Sha shidda

Service ya kawo Amal garin Lagos, da farko gidan Friend in shi ya tura ta zama. Sai dai ba ta cika sati daya ba a gidan ta fuskanci akwai takura a al'amarin gidan sosai wanda ba haka ta saba ba a gidan su,  she is free to do everything she likes. Hakan yasa ta tattara kayan ta ta koma daya daga cikin apartments in baban ta da ke lagos in. Ko da ya samu labari ya tmby ta ya akayi kawai ce mishi tayi she needs to be comfortable, shknn zancen ya mutu. A lagos mu ka hadu da Amal kasancewar ta mutum mai rauni tana gani na a hali na taimako ta ceto ni, a wannan lokacin nima in bautar kasan na ke a asibitin koyar na jam'iar lagaos a Ikeja. Ta sani a jikin ta sosai ba tare da wani shakku ko fargaba ba. Tare mu ke zama a Abuja a gidansu, ko kuma Lagos a apartment inta.

Tunda nasan ta nasan Zaid,  na kuma san alaka mai karfi da take gudana a tsakanin su. Zan iya cewa suna rayuwa ne kaman na mata da miji duk da ko ba auren tsakanin su. Iyayen ta sun ki bashi auren ta duk da yana da burin hakan amma hakan bai hana ya shigo gidan su freely duk time in da ya ga dama ba a matsayin Friend in ta ko kuma yazo wurin Salim, wanda tare su kayi karatu a UK.

Kusan su in Kwarya tabi kwarya ne saboda shi inma dan masu hannu da shuni ne. Baban shi babban Custom officer ne da yaji kudi har ya gode Allah kafin yayi ritaya. Intrestingly, maman shi kuma na aiki da SSS ne. Business in Telecommunications ya ke yi a Abuja sai kuma Natural drinks da ya ke da shops in su branch branch a cikin Abuja. Shakes, Zobo, Ginger, Smoothies, mocktails, Yoghurt nd ice cream. Ba mu dade da haduwa yayi offering employing ina karkashin Drinks shop in shi duk time in da nake Abuja. Amal ba tayi wani tunani ba sai ma jin dadin da tayi, i get something to lives on. I really enjoy the work, the pay and everything.

Da shigar doguwar play gown na atamfa da Dan karamin veil na fito falon. Zaune su ke akan dinning suna breakfast ko kuma ince brunch, Shabiyu da rabi na rana har ya gota.

"Sis ina zuwa haka?" Amal ce tayi maganan da spoon in da zaid ya sa ma ta a baki, shi ke ba ta abincin.

"Shopping, ina son toiletries and some groceries. Akwai abinda kike bukata ne?"

"Just pomegranate, ina son yin cocktail in shi"

"Yaya na fah" na fada ina kallon Zaid, tun dazu ya ke faman Satan kallon fuskana.

Siririn murmushi yayi Wanda ya tsaya iya labba "Kanwata kenan, ai kin San mai na ke so" nan take na gane abinda ya ke nufi. Harara n shi nayi, amma idon Amal hararan wasa ne "Kaima kasan ba zaka taba samun wannan ba, I can't never go that far"

Clueless Amal cewa tayi "Jikin abinki Sis kinji, Traffic in Lagos in nan ina mutum zai yi nisa" bansan lokacin da na saki dariya. A wurin Amal Zaid na ke wa dariya, shi kuma a wurin shi ita na kewa dariya. Unknown to them dukkan su na kewa dariyan. Cikin farin ciki na isa store in, bayan na gama dukkan siyayyan da zanyi ne na ja motan sai Unguwar agege.

A bakin wani katon gida nayi parking, sai dai duk girman gidan bai da plasta ko fenti a jikin shi. Tun daga kofan gidan na fara cin karo da matasa, yan mata da Yan dudu. Daga masu shan sigari, tabar wiwi sai ko masu faman caca ga kuma kidan da ke ta faman tashi. Duk inda na wuce shewa za kaji na tashi suna kiran "Ah Yar baiwa manya yau an shigo kenan" daga musu hannu kawai na ke na wuce a haka har na karasa cikin gidan, inda dakuna ke nan birjik.

