Sha tara

Daren ranar da kyar na yi bacci ina tunanin ire iren abubuwan da su ke afko min a rayuwa irin tawa ba tare da na shiryawa hakan ba. Wani bakin cikin da duhu naji ya mamaye zuciya ta sanadiyan tunanin da na afka na wacce ta yi sanadiyar zuwa na duniya, Anty na wacce ban san a wani irin halin rayuwa ta ke ba a yanzun. Anya Anty ta min adalci kuwa? Anya ba ta da komasho a cikin irin rayuwan da na ke ciki a yanzu? Ni kam ina ji a jiki na da ta na cikin rayuwata har izuwa yau to ko ba abinda zai in fada cikin mugun rayuwa irin wannan.

Da wani mugun ciwo kai na tashi washegari, da kyar na samu na hada tea na sawa ciki na kafin na nufi cikin gida domin gaida Mum, mahaifiyar Amal. Baiwar Allah zaune na same ta a dakin ta kan Sallaya tana ta faman azkar. Sai da na jira ta idar sannan mu ka gaisa, faran faran ba ta da wani matsala. "Mum akwai abinda kike so ne in samo miki?" Cikin fara'a tace "toh dan hado min tea sai ki hado min da wheat bread ina please"

Saurin fita nayi domin kawo ma ta abinda ta bukatan, irin matan nan ne da duk da yawan su al'adan shan shayi da asuban fari bai bar ta ba. Ta kan ce shi breakfast da wuri fa ba abinda ya kai shi mahimmanci, kuyi kokarin tashi kusa abu a cikin Ku in yaso kwa koma baccin na Ku da ya zame muku jiki. Ina son matan saboda ba ta da wani matsala illa mugun son yara da na ke tunanin shi ya jawo illa akan yaran na ta. Ba wanda ya wani dauka ta a cikin su, ga ta yanzu ciwuka na sa ta a gaba wanda duk na ke tunanin na matsalan yaran nata da ma wadanda su ke gidan ne ke sa ta a gaba.

"Mum jirgin mu zai tashi by 12:00 pm, zanje zamu dawo tare da Amal in sha Allah" alaman murna ne ya nuna akan fuskan ta sosai tace "to Allah ya dawo daku lfy Suhaima, ni kam kwanan ina mugayen mafarkai akan Amal da ke sa zuciya ta wasi wasi, nikam Amal na azkar kuwa ko karatun Qur'an kaman yanda na ke ga kina yi" shiru nayi kai na a kasa saboda har ga Allah ban so in mata karya, ni kaina na san sakaci da su yasa rayuwata cikin tangarda balle kuma Amal da sallan ma sai lokacin da taga dama.

Girgiza kai tayi tace "ni kam na yaba da halin ki amma yana da kyau ki dinga sa yar'uwarki kan hanya. Fa'idan kawance da mai ilimin kenan ai, a hankali a hankali sai kiga ta dau hanya"

"In sha Allah Mum" na fada kawai amma a raina ina tunanin yanda mu matasan yanzu ba mu iya wannan ba illa kallo da mu ke mishi a matsayin sa ido da shiga rayuwan mutum. If you are matured and responsible, to shine fa ka kasance ba ruwanka da rayuwan dan uwanka, everyone get to do what he likes and kai da kake tare dashi you  have to respect his decision, wayewan fa kenan.

Office na fara zuwa nayi abubuwan da ya kamata sanin zan dan kwana biyu ban nan. Na kammala kenan kiran Fari'ah ya shigo waya na. Da ke na riga da na mike kuma nasan wayan nasan wayan da zamu yi da ita na bukatar sirri. Bakin window na karasa ina kallan waje sannan na ba wa kofa baya.

"Hello Aminiya kina jina?" Faree ta fada tana mai kwantar da murya. Bayan mun gama gaisawa ne ta ke tmbyn ya ake ciki da motive inmu.

