Talatin da daya
Rayuwata
Babi na hudu
"Bafferh" na fada ina kallon shi cike da mamaki.
Da sauri ya karaso yana rike min hannu "Adda kuka me kike? Mu je ki kaini wurin Umminmu ni fa na dawo ba zan kara komawa ba kuma" wani irin faduwan gaba naji jin abinda ya ke fadi, kenan shima yana cikin damuwa?
"Adda mu je mana, ina so in ganta" cike da tausayi na girgiza mishi kai
"Bafferh Ummi ta tafi ance min ba zata kara dawowa ba"
Kallona yayi ya kasa magana, kuka ya fashe dashi. Na jawo mu ka zauna nan muna ta kuka. Anty Amarya ta fito ta same mu a haka. "Suhaima lfy? Kuka zauna kuna kuka haka?" Ko kafin inyi magana ta dau Bafferh tayi dakin ta dashi, ni ma nabi su a baya. Daga alamun ta na gane tana jin tausayin mu. Lallashin Bafferh tayi sannan tace min in daina kuka kar ya cigaba dayi. Matan na da kirki sosai, don duk lokacin da na ke gidan in naje wurin ta, ta dinga min kyauta kenan, sweet kala kala da kayan kwalliya. Sau daya ina jin yan gidan na fadin ta na da rowa ga sa aiki sai dai ni banga hakan ba. Aiki kam tun kafin ta sani ma zan mata, su Lance abinda ya sa ta ke sona kenan. Ni kam ban damu ba, nayi na dole ma balle Wanda za a yaba min? Sau dayawa godiyan da na kanyi wa a Anty Yana kenan, a tunanin ta cuta na tayi. Sai dai duk inda naje ana jin dadin zama dani saboda son aiki na sabanin yaran ta masu son jiki.
Ranar wuni mukayi ni da Bafferh, gani yake kaman na koma mishi Ummin, ko ina nayi yana nanike dani har tsokanan shi ake. Ko da Ajidda ta zo mu tafi wasa fir na ki binta saboda Bafferh nan fa Goggo tayi ta mana dariya, wai an jimu a rana duk son zuwa yawon mu.
Drama bai tashi ba sai da yan Maiduguri su ka tashi tafiya, kuka Bafferh ya sa ka yana cewa "shi fa Ummin shi ya ke so" yin duniya anyi yaki ji yace ba zai koma ba. Ni kam har ga Allah so na ke ya koma saboda ba San gwara mishi can akan nan. Saboda ya tabbatar min ba a dukan shi kuma ba aiki sai dai ba Wanda ya damu ya kula dashi. Karshe dai da karfi Abbah ya sa shi a mota yana kuka ina kuka haka muka rabu.
Ina primary five headmaster inmu ya dauke ni a cikin wadanda za su zana common entrance, a cewar shi INA da basiran da zan iya ci. Ko da naje na na Goggo lbr tayi ta jin dadi, kawata Ajiddah ko cewa tayi "Suhaima kicewa Abban Ku ya kaiki GGC Damaturu kinga nima can zani" zaro idanu nayi nace "sai dai in fadawa Goggo" ko da na Sanar mata kallona tayi tace "anya Suhaima zaki iya makarantar kwana?" Ganin ina shirin mata kuka tace "shknn zan fada mishi, gama ni ban yadda da zaman da kike wurin Yana ba" ban amsa mata saboda INA tsoro, sai ma murnar da mu ka hau ni da Ajiddah, daman ta fini da aji daya, to yanzu zamu dawo dai dai da ita kenan, gsky na ji dadi.
Common entrance na fitowa naga na ci exams in dai dai yanda ake bukata. Kaman wasa Abbah ya amince, nan fa ya hau min shiri ni ko zumudi na ya ki boyuwa. Ina ji Adda Falmata na cewa "shegiya, daman daga can seniors in makarantan su kashe ki Kowa ya huta, ba dai boarding ba? Ga ki gashi. " komai ban ce mata saboda nasan za ta fadi abinda ya fi haka ma.
Ba laifi Abba ya min kokari sosai, haka ma Goggon nina biyu. Anty Yana kam ko ranar da zan tafi da na mata sallama, tsaki ta ja tace "kiyi ta tafiya ni kam ba matsala ta bace" salin alin nayi tafiya ta ban ma kowa magana ba sai Al-lawan da ya raka ni har makarantan. Shi ma ce min yayi "Suhaima kiyi karatu kinji?" Gyada mishi kai kawai nayi daga nan ban kara cewa komai ba har mu ka rabu.