"Ah ah kawa yau kece a gidan namu" daga baya na naji an fada, saurin juyawa nayi muka hada ido da zeenah. Rungume juna mu kayi cike da farin ciki. "Yau lafiya da kanki a gidan namu?"

"Kawa fa ban son sharri sai kace da in ban zuwa?"

"Yaushe rabon ki? Ke da sai dai a ganki a mashaya" dariya mu ka kwashe dashi irin na yan duniya, hade da tafa hannu. "Yau dai nazo ai, Allah ya sa mutuniyar ta na nan"

"Ai ko kinci saa, Yanzun nan dawowan ta daga Calabar, kin San mutuniyar na ki ba dai yawo ba"

A tare mu ka karasa wurin dakin Muna cigaba da tattaunawa. Sabbin fuskoki dayawa a gidan, Wadanda na sani da kuwa kusan ince hassada ke tsakaninmu dasu, a ganin su na samu cigaba. Sai masu mutuncin ne zaka ji suna fadi "Yar baiwa manya an shigo kenan?"

A dakin ta na iske ta zaune tana fidda kayan da ta dawo dasu tana ta faman hamma "Sarkin tsafta ba ki bari ki farka daga baccin sannan a gyara kayan" na fada bayan na zauna a bakin gadon dakin ta.

"Ke kin San ba zan iya ba ai, na jiyo muryan ki ai kuna magana da uwar tsugudidin can. Allah  Allah na ke ma ni kar ki shigo min da ita"

"Ita ma kinsan baza ta shigo ba ai"

"Keni ba wannan ba daga ganin bakin ki nasan akwai magana. Daman tun da jiya aka kira ni ya shigo gari kuma kunyi rawa tare nasan akwai maganan"

"Me kika je yi calabar wai?"

"Abinda kika sani kuma! Sabon saurayi nayi shi na raka" girgiza kai nayi sannan nace "He propose Yesterday fa"

Saurin gyara zama da tayi tare da sakin gyalen da ke hannun ta"Allah mutuniyar? Na mugun yarda da ke ai" a tare mu ka saki dariya  "kuma mai kika ce mai"

"Na nuna mishi kin amincewa ta, in ba haka zai zamo ba yarda tsakaninmu. Ina son fada miki ne dai kawai kisan mai ake ciki"

"Mutuniyar a ciba da gashi, mu bi komai a sannu kaman yanda kike yi har mu cin ma nasara"

"Toh shknn mutuniyar bara na tafi, kya sanarwa Anty abinda ake cikin"

"Yaushe zaki Abuja? Ya kamata ki leka ta da kanki. A gaida sweet Amal" harara na watsa ma ta Wanda ya sata dariya. Nace "Kwanan nan za muje da Amal in, dole ma inje."

Ko da na koma gidan, Amal kadai na iske. Zaid ya fita meeting in da ya kawo shi garin.

Rashin takaimaiman abun yi yasa mu zaman kallon Korean series, The Doctors. Film ne mai ilimantarwa sosai. Musamman, a wurina, da nayi karatun likitancin.

Wurin la'asar, ta ke sanar min tana son yiwa Zaid girki zai yi baki. Jikin ta har wani rawa ya ke, har ga Allah banji matar shi ta sunna ma tana mishi hidiman da baiwar Allahn nan ta ke mai. Sau da dama na kan so bata shawara akan sha'anin Zaid in, sai dai zuciya ta ke garagadi na akan shiga abinda ba ruwa na. Musamman ma dan sanin ba abinda ya shigo dani rayuwar tasu ba ne.

Samari da Alhazawa kala kala da su ka taka Zaid a kudi, matsayi, ilimi harma da wayewar kai kan nemi kulla alaka da Amal in. Mafi yawancin da shedanan su ke nemanta. Sai dai duk da haka akwai masu son ta da auren da gaske. Amma ba wanda ta ke kulawa Sai shi, ta na mishi wani irin zazzafan soyayyan da ita kanta ba zata iya kiyasta wa ba. Mace mai aji, kwalisa, kyau, budewar ido da ilimi amma soyayya ta iya taka ta hade da mata juyin waina a duk lokacin da ya so hakan. Maza dayawa za su so ace su suka samu wannan garabasar.

