Talatin da bakwai
Rayuwata
Babi na goma
Ranar gabadaya wuni nayi a kitchen a sandiyyan da bakin da aka yi a gidan. Wandan da kwata kwata ma banda hadi dasu. Amma hakanann na jifgan musu aiki. Abinda na lura kuwa shine kaman duk yan'uwan Anty Yana irin halin ta ne dasu, sam sam ba wanda ke da kirki cikin su. Duk randa mu ka hada hanya banda zagi datsangwama su inma ba abinda ke shiga tsakanina dasu. Cikin wadanda su ka zo ranar kuwa har da wata yar uwar su Safina, mugun halin ta kuwa sak irin na Adda Falmata, shiyasa nake ga tasu yazo daya.
Bayan na gama kwasan aikin ne, a gajiye likis na nufi dakin da niyyan sannan in nemi gado dan banji zan iya wani abu a ranar. Abun mamaki, kaya na nagani na makaranta sun yi watsa watsa dashi a tsakiyan dakin. Still nayi ina kallon su, a raina kuwa na tsaya neman meya hada su da kayana. "Bakar munafuka karaso da uwar ki gantallaleyi yau dai Allah ya kama ki" Adda Falmata ce take maganan, daga irin kallon da take min nasan yau nai kwata na a wurin ta kuwa sai yabda Allah yayi kawai. Ban karasan ba duk da nasan irin abinda zai biyo baya, bugu ne na riga nasan bawanda bazan sha ba a ranar, don haka gwara inki matsawan ko bakomai a min wanda ke da dalili komin kankantan shi kuwa.
"Ba na fada miki na taba ganin su a Ajeyari da wannan abokin Al-lawan in da suke zuwa daga kaduna ba, kika ce mai zai yi da ita?" Safinan ce wannan karon ta ke magana tana nuna ma Adda Falmata, pictures inda Amir ya bani ana washegari za su tafi. Wata kam sai a lokacin nasan in bala'i ya maka yawa ba wawanci da baka iya yi. Domin dai a lokacin daren da Amir zai tafi na tuno, yanda yazo ya same ni yana gaya min ba fa a daga tafyn su ba, gobe in sha Allahu za su tafi. Ban san sanda naji kwalla sun ciki min ido ba, akwai shakuwa na musamman kuma na daban da ke tsakanina da shi. Shi kanshi ya fuskanci halin da na shiga amma kuma sai ya dan fuske gudun ya sani kukan gabadaya.
Cikin siririn murya mai dauke da rauni nace "Sai yaushe kuma?"
"Wani Long vacation Suhaima, ai muna waya in sha Allahu ba wani matsala" juya kaina nayi a hankali wasu banzayen tunani su ka fara min yawa a kwakwalwa.
"Long vacation Amir, shekara daya fa kenan kuma kake kiran ba matsala? Abubuwa da dama za su iya faruwa a shekara daya, Haka kuma abubuwa da dama su kan iya canjawa ciki kuwa har da yanda muke ji akan junan mu. Za ka tafi bayan ka riga da ka saba wa zuciyata kusanci da kai, banjin xai iya rashin ka na wannan lokacin" shi din ma jikin shi ne yayi sanyi, juyiwa yayi ya fuskance ni da kyau
"Hakika Suhaima da ina da wani hanyan da zan iya ganin kafin cikan wannan lokacin wlh da nayi, za a iya ganina har yanzu karami amma Wlh ban dau lamarin ki da wasa. Ina sonki irin soyayyan da ban jin zan kara duban wata ya mace a duniya dashi ba fa wai zuciyata kadai ke sonki, Aa da dukkan dyj wani abu da ke jiki na nake sonki My future wife, Dan Allah ke daina damuwan nan kinsan ban so ko?" A shagwabe na daga mishi kai, tun asali daman ni din shagwabibiya ce, rashin Ummina ya sa ba wanda ya fuskanci hakan. Amma tun da na samu Ameer na ke sakin abu na kuma shi abun burge shi na yake, ya sha fadin yana kaunar mace mai shagwaba. Don ko Anty Nainerh, she is the weak one among us, shiyasa nan da nan za ta rafke.
