Talatin da uku

Kaduna, Nigeria.

Barr Mustapha dauke da dan shi haydar a jikin shi, ajiye manuscript in yayi gefe yana kara kallon yaron nashi da kyau da ke ta faman wasan shi hankali kwance. Bai tunanin duk halun irin na mimin shi zata iya barin dan ta Haydar cikin irin gararamban Rayuwan da Suhaiman tayi fama dashi. Shi kam yafi yarda ma ace littafine dai ta kirkira hakannan ta rubuta. Eh ya sha jin labarin wahalan kishiyan uwa da yara da dama ke sha, sai dai bai taba gani ya faru akan wanda ya sani ba. Shi kam saboda irin haka ne yake jin mimin ta ishe shi rayuwa sai dai irin sabbin halin da take ta faman tsiro dasu ya ke sa shi jin ba shakka zai iya sa ma kudurin alkalami ya ja layi akai.

Dai dai lokacin kuwa maryam inta farka daga nauyayyan baccin da take ta faman yi. Ya san ta kan yi bacci sosai amma bai kai bacin na yau ba. Shi da ya dawo bayan wasu kwanaki daga wani gari dole yana bukatar matar shi amma ina bai samu daman hakan ba saboda mugun baccin da take tayi. Kallon ta yayi yana wani nazari a zuciyan shi, tabbas mimin haka ta mishi a cikin Haydar. To kuwa ba shakka ya fara zargi yanzun ma tana dauke da ajiyan shi. Hannun shi yasa akan wuyan ta yana kallon cikin idanuwan ta, nan da nan kuwa ta sha mur hade da fadin "Ba zanje asibiti ba lafiya na kalau" tabe baki yayi ya hada mata da harara "ko baki je asibiti ba ni xanje chemist, am suspecting something"

Dan zaro idanu tayi amma dake ta fara sanin kan duniya sai tace mishi "Ba sai ka sha wahala ba ma ai, am two months pregn..." Bai tsaya sauraran karshe zancen nata ba yayi saurin mikewa tsaye, mutna ne yayi saurin mamaye kan fuskan nashi saidai zanceb da ya biyo baya yasa annurin shi gabadaya daukewa. "Ni fa wlh ban shirya kara haihuwa ba, Haydar ma nawa yake? I can't believe drug in da nake sha bai yi min aiki ba" kallon ta kawai ya dinga yiyana jin kaman yaje ya sheke ta da duka, a gaskiya maryam ta fara bashi tsoro ma shi. Abinda ya daite mishi kai a matsayin shi na lawyer ya sha ganin mata sun kawo karan mijin su akan tilasta musu shan maganin hana daukan ciki bayan su suna bukatan hakan, ko kuma wanda suke son rabuwada miji saboda bai haihuwa. Amma shi nashi matan da kanta mata ke shan maganin ba tare da sanin shi ko yardar shi ba. "Mimi me ke faruwa da ke?" Kokarin danne zafin da ya keji yana taso mishi yayi sanin ba zai amfana mishi komai ya mata wannan tmbyn. Kokarin bayani ta fara mishi,  sai yanzu ya dan fuskance ta. Duk dai bayanan bai wuce na yanda ba taso ta hada yara biyu ba, Haydar ma bai gama girma ba kuma tazo tana wahala biyu. Most importantly a gare ta kuwa shine jikin ta, ya fahimci hakan ne saboda yanda ta ke ta emphasizing abun.

