Talatin da biyu

Rayuwata

Babi na biyar

As usual washegari da safe ita ta samo min ruwan wanka, ban ce mata kala ba itan ba ta tanka ba sai ce min tayi "Suhaima dan Allah Ku dinga karatu da Halima she is lacking behind sosai" turo baki haliman tayi, abin ya ban dariya. Halima irin shagwababbin yaran ne komai ba su San wahala, sau dayawa ina kokarin jawo ta muyi karatu sai dai wasa na janye mata hankali tilas na kyale ta.

Ba ta taba kawo wani abu a shirinmu da yayar ta ba, a tunanin ma kokarina ya sa yayar ta ke jawo ni a jiki saboda in dinga koya ma ita haliman abu abu. Itana sosai ta ke ji dani, komai Suhaima kaza Suhaima kaza.

Muna cikin prep sai ga Anty Nainah ta shigo har ajin mu. Har seat ina tazo ta same ni ina note. Daukan note in tayi tace min "taso muje" ba musu na bita, hall ta kaini, duk seniors a ciki suna karatu. Gefe daya tasa mana kujera mu ka zauna "cigaba da note inki" tun daga nan ba ta kara ce min kala ba nia ban tanka ba sai dai duk na kasa abun kirki saboda kallon da ta ke bina dashi. Can dai da ta gaji ta ce min "abinda na fada jiya ya bata miki Raine?" Girgiza ma ta kai nayi ba tare da na dago ba.

"Then, why are you not normal, akwai wani abu ne? Ki gaya min kinji" wani iri naji jin yanda ta damu da matsala ta. Ajiye note in nayi nan da nan sai ga hawaye a idanuna. Hakuri ta fara bani, kawai na girgiza mata kai. A hankali na fara bata lbrn halin da na ke ciki a gidan mu. Na sha mamakin yanda ta dinga kuka, daman she is so sensitive. "Kuma ba Wanda ya taba fada miki inda Ummin ta ke?" Girgiza ma ta kai nayi, nan fa ta hau rarrashi na. Sai cewa tayi "I think i have a plan amma kar ki damu slowly zai yi working" bangane me ta ke nufi ba amma dai kawai nayi shiru.

First visiting in da aka fara yi, mum insu na zuwa ta dauke ni mu kaje "mum ga kanwata fa Suhaima kawar Halima"

"Au itace Suhaiman? Zo yata ki zauna kinji" ban yi wani mamakin yanda ta sani ba considering yanda mu ke da yaran ta. Ban tashi mamaki ba sai da naga provision in da aka musu kashi uku ne, wato har dani a ciki, rasa bakin magana nayi domin a bin yafi karfi na. Gabadaya yan gidan su na da kirki. Banyi tsammanin za a zo min ba. sai bayan la'asar kwatsam na ga Goggo da Adama. Na ji dadin zuwan su sosai, again Anty Amarya ta zo da Anty bilki tare da yan gidan su Ummi. Goggo ta bada sako a bani, ba ta samu zuwa ba saboda kafan ta ya matsa mata kwana biyu kuma. Su Adama ne su ka zo da sakon Abbah. Ba laifi ranar nayi murna sosai.

Na maida hankali na ga karatu sosai, ganin nan yafi Islamic center competition. Muna karatu da Halima da wasu friends inmu Wanda mostly ni ke koya musu abubuwan da na gane a aji. School activities ko irin su labor sau dayawa ba mu cika yi ba saboda Anty Nainah ba ta bari a samu ga senior Zainab kawarta so ba yanda aka iya. Zagi kam muna shan shi, taren latti kam ban yarda a kamani sai randa tsautsayi ya afka. Tsakanina da malamai ko lafiya kalau, domin ba malamin da zai yi pointing ina yace ina da matsala dashi, sai ma yabo na da su ke yawan yi. Har seniors in ma sai dai irin Wanda ke daura ma mutum laifi ba gaira ba dalili. Sai da yan ajinmu da yan gaban mu akwai masu jin haushi na saboda Anty Nainah. Ni dai ba Wanda na ke shiga sabgan shi, kwata kwata ban cikin marasa jin mate, da banda duka ba abinda su ke sha a makarantar, kullum suna cikin case. Halima kam ba ta da wayon da har za ta ma wani rashin kunya amma Ajiddah kam A ce. Nayi nayi ta daina amma ina, abin yafi karfi na, ya zamo sai dai in tazo tana kuka in lallashe ta.

A gaskiya ni dai banji rayuwan makaranta kaman yanda kowa ke ji ba, don na gwammace ayi ta zama a makarantar akan gida. Duk lokacin da nayi tunanin saina yi godiya ga Anty Nainah, domin ita ce silar komai...

