Talatin da tara

Rayuwata

Babi na sha biyu


Rayuwa sam ba ta min sauki ba, imagine a dan kankanun shekaruna na riga na gama sa wani a rai. Sai dai ya tafi ya barni a inda ya tsinci ne tun a farko, cikin kangin wahala ds takaicin rayuwa. Wai din na a lokacin ina zama gidan Goggo. Sai dai ina girma ina kara tuno mahaifiyata, Ummi da ta tafi ta barni ba ko waiwaye balle ta san hakin da nake ciki. Abun jarin haushin, ba ma ni kadai ba hatta yan uwanta ba wanda zai buda baki yace ga inda Ummina ta tafi. Daga ita har Maijiddah. Kanina Baffah kuwa tun yana maganan ta, har ma ya fara mantawa da ita. Sai dai yanzu shi bai ma garin Borno. Kaman yanda naji wai, cousin insu Abbahnmu tazo ta roki alfarman a bar mata shi saboda ba ta taba haihuwa ba. Hakanan kuwa suka dauke shi suka bada. Kasan ma gabadaya ita ba a nan take da zama ba. Shi inma dai rabo na dashi yayi shekaru.


Anty Nainerh ta tafi school Abuja, musamman ka fin ta wuce tazo ta same ni har gidan Goggo, kaman yanda ta saba wannan karon ma gifts ne kala kala ta kawo min. Da ke Haleematu na makaranta ita da wata kawar ta suka zo, Faree'ah. Lokacin na fara sanin ta, haka kuma daga yanayin kallon da take bina dashi kadai na fuskanci ita in su Anty Nainerhn ne. Ban ma kara tabbatarwa ba sai da naji tana ce mata "wai ke faree miye haka? Wannan wani irin kallon iskanci ne, na dai gaya miki ba irin ki bace ko?" Ba ta ma yi zaton naji zancen ba saboda na fita daga dakin su kayi shi. "To wai ke meye sa baki gwada naki sa'an na she will accept you, i can see she likes you Allah" van san wani irin reaction Anty Nainerh tayi ba na dai ji tace mata "Ba lallai ki gane ba amma Suhaima ba irin wannan son ta ke min. I know she likes me as a sister ko as a friend ko dan saboda kula da itan da nayi a school. Ba zan kuma iya destroying rayuwan ta ba kaman yanda ni nawa rayuwan ya zama. Yarinyar nan da kike gani ta sha enough wahala a rayuwan ta ba kuma tayi deserving rayuwan da mu muje ciki ba. Ina so ko yayane ne taji dadin rayuwa, shiyasa ban takura mata ba."


"Hmm ehm" shine kawai ahinda Faree'an tace daganan kuma sai na shiga dakin. Sai kuwa a lokacin na gane dalilin da yasa Abty Nainerh bata taba nema na da wani abun banza ba. It so clear she likes me like a sister. Haka dai na raka su suka tafi, wannan karon ma har wani waya ta kawo min, babba ne ma na wannan karon. Amma ni bai dame ni ba sabida wanda bake ganin za muyi wayan tare dashi, we are no longer together.


Ba zance ina da Farin jini ba, i mean ban kai Ajiddah ba. Duk da hakan ina haduwa da maza da yawa da su kan so in basu dama, sai dai ban bada fuska saboda Amir a lokacin sai akan Mai Aliyu, kaman yanda na fada muku sunan shi. Yana da ilimi sosai na arabi da na boko, malaman makarantan na matukar alfahari dashi. Duk mazan da su ke da shekaru 16, 17, 18 zuwa 19 haka za ka same su da matukar rawan kai, rashin ji da sauran su. Sai dai banda Mai Aliyu da ka ganshi ka ga natsuwa sosai a tattare dashi. Mafarin maganan mu ko watarana Mr Auwal, malamin da ke koya mana physics ya shigo ajin, sai dai har ya fita ban gane komai ba, ban ma san ina aka sa a gaba ba. Physics na matukar bani wahala duk da yanda na ke son maths. "If there is something you don't understand, remember you are free to meet me in my office. See you tomorrow class" charab! Abinda ya fada kunne na kenan, ai ko dole in je in sa me shi. Ana tashi break nayi hanyan office in nida wata kawata Aisha da ta raka ni amma sai ita ta tsaya a waje.