Murmushin dole yayi yana kallonta yace "ni kam tun yaushe na sanki ne?" Bata bashi amsa ba don haka ya cigaba da cewa "Tun kina ganiyar neman tsokanar ki lokacin kina yar kankanuwar ki don haka ki daina tunanin wani sauyi daga gareni a gaba. Sannan bance miki planning ba abu bane mai kyau sai dai kuma laifin shine zuwa da kika yi kika fara ba tare da shawara dani ba bayan kuma kinsan ina da hakki akan haka" still dai ba tace komai ba don haka ya mike again sannan ya kalle ta da kyau "ki tashi ki wanke idanun ki muyi maganan fahimta a tsakanin mu, ni dai gargadin da zan miki shine in baki canja wannan halayen da kika kirkiro lokaci guda ba to kuwa tabbas zaki ga abinda baki taba tsammani ba. Bazan ce miki ga abinda zai faru ba amma the worst can happen" ta dan tsorta jin yanda yayi maganan iya gaskiyan shi, ita kam ba ta saba ganin hakan a tattare dashiba don haka tayi kokaron maida abun wasa "Wlh gabadaya ka canja" dan turo bakin ta tayi. Bai kuwa san sanda ya saki murmushi ba don duk sanda tayi haka ji yake ta burge shi sosai. Hannun shi yasa ya dan jawo bakin kafin yace "ke ma in canjawa kika yi ai maman baby" maganan yayi yana kai hannun shi kan cikin ta. "Ina son yara sosai maryam sodon't push me, in har baza ki bani zan nemo su ni kuma daga wani tsotsan" cikin kwanciyar hankali ya mata maganan. Ya kuwa hango tashin hankali kwance a cikin idanun ta, sam mimin shi ba ta kaunar maganar kishiya. To dake shi in ma ba ra'ayi  yi gare shi ba, daman Suhaima ce ta tsole mishi ido da kyawawan halayen ta but kwana biyun nan barin ma da ya san labarinta ya fara ja baya da abun. To daman fa? Kana tsammani abu ne sai kuma kaga akasi mai girma daga wurin shi. Koma dai menene he is still willing to help her. Ba kuma shi ya kara samun sararin cigaba da karanata labarin taba sai da ya shiga office insu da ke a garin Kaduna.

Rayuwata

Babi na shidda


Wani hutu da muka yi JSS2, second term. Wurin karfe Tara da rabi na dare Anty Yana ta bani aiken bread, sugar da lipton. Sanin ba daman mata musu, gashi Abbah bai gari ya sa na amsa na fito a tsorace. A kofan gidan Al-lawan ne. Zaune da abokanan shi suna hira, ban bi wani ta kansu ba nayi Saurin wucewa burina in yi Sauri inje in dawo.

Na wuce su kadan naji kaman ana bina, ban damu in waiga sai ma kara saurin da nayi. "Yayi ke sauri ko baki son rakiyan ne?" Daga baya na naji maganan ta fito. Na San muryan Al-lawan bane saboda haka na ki juyawa. Sauri naji an fara har sai da ya kamo ni yace "ban miki sallama ba ko? Afuwan beauty Assalamu Alaikum" a hankali na juya na kalli gefe na, na dauka daya daga cikin abokan Al-lawan ne ga mamakina wannan kam bakon fuska ne ban San shi ba. Gudun magana ya sa na amsa sallaman nashi. Daganan ba Wanda ya kara magana cikin mu har mu kaje shagon na siyo abinda zan siyo mu ka dawo. Bakowa a kofan gidan, duk abokanan Al-lawan in sun watse. Har kofan gidan ya raka ni "mu kwana lfy Suhaima" bance mishi kala ba na shiga gidan, na kaiwa Anty Yana sakon ta. Kallon Lipton in tayi tace "ke kam na rasa kwakwalwa irin taki kin taba ganin mun sha top tea ne a gidan nan? Kin sanni kin San ban son iskanci don haka ki koma ki canjo maza" sunkuyar da kai nayi cike da takaici na rasa abin yi, gabadaya tsabagen sauri yasa ban tsaya na duba abinda aka bani ba. A hankali na fara magana "Dan Allah Anty Yana kiyi hakuri wlh gobe da sassafe zan canjo"

