Sha Uku

Fuskan tan abinda ba ka shirya mai ba karamin rikice ne dashi ba. A kwana biyun nan gabadaya Barr Mustapha ya shiga wani mawuyacin hali. Da dukkan zuciya da karfin guiwan shi ya ke jin son tsaya ma Suhaima. Sai dai, gabadaya ya kasa gane in dai zai fuskanto wa abin. Yayi magana da Faroukh sai dai bai samo wani abin Kirki ba. Yawancin labarin akan abinda ya sani tsakanin Suhaiman da budurwa zayd ne da kuma shi kanshi zayd. Ga fahimtar Faroukh, suhaima na da wani mugun nufi tuntuni akan zayd da ta ke boyewa. Abubuwan dai duk rudani su ka kara mishi, shi da ya ke neman hanyan kare ta gabadaya points in da Faroukh ya bashi is aginst her. Karin karawa yana mamakin a ce wai Suhaima ce ta aika ta wannan abubuwan. Tirkashin fa kenan!

Yau ya ke shirin koma wa Abuja, yana bukatar ganin Suhaiman su cigaba da tattaunawa kan lamarin. Abinci mai rai da lafiya Maryam ta hada mai, yayi farin ciki sosai duk da bai iya sakin jiki ya ci abincin da kyau ba. Hira ta ke mishi jefi jefi tana sako mishi kishin ta "Mu dai kam Suhaima ta dauke mana kai" za ta fada sai kuma ta waske kaman wasa ta ke. Sai dai ba halin mimin nashi da bai sani ba, a yanzu ba wannan bane matsalan domin bai da karfin guiwan yi mata bayani ba, in har ita da kanta ba ta san ya kamata ba.

Buzz buzz, karan wayan shi ya dawo dashi daga tunanin da ya dan fada. New numba ne hakan ya sa shi sharewa sai dai yanda calls ke ta shigowa wayan ya sa shi daukan wayan dole. Sai ya dauka ya ji muryan mace sannan ya kara duba numban da kyau, sai lokacin ya gane numban da suhaima ta bashi ne.

"Hello" yayi saurin fada gudun ta katse wayan.

"Ehmm ina jinkaaa ai,  na ji kayi shiru ne" ciki da duniyan ci ta ke magana, sai dai daga yanayin sautin muryan ta za ka gane hausa bai gama zama a bakin ta da kyau.

"Dan Allah ina magana da Zeenah ne?"

"Zeenah ke magana amma fa in kana bukatan harka ne dole kayi hakuri zuwa ranar Alhamis, bana cikin lagos" shiru yayi yana mamakin rashin kunya a fila irin wannan, sai kuma wani abu ke gaya mishi to daman kana bukatar ganin kunya gun karuwa ne?

"Amma kina ina ne? Dan gsky a matse na ke kuma ke kadai ce na ke ganin za ki iya kore min kishin ruwa ta" ya mata hakan ne don ya samu hadin kai sosai a wurin ta.

Wani shakiyin dariya tayi tace "toh fa, maza a samu labarin mu kenan. Gsky nayi nesa da lagos sosai"

"Kar ki samu wani damuwa ko ina kike dole ne in biyo ki ai" ya amsa ta cike da kosawa wannan karan, burin shi dai yaji garin da ta ke in yaso daganan ya tattauna da Dr sun san yanda za su bullo wa abun.

"Asuban cin bari garin kaduna zan yi zuwa birnin tarayya gobe in Allah ya kaimu" ai bai san sanda ya saki wani ajiyan zuciya ba, jin komai na kokarin zuwa mi shi da sauki.

"Yana ji kayi shiru?" Ta kara fadi, don har ta fara murnar kamun da tayi.

"Ina garin kaduna yanzu haka, ya za ayi mu hadu"

"Kai kai ina tare da wani mugun ne fa, da zai yiwa da mun hadu a Abujan gobe in za ka iya" ta amsa shi tana faman ya amince ds hakan, wanda ta ke tare dashi in bata ganin zai bata damar fita wuri ita kadai.