A haka muka fara jarrabawa, Karatun na ke sosai bbu kama hannu yaro, duk da duk yawancin karatun koyawa mutane na ke hakan ba karamin taimako na yake ba. Sai dai karatuna na islamiyya kam ya ja baya sosai, duk ina bitan qur'ani amma kuma ban samun kari. Ko da na fadawa Ummi ce min tayi "bakomai in mun koma gida za mu cigaba"

Tun da mu ka fara jarrabawa na rage zuwa gun Anty Nainah, sai ya zamo yawancin sai dai mu hadu kan hanya. Ta kance "lallai kanwar tawa ta manta dani, karatu ya dauke min ke" dariya kawai na ke in wuce, duk da haka ba ta fasa min komai da ta ke min ba.

Ranar da aka gama jarrabawa da yamma, mu ka fiddo wankin mu zamu yi ni da Ajiddah. Ita dai Halima ko gwada wankin ma ba ta taba yi ba, ni ban ma tunanin ta iya ba kwata kwata. Tana gefe da wasu mate inmu, dayawa suna wankin kaman mu wasu kuma muna hira. Sanyi ake sosai da ke farkon December ne masu kokarin wanna na hada hadan daura ruwan zafi a katon murhun da aka kawo da babban tukunya. Anty Nainah ne su ka shigo da senior Zainab, da alamun su ma ruwan wanka su kazo nema. Har ta wuce ba ta ganmu ba, Halima ta fara kwala mata kira. Da sauri ta juyo tana fadin "yauwa daman ina nemanki, Ya Zaid na son Ku gaisa"

"Waya kuka yi dashi?" Ta tmby. Ya Zaid saurayin Anty Nainah, duk cikin samarin ta tafi ji dashi kuma tafi son shi, Family friend in sune. Kuma iyayen su mata first cousins ne. Saboda shi kullum tana gidan su a Abuja Hutu. Shi ma musamman in yana kasar yana zuwa Damaturu kawai don ya ganta. A gida kowa ya Sani, jira ake dukkansu su gama karatu kawai ayi auren.

Magana su ka cigaba da yi tsakanin su. har za ta wuce ta dago kai ta ganni. Harara ta bini dashi sannan ta girgiza kai. Murmushi nayi domin tabbas na san na mata laifi. Kasa shiru tayi tace "abin har ya kai ki ganni ki ki min magana ko?" Hakuri na hau bata tace min "Wayace kiyi wanki? Bana hana ki ba"

"Yi hakuri Anty ba zan iya bari wasu su min wanki na bane bayan zan iya da kai na" sa wa ta ke a mana wanki, ni kuma ban son hakan. Ta yi ta wahalar da yaran mutane a kanmu tana sa ana jin haushi na a banza. Yanzu haka na gaba damu sun fara cin buri wahalan da za su bamu in har ta bar school in.

"Shknn tunda ba kya so ni sai in miki da kaina, ban so kina wahala kwata kwata" dariya nayi nace "kar ki damu ni kam na saba"

"Ai abinda ya sa ma ban son kiyin kenan. In kinzo school sai ki huta kar abun ya hade miki biyu na gidan ma i will tackle it"

Dariyan takaici nayi, a raina ina fadin ko taya za tayi hakan "Allah ki barshi kawai zanyi" na ce mata amma fir taki. Dole na barta, amma kuma nima na cewa nayi sai da mu kayi tare duka har da na Ajiddan mu kayi mu uku, ba laifi tana kokarin yi ma Ajiddan ma abubuwa ganin Kawa ta ce.

Haka satin banzan ya wuce, kullum ba abinda ake banda zama ayi ta hira sai ko masu kokarin karatun novel. Tsakanina da Anty Nainah ko mun saba sosai har ji nake daman ita ce yayata ba Adda Falmata ba. Har Saurayin ta Ya zaid ta na bani muna gaisawa, shima yana da kirki sosai. Har kitso ta sa aka mana kanana masu kyau da lalle.

Ranar hutu da safe, cike da farin ciki dalibai ke ta fita assembly cike da farin cikin tfy gida. Ni dai ganinan ne kawai, ko bakomai ina son ganin Goggo, in ga kafan na ta ko ta samu yayi sauki. Ban wani maida hankali a abinda ake yi ba a assembly sai da naji an kira sunan Anty Nainah a matsayin wanda ta zo na Uku a ajin su. Na San ina da kokari sosai amma ni ina zama in duba abinda aka koya mana, ina bita sosai. Amma Anty Nainah ba ka taba ganin ta tana karatu, kai ba ma tayi. Kawai dai she is naturally brilliant.