Bambancin wannan mazan da Zaid Almansur kuwa shine; in ka cire kyau da ke akwai, Zaid mutum ne dan duniya da ya matukar kwarewa wurin aika ta duniyancin. Ya San mata ya San sirrin su, hakan ya bashi daman siye su cikin sauki da kwanciyar hankali. A tsarin shi bai siye mace da kudi ko da wasa illa zalla soyayya, kwantar da kai, iya kalamai da kuma irin tsarin shigar shi. Sai dai in bai ga classy mace ba, in har ranshi ya biya to fa sai ya samu. Upon all matan da yayi harka da su daga matar shi sai Amal ne bai iya rabuwa dasu ba. They were more like friends da Amal Kafin su fara soyayyan, hakan ya sa ba iya rabuwa in da ita, saboda he really needs her as friend. Ita kadai ce har ranshi ya so ta da aure.

Da kanta ta ke labarin abinda ya faru lokacin da aka hana ta auren shi. Tunda ta taso ba taba cin karo da abinda ta ke so kuma ya gagare ta samu kaman shi ba. Alkawari ta daukan wa kanta muddin aka hana ta auren shi to tabbas sai ta bashi kanta; ma'ana ta mishi kyautan budurcin ta. Hakan ko ya faru, a daren ranar ta fita ta bar gidan su direct ta karasa apartment in shi. Cikin rudu ta shiga gidan, a falo ta same shi yana faman kwankwadan barasa. Ba tayi wata wata ba ta nemi ya bata ta sha in har zai yaye mata damuwa. "It can be addictive" yace mata. Ita dai tace taji ta gani. Dalilin fara shashaye shashayen ta kenan a duk wani lokacin da ta tsinci kanta cikin damuwa. Daga baya ma da ya zamo mata jiki ko da ba ta da damuwan komai shan abinta ta ke. Ranar a gidan shi ta kwana rungume a jikin shi, wannan kam ba wani abu bane a wurin su daman, he hug, kiss and feel her body whenever he feel like doing so. A washegarin ranar ne ta sanar mishi. "She don't want to wait anymore kuma tunda an hana su aure, she want have the sex" ba tare da wani musu ba ya amshi budurcin ta a ranar. Kaman matan shi ta aure haka yayi treating ita. Duk iskancin shi bai iya mata don yanda ya ke boye mata neme nemen matan shi ko Matar shi bai ma haka.

Sai a kwana na uku sannan yayan ta Saleem yazo ya same ta a gidan. Daman tunda aka bincika duk wani yan uwa da kawayen ta ba a ganta ba ya San ta na wurin shi. Kusan dambe su kayi tsakanin Zaid da Saleem, da kyar ta samu su ka rabu sannan saleem in ya Sa ta a gaba su ka dawo gida ba. Bakin cikin duniya kam ba Wanda mahaifiyar ta ba ta shiga ba, ta yi kuka har ta goge Allah. Ita kuma irin tata kaddarar kenan akan yara ya ke. Baban ta kan rantsuwa yayi ba zai taba bada auren ta wa Zaid ba. Kulle aka mata na kusan sati biyu kafin hutun ta ya Kare  ta koma inda ta ke makaranta a UK. Sai dai ba UK ba kowani  kasa Amal taje a fadin duniya, abu ne mai sauki a wurin Zaid ya hau jirgi zuwa inda ta ke.  A ganin shi rabuwa da ita ba karamin asara bane a wurin shi ko bayan hakan ma yana mugun tausaya ma ta, yasan ko wani hali ta shiga shine sila. Tun daga lokacin ta zama ruwa in dai akan zaid ne, clubs, parties, hotels ba inda ba ta taka ba. Ya sha maido ta har cikin gidan su a buge ba ta San idan kanta ya ke ba, kaman jaririya haka zai fidda ta daga mota ya kai ta har dakin baccin ta. Apartment inta na gefe ne, iyayen kuma na cikin gida shiyasa har ya ajiye ta ya tafi ma ba su sani ba.

...

Wurin bakwai da kwata na dare su ka shigo. Zaid ne da bakin shi guda uku. Biyun kam samari ne da ba zasu wuce 26 zuwa 28 ba, dayan kuma babba ne dan zai ma fi zaid in a shekaru.