"To mai zai hana ka zuwa amma?" Yanzun ma da shagwaban na mishi magana, sai da ya saki wani irin murmushi wanda kana gani kasan sautin muryana ba karamin ratsa shi yake ba. Kai ina son Amir, irin yanda ba zan iya fasaltawa ba. "Final year fa zan shiga, zan yi jamb, waec, Neco ga zaman extensions in da zamu yi kusan uku sannan kuma inyi facing graduation. Kar ki damu i want to focus ya da zan samu admission in University nan da nan inyi kudin da zan aure ki in fidda ki daga wannan kangin, i don't like your curre t situation Suhaima zan so ace ina da daman fidda ki, i want to fight for us no matter what" Wani irin dadin da na manta rabo na dashi naji yana ratsa ni "My heart can't never be free for anyone my future, i love you" Cike da kunya nayi maganan, wanda hakan ma yace yana burge shi. Kalaman kuwa duk a wurin ajiddah nake tsinta, ita ce malama ta a kowani fannin na rayuwa. Hannu na ya kamo duka biyu ya daura fuskan shi yana so in dago kaina sai dai na kasa hakan. A hankali shima yace "Na dade da gane we are made fir each other my love saboda tun ranar da na fara ganin ki, zuciya ta ke doka miki" ya fada yana taba saitin zuciyan nashi. Duk yanda na so daurewa ranar sai da nayi kwalla lokacin da zamu rabu. Life is crazy, so as love.
Rankwashin da Adda falmata ta zabga min akai ne ya dawo dani daga duniyan tunanin abin kaunata da na shiga. Ban ma jin bala'in da take min tsabagen yanda saukan rankwashin nata ya gurgiza kwakwalwata. "Uban wa ya baki wayan nan?" Tmby da ya fito bakin ta kenan. Ban ko yi wata wata ba nace "Amir ne"
"Uban waye shi?"
Kai tsaye nace "Wanda Anty Safina ta fada miki" dukkan su wani irin kallo su ka jefe ni dashi, ko basu furta ba na son so suke suce wato wuyana ya isa yanka. "Dan wani dan iskan barawon ne shi da zai iya saya miki wayan?" Ta fada tana kallon wayan, kallon shi kawai take tana sakewa don ban ma san kudin wayan na da tsada hakan ba sai da naji tana fadan kudin.
"Amma dai kinsan Falmata hakanan dai ba zai dauki wannan abu mai uban tsada ya bata ba ko?" Kaman wacce aka zabura Adda Falmata ta juya tana kallon safina alamun son karin bayani. Algunguman sai cewa tayi "kila dai tana tsammi shi wani abu maza ai basa abu hakanan a zamanin nan wlh" tsaki Adda Falmata taja tace "wai me kike nufi ne ni?"