Su biyu ne a office da wani English teacher na SS3 Malam Aminu. Ina zuwa na nemi izinin shiga aka bani, sabon gaisuwa na musu su duka biyun ba tare da na duba daliban aji shiddan da ke zaune a wurin ba su biyu suna magana da Malam Aminu. Bayanin abinda ya kawo ni na mishi "oh okay where and what do you not understand"


"Everything sir"


"Oh! This is serious" shiru yayi ya dan dago yana kara kallo na "do you know what? Please just come back when am less busy i shall try and guide you then"


"Okay, Thank you sir" har na juya zan fita naji ya ce "or Aliyu can you please help me tutor the lady?" Lokacin na juya na kalle shi, murmushi ne a kwance kan fuskan shi yace "No problem sir"


"So please meet him" yana fadin haka ya cigaba da abinda ya ke. Barin marking in da su ke ma Malam Aminu yayi yace min "let talk outside" bance komai ba na bishi, ina jin Malam Aminu na fadawa Mr Auwal "ka dai zo ka kwace min student kawai" dariya su kayi.


"Naji conversation inku da Malam but we have to fix time da zamu dinga haduwa muna lesson" godiya na mai bayan yayi fixing time in. Haka kuwa aka yi ya fara koya ma karatu, kai ba ma physics ba kadai duk subject in da na samu matsala sai dai in ban same shi ba. Yana da kokari sosai, don shi ya fara sa min sha'awan yi medicine da gaske a raina. Shi kuma abinda ya faru, school ne gabadaya ya dauka, ana ganin mai Aliyu da mace kullum suna magana. Kafin dai mu yanke ma alakan mu suna su sun yanke mishi. Tun ana fad a makaranta har abun ya fara shiga kaina ya zauna, dake kuma ban manta abinda ya fadu tsakanina da Amir ba sai nake dari dari dashi. Har watarana ya same ni da zancen mai nake gani akan abinda dalibai yan uwan mu ke fada. Kai tsaya nace mishi "jita jita da kananun magangana tunda dai ba wanda muka taba fadawa hakan" tun daga yanayun fuskan shi na gane bai ji dadin amsan nawa ba. Sai dai i've had enough from boys da ba zan iya kaea barin wani yayi breaking heart ina so easily ba. Da na maida zancen wasa shi ma sai ya share. A haka na shafe shekara daya da rabi a nana Aisha har dai na shiga SS1 kenan. Lokacin Mai Aliyu har ya gana nana Aysha amma dake a nan fawari yake sai ya zamto muna yaan haduwa daahi. Don har Goggo ta san a matsayin wanda ke koya min karatu. Jika na ma take ce mishi. Ajiddah ko da ta samu kabarin shi, shi din ma supporting tayi tana fadin "To shi wancan banzan Amir in dan ma ya samu kin kula shi? Ai Mai Aliyu ma ya fishi komai Allah" ni dai ban ce mata komai ba haka kuma ban gaya mata akwai wani abu tsakanin mu dashi. Kiri kiri nasan yana sona amma ban bashi fuskan fadan hakan ba, duk lokacin da yayi yunkuri kuma sai in tare. Ina jin wani sa'in Goggo nace mishi mijina, duk dai na gama gane take taken su amma ban shirya kara shan wahalan da na fuskanta a baya ba.


Kwatsam ba sai ciwon kafan Goggo ya taso gadan gadan ba, tun ina yawan shafa mata man zafi har abun ya zo yafi karfin man zafin. Dole sai da aka hada da asibiti, tun tana daurewa taba tafiya har abun ya fara gagara. Wani lokacin kasa zuwa makaranta nake in zauna jinyan ta, saboda dai ciwon kafa dai yace bai san zance ba sam. Kusan sau uku ina raka ta maiduguri muna zuwa ganin likita, sai an dawo an fara samun sauki sai kuma abu ya koma sabo. Ba Goggo kadai ba ni kaina sai da na sha wahaln jinyan nan.


Bayan na gama exams in second term ne muka nufi Maidugurin baki daya da niyyan zaman asibiti a duba kafan da kyau tun da tashi ma yanzun ya gagara. Na sha zama ni kadai inta kuka abu na a bayan idon Goggon. Haka muka dinga zaman asibiti, ni ke kwana da Goggo sai washegari da safe daya daga cikin matan baffan maiduguri tazo da yarta ni kuma in koma gida in huta. Duk da ma ba wani zaman nake ba, ina komawa gidan zan fara kokarin hada mata abinci dan nasan goggo ba abincin kowa ta ke iya ci ba. Hakanan zan koma mu cigaba da zama, abu sai ya fara sauki sai kuma ya kara rincibewa. Ni kaina sai da nayi kusan kwana uku a na samin drip, rayuwa dai ta dawo da rashin dadin ta. Gashi ko a gidan baffan maiduguri ba sa ana daga wanda ya girme ni sai kannen baya na. Matan gidan duka duka uku ne, biyun manya ne suna ganin sun finkarfi na din ko maganan arziki bai hada ni dasu, dayan ko karama ce sosai don ko magana ba gama iyawa tayi ba.