Wani mugun tsaki ta je "Wlh Suhaima sai kin canjo Lipton in nan, gwara ma ki tashi ki tafi kafin dare ya kara yi, bana cike da iskanci, ke da kika yi gadon yawa ma har ke wani fadawa mutum dare? Uwarki tana can yawon duniya?" Wani tululin bakin ciki ne naji ya tsaya min a kirji. Na kan rasa dalilin da yasa har yanzu ban iya jurewa duk zagin da za ayi wa Ummi sai naji bakin ciki, sau dayawa abinda Adda Falmata ke using kenan tana ba ta min rai. Jiki a sanyaye na tashi na nufi wajen, idanuna sun yi ja kafin kace kabo na hawaye sun fara saukowa. Rayuwa kenan, da na dawo daga islamiyya Ummiy ba ta kara Bari na fita waje sai kuma washegari. Amma yau ni ake aika wurin karfe goma.

A haka na fita ina share hawayen da ke zuba daga cikin idanuna. Na danyi nesa kadan daga gidan mu naji kaman ana kallo na. Dago kai nayi na hango shi a tsaye, da dan nisa dani yana kallo na. Sauke kai kasa nayi na cigaba da kuka na, "Me kuma kika fito yi again?" Ban ma San ya zo inda nake ba sai maganan shi naji.

Na yi niyyan share shi sai kuma naga illan hakan, ko bakomai zai iya rakani kuma tabbas tsoro na keji.

"Lipton zan canjo, ba shi ne ake so ba" girgiza kai yayi "mu je in raka ki, kiyi hakuri komai lokaci ne watarana sai labari." Wannan karon ma har mu kaje shagon mu ka dawo ba Wanda ya kara magana, sai da mu kaje kofan gidan mu yace "Sunana Amir, sai da safe" juyowa nayi da murmushi akan fuskana na furta "nagode Ameer" gyada kai kawai yayi ya min alama da hannu akan in Shiga gidan.

Washegari ma haka ya kara faruwa har shagon ya rakani, a dawowa ya ke ce min "Al-lawan yace JSS2 kike a GG?" A hankali na amsa mishi da "eh"

"Beautiful young girl ashe na girme ki ma sosai" murmushi nayi, "ai daga ganin ka ma ba yaro bane"

"Allah da gaske beauty, SS2 fa kawai na ke"

"SS2 ba kawai bane, wani school?"

"New horizon" zaro idanu nayi "amma ba a garin nan ba?" Girgiza kai yayi yace "A Minna ne, Niger state?"

"Kuma tun daga nan kake tfy? Nasan da nisa" dariya ya min yace "beauty kenan da a garin nan nake ai da kin Sanni, Kaduna na ke zama amma mu yan asalin garin nan ne hutu mu kazo" sai a lokacin na gane dalilin da yasa ban taba ganin shi sai lokacin da ya raka ni shagon. Tun daga ranar kullum dare Anty Yana ba ta fasa aike na na haka kuma Amir bai fasa min rakiya ba, muna tafe muna hira dashi. A hankali sabo mai karfi ya shiga tsakanin mu. Ba wani girma na Ameer yayi ba a lokacin ina sha hudu shi kuma yana sha shidda. Tun yana raka ni haka kurum ranar da mu kaje ya Sani dole sai da na dauki drink, ban so amma dole ya tilas tani, a cewan shi ban dauke shi  Yaya ba kenan.

5 days ya rage mu koma school, hakan yayi dai dai da komawan su Amir Kaduna. Ban san na saba dashi sosai hakan ba sai da ya ke fada min tafiyan nasu. Ji nayi gabadaya ba dadi, kaman in hana shi tafiya sai dai ba dama. Ana washegari za su tafi da yamma, ni kuma ina shirin tafiya Ajeyari Goggo ta aiko inje. Hanyan kwaltan da ke tsakiyan layin Wanda ba nisa damu na nufa duk da nasan nan in yafi wahalan samun abun hawa akan babban kwaltan. Har ga zuciya ta ina jin son in ga Amir na karshe dan na san zai yi wuya in kara ganin shi nan kusa. Hakan shine makasudin da yasa na nufi wannan kwaltan saboda kusa ya ke da gidan su. Gida uku ke tsakanin su da gidan su Adama, inda shi kuma gidan su Adaman ana tsallaka kwaltan shine.