"Haba yan mata da dai kin taimaka min mun hadu a yau in, na fada a kagauce na ke fa" shiru tayi tana tunani sannan tace "zanyi kokarin fitowa mu hadun amma fa ba za mu dade, dama za kayi hakurin goben ne"

"Kar ki wani damu ba sai kin daden ba in yaso na kara biyo ki Abujan mu karasa a can. Yau dai a takure na ke wlh" dariya tayi sannan tace "yanda na ke jin ka in nan na san gurzu, ina dai fatan ka tanaji dumus dayawa"

"Kar ki wani damu kinji, ki dai lallaba ki zo in kawai" a marairaice ya ke maganan yanda zai samu tazo in kawai.

"Zan fito nan da yan mintuna bayan mugun nawa ya fita wani meeting, ina zan ganka?"

"Hotel seventeen, in ki fito ki kirani" yana kashe wa ya fara mamakin yanda tayi saurin amincewa dashi, to yanzu kaddara ma ace ba dan yankan kai bane ace wani mugun nufi ya ke dashi akan ta fa. "Allah ya kyauta mana amma karuwanci ba karamin illa ya ke dashi ba" ya fada a ranshi yana jan motan zuwa hotel in, don ya jira ta a can.

Ya kusa cika mintuna talatin a haraban hotel in kafin ta iso. "Muje ko?" Ta fada tana kashe mishi ido, murmushin dole hakan ya sa shi. Sanye ta ke cikin light brown abaya mai stones a jiki, shigan ya mata kyau ba laifi a hakan kaman na kwarai. Daga ganin alamun ta kadai Mustapha ya gane akwai rawan kai da surutu a tattare da ita.

"Kinsan me? Please zauna muyi magana kinji" zaro idanu tayi tana kallon shi tace "ban fa da enough time yana cika zan bar wurin kaga ko yanda na ganka in nan nima raina ya biya" dagowa yayi ya kalle ta, rashin kunya fal idanun ta.

"Karki damu ki zauna muyi magana Dan Allah" ba dan taso ba ta zauna tana kallonshi kamar wata mayya mai niyyar lashe shi. Au'uziyya yayi dan neman sharrin shaidan sannan yace mata "kiyi hakuri in na sa ran ki ya biya kaman yanda kika fada,  gsky na kira ki nan ne saboda ina so muyi magana" da fari mamaki ne ya cika mata idanu sai daga baya kuma jikin ta ya fara yin la'asar. Ita har ga Allah ba ta so hakan ba. Hakuri ya kara bata sannan yace "ko kinsan wata Kawa Yar baiwa?"

"Naam" tayi saurin fada tana kara zaman ta da kyau.

"Na san ta mana, ba dai ita kake nema ba ko? Domin dai ta dade da barin barik... au" saurin rufe bakin ta tayi sannan tace "yi hakuri fa, mun yi kawance da ita a da sosai amma tun da mu ka rabu ban san inda ta ke ba sai dai in ta neme ni, kuma yanzu an kwana biyu gsky banji duriyanta ba" shi dai mustapha gabadaya sauraren ta ya keyi kawai, amma tunda ta danganta kalman barikida Suhaima yaji gabdaya zuciyan shi na dokawa da sauri. Shin me kuma zai ji gaba? Mai ya kai Suhaima bariki? Abin dai sam sam ba kama. Diran mikiya bakin ciki ya mishi a zuciyan shi, ko dai gsky anty ne ke son tabbata? Karuwan ci fa kenan?

Fuske wa yayi kokarin yi yace "Tana hannun yan sanda ne yanzu haka ana kotu."

"Kawa na hannun yan sanda? Shegiya Faree" saurin rufe bakin ta tayi tace "Sorry Dan Allah, gabadaya ban ji dadin abinda ka fada min bane. Duk da ba ma tare yanzu da kawa ina kaunar ta sosai a zuciyata ina kuma yawan kewan ta, kasan haduwan jin..."

Saurin katse ta yayi "Bail mu ke nema, ta bani numban ki in neme ki, tace ko nawa mu ke bukata na bailing in zaki bani" shiru ta dan yi tana kallon wani wuri, gabadaya yanayin ta ya canja "Allah sarki kawa wlh da masharran ta ta hadu da ni na sani. Ka fada ko nawan kake bukata sai in baka, amma babu cash sai a bank. In kuma cheque ne ma toh" hatta muryan da yanayin idanuwan ta sun canja.