Daga kafan ma ba abu sai ya fara taba wani abun ba, misalin jinin ta na hawa, ga diabetes da take dashi tun tuni sai yanzu ya hade gabadaya yana bata wahala. Ga kuma yawan zafin jiki da cikin ciki. A cikin tsakan jinyan nan aka koma makaranta. Na so a barni inyi zamana na yafe karatun don banga amfanin shi Goggo tana kwance ba amma haka aka tirsasa ni dole na dawo. Wani bakin aikin, gidanmu na sabon fegi aka sake wulla ni. Ba ko kunya Adda falmata ta cigaba da gallaza min azaban da ta saba. Haka kuma dukkan ayyuka su ka maido min dashi, gashi Abbah kocokam yana Maiduguri dake aikin nashi ma wannan karon yana zama a maidugurin ga kuma jinyan Goggo. Sai ya zamto Anty Yana ma yawan ci tana can, mu kadai ne dai a gida. Ko makaranta da kyar nake samun inje, saboda ba ni da kudi wanda aka bamu kuwa Adda ke dannewa. Gashi yanzu ba ta da wani aiki sai zaman hira da samari, yau wannan yazo gobe wancan yazo. Ni ko rana daya da Mai Aliyu yazo mu ka dan gaisa, sai da ta min shegen duka wai da gaske dai na zama yar iska. Ban dai tanka ta ba amma har ga Allah yanzun ban wannan tsoron nata da nake yi da. Danni na ma raina ta yanzun kawai ina kokarin bata gitman tane amma ita sam bata ganin hakan. Duk weekend in dai Abbau yazo ina bin shi maiduguri in gano jikin Goggo dake ma an sallamo ta ba wai don ta warke ba sai dan taki zaman asibitin. Yanzu a a nan gidan Baffan Maiduguri take zama dake babban gida ne sosai.


Kwatsam ranar sai ga Anty Nainerh wai taje Ajeyari bana nan. Nayi farin cikin ganin ta kuwa domin dai an dade ba a haduwa ba. Katin bikin ta ta kawo min, na koyi mata murna sosai. Ko da na mata magana akan ina fatan ta canja ra'ayin ta data taba bani labarin irin zaman auren da tasan zata yi da mijin ta. Murmushi kawai tayi duk dai yanda na so zancen ba tace min komai ba. "Zaki zo ko suhaima?"


"A nan garin za ayi?"


"Daurin aure kawai za ayi a nan ga sai walima, A Abuja za ayi events in yakamata kije pls kanwata" dariya ma ta bani, saboda sanin kaina ne ba wani wanda zia barni zuwa garin Abuja. Balle ma a halin da Goggo take. Excuse na kawo mata da rashin lafiyan Goggo. Ai ko har zuwa tayi ta dauke ni da weekend mu kaje maidugurin dubo ta. Da zamu tafi Adda Falmata na ta sakin habaicin ta sai dai ni kaina nasan Anty Nainerh kaman ba ta da time inta baki daya. Hakanan mu ka isa maiduguri, ai ko Goggo ta ji dain ganin ta gama ita duk wanda ya ke kyautata min tana son shi. Kai ysohuwan nan ta nuna min kauna iya kauna a rayuwata, ba ni da wani abun da zan iya gode mata. Kafin mu tafi ne ta jani gidan su Faree'ah, kaman wancan karon kallo na kawai take tana fadin 'kina na dai abinki Suhaima ko" dole tasa sai da muka dan yi hira da ita duk da ni ban ma da wani abun fada mata.


Lokacin bikin Anty Nainerh mu ka kara haduwa da ita. Anty Nainerhn tayi farin cikin zuwana, har ankon ta na kawaye sai da ta min. Halimatu dai har yanzun ba mu wani shiri da ita sosai, to dake ma ba wani dadew aka yi ba a na daura aure aka debi amarya da wasu mutane aka nufi garin Abuja. Anty Nainerh ta tafi gidan mininta ni kuma na koma cikin azaba da wahalan gidan mu. Kuma kwatsam ba sai ga yaya baba ya dawo gidan ba. Ina ganin shi nasan bala'i ya afku gashi kuma lokacin ina tsaka da jarabawa. Bai dade da dawowa ba sai ga Anty Yana ita ma ta zo, ko ta ina dai na gane bala'i kawai ke jirana. In dai suka hadu su ukun nan to fa nasan zancen zai lalace.


