Sha takwas
Tun daga lokacin ya fara kirana a waya. Da farko ko ya kira ni zancen business mu ke yawan yi dashi, a hankali sai ya fara gangarawa gun inda ke mishi kaikayi. Sai ya gama sa na lissafo mishi estimate in customers in da ake samu per day sai yace min "Jewel wlh your voice is sweet" share shi na ke yi a dukkan wadannan lokuttan ina kokarin canja akalan hiran. "Ina jin dadin muryan ki sosai, kefa?" Murmushin kawai zan yi in kashe wayan ina mai girgiza kai da cije lebbe.
Haka ma ku cigaba da kasance wa duk da Zayd bai samu wani Fuska a guna Ba hakan bai sa ya janye ba, duk in ya kira ni zan dauka amma ban wani biye mishi. Wani zuciyan ya kan ce min in share shi kawai sai dai wani na hana ni sanin abubuwan da za su biyo baya in na share shin. Zuwa lokacin kuma hakurin su Faree ya fara karewa, sau dayawa ta kan kirani tace min "Aminiya ya isa haka please mana, just get to action." Tun ta nayi kadan kadan har complain inta ya fara yawa, sau da dama ina mamakin yanda damuwan ta akan Abun ya fi na Anty Umaymah yawa sai dai in share.
Ana gobe za mu je Lagos ni da Zayd in wurin Amal, Da yammaci likis waya na ya hau rururi da sunan da na sa mishi kan Screen.
"Kanwata please ki same ni a bakin Telecom company yanzu nan" bai jira nace mishi komai ina daukan wayan ya koro min bayanin.
"Okay ina dan wani aiki ko za ka bani 15 minutes?" Na amsa kawai saboda ina Neman Excuse in da zai gaji ya wuce. Shiru yayi har na dauka ma ya amince sai kuma naji yace "ke dai kin iya rigima, ai yanzu ma zaki dawo zo please kinji" bai jira na amsa wayan ba yayi saurin katse wa. Dole na na tashi na fita, ban ma kowa magana ba ko da na fito wurin shop in duk da sannun da su ke ta faman min. Staff daya ne yace min "madam are you going out"
"Yanzu zan dawo" nayi saurin amsawa na fita daga wurin gabadaya. Ina fita daga building in na hango motar shi a inda ya ce min, karasa wa wurin nayi kokarin yi ina kokarin kiran numban shi "Gani na fito fa" na fada ina kara karewa motan kallo, da ke tint glass ne kwata kwata ban hango shi.
"Ai na ganki" ya amsa sannan katse wayar, siririn tsaki na ja, ni kam har raina na tsani mutum ya kashe min waya ban gama magana ba bayan ni na kira shi.
Tun kan in karaso naga ya bude min kofan, shu'umin murmushi nayi bayan na karasa gun motan, a raina kuwa fadi nake “ko yau wannan da mai yazo?" Ina shirin shiga motan kaman ance in dago kaina, ido hudu mu kayi da Faroukh shi ma ya fito daga cikin Company in yana bi na da wani irin kallo, kallon da na lura tun ranar da mu ka hadu a vows ya ke bina dashi sai dai ko in bamu hadu ba. Tabe baki na dan yi sannan nayi shigewa ta motan na bar shi yana kallon direction ina har na rufo kofan.
Idanuwan Zayd gabadaya a kaina su ka dauka da wani irin kallo da ban cika ganin yanayi sai lokutta irin wannan in mu kadaice mu biyu. "Jewel, ya fama da aiki" ya fada yana kokarin kamo palms ina, ban ce mishi komai ba har ya hade fingers inmu a tare "what do you want to tell me, ina da ai..." Knocking in da naji je wanda ke fitowa daga setin window in shi ya sa ni yin shiru. Idanuwan shi ya juya zuwa wurin glass in, ba tare da sakin hannun mu ba ya sauke glass in. Faroukh ne tsaye a wurin, muna hada ido shi naji gaba na ya bada dam, amma dan karfin hali irin nawa sai naki janye nawa idon. Shine ya dauke idanuwan nashi wannan karon zuwa fingers ina da na Zayd da su ke hade. Sai lokacin na nakara na fara kokarin raba su, dam Zayd ya rike ya ki Baron hakan ya faru "Ya akayi Faroukh?" Naji Zayd ya tmby.