Ina cikin tunanin naji ana kiran "Suhaima Adam Bello" ni abin ma mamaki ya bani Saboda ban ma San anzo ajin mu ba. Bayan nan ma har ga Allah ban taba kawo zan zo first position ba Saboda competition in da akwai. Cike da farin ciki na amso result ina da gift in da aka bani. Ina ji a raina daman Ummiyna na nan in nuna mata, na San ba karamin alfahari za tayi dani ba. Anty Nainah ce ta rage min damuwan da na ke ciki Saboda yanda ta nuna jin dadin abinda na ci sosai. Wannan Karon ma da kyautatukan da ta bani.

Ban San wa zai zo dauka na, sai dai shiru hakan ya sa na fara zargin ko Abbah ba ya gida ne? Gashi su Ummi har sun tafi ban bisu ba. Ana zuwa daukan su Halima, Anty Nainah ta sa dole sai da na shiga motar su muka tafi. Ba gida mu kaje ba, gidan su da ke Commissioners quarters mu ka wuce. Sai da muka huta, muka ci abinci, nayi wanka. Mum insu ta bani bakin Abaya mai kyau na sa sannan mu ka tafi da driver in su da Anty Nainahn gidan mu. Ita kam Halima cewa tayi ta gaji, ramakon bacci za tayi ba zata bi mu ba.

A kofan gidan mu su kayi parking sannan mu ka fita. Da Al-lawan na fara cin karo, kallona yayi da murmushi a fuskan shi yace "kin hutar dani wlh Suhaima da yanzu na ke shirin zuwa dauko ki" na kan rasa kirki irin na Al-lawan. Wai a hakan shi kadai ne mai mutunci a gidan, amma har bayan azahar ace sai lokacin za a tafi dauko ni, bayan tun 8:00am na safe ake sakin dalibai. Gaisawa su kayi da Anty Nainah ba tare da ya tmby ni ita ma muka shiga gidan. A kofan shiga na ga Yaya baba, da ke lokacin December ne sunyi hutun school su ma.

Tsayawa yayi da mamaki yana kallon mu. Sai dai suna hada ido da Anty Nainah na ga ya saki murmushi. Daman dai na sa za a rina Saboda son matan shi yayi yawa, mamaki ne ya kama ni jin ta ambaci sunan shi. "Adams kai ne"

"Nainah ke ce a gidan mu?" Ya fada yana zaro idanu. "Mu dai shiga daga ciki" ya karasa, yana binta da kallon mamaki. Akwatina da ke hannun ta yayi saurin amsa, abin ma Sani sakin baki yayi gabadaya. Ba kowa a falon, hakan ya Sa nagane duk suna daki kenan. "Bara kira Anty Yana" ya baba ya fada yana nufan hanyan dakin ta. Girgiza kai kawai nayi na fara kokarin daukan akwatin nawa da ya ajiye na cewa Anty Nainah "bara in kai daki"

"Muje mana" ta fadi tana jan akwatin. Dakin na nan yanda na San shi ba, bai yi wani dauda ba sosai amma kam ba kaman ina nan ba. Kan gadona Anty Nainah ta zauna yayin da na ke nema wa akwatin wurin zama. Da ke daman gadaje biyu ne a dakin, daya nawa daya na Adda Falmata. In har ba ayi baki ba fa amma, domin ko da mutum daya ne ya zo gidan dole na nake sauka kasa in kwanta.

Adda Falmata ce ta fito daga toilet tana bin mu da kallo. Ganin haka Anty Nainah tace mata "sannun ki" kaman Wanda aka sa dole ta amsa da "yauwa sannu" gudun laifi yasa na gaishe ta tana tabe baki ta amsa. Ina gamawa muka fita falon. Ya baba sai murmushi ya ke, Anty Yanan na zaune kan kujera. Faran faran su ka gaisa da Anty Nainah sannan nima na gaishe ta. Ban tabbatar da an amshi bakuntan Anty Nainah sai da naga Sadiya ta kawo ma ta ruwa, zobo da donut. Ba ta wani ci ba tace za ta wuce gida. Ba Wanda ya tmby ta su suka dauko ni daga makaranta ne? Itan ma ba tayi bayani ba. Har Mota na fita rakata Yaya baba na bin mu a baya. "Adams ina abokin ka wai? Still alive?" Ta fada tana murmushi

"Eh dole kice haka ai tunda kin wulla mu a kwata"

"Wane ni? Yanzu ma ba wannan ba ashe Kaine Yayan Suhaima no wonder jinin mu ya hadu da ita ashe kanwata ce" washe hakora yayi yana fadin "kwarai kuwa"

Wayarta ta mika mishi tace "sa min numbanka ina so in dinga jin kanwata"

"Au kanwarki ma kawai ko" dariya tayi tace "after all is your number, we will talk, Suhaima sai munyi magana ko?" Gyada mata kai nayi ina fadin "nagode Anty Allah ya saka da alheri" harara na tayi sannan ta shigo mota su ka wuce.

Muna shiga falon, Anty Yana ta cewa Ya baba "wannan ba yar gidan Barr Bello jajere bane?"