Sannu a hankali na fara rayuwan boarding, ban wani maida hankali ga yin kawaye sosai ba saboda tun can daman ni ba mai yin kawayen bane. Balle ma ga Ajiddah. Sai duk da haka akwai wadanda mu ke mutunci da su ba laifi. Senior kuwa tsakanina da su dar dar ne saboda ban San abinda zai sa ni shiga case. Da ke akwai yayyin Ajiddah a makaranta muna samun gata sosai, ko ma ba don yayuin ta, Ajiddah mace mai farin jini sosai, tana da kyau ma sha Allah. Duk wanda yayi boarding ya san yanda seniors ke son shiri da kyakyawa mai gashi, kuma Ajidda ta hada duka.
Duk wani wahalan labor da aiken seniors bai wani damu na saboda nasan ina Wanda ya fi shima.
Sannu a hankali malamai su ka fara gano ni cikin dalibai masu mai da hankali sosai. Musamman bangaren maths da sciences. Ko da mu kayi tests, na ci sosai ba don komai ba sai don dedicating time ina da nayi wa karatu. Malamin maths, malam easy ake ce mai. Duk sati ya ke mana test a bangaren maths. Ganin duk tests in da yake ina kokari sosai ya sa yace yana son sani a wani quiz da ake zuwa duk shekara, ba a daukan yan JSS1 amma zai nemi izinin principal ko za ta iya bari na in Shiga. A yanda malam easy ya fada, da kyar ya samu principal in ta amince don haka dole in maida hankali domin kar in bashi kunya. Lokacin yi min extra lesson ya bani, dole duk abinda na ke lokacin na ke barin shi inje. Gab ake da tafiya hutun sallah kuma ana dawowa za a tafi quiz in.
Yawancin weekend na ke lesson in. Sai dai wannan lahadin na so inyi latti, hakan ya sa na gama shiryawa da sauri sauri na nufi hanyan classes. "Keh dan zo nan" gaba nane ya fadi saboda kiran da wata Senior ta min. Banda wani mafita dole na je. Bucket mika min inje in debo mata ruwa. Wani tashin hankalin na sake shiga Sanin layin da ke wurin diban ruwan. "Dan Allah kiyi hakuri, malam easy ke jira na zan je lesson a class" na fada nayi rau rau da idanu, rashin yanda zan yi ne ya sa na fada mata hakan. Daure fuska tayi tana kallona yayin da sauran kawayen ta da ke wurin su ka fashe da dariya. "Ke ban fa san iskanci da karyan banza wani lesson za kije da weekend"
"Ba karya na ke Allah, yana jira na ne."
"Au da gaske dai ba za kije ba din" wata kawarta da ke gefe ta fada. Dayan kuma cewa tayi "daman yan JSS1 in nan suna fama da raini wayau."
Shiru nayi na kasa magana. "Suhaima Adam Bello, Suhaima Adam Bello where are you" da karfi naji ana kiran sunana, juyawa nayi naga wata yar class in mu da tazo daga kudu "Yes" na amsa ina kallon ta.
"Malam easy, the maths teacher is looking for you" ban amsa mata ba sai kallon Senior in da nayi, inga ko ta tabbatar da abinda na fada yanzu.
"Suhaima wai ba ki tafi lesson in ba?" Naji an fada daga baya na, ina waiga wa naga Halima Bello jajere, ita ma ajin mu daya kuma dakin mu daya da ita. Kallon senior in da ta kirani tayi tace "Anty Nainah ke kika kirata? Kawata ce fa, lesson kuma za ta"
"Wuce ki tafi" kawai senior in ta fada, da sauri na karasa kar wata ta kara kira na.
Ranar hutun sallah Abbah da kan shi yazo daukana, shida Ya baba ne Wanda ya fara karatun jami'a a Bayero University Kano. Komawa na gida ne na ji Al-lawan na fadin ya zabi can ne saboda abokin shi Umar sanda ya koma can wurin mahaifiyar shi kuma shima a can ya ke karatu. Ni kwata kwata na manta da wani Umar Sanda can sai da aka fada na tuna na dade ban ganin shi ashe ya bar garin ne, an rage mugun iri, na raya a raina.
Kallon arziki ban samu ba balle tmbyn makaranta da karatu, sai ma aikin da aka cigaba da gasa ni dashi. Wannan karon kam ragaman girkin gidan gabadaya aka sakan min ba mai ta yani sai dai Adama in ta shigo, in ba muyi fada ba kenan, dan kwata kwata ba ma jituwa da Adama abu kadan ke samu fada, gata da saurin fushi nan da nan. Mun fi jituwa da Ummi akan ta. Da ke hutun sallah ne kwana goma nayi mu ka koma school, wannan karon su Bafferh ba su zo ba.