"Sorry Oga na ganka a ciki i want to give you the papers sai dai kafin na dauko na ga ka fito" magana ya ke yana miko papers in. Amsa Zayd yayi ya dan duba "Sannu Faroukh you did very nice, please help me ka ba secretary ina zai shigar min da su" handing papers in yayi back to Faroukh. "Okay, zan bashi" Faroukh in ya fada ba tare da ya kara kallona ba ya bar wurin.
Sai dai Zayd ya daga glass in window in sannan ya juyo ya raba fingers in namu, hannun gabadaya ya maida kan shoulders ina bayan ya dan matso yace "Kunyan Faroukh kike ji? Ba ki so ya ganmu tare a haka ba ko?" Yana maganan ne idanuwan shi na sauko akan nawa, tun da ya lura ban son hada ido da mutane to sai ba mu hadu ba sai yayi kokarin saka idanuwan shi cikin nawa.
"Please mana..." Bai bari na karasa ba ya cigaba da maganan shi "Ni kuma kin ga ina so kowa ya san mu tare, i want to show the world you are mine" yanayin da naga yana kallon cikin idanun ya sa ni na kasa resisting, saurin jan Veil in nayi na rufe rabin Fuska na ta inda zai iya kallo. "Mine, or are you not" yana maganan yana kokarin janye veil in ni kuma ina sa hannuna ina kare rufewa.
"Okay, yanzu kuma kunya ta a keji jewel?" Ban ankara bayana ya saki ni sai ji nayi ya fisgi motan da speed sosai. "Where are you taking me to?"
"Shhhh" ya amsa min daganan ko ban kara ce mai komai sai gudun da ya ke ta faman kwasawa a cikin Abuja. Tafiya yayi sosai don har ya fara barin cikin Abuja sannan naga ya gangara gefe titi ya hau wani da yayi cikin daji, Tafiyan mintuna basu goma sha biyar ba ya kaimu bakin wani katon gate da aka rubuta Degolden Resort na ga anyi carving a bakin gate in. Muna isa, wurin gate in ya fiddo musu wani card kaman gate pass ne suna gani aka yi saurin budewa ya ja motan ciki. Daga nan ma sai da aka kara tafiyan mintunan, daga cikin motan ina hango different Halls, shops sai dai duk a kulle su ke. Ba straight bane ba ma sai anyi ta kwane kwane ga yanayin wurin the more muna tafiya muna kara shiga daji daji. Mun wuce Basketball court, snooker table, Swimming pools, birds cage kala kala. ni kam na mujiyan na zuba ina kallon ikon rabbi a duk inda aka keta, shi dai hankalin shi na kan tukin da yake da kuma cool music da ke ta faman tashi a cikin motan tunda mu ka baro Al-mansur Telecommunication center. Na tafi cikin duniyan tunani naga yayi parking a gefe, kallo na yayi murmushi kaman zai yi magana kuma sai ya fasa, bude motan yayi ya fita nidai bin shi da kallo kawai na ke har ya zagayo ta saitin inda na ke ya bude kofan. "Bismillah gimbiya, ko in dauke ki ne?" Lokaci daya yayi maganan kuma yana miko min hannu shi. Basar dashi nayi na fito daga cikin motan ina kara kallon yanayin wurin da ke ciki da different flower species hade da bishoyoyi da ke ta faman kadawa. "Do you like the place?"
"Sosai ma, it so lovely" irin kallon da na ce yana min in muna mu biyu kadai ya bini dashi "I've never bring a lady here, you are the first"
Saurin bata rai nayi ina bin shi da harara "don't you believe me jewel?" Sautata muryan shi yayi yayin da ya ke magana.