Tabe baki nayi duk da daman nasan sanadiyyan kiran na ta "Komai ya tafi yanda ake bukata, Zayd Al-mansur is already on our trap sai dai ina son Ya shiga da kyau ne ta yanda ba shi da wani hanyan da zai zame mishi mafita" dariya ta kwashe dashi irin namu na yan duniya tace "Allah Aminiya yaushe za ki shigo ne? Ko kun riga kun lagos in ne?"

"Ehmm yau zamu da shi gogan sai after one week zamu dawo Abuja. In na shigo zan yi kokari in ganki sai kiji details in, Allah ya sa dai kina gari? Ba ki bi wani jirgin ba" yanzu ma shewa tayi tace "Dadi na da ke mutuniyar akwai hango abu, wlh ban Lagos ina Jigawa?"

"Jigawa dai Mutuniyata? Yau kuma nan Shegen garin ya jaki" tsaki taja tace "ai fa ke kuma dai, to ba ma shegen bane sai dai kuma shegiyar don wata hadaddiyar miya idanuwa na su kayi tozali" tabe baki nayi nace "To Allah kyauta, sai nazo"

Ina kashe wayan na juya, wa zan gani? Faroukh ne a tsaye cikin Office in, kallon da ya ke bina dashi ya isa tabbatar min sarai yaji dukkan abinda na fada a wayan. Ni tabbas naji karara kofa amma da naji shiru, sai na dauka an koma ne. Jikina ne gabadaya yayi sanyi domin ko shakka ban yi Faroukh yaji abinda na fada gabadaya, kaman wanda ake turo shi, to in ba haka ba, ni kam na rasa gane dalili.

"Oga yace in kai ki airport" kawai yace sannan ya bude kofa ya fita daga office duk da nasan akwai more to the explanation da Zayd ya mishi, tunda munyi dashi zai zo ya dauke ni ne.

A gajiya nayi da shirun da ke cikin motan, ga kuma wani guilt da ke cina da rashin gsky. "Kunyi magana da Zahra?" Na fadi maganan ko zan samu ya kauda waccan tunanin a ranshi, kar zuciyan shi tayi zafi a gaban zayd.

Kaman bai zai tanka ni ba, can kuma ko me ya tuna sai yace min "Tace meyesa ba ki kirata ba taga numbanki" A dake ya fadi maganan.

"Eyyah i will try calling her" na amsa ba tare da wani damuwa da yanayin shi ba.

"It better if you don't" da mamaki karara a fuska na na juya ina kallon shi, karantar yanayin fuska na yace "Because i want you to stay away" yana fadin haka yayi shiru, nima ban ce kala ba sai shi in ya kara cewa "i already like Zahra kuma zan so r/ship inmu yafi haka nan gaba kadan so i will prefer if you stay away saboda having somebody like you in her life will be a bad influence to her, ni kuma zai yi tarnishing abinda na ke nema a wurin ta"

Tab! In da akwai sauran kokonton yaji waya na ko bai ji to yanzu gabadaya ya goge, Faroukh yaji conversation ina da Aminiya sai dai duk da haka ina ganin ya zake a maganganun shi. Kuma bazan dauka ba tunda dai ban shigan mishi rayuwa. "Am sorry if i of..." Saurin dakatar dashi nayi da babban murya nace "Ya isa haka Faroukh, ya kamata ka san right words in da za ka fadawa mutum. Ba ka sanni ba baka san manufata ba don haka you have no right ka dinga fada min duk abinda yazo bakin ka" tabe baki yayi yace "am saying the truth" banza nayi dashi saboda yanda na ke jin zuciya na tafasa tabbas in na tanka ba zai mana da kyau ba kwata kwata.

Ya na kaini airport bai tsaya ko jiran Zayd ba ya wuce. Sai waya na sa na kira Zayd in mu ka hadu.

"My jewel" ya fadada fara'an shi yana gani na, murmushin karfin hali kawai nayi mishi ina fadin "shine jiya ko kira bayan kace za ka kira"

"Am sorry babe, ban fa bar wurin Salim bane sai wurin 12, nasan you already sleep kuma" turo baki nayi na juya kaman nayi fushi in nan.