"Eh tace mana Anty Yana" Ya amsa

"To ke Suhaima ina kika Santa?"

"Anty Yana Yayar kanwata ce Halima, su suka dauko ni daga makaranta" tabe baki Anty Yana tayi tace "ke kam kin iya kwashe kwashe" ban tanka ba sai Adda Falmata tace "ni kam ba NTIC mamudo ta ke bane?"

"Baban ta ya cire ta wai ba taji, kinsan lokacin soyayya su ke da Daddy Dafchi Saboda shi ma aka cire ta"

"Yaya baba Daddy abokin ka" Adda Falmata ta tmby. Ni kam wuce wana daki nayi domin in shirya.

Tun daga lokacin na samu sauki daga gun Ya baba, ban San me ya shiga tsakanin su da Anty Nainah ba amma yawancin kullum sai ya bani wayan shi munyi magana da ita. Kai har abubuwa ya kan siyo min hakanan kurum. Adda Falmata kam in dai gaban shi za ta min abu ba ta isa ba. Wani aikin gidan ma dole ya ke sata ta taya ni, hakan yasa na samu dan sauki a abubuwa da dama.

Wani weekend ina gidan Goggo, mun je islamiyya da su Ummi mun dawo, ina shafawa Goggo man zafi a kafan ta kawai naji sallaman mutane. Anty bilki ce ta leko dakin Goggo tace min "Suhaima ki zo wasu yan mata sun zo suna tmbyn ki" "toh fa" na ambata ina tunanin su waye za su zo wurina.

Halima na fara gani sai ko Anty Nainah a gefen ta. Kasa boye mamakina nayi kawai na tsaya ina kallon su ina zaro idanu "Ko mu tafi ne?" Anty Nainah ta fada. Da gudu na karasa na rungume ta sannan na rungume Halima. "Mun zo gaida Goggo ne" Anty Nainah ta fada. Dakin Goggon na kai su, su ka gaisa. Sun kawo mata fruit kala kala. Wasa wasa su kayi ta hira da Goggo, daman na bata lbrn ta ai ko na tayi ta mata godiya da sa mata albarka. Na dauka lokacin za su tafi amma Halima tace min wuni za suyi. Har side in Anty Amarya mu kaje, mun dade a can. Kasa hakuri nayi na tmby ta tsakanin ta da Ya baba "son mata fa gareshi Anty" dariya tayi sosai har da rike ciki sannan tace min "come on am just fooling him around saboda ya kula min da kanwata ni da nake da mijin aure" lallai na jinjina wa idea inta. Tare mu kaci abinci muna ta lbr da ita. Halima ko Ummi na shigo su ka kebe suna hira, daman Halima ta fi shiri dama sabo da Ummi a kaina. Hakan yana da alaka da rashin surutu na, sai Wanda ya San ta yanda zai bi da nine mu ke sakewa dashi. Sai bayan magriba sannan mum tazo daukan su. Ita ma har ciki ta shigo ta gaida Goggo sannan su ka wuce. Har a raina naji dadin zuwan su sosai.

Kaman da wasa har hutu ya kare mu ka koma makaranta. Sau da dama na kan zauna inyi tunanin guduwa nima a nemi ni a rasa kaman yanda mahaifiyar tawa tayi, sai da na kan tmby kaina ina zanje? Na kanji ana cewa duniyan fadi gare ta, ni ko ba wanda na Sani balle in he wurin. Wahalan duniya kam ba Wanda ban sha ba wurin Anty Yana da yaran ta, har sadiya tsab ta ke takani, ta fada min abinda ta ga dama kuma a zauna lfy. Ance ba a sabo da wahala amma nikam ba ya zame jikin a cikin gidan nan. Sai da akayi zamanin da ko tsinke in wani zai dauka sai na zo na dauko mishi. Duk ciki ba abinda ke kona min rai kaman aiken daren da ake hada ni dashi, duk dare kaman aikin farilla dole sai nayi shi duk don a dalilin rashin mahaifiyata. Ummi ba ta min adalci ba a rayuwa, kowani memories inta banda shi na arziki. Wadanda na dan rike ma a hankali su ke tafiya, tun ina yawan tuna t har yazo sai an zage ta ko an aiba ta ta ke fado min a rai.

Rayuwan makarantar ya cigaba da tafiya kaman yanda ya ke a kullum. Class, hostel, dinning, masallaci da sauran su. Still Anty Nainah ta tsaya min sai dai a yanzu ban yarda ta sa a min abubuwa saboda nagane bakin jini hakan ke ja mana. Duk abinda mu ke bukata sai dai muje tare da ita a nemo shi yafi sauki, sannan ko dan Halima da sangarcin ta yayi yawa. Bada ban Anty Nainah i used to wonder yanda za tayi coping da school life in.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top