Kaman yanda zata nafi minti Bakwai ina jira amma shiru ba abun hawa. "Suhaima ina zuwa?" Daga baya naji maganan. Mamman ne kanin Umar Sanda, shima abokin su Al-lawan.

"Ajeyari" na amsa, da ke ba laifi yana da kirki muna dan dasawa dashi.

"Yaushe za ki dawo?"

"Zan dan kwana biyu gsky" zaro idanu yayi yana kallona kaman Wanda na fadawa abun tsoro. "Suhaima Dan Allah dan jira ni a nan kar ki tafi pls" ko kafin in bashi amsa ya sa gudu sosai ya tsallaka kwaltan. Ikon Allah na tsaya gani ganin gidan kakannin Amir ya nufa.

Hankali na na kan hanyan gidan kwatsam! Naji an daka min duka. Ko ban duba ba na san Adama ce saboda ita kadai ne mu ke irin wasan da ita. "Ke koh ba nace ki bar duka na ba wai?" Harara na tayi sannan tace "ai ban hana ki ramawa ba ko? Ina zuwa?" Na bude baki zan amsa ta kawai naga Amir ya karaso inda mu ke da gudu yana ajiyan zuciya mamman na bayan shi. "Lafiya wannan gudun haka?" Adama ce ta fada tana bin su da kallo.

Nuna ni da hannu Amir ya fara yi yana fadin "ba ita bace za tafi ba ta min sallama ba" dauke idon ta daga kai na tayi tace "Suhaima ina za ki? Miye hadinki da shi?"

"Ajeyari, Goggo ke nema na" nan ta ke ta ba ta  rai "Dan rashin mutunci ki ta ko har titin kofan gidan mu ki wuce ba ki min sallama ba ko? Ni na taso da kokari na zan zo wurin ki, kin kyauta" saurin Fushi irin na Adama yana daure min kai. banga abun fushi a wannan  ba, sai dai tun kafin in yi magana ta tsallaka ta kama gaban ta. "Au ashe bani kadai kike shirin yi wa laifin ba Suhaima, kawar ki ce?" Gyade wa Amir kai kawai nayi.

"To muje ki bata hakuri" girgiza kai nayi "share ta ko naje yanzu ba za ta kula ni ba, in dai Adama ce da kanta za ta sauko ta neme ni"

"Shknn tunda kin ce hakan, ina da magana da ke muje in raka ki sai ki hau motan ta gwange. We need to talk and zanyi picking waya ta a gida"

Banyi musu duk da nasan nisan inda ya ke maganan. Ba wani nisa bane dashi tunda ana zuwa da kafa sai dai ni ban yadda in bi ta wurin saboda zagaye ne. Tun kafin mu karasa wurin gidan su ya kira da karamin wayan shi aka kawo mishi wayan mu ka wuce. "Kin kyauta fa Suhaima, you are planning on leaving babu sallama ko bayan kuma kinsan gobe zan bar garin nan.

" Ni ban san zan je fa, Goggo ta aiko inje. Kuma da na fito ban ganka ba"

"Gskyn ki kuma you have no other way to reach me, I think you need a phone"

"Nayi karama da rike waya fa" dariya ya min sosai sannan yace "wa ya fada miki, kina nufin yanzun in na tafi shknn ba zamu dinga gaisawa ba kenan?"