"Yana kwanciya da ita mana tana buda mishi kafafu"
"Ya subhanallah!" Shine abinda ya futo daga baki na. Adda falmata kam wani gigucewa tayi ba ta ma kalle ni ma sai ma daga kai da take ta faman yi alamun fahimtan abinda yar'uwan nata tace "Tabbas hakan nema" ba ko karamin doubt ta furta hakan daukan wayan tayi ta juyo tana kallona. Kai duniya wanda ya tsane ka ba zai taba son ka ba wlh, kiri kiri matan nan ta dauki wayan nan duk da makudan kudin da ta ambata ya kai, haka tayi sama dashi ta sa iya karfinta sannan ta sake shi a kasa. Hakan ma bai mata ba kaman wata mahaukaciya ta kara zabura ta dauko wayan ta kara hadashi da bango har sai da ya tarwatse. Budan bakin ta kuwa ce tayi "bai ki matsayin da zaki rike wayan da ban taba rike ta ba wlh, na fasa ne don kar ma in nuna ace in bar miki bakin ciki ya kashe ni gwara in dagargazan inki fadawa Abban duk da na sofada mishi ne ya dau mummunar mataki akan ki" Safina kam sake baki tayi tana kallon wayan "Amma Falmata baki da hankali ai da sai ki bari ke din ki amfana da ita" girgiza kai tayi sai wani huci take kaman wata zakan ya "Allah ya kyauta, wlh na fi karfin in rike abinda wannan yarinyar ta rike. Gwara kowa ya rasa" Tabe baki Safina tayi tace "ai to da sai mu saida" wannan karin kam dariya tayi tace "Ayya Safina baki san ni ba ashe, ai duk tsada da mahimmanci abu in dai zai biyi ta hannin wannan yarinyar to wlh ban son shi. Na rifa da nafi karfin ta, kai ban ma yarda dake ba" Tace sannan ta mike ta fara kokarin zubi da sauran kayana, Safinan na taya ta. Ni dai motain kirki banyi ina gani har aka gama fiddo kai, ban ankara ba naga sun hankado jakan da letters in Anty Nainerh ke ciki. Jiki na rawa nayi saurin daukan jakan na rungune shi a jikina, ashe babban kuskurw nayi domin kila da ban dau jakan ba da basu bude ta ba. Amma abinda nayi ya jawo gabadaya hankalin su ya koma kan jakan, wani irin fisgewa da suka yi a jikina sai da yaja nayi wani taga taga kafin na fadi sharban a kasa. Amma ba tani ma suke ba, illa ma rige rigen bude jakan da su ke. Sai da su ka zazzago papera in gabadaya sannan karaman wayan ya fado. "Au kice ba ma shine na farko ba?" Safina ce ta fada sannan tayi saurin kunshe wayan saboda kar Adda Falamata ta fasa. Sarkokin duk da Anty Nainerh ta bani su ke ta fiddowa suna sakan baki. Adsa Fakamata banda kwafa ba abinda take, Safina ko sai faman fadin "Ai na gaya miki daman jikin ta ta bashi, in ba haka ba shi mahaukacine da zai kwashi wadannan duk abubuwan ya bata? Allah ma yasa kanshi kadai ya tsaya" ni ko roka na daya kar su bude takardun nan, don in abun ya tsaya a Ameer kadai to fa komai zai zo da sauki. Sai dai ban gama wannan tunanin ba na gama Adda Falamata ta bude wani takardan tana karantawa. Girgiza kai naga ta fara yi sai ga wani murmushin mugunta yaba fito daga fuskan ta. "Lfy kike murmushi Falmata?" Amsa Safinan tayi da cewa "Kema dauki daya ki karanta you must smile" haka kuwa akayi, ina jin suna karanta letters in a fili. Wanda kiri kiri ke kunshe da kalaman soyayya, gashi kuam sun ga sunann mace a karshen ko wani letter. Daman duk letter in da ta bani a kasa sai ta rubuta Nainerh, sannan ta sa date.