Leko fuska na ya dinga yi yana dariya "to ba nace kiyi hakuri ba? Ai shknn ko babe a min afuwa please ba zan kara ba" kara hade rai nayi "dariya ma na baka ko?" Hakurin dai ya dinga bani har na sake na juyo yana ta tsokana wai ashe na damu dashi, nima ko biye mishi nayi nace “to daman wa ya isa yaki ka, kawai saboda Amal ne daman”

"Kar ki damu soon wannan tunanin zai zama history my jewel" ba mu wani dade a wurin ba jirgin mu ya daga zuwa birnin ikko. Ko a jirgin ma hadaddiyar soyayyan shi ya dinga nuna min, yanda ya ke min sai kace wata kawai. Wlh Zayd ya iya soyayya kaman turawan da ya zauna tare da, lallai dole Amal ta afka dayawa.

Ko da muka isa Apartment in, Amal bata nan. Nace mishi ina jin yunwa tun tea in da na sha da sassafe ban kara cin komai ba "bara in je in nemo miki abinci, what do you wanna eat babe" girgiza kai nayi na dan turo baki "Ni na gida na ke so"

Kallo na yayi kaman ya cinye, yaja ni dakin da na ke sauka "kwanta ki huta to babe bara in sama miki wani abun" ba musu na nemi wuri na kwanta, shi ko ya dau apron yayi kitchen don har bacci ya fara deba na duk da ma fast food ne ya yin.

"Muje in baki a baki ko babe" hararan shi nayi "in Amal ta shigo fa?" Ba tare da wani damuwa ba yace "kinga shknn ma, na huta dogon speech in da zan ba ta tunda ta gani da idanun ta" rufe baki nayi "rufa min asiri" a bakin ya bani kuwa cike da nuna min zallan soyayyan shi, ni kuwa ina kara narke mishi duk da tausayin da na keji na gauraye dukkan jiki na. Domin na san so, na san menene shi. Ban ko shakka irin wannan Soyayyan Zayd ya ke min a lokacin da ni kuma na ke jin zuciya kekeshe kaman wani dutse. Sai dai wani baiwa daya da nake dashi, am so good at pretending fiye da tunanin mutum ma.

Muna zaune a dinning Amal ta shigo, kaman na sani tashi na daga kan chest in shi kenan. Tana ganin mu ta rigo a gujen ta, jikin shi ta fada ta kankame shi sosai "i so miss you love" ta fada tana sumbatar left cheek in shi. Da ke yana facing ina ne ita kuma bayan ta na ke facing, sai nayi using wannan opportunity in na dan hade rai alaman ina kishin abinda ke gudana a tsakanin su. Da idanun shi ya dinga roko na na mai afuwa, sai ma na basar na mike zan bar wurin alaman da gaske na ke.

Ban san lokacin da Amal ta saki Zayd ba, sai dai ji kawai nayi ta riko hannu na "So Sorry Frnd, am so happy seeing him ne" dan bata fuska nayi ina kallon direction in shi nace "shine ni kuma a ka manta dani ko?" Ita kam har ga Allah ta dauka da ita na ke, side hug ta min hakan ya bani daman kara hada ido da Zayd, still ina iya hango neman afuwa a cikin idanun shi, dauke kai na kawai nayi.

Ita kanta Amal sai da ta dan ga canji daga wurin a ranar duk ko da yanda yayi ta kokarin kar ta gane hakan, amma fushina da na ke nuna masa in ba ta kallo yasa kokarin nashi faskara. Ranar, bai kwana a gidan ba yace mata akwai wani abu da yake son covering. yana fita abinda ya fara yi shine siyan sabin sim, ya tura mun mssg dashi nayi saving.

Muna dakin Amal ina taya ta dan tattare tattaren da ta keyi na barin garin, complain ta ke min "Frnd ni kam anya ba wani matsala da Bestie na kuwa?"

"Wani irin matsala fa ke da masoyin na ki kuma?" Mamaki na ara na daura wa fuskan kaman ban san komai akai ba.