"Cheque in mu ke bukata, kudin yana dayawa zai kai millions ba daya ba ba biyu"

"Ko yafi hakan ba matsala" a ranshi tunani ya ke ina su ka samu wannan kudin? Shin na Suhaiman ne ko kuma na ita zeenan? Ba wannan ke gaban shi ba dai a yanzu "Ba kin ce zaki Abuja ba gobe?" Nodding kai tayi, yace mata "tou shknn mu hadu a Abujan zan kira ki,  just make sure kin dauki wayan sannan ina so mu tattauna kan case in amma na ga kaman yanzu kina sauri ko?"

"Mu hadu a Abuja" kawai tace tana shirin mikewa "oh sorry" tayi saurin fada sannan ta koma ta zauna. "Ni fa nayi burin samun wani abu, gashi kuma cinikin mu bai fada ba ya za ayi kenan?"

Confuse look ya aika mata, da ta gane hakan sai tace mishi "ka gane tunda wancan in ba zai samu ba sai a bani wani abu na sa min ran da akayi" dan siririn dariya yayi da yaga gano inda ta nufa "nawa zan baki toh?"

"Tunda maganan kawa mu kayi i won't charge you much, ko 30k ma ai yayi" dariya yayi wannan karon sosai, lallai kudi sauki ne dasu a wani wuraren, wato ita har tayi aikin dubu talatin. Yanzu akan wannan kananan kudin wai su ke saida Jikin su anyhow? Hmmm! Allah ya kyauta kawai. "Send me your account details" ya fada sannan duk su ka mike a tare.

...

Bayan ya gama dukkan wani abinda ke gaban shi, ya kama hanyan Abuja. Yana tafiya yana tunanin yanda zai bullo wa case in zeenah. Ga na wurin Faroukh, zai so ace Faroukh in ya zame mishi shaida sai dai yana tsoron yanayin Faroukh, duba da har yanzu bai amince da Suhaiman ba. Ba laifi akwai kokarin da Dr Fahad ke mishi, wanda ya ke fatan gabatar dasu a gaban kotu har a samu daman bail in.

Yana isa bai ko tsaya wani hutu ba, police station ya wuce domin samun daman ganawa da Suhaima. Yau kam yanayin ta gabadaya ya baci, ta kara duhu sosai, idanun ta sun shige ciki, tayi wani fayau kaman mai fama da wani babban cuta. Kallon ta Barr ya tsaya yi yana jin wani tausayin ta na ratsa shi.

"Yi hakuri ba mu samu daman bailing inki ba" shine farkon abinda ya fara fitowa daga bakin Barristern.

Ko murmushin karfin hali ba ta kakalo ba, fuskan ta kaman yanda ya ke tace "kai fa kace shari'a sabanin hankali ne ina" daga kan shi yayi alaman tabbatr da maganan shi.

"Kun hadu da kawa" ta tmby, kanta a kasa ta ma kasa focusing mai za tayi. Tunani? Ta gaji da hango abinda ba lallai faruwan shi ba, haka kuma ta gaji da tuno abinda ya riga ya wuve kuna ba za ya gyaru ba. Bakin ciki? Wannan ya zama ita domin sun dade suna rayuwa a tare. Kuka kam ya fi karfin ta tun da fintinkau ya ki zuwa mata har ma a cikin wannan bala'i. Rudu da wasi wasi kam ba wanda ba tayi ba. Shiyasa dai gatanan kawai tana jiran yanda kaddara zai yi da rayuwan ta.

"Ban samu daman ganin ta ba sai jiya a kaduna, zamu hadu amma yau a nan za ta bani cheque in"  da kai ta amsa mishi.

"Ina bukatar jin labarin ki Suhaima, i mean abinda ke tsakanin ku da Zayd Al-mansur na ke son sani in details domin in san yanda zamu bullo wa shari'an nan" shiru tayi bata bashi amsa ba, a ranta kuwa tunani ta ke shin ta ina ma za ta fara?

"Ki daure ki fada min daga ko ina nema" furucin shi kaman wanda ya shigo zuciyan ta. "Na san is not easy but we have to talk" ya kara fadi.

"Labari ne mai matukar tsawo barrister, ban jin zai labartu a nan. In munyi nasarar na fita daga nan zan fada maka komai daki daki" ajiyar zuciya ya saki alaman gamsuwa.

"Shknn but bara na miki wasu yan tambayoyi" ba tare da ta amsa ba ya cigaba da fadin "ranar da abun ya afku kina ina ne?"