July


A duk lokacin damuna a jahar yobe, in dai ruwan mai karfi ne, mafi yawancin lokuta hadarin yana hadewa da kura sosai. Kai wani lokacin ma za a gama kuran sosai ya taso da kasa amma kuma ba ayi ruwan saman ba. In abun yayi tsanani motocin da ke kan hanya har parking in dole su ke sai in an fara ruwa su ke samun ganin hanya da za su iya cigaba da tafiya. Bakomai ke sa hakan ba sai yalwataccen yashin da ke garin, har za kaji mutane na fadin akwai inda in har ba safa kasa ba ko takalmi mai tsawo in har zaka yi tafiya kasa, kafafuwan sai sun yi butu butu da kura kafin ka isa inda za ka. Saboda wannan kasan yasa lokuttan sanyi za kaji sanyi yayi yawa sosai, lokuttan zafi ko har ba a magana, rokon mutane yawancin kar azumi ya shigo ruwan sama bai sauko ba, ba karamin wahala ake sha. Anty Amarya ce ta ke fadin tabbas ladan yan garinmu daban da na wasu garuruwan da basa fuskantan zafin har haka. Goggo ko inna kan ce mata "Amarya am abun ba daga nan ya ke ba" saboda wannan zafin ne za kaga da matukar wuya yaro karami ya ce zai yi azumi kaman yanda yan irin Kaduna, kano da Abuja kan yi.


Ganin irin hadarin da ya fara tasowa ne yasa na ke sauri sauri in gama wanke wanken da ke gabana kafin ruwan ya kai da saukowa. Saboda nasan yanzu kura ya maida min aiki na baya, in dai na gama na kulle kitchen in shikenan. Wanki na sha ranar bayan girkin da nayi na rana da na daren da na sauke kafin na hau wanke wanken. Da ke na maida hankali na kocokam kan aiki nan da nan na gama. Na tattare kitchen nayi saurin shiga cikin gida domin in samu inyi wanka. Sai dai me? Ina shiga cikin gidan naji Anty Yana na wakan "wai kun ga hadarin da ke garin nan kuwa, yanzu za a dauke wuta ba battery a lantern gashi ba candle ba ma mosquito coil gabadaya ya kare" wani irin faduwan gaba naji  domin nasan ko min karfin ruwan nan sai na fita na samo abubuwan da ta lissafa in nan.


"Anty Yana aje a siyo mana to" Adda falmata ce ke maganan tana daddana wayan ta. Gaban na ne ya kara fadi sakamakon karan hadarin da aka iya jiyowa tun daga cikin gida. "Sadiya dauko kudi maza a jaka na ki ba Suhaima ta siyo" salin alin naje na dauko hijabi na na amsa kudin na fita. Kuran ne dai ke tashi sosai, ba Wanda kake gani a waje kwata kwata. Runtse ido nayi na fita daga gidan baki na dauke da addu'a. Ina bude idon domin neman hanya tuni kasa ya cika idona ta yanda har ban iya ganin gaba na da kyau. Dole na nemi gefen gidan makotan mu na rabe, da ke akwai rumfa a wurin. Rakubewa nayi ina rawan sanyi har ruwan saman ya karasa saukowa. Ganin haka nayi saurin fita na shiga ruwan nan da gudu na nufi shagon, ruwa ne mai hade da iska sosai irin Wanda ko da lema ka shiga iskan zai dauke leman. Hakan yasa ina gudun amma kaman ban yi sakamakon iskan. Idanuna har rufewa yayi ban ganin gabana amma dan bala'i aka haka na cigaba da gudun nan. Ban sa na ci karo da bishiyan maina sai da naji abu ya takore ni na kasa tafiya, da kyar na iya bude ido naga bishiyan maina a gabana. Wani irin nauyi kaina ya dauka sai a lokacin na gane kenan kaina nane ya bugi itacen. Na kai minti biyar a cikin shock kafin na farga, kara shigewa ciki bishiyan nayi na rufe ido na da ke matukar zafi, duk da ruwa na zuba sosai nasan yafi akan in kara shiga cikin ruwan nan. Ruwan kam an dauke lokaci ana yin shi sai da aka kira sallan magreeba kafin ya dan tsagaita. Duk na jigata, ga ido na da ke faman radadi, ko ban kalli madubi ba nasan suyi ja ga kuma sarawan da kai na keyi.


A haka na nufi shagon da gudu. Duk na jike, har diga nake yi na karasa. Sai dai kash, ina isa shagon na tarar da an kulle. Ma'ana dai sun tafi massallaci. Wuri na samu na rakube ina rawan sanyi da ya gaman shigan ko ina a jikina, ga kayana da su ke jike gabadaya har ta pant in da ke jikina ma a jike ya ke.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top