"Kaman he is not himself yau in" wani tunani ne ya fado min, nayi saurin cewa "maybe yana da wani damuwa ne, kinga tunda mu ka baro Abuja haka na ganshi" dan runtse ido tayi ta bude "but we tell each other everything"

"Kar ki damu fa maybe kuma bai jin dadi ne, kila da yaji..." Ringing in da ya shigo wayana ya sani yin shiru, sabon numban nan ne dai da Zayd ya siya. Murmushi da na saki sai da ya sa Amal kallona, da sauri na suri wayan nace "ina zuwa Frnd" dakina na shigo sannan na dau wayan nace "kasa yaran mutane a tunani fa My Man"

"Allah ko? Suwa kenan?" Dariya nayi nace "ni da kawata, ina ta tunanin ka manta dani ba ka kirani ba, kawata kuwa tun dazu maganan ka take ta faman min"

"Oh Allah ni Zaidu gimbiya ta min hakuri to mana, tasan yanda Zuciyata ta kwadaitu da nin muryan ta kuwa? Jira kawai take gangar jiki ya kadaici sai ta danno muradin ranta" dariya nayi sosai "tou kai wa ya koya maka wadannan kalam a hausa?"

"Ai ni ban yada yare na ba jewel" daganan hira muka cigaba dayi dashi yana ta kara jaddada min girman soyayyan shi a gare ni. "Ina zuwa please Bestie na kira na bara ince mata bacci na ke saboda headache kinga sai ta kyale ni mu sha love inmu ko?" Ban ce komai ba, bai kuma kashe wayan nawa ba sabida ina jin sanda yace ma ta kan nashi na ciwo tun safe. Baiwar Allah sannu ta shiga mishi duk muryan ta yayi sanyi. Yana kashewa ya saki muryan shi ya cigaba da sako min zancen soyayya.

Bai dade ba Amal in ta shigo daki na "oh ni Frnd saurayi kika yi haka ake ta faman waya haka?" Sauke wayan nayi nace "Eh to kusan haka Frnd, am getting to know him ne ma" tafa hannunuwan ta tayi tace "wow! Finally kinyi admitting wani bf inki ne, i want to hear the voice of this lucky guy gskg" to fah! Ido ya so raina fata domin na san Amal ko kakayin maye ta ke sai ta gane muryan Zayd in "kar ki damu Frnd zaki san shi ma soon, kawai yanzu ina so in san kamun ludayin shi ne, kinsan mazan ba tabbas wlh sai kaje kasa an saba dashi ya maka halin yan duniya"

"Ke dai bari kowa ka gani case in kenan, maza sun zama abinda su ka zama. I feel lucky to have Zayd, he is different" tana fadin haka ta fita daga dakin, am sure zayd gabadaya yaji conversation inmu, maimakon yayi focusing kan abinda tace instead ce min yayi "Wato ni dinne ma baki san kamun ludayin nawa ba ko jewel?" Darawa nayi nace "ai gsky ne gayu ba tabbas"

...

Kusan kwana mu kayi muna waya, hakan ya sani baccin safe sosai washegari. Sai wurin sha biyun rana ya shigo gidan, nima muryan shi naji na fito falon saboda naji yana suna hira da Amal. Kaman yanda mu ka saba a da can haka muka gaisa dashi yana fadin "kanwata kenan sai yanzu garin ya waye miki don ba aiki ko?"

Amal na jin haka tayi caraf tace "Love ai bakasani kanwar ka Soyayya ya maida ta haka, jiya kwana tayi tana waya don haka ka shirya kunyi suruki" kallona yayi muka hada ido ya sakan min murmushi da wannan kallon nashi na daban. "Kanwata wai haka?" Gyada mishi kai nayi, yace "Ma sha Allah kice muna da shagali"

Tun daga ranar ya komo gidan, a boye mu ke duk wani abun mu inta fita kuwa yanda kasan mun samu duniya sabuwa. Sosai ya nuna min damuwan son fadawa Amal tsakanin mu, nina dakatar dashi, nace ya bari mu koma Abuja in yaso a can in, komai ta fanjama a san nayi. Hakan kuwa aka yi, sai dai duk dare zai baza musu kayan mayen su yayin kaman yana sha, sai ya tabbatar ta tafi duniyan ta ta fara bacci mai nauyi zai dauke ta ya kai ta daki ya kwantar sannan ya taho wuri na. Direct kan gado ya ke hawa ya rungume ni muyi ta hiranmu har muyi bacci sai na tashi asuba zai koma dakin ta. Ba abinda ya taba shiga tsakanin mu ba hugging sai kuma hannuna da ya ke yawan rikewa ko kuma ya shafa fuskana ya sumbaci cheeks ina sabanin Amal da na san ba abinda bai shiga tsakanin su ba.