"Cikin gidan, daga ni sai zayd in a gidan" kai tsaye ta bashi amsa. Shi kam amsan nashi kara daure ma sa kai yayi, amma duk da haka dai ya cigaba.

"Bincike ya nuna anyi poisoning in shi, shin kinsan lokacin da ya ci abincin na karshe kafin  tashin gobaran?"

"Ni na dafa, yazo yace min yana jin yunwa, in taimaka in sa mishi wani abun, so i cook" ba tare da wani tunani ba ta ke bashi amsa, hakan ya ke tabbatar mishi iya gaskiyan shi kenan.

"Kinyi baki ne a ranar?"

"Mutane dayawa sun zo gidan a wannan ranar, sai dai duk sun bar gidan wuraren la'asar kafin ya dawo bayan magreeb shi daya."

"Kaman su wa kenan?"

"Mostly mutanen da mu ke aiki da su ne a karkashin Al-mansur. El-yas, pat, UK, Faroukh da Mr Bash."

"Kuma ba wanda kike zargi, ko kuma akwai wanda ya shiga kitchen inki a ranar"

"Kitchen is available to all of them ai"

"Amma waye last in tafiya"

"Na fita na bar Zayd da Faroukh tare a gida suna tattaunawa akan wani business insu, ban dade ba na dawo amma sun riga sun tafi by then" nodding kan shi yayi a fili yace "this is really complicated, i have to find all of them gsky"

"Amma kinci wannan abincin da kika dafa?" Girgiza kai tayi tace "ya kawo min snacks da shakes, nafi son su akan normal abinci musamman da dare."

Rike kai Barr Mustapha yayi yana jin kan nashi na wani irin sara wa na wahala. A can kasan ranshi wani abu na fada mishi wahalan banza kawai ya ke, anya Suhaima ba ta da sa hannu a cikin wannan lamari? Saurin koran tunanin yayi, shi dai kam ko ma menene yayi niyyan sai ya ga abunda ya ture wa buzu nadi.

"A cikin wadan da kika lissafo wa kika fi ganin zai bani hadin kai in na nemi magana dashi?"

"El-yas" tayi saurin fada "abokin Faroukh ne, best friends dan naji Faroukh in ya sha fadin El-yas ne ya mishi hanyan aikin da ya keyi" jinjina kai Barr yayi, tabbas ya san El-yas kuma abinda ta fada hakan ne.

"Anya wannan zai bani abin kirki? Alamun shi sun nuna he hardly talks"

"He is somewhat reserve" tace hade da dan yin shiru "amma i trust him ya fadi abinda ya sani"

A nan su ka tsaya sannan Barrister Mustapha ya mata sallama ya wuce. A ranar ya ke son ganin El-yas in.

...

Bai da numban El-yas in, hakan ya tilas ta mishi kiran Faroukh ya amshi numban. "Numban El-yas kuma?" Faroukh ya tambaya yana jinjina maganan bayan uncle in nashi ya sanar mishi bukatan shi.

"Ban kira ka min tmby ba Faroukh, just send the number i ask, okay?" Yana gam fadin hakan ya katse wayar.

Siririn tsaki Faroukh ya ja, kafin ya bude wayan shi domin tura numban. Wlh da ba Uncle Musty bane ba, da ba zai tura numban ba. To wai meye sa shi ba zai fuskanci gskyn Al'amari bane ya kyale yarinyan nan? Shi kam Allah bai daura mishi kaunar ta ko na minti daya, sam ba ta mishi, ko dan ya san asalin wacece ita ne? Amma ya san mai zai yi, Maryam zai je ya samu, ko da ba sa shiri ya san yanda mijin ta ke fifita maganar ta, ta hanyan ta zai cima nasara in har ta iya sa Uncle musty ya bar case in yarinyar nan.

Shi ko Barr yana ganin numban, bai ko kara bi ta kan Faroukh ba ya danna wa El-yas kira.

Bayan sun gama gaisawa ne yace "kana magana da barrister mustapha n..."

"Uncle Musty" El-yas yayi saurin fadi. Hakan ko yayi mishi dadi, ko ba komai maganan da zasu yi will not be formal kenan.

"El-yas ina son ganin ka"

"Okay Uncle, amma ina dan wani aiki yanzu ko bayan magrib ne in ba damuwa sai in sam har gida"

"To shknn ba wani matsala ai" barristern ya fada yana mai fatan El-yas ya cigaba da bashi hadin kan da yake nema.