"Al-lawan na da waya in ka kira shi zamu gaisa ai"

"But, shknn dai" bai kara taso da maganan ba har mu ka isa bakin titin. I wasn't feeling comfortable for what am doing at that because am so young for that. Sai dai is not like i have anybody to tell me what is good or wrong. Ni dai a lokacin duk Wanda ya ke min faran faran ganin shi na ke a matsayin Wanda bai dauke ni wulakantaciya kaman yanda ake min a gidan mu. Lbr ya dinga bane, mostly duk na school in su ne ko kuma na Kaduna da friends in shi har mu ka isa bakin kwaltan.

"Ko in raka ki ne inje in gaida Goggo?"

"Aa nagode" nayi saurin fada.

Dariya yayi yace "matsoraciya kawai" wani dan karamin zoben azurfa ya Ciro mai matukar kyau a karamin yatsan hannun shi. Bai ce kala ba ya ja hannu na ya saka min a yatsa. "Don't you ever remove this, it a gift for our friendship" ba zan ce ga abinda na ke ji a lokaci, illa abinda ake kira "Infatuation" dayawa yan mate inmu a school su kan bada lbrn samarin su. Musamman Ajiddah da na fi kusa da ita, tana da saurayi daya da ta ke mugun so, ba a Sani ba a gidan su aboye su ke haduwa. A cewarta sun yi alkawari, so gani na ke kaman wannan ma normal ne kawai ni saboda ban taba bane. Sai dai ni Amir bai ce yana so na ba.

"Ni me za ki bani?" Da sauri na duba hannu na, bakomai sai zoben da ya sa min, haka kayana ba abinda zan iya bashi. "Shknn na biki bashi in na kara zuwa zan amsa" A haka muka rabu na nufi gidan Goggo shi kuma ya koma.

Muna kebewa da Ajiddah na ba ta labari. Dariya tayi da alamun abun ya mata dadi sosai tace "ban lbr ya yake?"

"Fari ne dogo"

"Yana da kyau"

Shiru nayi ina tunani can nace mata "yafi Yaya baba" tunowa da nayi ran da taga Ya baba tana koda min kyaun shi "Suhaima ashe haka Yayan ki ke da kyau? Suhaima Yaya baba kaza, suhaima kaza" sai da na gaji na share ta sannan ta bari. Yanzun ma bude baki tayi "keh! Kawata sai kace a film in indiya?" Ina mamakin yanda Ajiddah ke son mutane kyawawa duk da yanda ta ke matukar kyau. Hakan Anty nainah ta dinga "kinsan wannan Anty ta Ku kyakyawa ce kuwa Suhaima? Allah ta fi Halima kanwar ta kyau." Nan dai ta Sani a gaba sai da na ba ta labarin Amir da yanda mu ka hadu dashi. Na fada mata ba sona ya ke ba saboda bai fada min ba. Sam ta ki yarda a cewan ta zai fada ne ma.

Sosai Ajiddah ta dinga encouraging ina kan Amir, har sai da naji ya kwanta min sosai a rai. Daman an ce Wai duk abinda ka sa a ranka...

"Ya baki numban shi?"

"Aa amma ya ce zamu gaisa ta wayan Al-lawan"

"Kinga ni daga nan ba sai ki dau numban ba, ko a makaranta sai Ku dinga gaisawa" nan ta ke nayi na'am da shawaran Ajiddah, ban kuma kara neman Kowa da maganan ba. A ganina duk Wanda zai ban shawara ba kaman Ajiddah don ita ce kama na kuma itan ta riga ni fara fuskantan abinda na ke fuskan ta yanzun.

Wannan karon Yaya baba da kanshi ya maida ni makaranta. Ba laifi tunda su ka fara shiri da Anty Nainah ya ke dan kyautata min. Wannan karon ma da alamun Anty Nainah ya ke son gani. Kayana na dauka nayi cikin school, ko da na dawo ba iske su tsaye da Anty Nainan Suna magana. Tana ganin ta saki fara'a, banyi mamaki haka kuma ban hade rai ba sai dai still ban mata dariya ba.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top