Nace "na yarda fa kawai dai naji ba dadi ne because i know you've taken them somewhere better than this" dariya yayi sosai yana kara gyara tsayuwan shi, folding hands in shi yayi yace "Bawan Allah Zayd, am so lucky ana kishi na" yanda yayi da fuskan shi ne ya bani dariya har na dan dara. "Ni banda wurin da yafi wannan a heart ina, tab kinsan matsayin place in nan a wurina kuwa? To Amal ma ban taba kawo ta wurin nan ba" Fara tafiya yayi yana maganan, da hannu ya min alama da mu je.
"What about your wife?" Dan cije lebe yayi yace "Jewel kenan to Amal ma nace ban kawo ta ba balle Amina"
"Don't you love her?" Girgiza kai yayi yace min "She is my first love" dan zaro idanu nayi ina kallon shi alaman I need more of the story.
"Not now babe story for another day"
Wani wuri daban mu ka kara shiga kaman wani dan lungu don har ga Allah har na fara tunanin wani abun ya ke shirin min ga garin ya fara duhu duhu. Ganin kallon da na ke mai ya gane hakan, dariya ya dinga min nan da nan kuwa na daure, saboda karfin hali irin nawa.
Dan fili kadan ne karshen long lungun, ina ko daga kai na ciki karo da wani karamin hut, green plants ne aka sa aka yi decorating gaban shi da ta dan gefe gefe a jikin ga wani crystal light da ke ta sparkling daga ko ina na jikin hut in. Saurin runtse idanuwa nayi na bude su still na ga wannan hut in a gabana sai kace wani fairy tale because i can't completely describe yanda wurin ya hadu, ga wani shiru, iska da natsuwa da ya mamaye wurin gabadaya. Shi dai yana tsaye a gefe na hannun shi aljihu yana ta faman smiling yayin da idanuwan shi ke sauke a kaina da dai irin wannan kallon da na ke ganin it specifically for me. "Muje ko" ya fada yana nuna min hannu, da kyar kafafuna su ka iya motsawa ba tare da gazawa ba zuwa gaban hut in. Sai da muka hau matakalan stairs wurin uku tukun mu ka hau gaban hut, nan ma crystal light in ne ta gefen inda mu ke taka wa ga kuma pink and red roses a ta kasan wurin da su ka hadu su ka ba ma wurin gabadaya wani romantic ambience.
Yanayin jikina gabadaya sai da ya canja, ina Jin wani fargaba hade da firgici na ziyarta na, ba Wai na tsoro ba Aa, tsoron abinda na sa kaina naji yana diran min. Hakanan na ciki gaba da bin shi muna tafiya har zuwa hut in shi, cire flat shoe in nayi kaman yanda na ga yayi wa nashi. Grass carpet ne shimfide a kasan wurin sai kuma wasu green pillows da ke zube a wurin gefen indoors Fairy Lights Da small poppy chandelier a saman hut in. Iya haduwa wurin nan yayi, ban karashe mamaki ne ba sai da muka karasa karshen Hut in ta back view. Ruwa ne zaune a wurin kaman wani ocean, Ashe gabadaya baya wurin Ruwana ga haddadun pebbles masu kayatarwa a wurin ruwa. Kaman wata yarinya da gudu na karasa kan stairs in da zai yi leading in ka wurin ruwan, biyo ni yayi yace "daga ganin ki kinyi wasa da ruwa da kina karama" saurin rufe idanuna nayi ina tunani lokacin da ya ke fadan. Share thought in nayi na bude idanu ina fuskantan wurin da ke gabana. "This is just amazing, like are we really in Nigeria" gyade kai sama yi sannan ya dan duko yace "I like seeing this happiness in you" sosai nayi dariya ina jin wani farin ciki na daban na mamaye ni.
"Jewel can you please close ur eyes?" Kallon shi nayi da alamun tmby "trust me" yace, rufe idanun nawa nayi ina tunanin ko dai ruwan ya ke so ya wulla ni ne? Hannu na naji ya jawo ya zira abu. "U can open" hannu nawa na bi da kallo wani irin sparkling bracelet na gani, shi ma hannu nawa ya ke kallo "I know it will look good on you" ban ankara ba naji ya riko hannun ya dan yi pecking kan bracelet in.
