yi.
Malamin na fita wasu daliban su ka fita a guje. Maryam ta firgita sosai. Sai daga baya ta gane ashe wai gudun su samu wuri a ɗayan ajin da za'a yi karatu su ke yi.
Allah Ya gani ba zata wani fara gudu cikin makaranta ba. Hakanan kawai ana zaune ƙalau.
Shima dai wannan ajin sammakal. Bata tsinci komai ba. Tashin hankali, yau fa ake yinta. Ƙwalla ta ji sun cika mata idanu. Idan a haka zata yi karatun ai zero kawai zata riƙa ci. Dama haka karatun jami'an ya ke? Akwai matsala.
Duka classes ɗin ranan zuwan banza ta yi. Washegari ma haka. Gata ita kaɗai kamar mayya. Sai yanzu ta ke ganin gaskiyar Hamida.
Haka satin ya ƙare Maryam ba zata iya cewa ga abu ɗaya da ta fahimta ba. Bata cuci kanta ta tambaya Hamida ita ya ta ke yi.
"Tuni na yi ƙawa Sumayya in faɗa miki. Ta yi SBRS, ta ɗan san kan abubuwan. Ai ba'a cewa dole sai an zauna kan kujera. Da kin shiga kawai ki sa littafi gaban seat ki yi zaman ki, nan ne za ki fahimci komai. Amma yaushe za ki ce sai kin zauna kujera banda abunki Maryam."
Maryam ta ɗauki shawarar Hamida sai a lokacin ne ta fara fahimtar inda aka dosa.
Ranan alhamis ta fito aji ta ji ana kiran, "baiwar Allah! Baiwar Allah!" Ba ta yi tunanin da ita ake ba sai da ta ji hannu a kan kafaɗarta. Yarinyan nan ce da haɗu da ita ranan da ta je kwafo time-table. Baƙa ce sosai sannan tana da jiki amma da tsawonta.
"Yi haƙuri ban san sunan ki ba. Sunana Zubaida."
Maryam ta yi murmushi ta faɗa mata sunanta.
"FSLT za'a yi class ɗin?"
"Eh. Ba ki da time table ne?"
"Wallahi na manta shi a ɗaki kuma ban riƙe ba."
Sauran lectures ɗin ranan tare Zubaida ta yi su. Sunanta Zubaida Salis asalin su ʼyan Yobe ce amma suna zama a nan Zaria. Itama mahaifinta ya rasu amma shi be daɗe da rasuwa ba.
Sanadiyar ƙawancen Maryam da Zubaida kenan. Sai ya zamana kullum tare su ke tafiya lectures. Zubaida a Amina Hall ta ke idan ta fito sai ta jira Maryam a ƙofar hostel.
Hamida ta yi ta tsokanarta wata rana Maryamah ta yi ƙawa. Sun saba sosai da Zuby kaman yanda ta ce ana kiranta a gida. Yarinyar bata da matsala akwai ta da faram-faram sannan tana son karatu abunda ya ƙara haɗa jininta da na Maryam kenan.
•
•
•
•
•
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top