"Sai ka turo min da address" El-yas in ya fada kafin su yi sallama. Suna gama wayan, barr ya tura mishi address in kaman yanda ya bukata.

A ranar duk yanda ya so ganin Zeenah, hakan bai samu ba. Ta bakin ta dai tace mishi tana cikin garin, amma ba su riga sun rabu da wanda su ka zo tare ba. A cewar ta, ya bari gobe in ya tafi tunda maganan su mai tsawo ne sa yi ta.

Duk gajiya ta dibe shi dayawa, da kyar ya samu ya yi wanka. Hakanan ya lallaba ya sa abu a cikin shi ba wai don yana jin yunwa ko abincin na mishi dadi ba. Aa, ya san yana bukatar hakan ne. Shi da kwanciyar hankali kuma ai sun yi hannun riga,  daga nan har rana da zai ga karshen wannan abu da ya taso mishi kwatsam zaune.

Mimin shi yayi kokarin kira ko zai samu wani dan natsuwa, komin kuwa kalilan shi. Sai dai ba alamun ya samu abinda ya ke bukata in, domin mimin kam banda complain in yayi tafiya bai kira ta ba, yanzu ya daina damuwa da ita kaman da. Banda mita dai da korafi ba abinda tayi mai. Gabadaya ji yayi kwakwalwar shi na neman cukurkude wa, shin wai meyesa mata su ke hakan ne? For once ace ba zata taba lura da damuwan shi tayi kokarin kwantar mishi da hankali ba? Duk da ya san halin matar shi, zallar kishi ke nukurkusar ta. Amma koma yaye ne ai ya kamata ace ta fahimce shi ko? "Mimi banda karfin biyewa rigiman ki please am not so well, ina haydar? Duk kuna lfy?" A hankali ya ke maganan yana jin kanshi na wani irin juyawa. Mutuniyar tashi ko maimakon ta fahimce shi, sai kukan kissa ta sa mai, wai yanzu kwatakwata bai ta ita, ya za ta mishi complain ya nuna ma ta bai da lokacin ta.

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shine abinda ya furta cikin ran shi. "Dan Allah ki daina irin wannan mimi, wlh kina daga min hankali. What is your focus kuma? Bayan kin san mijin ki yana son ki, duniya ma shaida ce. I love you so much okay? Ki kula min da ku, da ajiyan da na ke fatan nayi kuma"

Sai a lokacin tayi dan dariya tace "i love you much more better love, duk muna lfy. Ajiyan ka kuma nima ina fatan hakan." Dariya yayi bayan sun gama wayan "mata rigima!" Ya furta a fili, duk dai abun dolen shi ya sauko,  ya kwantar da kai,  ya lallaba ta su ka rabu lfy.

Kiran Dr Fahad ne ya shigo wayan shi, likitan ne ya mishi bayanin duk abinda su ke nema yanzu haka yana kan process. Sun dade daga nan duk suna magana akan case in ne. Its an achievement, da su ke kokarin aiki tare akan case in. Duk da ko kowa ya san zuciyan kowa game da yarinyan da su ke kokarin karewan. Sai dai, sunyi matukar kokari wurin kauda wannan su ka tasa ma abinda ke gaban su a yanzu.

Dr Fahad shi har ga Allah, shakuwa ce da fahimtar juna ya ja mishi duk abinda ya ke ji akan Suhaiman. Ya yarda da ita a cikin lokaci kankani. Yayin da shi kuwa Barr, qualities inta ne da ya gani a bayyane, ya ja ra'ayin shi tun farko akan ta. Duk da bai ta taba furta ma ta ba kuwa, ta hango hakan a wurin shi. Tsakanin shi da matar shi kuwa, soyayya ce daga Allah. Shiyasa duk abinda za ta mishi a duniya ta ke cin riban wannan. Duk fa da haka,  bai hana jin yana kwadayin wannan abubuwan da bai samu a wurin ta ba. Yanda ya ke jin son wadannan abubuwan da ya rasa gun burin zuciyan shi, yana jin zai iya aura kowacece kuwa in dai itan zai samu wannan natsuwar a wurin ta.

Ni ko nace Maryam, kalubale a gaban ki babba ma kuwa...

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top