"Jewel i want to hear your opinion please kinji" with no idea na kalle shi yace "Wlh ina son ki, soyyayan da ban shirya ma ta ba, ina miki wani irin so ma dabban da ban san kalan ta ba sai akan ki. Da gsky na ke son ki Suhaima Adam Bello, i want you to be mine forever, i want to marry you mu rayu tare cikin aminci" daga cikin. Idanuwan shi na ke hango iya zallan gskyn abinda ya ke ambata min, idanun har sun rikide sun canja kala. Wani tausayin shi na daban na ji yana ratsa ni yayin da zuciya ta ke tafasa knowing i have to do this without feeling anything akan shi.
"What about Amal?" Na tmby ina jin wani zafi na daukan gabadaya jikina duk da ni'iman da ya mamaye wurin.
"In har kin amince dani i will tell her everything, I want her to know ba ita kadai ba ma kowa" yanda sautin maganan ne fita ma zai tabbatar ma ka iya zuciya abinda ya ke nufi kenan.
"Ba ka tunanin yanda zata ji?" Folding lips in shi yayi da hannun shi.
"Kedai ki bar min komai, I know Amal than anyone knows her. Nasan yanda zan bullowa abun" ita ma Amal in wani irin tausayin ta naji ya mamaye ni nan take, tabbas ba ta dauki matsayin Zayd a wurin ta abun wasa ba. “zan dan taba rayuwan ki Amal ina fatan za ki yafe min” a raina nayi maganan sannan na kalli Zayd nace "nasan zai jawo mana matsala kuma zai tsarwatsa abota da ke tsakanin mu na har abada. She won't take this lightly"
Rike kanshi yayi yace "ina son Amal so na musamman saboda shakuwan da ke tsakanin mu da ita daban ne sai dai yanda na ke ji a kanki jewel in ban same ki ba to wlh zuciya ta za ta iya fashewa" Jan hannu na yayi ya dauka saitin kirjin shi ina jin yanda zuciyan shi ke buga da sauri da sauri. "Zan aure ki in kasance tare da ke cikin kowani hali Suhaima. Tun randa idanuna su ka ganki zuciya na ke dokawa da soyayyan ki tun ina kin abun har na kasa jurewa, it impossible dole na ke jin kasancewan mu tare"
Tausayin shi da yabi jikina nane ya sa shi tunanin zantukkan shi na kai wa inda ya ke so ya kai. Kara matsowa yayi daf dani ta yanda har muna jin hucin juna, goshin shi ya daura kan nawa yana kallona cikin idanu kaman mai son karanta na "Will you accept my proposal?"
Gyade kaina nayi sannan nayi saurin runtse idanuna, a yayin da jikina ke faman daukan rawa. "Thank you" yayi saurin fada hade da min light hug, for the first time in his life ya rungume ni. A duk sanda jikin wani Namiji ya taba ni sai nayi kokarin janye jikina sai wani tunani ya zo min in fasa in basar.
Mun dan jima a wurin har a kayi Sallan magreeb, mu ka tashi mu ka gabatar da Sallan da ke Abaya ke jiki na. Hira mu kayi sosai wanda mostly rayuwan secondary school in shi da University ya dinga bani wanda dukka ba a Nigeria yayi ba.
Sai wurin 8:00 pm mu ka bar wurin, Shopping ya kaini a Shopright, da ya lura ban daukan abubuwa duk abinda ya san ina so dan zaman mu ni dashi da Amal sai da ya daukan min da abinda bai san ina so ba. Kudi sunci Uban su a wannan ranar kam.
Za mu fita daga store mu ka kara cin karo da Faroukh, sai dai wannan karon tare su ke da El-yas. Wannan kallon banzan da ya ke yi min ya kara bina dashi, dauke kaina nayi zuwa El-yas mu ka gaisa faran faran.