Mun koma ba dade ba mu ka tafi quiz in, a nan stadium inda aka tara makarantu dayawa. Ga mamakina harda wannan senior in da naji Halima Bello jajere ta kira da Anty Nainah. Mun yi kokari sosai da ke kowa dai dai dashi yayi. A ranar aka fadi sakamakon kuma munyi nasara. Tun daga nan nayi fice a wurin malamai kowa ya sanni kuma yana yabawa yanda na ke maida hankali. Ni dai duk wannan bai wani dame ni ba, ni dai burina in san abinda na ke yi ko zan samu in cikawa wa kaina burin zama wani abu a nan gaba.
Haka rayuwan makarantar ta cigaba yau dadi gobe rashin ta. Zuwa yanzu na riga da na sa wa zuciya irin ta wa kaddarar rayuwan kenan, shiyasa ko kadan ba aji na a cikin masu complain in an sa mu abu a makaranta. Watarana da yamma bayan an tashi prep mu ka tsaya share aji dani da Halima da wasu classmates inmu guda biyu. Da ke an yi kura gabadaya ajin ya dauka har desks da chairs. Muna cikin aikin Halima ta ja gefe ta zauna tana maida numfashi. Bintu da mu ke tare ne tace "Halima ki fa tashi mu karasa aikin nan na sanki da ragwanta yanzu sai kice kin gaji bayan kin san duty inmu ne" ban kawo komai a raina ba saboda duk Wanda ya san Halima ya Santa da son jiki da shagwaba, komai yayarta ke mata a makarantar, irin yaran nan ne da basu saba da aiki a gida ba. Kaman da wasa na fara jin nishin yayi yawa irin na Wanda ke kokarin yin numfashi. Da sauri na ajiye duster in da ke hannu na na nufe inda ta ke "Lfyn ki kuwa" lokacin dukkan su biyun sun bar abinda su ke ganin da gaske ba lfyn ba. Kokarin daga ta mu ka fara ganin yanda abin yayi yawa, kaman numfashin na nema kwace mata gabadaya. "Mu wuce dispensary" na fada da sauri mu kayi hanya. Magana naji ta fara yi duk da kyar ya ke fito "in inha inhaler" abinda ya sauka a kunne na kenan. Nan ta ke na tuno ta taba fada mana tana asthma, sai dai ba Wanda ya dauki abin serious ganin bai taba tashi ba. "Yana ina Yana ina?"
"School bag" abinda kawai naji ta anbata kenan na afka da gudu nayi hanyar hostel su kuma su ka wuce da ita dispensary in. Duk nisan hostel da classes area, cikin minti kalilan na isa saboda gudun da na ke faman yi. Naci sa'an dauko inhaler ba tare da na tanka duk wani Wanda ya ke min magana ba. Na kusan fita hostel naci karo da yayar ta tee da assistant headgirl inmu. "Halima" kawai na fada ina nuna mata inhaler, ban saurari me za tace ba na cigaba da gudu. Ko da na isa dispensary in na tarda nurses in tsaye sun rasa mafita, da alamun jira na su ke. Ina mika musu ta shaka sai gashi ta saki ajiyan zuciya ta kwanta. Ruwa ba karba a wurin nurses in na sha saboda gudun da na sha, ban san dalili ba naji kirji na na faman zafi. Baya min haka sai in naje debo ruwa yawancin. Dai dai lokacin sister in nata su ka shigo a rude, wurin haliman ta karasa tana duba ta.
Nishin nishin da na ke tayi yasa nurse in tmby na lfy "kirji na na zafi sosai" na fada.
"Ina ga saboda gudun da kika yi ne, bara na baki magana sai ki kwanta ki huta" Sistern Halima ce ta juyo tana kallo na "sannu koh, mungode" gyade mata kai kawai nayi na amshi magani.
Ban san bacci ya kwashe ni sai farkawa nayi naga su bintu sun tafi sai sistern Haliman da friends inta. "Sannu ko? Kirjin ya daina?"
"Eh" na amsa mata.
"Ba kuma inda ke miki ciwo" girgiza mata kai nayi, inaji tana cewa "nurse za mu iya wuce hostel dasu."
"Suhaima tashi mu tafi hostel" ta fadi sai dai tun kafin na tashi ta fara dagoni. Tana rike dani, kawar ta ta rike Halima mu ka isa hostel. Maimakon naga mun nufi hostel inmu sai naga ta dau hanyan nasu. Ban samu daman cewa komai ba har mu ka isa. Tea mai kauri ta hada ta bani nasha bayan ta tafasa ruwan zafin a heater. Ga mamakina chips, kwai da kaza ta ajiye mana muci ni da Halima, ina mamakin inda ta samo shi sai dai ba halin tmby. Kasa sakin jiki na ci abincin nayi. "Suhaima kifa ci abin nan da kyau kina jina?" Murmushi kawai nayi na cigaba da turawa.