Ranar POP inta da kanshi ya kai ni wurin Faree, da ke a gidan wata mata mu ka hadu da ita ni kuma nace mishi gidan friend ita ce. Ya ajiye ni akan zai je ya dawo.

A kayataccen falon na samu Faree kwance akan cinya wata hamshakiyyar mata tana susa ma ta kai. Tana gani ta dago tana fadin "Mutuniyata kin karaso kenan?" A daddafe na amsa ta sannan na gaisa da matar da ke ta faman kallo na kaman ta ga wani abinci. Lura da hakan Faree tayi ta dage ta daka ma ta duka kaman wata sa'an tace "Baby na kar muyi haka da ke mana" ban ce komai ba, Faree ta jani zuwa wani karamin falon, kaman gidan ta ta fita ta kawo min drinks da fruit. "Ban lbr mana Aminiya kin tsaya kina kallo na" tabe baki nayi nan na kwashi komai da ya faru tsakanin mu da Zayd na fada mata.

"Kin sanar da Anty Umaymah?" Kyabe baki nayi nace "kinfa san ban cika son zuwa wurin ta yanzu nan sai ta nemi ta sani yin wani abun da ban so" dariya tayi tace "kodai ta ji yar dake dadi ba, you are lucky ma abin ya fara fita akan ta irin irin ku ne dai ta kasa iya resisting" tsaki naja nace ba wannan ba "yanzu miye abun yi ne wai kuma?"

"Keep getting his trust da love har sai ya rabu da wannan Amal in koma ma samu muma hankalin ta ya dawo gare mu" girgiza kai nayi nace "Allah shirye ki dai Amina baki ga maza baki ga mata?" Tsaki ta min ta je "ke kika sani"

"Yanzu haka fa tare mu ke da Zayd in yanzu zai dawo ya dauke ni ma" zaro idanu tayi kaman kuma wacce aka tsikara tayi saurin tashi "ni dai ina son ganin zaid in nan Allah yau sai na ganshi face to face kuma naji voice in shi" ban ce mata komai ba sai gashi zayd ya kira ni na bita mu ka fita. Matan nan na dazu ina ce mata "zan tafi sai anjima" amma ina gabadaya hankalin ta na kan kalle min yanayin jiki, sai ji nayi Faree ta dau takalmi ta wulla ma ta, firgita tayi sosai. Faree ta bitada harara tace "wai ba na hana ki ba?" Murmushi tayi kaman wata mai cuta tace ma fari'an "Afuwan dear" ji nayi raina yayi cunkus nace wa faree "ita kuma wannan kaman wata sakara" dariya tayi tace "ba zaki gane bane ai ke Aminiya tun da kin ki hawa network dakyau,  she is a sub dole tayi acting haka" share zancen nayi saboda i don't want to hear more kuma.

Muna fita na ma Zayd knockin "dan fito please honey kawata na son ku gaisa"

Kaman wani sakarai yace "ta san tsakanin mu kenan" na amsa shi da kai, saurin fitowa yayi ya isa inda ta ke. Faran faran su ka gaisa, sai dai kallon da ta ke jifan Zayd in dashi ya sa ita ma ta koma min kaman wata sakaran kuma.

"Take good care of her" faree ta fada, sosai Zayd yaji dadin encouragement inta, makudan kudi ya fiddo a aljihun shi ya mika mata. Tayi saurin amsa tana godiya, ja wani tayi a kunne ta rada min "He is hot" girgiza kai kawai nayi na zagaya na shiga motan mu ka wuce.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top