Garam! Kake ji, wata yarinya ce ta shigo cikin store in da dan gudun ta kafin ta ankara har sun ci karo da Faroukh. Kallon banzan nan dai na ga itama ya bita dashi yayin da El-yas da Zayd ke faman mata sannu ganin yanda ta zube a kasa. Karasa wa wurin nayi da azma ina kokarin dago ta sai jin kukan yarinya mu kayi a baya tana kiran "Anty jala Anty jala" ganin mutane sun dan fara taruwa a wurin ya sa Faroukh daukan yarinyar yana dan jijigata, dago wacce aka kira da Zahran nayi ina mata sannu, da force murmushin da ke kan Fuskan tace "Nagode" zaunar da ita nayi akan chair in da ke dan gefe ina amsa security in da ke wurin. Kallo Faroukh ya bimu dashi kaman wanda aka sa dole ya je ya kawo ma ta ruwa yana ambatan "Sorry" amsan tayi ta kurbi ruwan da kyau hankalin ta gurin sister inta da tayi wani irin lafkewa jikin Faroukh "tun da kinsan na fadi ai sai muje mu nemo costume in yanzu, Yaruwa ko kinsan inda zan samu Costumes kinsan gobe hallowen a school gabadaya ta birkita min lissafi sai an nemo mata Sophia, the first costume a dole"
"Ba matsala muje ki gani" ce masu Zayd nayi zan nuna mata wurin, da ke ground building in wurin ya ke nan da nan mu ka isa. Luckly an samu costume in sai dai an cika mi shi price in da yafi adadin kudin da ke hannun Zahran."
"Kin bani wahala a banza ni dai, gashi ma kudin da aka bani ba zai isa" tsaki taja tace "ma koma gidan hakanan ai" bare baki babyn tayi kaman za ta fashe da kuka. Surprisingly, Ciro debit Faroukh yayi ya mika aka cire iya kudin "lah ai da ka bar shi ma" zahran ta fada, murmushin gefen lebe yayi yace "kar ki damu" wani irin kallo na daban naga yana aika ma ta har ta mai godiya za su wuce nayi saurin tsaida ta. "Zahara can i get ur number?" Tsab ta karanto min su gabadaya. Ni ko ina zuwa wurin motan Zayd inda su ke tsaya dukkan su Ukun na mikawa Faroukh waya na "her contact" nace ai ko gabadaya su ka dara.
"Kin kyauta wa mutumina gsky" El-yas ya fada yana daga gira. Kaman ba zai karbi wayan ba sai kuma ya amsa ya dau numban. For the first and last time a rayuwan shi yace min "thanks"
Har cikin gidan su Amal Zayd ya kai ni. Da ya dan yi parking zan fita ya rufe motan yace "sai yaushe kuma za mu kara fita"
"Anytime, amma kar ka kara min bazata daga yanzu za ki dawo. a bude fa na bar office ina da bag ina da abubuwa a ciki" dariya yayi yace "ai kece kin iya daru, yanzu dai zan tafi amma zan kira ki in naje gida"
"Okay" na amsa ina kokarin bude motan sai dai still a kulle ya ke, juyowa nayi na kalle shi yace "won't you say Good night to your babe?"
Dariya nayi nace "okay Good night bude min In tafi pls ma yi wayan" dariya yayi sosai yace "ke dai na gane so kike ki fita kar a ganmu tare a mota ko" ban ce komai ba dai, peck yayi saurin kai min kan cheeks yace "To Gud night" abinda na ke gudu dai dai lokacin aka fara knocking in glass in. Muryan Salim Yayan Amal ne ke cewa "Don me kake yi a mota tun dazu Wai" kin budewa yayi ya kalle ni a hankali ya miko min hannu Wai "shake me" saboda ban son rigima ya sa na mika mai hannu. Sannan ya bude motan gabadaya mu ka fito. Kallon mu Salim yayi ya basar. A daddafe na gaida Salim in sannan nayi saurin karasa wa apartment in Amal.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top