Tun daga ranar ta fara kyautata min komai za ta wa kanwar ta zata min, har Ajiddah ta fara jin haushin na daina bin ta wurin yayyin ta. Sai dai ko ban so zuwa wurin Senior Nainah ba dole ta ke Sani sai naje. Kullum zata sa a debo mana ruwan wanka, ba ruwan da layi za mu Shiga har dinning ma haka, da za a wuce gida har wanki ta min. Ana gobe za a tafi ta aiko min hadaddun turare designers da takalmi heels. Abin ya bani tsoro saboda zuwa lokaci na san abinda ake cewa school lovers, ko kuma ince school mummy da school daughter, yawancin sune za kaga suna wannan kyautan wa junan su, gudun tunani abin da ba haka ba. Godiya na mata sosai saboda ba daman in ki amsa. Kowa ya tashi a cikin Damaturu ya San baban su babban mutum ne mai tashan kudi, hakan ya sa ba abun mamaki bane irin kyautar da ta ke. Ni dai kowa na marmarin zuwa gida amma fa banda ni saboda nasan azaban da zan tarar.
Abbah da kan shi yazo daukana, shida Ya baba ne Wanda ya fara karatun jami'a a Bayero University Kano. Komawa na gida ne na ji Al-lawan na fadin ya zabi can ne saboda abokin shi, Umar sanda ya koma can wurin mahaifiyar shi kuma shima a can ya ke karatu. Ni kwata kwata na manta da wani Umar Sanda can sai da aka fada na tuna na dade ban ganin shi ashe ya bar garin ne, an rage mugun iri, na raya a raina.
Kallon arziki ban samu ba balle tmbyn makaranta da karatu, sai ma aikin da aka cigaba da gasa ni dashi. Wannan karon kam ragaman girkin gidan gabadaya aka sakan min ba mai ta yani sai dai Adama in ta shigo, in ba muyi fada ba kenan, dan kwata kwata ba ma jituwa da Adama abu kadan ke samu fada, gata da saurin fushi nan da nan. Mun fi jituwa da Ajiddah akan ta.
A ranar da mu ka koma makaranta da dare, Anty Nainah (kaman yanda Halima ke kiran ta ta Sani nima in dinga kiran ta) har corner ta tazo, provisions mai uban yawa ta kawo min. Girgiza ma ta kai nayi, na ce mata "ni fa Abbah ya siyan min dayawa" hararana tayi tace "na Abbah daban na wa daban, kuma kar ki kara fada min haka sai dai ko in baki dauke ni yayar ki ba" hakanan dole na na amsa, ba don raina na so ba.
Shakuwa mai karfi ne ya shiga tsakanina da Anty Nainah, ba don komai ba sai dan yau da gobe ya wuce wasa. Dole na saki jika da ita, ba irin labarin da ba ta bani, kai har na samarin ta. Wanda ya hada da malam idriss, social master inmu. Sosai ya ke son ta. Ba ma shi kadai ba malamai dayawa, sai dai shi in ta fi bashi fuska. Kowa ma zai so Nainah, ga kyau ga kokari, ga tsafta. Ko min ta fes fes gashi kuma ba abinda ta nema ta rasa. Akwai wata senior Zainab kyari a SS3, ita ce assistant headgirl, ba karamin dasawa su ke ba. A cewar ta kawarta ce. Dan duk sanda na je wurin ta bata nan to tana wurin senior Zainab. Ita ke kare mata duk wani sharrin yan SS3, ta tsaya mata sosai, ba Wanda ya isa ya mata abu a makarantar. Kai har malamai ba kowa ke taka ta. Abinda ke bani mamaki shine kowani abu na damun ta tsab za ta same ni ta fada min, ba ta la'akari da ta girme ni ko wani abu kaman tazaran ajin da ke tsakanin mu, tana SS2 ina JSS1. Ganin haka ya sa na ke kokarin bata shawara dai dai gwargwado iya wanda kwakwalwata da tunani na zai iya batan.
Watarana muna zaune a gaban hostel tana lbrn yayan ta da ke karatu a UK tace min "Suhaima ni kam wani layi kuke a sabon fegi?"
Kallon ta na danyi ina wani nazari tace min "ko baki so in zo gidan Ku in gaida mamanki?" Nan da nan idanu na su ka ciko kwalla, ganin haka ta rude tana tmbyna dalilin kuka na. Shiru na mata karshe ma na tashi na tafi. Ina ji ta na kira na share ta, ai ko ina hawa kan gado naji sallaman ta a hostel inmu. Pretending nayi ina bacci, bisa dole ta hakura ta kyale ni.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top