Zaman dirshan kawai nayi a kasa ina jiran the worst ya faru domin ba abinda su ka rage ba su karanta ba. "I can't wait to hold you, touch you, kiss you and tell you how much of you i want" dariya take sosai tana karantawa. A lokacin kuma na san banda bajin da zan iya defending kaina cewa ba abinda ya tava shiga tsakanina da Anty Nainerh na gogaggayar jiki. Wani kululun bakin ciki naji ya taru ya tsaya min a makoshi, ji nake kaman in na hadiye to rayuwa ta zan hadiye. Ba abinda nake gani a gabana illa tsan duhu, don har abinda su ke fada ma dawowa nayi banjin komai. Sai wani dum da ya taru ya min yawa, hakika bala'in duniya kuma banjin akwai wanda ya rage ban gani ba. Wannan wani irin rayuwa ce? Tmby da na dinga jefo ma kaina kenan. Ban kara jin komai ba sai karan dariyan su sadiya kai ba ma su kadai bane yawan su yasa na gane harda kawayen su, wadanda dayawa daga ciki akwai yan gidan su Sanda. Kafin kace kwabo gidan ya tashi banda ihun yara ba abinda kake ji suna ta faman fadin "An kama yar madigo an kama kazama matsinaciya, la'ananna" kidan da Abty Falamata da Safina ke faman yi yasa yara dayawa ke kara kutso kai cikin gidan mu har zuwa dakin baccin mu, a namin kida a na kira na da sunayen da ko makiyi na ban fatan wani ya ambace shi da hakan. Wlh a ranar na fara sanin kuka na kafe ma mutum yaki zuwa. Su Adama basa nan, nasan da hayaniya ya kai gidan su kuma da ko ita ko Goggo wani sai yazo. A haka Yaya baba su ka shigo shi da abokanan shi guda biyu. "Kai lafiya miye haka? Wannan wani irin waka ne?" Muryan shi kadai naji na gane shine, bakomai kuwa ya sani rike muryan nashi bane sai lokacin da yake duba na a fuska yana gaya min ba shi ya kar zomon ba dan uwata ta tagi in daina hararan shi. Sai kuwa lokuttan da ya dinga min dariya in ina wahala haka wahakan dayake bani dukkan lokuttan da nake zuwa gidan su deban ruwa. Hakika na fi jin haushin shi da irin su Safina, sabida ina jin cewa su baruwan su, don si in su Falmata sunyi kilan uwar su suke tayawa kishi. Ihu yake yana musu tsawa su daina wakan da suke, sai dai shi dinma nasan yana jin abinda nayi dariyan zai min kaman yaran. Da kyar yaran nan su ka fita daga gidan, ni dai gani kawai a wurge a kasa. Bai kuwa ko kalle ni ba naji yana cewa Adda Falmata "lafiya me ya faru?" Sai lokacin naji muryan Yaya baba yana fada min "Wannan baun kuma meya same ta?" Matsayi ma na samu da har ya iya tmbyn abinda ke damuna so dan ya kira ni da abu bai ya zama wani kayan gabbas ba. Shi dai dayan abokin bai ce komai ya juya ya fita. Da shu'umanci ji nayi Adda Falmata na cewa sandan "Ya Umar Sanda baki cairo yaushe ka shigo?" Bai amsa ta ba sai ma kallon da ya watsa mata akamun yana jiran amsan ta. Na dade da sanin cewa Adda Falmata na son Umar sanda, yanayin ta kadai a gaban shi daban ne.
Bata ce komai ba ta dauko letters in nan ta mika musu. Sandan ne yayi saurin amsa ya fara karantawa, girgiza kai kawai yayi sanann yace "To miye na tara mutanen Falamata? Ba kanwar ki bane? Meye sa baki hukun tata ba?" Ba tace komai ba, kuma nafi alakan ta hakan da ba ta son ta fadi abunda zai bata mishi rai ne, har yaga aibunta.
"No wonder munafukai ashe ni kuka sa a corner ko dan uwarki" Yaya baba naji yana maganan yana kwafa "ai gwara da kuka yi ma yar shegiyar haka ita ma Nainerhn sai naci Uwar ta wlh. Yan iska, tsinannu, asararru" Yanda ya fita kaman an kore shi sai kace zai je yayi ma Anty nainerhn wani abi, bayan nasan ko ganin ta yayi yanzu a gaban shi bai iya tabuka uban komai.
"Taso Suhaima" abinda Umar Sanda ya fada kenan, sai dai kallon banza ma bai ishe ni ba. In taso in mai uban me? Ya cigabada wulakanta ni bayan na baya daya min.
"Taso mana" ko kalla dai ban ce ba. Hakan yasa ya gane ba magana zan mishi ba.
"Shikenan tunda kin zabi hakan" kawai yace ya fita. Ko a jikina kuwa, don nasan shi inma wani muguntan ne a ranshi. Adda falnata kuwa cewa tayi "wlh da kin bishi yau ba dukkan da zan miki sai kin manta kanki" akan abinda ta min yau, wlh ji nayi dama dukkan da ta saba min in tayi.
Ko da Anty Yana ta dawo daga inda taje ta tadda labarin. Ba ta wani girgiza ba tace "to abun mamaki ne? Ku ka san mai Uwar ta take? Ai gado ba karambani ba" Ko kadan kalaman Anty yana bai dameni ba don dai duk tafi min yaran nata. Da ta ita ne ba ta damu Abba yaji zancen ba don letters inma ba wanda ta amsa ta karanta. Kai irin tsanan da Anty Yana ta min irin tsanan nan ne na komai naki baya gaba na, ko kadan ban dame ta ba kuwa. Illa iya ka ta sani aiki in mata kawai shikenan.
A cikin Yaya baba da Adda Falmata bansan waya kai ma Abba letters in ba bayan ya dawo. Ranar irin dukan da yamin ban jin ya taba ma wani a rayuwan shi, dukkan jiki na sai da ya farfashe ba kuma wanda ya bashi hakuri a cikin gidan mu. Ihu na yasa abun dangatawa da makota, Umar sanda shi ya shigo ya fisge ni daga wurin Abbah ko daya nemi kai ni asibiti kuwa na watsa mishi rashin kunya har ma da zagi sannan na gudu gidan su Adama. Goggon ce ta kaini asibiti, tayi jinya na ba wanda ya leko a gidan mu. Yan ajeyari kuma basu sani ba. Baban Adama yayi settling bills ina lokacin da za a sallamo mu. Kwana kusan uku gidan ta sai da ta fuskanci na ji sauki sannan ta sa ni a gaba tana tmbyna me ya faru. Tsab na sanar mata abinda ya faru haka kuma tsakanina da Nainerh. "Asha asha nifa shiyasa ban son makarantan kwanan nan kuma in sha Allahu kin gama ta" daganan ba ta kara min zancen ba. Abbah boye ma Goggon Ajeyari zancen yayi sannan kuma ya gargadi yaran shi akan fada mata in.
Unguwan mu ko gabadaya ya dauka, mata na biki kai har da kirkirarrun labaran da ban san daga ina su ka fito ba duk yawo kawai su ke, duk na bi na tsangwami kaina na rame na zama wani abun. Inda Allah ya taimaka kwata kwata Anty Nainerh ba tazo wurin a ba kaman yabda tasa da nasa ba abinda zai hana Sdda Falmata tasa a bita da jifa. Abu ya kai ya kawo ko fita nayi yaran sun dinga bina kenan suna min wakan da Adsa Falmata ta koya musu. A karashe dai Goggo har guda ta taka taje ta warware wa Abbah, nasan hakan ne sabida yanda ta dawo tana ta masifa. Daganan kuma ranar da dare yazo ya dauke ni, sai da na shiga motan na ga gabadaya kaya nane a ciki. Duk yands na so ko dariya ya min ba fuskan hakan. Ajeyari ya kaini, bayan sun gaisa da Goggo naji yana fadin "Goggo ga Suhaima na kawo miki za ta zauna a nan har tsawon wani lokaci" Wlh a loakcin naji wani irin sangi na ratsa ni.
"Ince ko makaranta za ta koma?" Goggon ta bida. "Na canja mata makaranta, za suje da Garba ya mata Register a Nana Aisha"
"Ma sha Allah" kawai Goggo ta fada. Bai wani dade ba ya bar gidan. Daga lokacin kuwa na fara rayuwata a ajeyari.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top