Abinci kam kala kala haka muka shirya shi tare da Amal da cook inta. Lokacin da su ka shigo na shiga daki, ina jin muryan bakin suna gaisawa da Amal. "My lady here" muryan zaid na ji yana gabatar da Amal. Duk da ban wurin nasan irin murmushin da ya ke kwance kan fuskan ta duk sanda Zaid ya gabatar da ita a matsayin tashi.

"Lady ina Suhaima ta fito ga business partners" ya fada yana kallon kofan daki na. Dai dai lokacin na bude kofan idanuwa na da nashi suka hade. Da idon ya min alaman wai nayi kyau. Harara na watsa mai, ganin duk sun ban baya. da gashi sai bakon shi daya ke facing ina. Siririn murmushi yayi ya dauke kanshi gudun a harbo inda ya nufa.

Dinning in na kara so, ina kokarin jan kujera  "sannun Ku da zuwa"

Ban ji amsan su da kyau ba, mikewa na kusa dani yayi ya ciro min kujeran da kyau. "Bismillah ko"

"Thanks" na fada a hankali ba tare da na kalle shi na zauna. Ina dago kaina, na ga wani irin kallon da Zaid ke jefan Wanda ya fiddo min kujera, ko ya gani ko bai gani ba, ohon mai. A hankali kowa ya fara serving kanshi, ana miko serving spoons, bowls da sauran su.

"My sister, Suhaima" Zaid ke pointing ina yayi maganar."so beautiful" na kusa da ni in ya fada yana jefa min wani irin side look. "Zaid akwai tattauna wa fa"

"Kar muyi haka da kai mana boss."

"Oga Hafeez da kanka? Kar Amarya ta jiki fa" Amal ke tsokanar shi, dariya yayi yace "kar ki damu lady Amal, da kaina zan fada mata"

"Sis meet my boss and business partner Hafiz sameer" Zaid ya fada, juyawa nayi ina kallon shi, shi in ma ni ya ke kallo.Hannu ya miko min, shaking hannu mu kayi yana fadin "Delicate skin beauty" murmushi kawai nayi, shi in ne nake tunanin zai ma girmi Zaid in.

"Oga hafeez dai ya dage" Amal ta fada, duk akayi dariya.

"El-yas here, shi ma muna aiki tare. He study interior architecture and design, he design all my shops, company building and apartments"

"Wow! So you are the man behind all these unique aesthetics."

Dariya yayi, Amal tace "Wai friend dan ma ba kije Company in ba, the interior designs were simply beautiful. Bara dai muje Abuja, ko dan ma ashe nan drinks shop za su koma. I can't wait to see the new designs on the shop"

"Madam kenan ina godiya, Am already working on the shop interiors ai"

"Then meet Faroukh Usman, Lady ke ma ba ki San shi ba. He is computer expertise and guru. Ba mu dade da fara aiki ba, but he is great"

"Nice meeting you Faroukh" a tare mu ka fada ni da Amal, yana murmushi ya amsa. He looks so nice and innocent.

Ana cin abinci ana taba hira, Wanda duk akan business in su Zaid in ne. "Sister na fada miki we are relocating ba, am tired of handling many small shops. Shi ne mu kayi deciding mu yi babba daya a one location kawai though zamu bar na cikin Universities. Location in yana gefen company inmu, An gama komai na gini sauran interiors in. I want you to be the manager there"

"Nice idea" Hafeez yayi saurin fada, ya kara da cewa "Ku yi magana da El-yas akan interiors inma kawai ba sai nayi ba tunda you will be the oga there" jin dai magana gabadaya na business ne, Amal kam ba field inta ba ne. Hakan ya Sa ta tashi ta koma kan couch ta bude macbook inta.

Ba dadewa Zaid ya bita, jawo shi yayi jikin ta ta shige sosai, su ka cigaba da kallon tare.

...


Bayan Barr ya bar wurin Suhaima zuwa yayi ya dinga shiga yana fita har sai da ya gano adadin kudin bailing in da za ayi requiring. Kudi ne masu matukar yawa, dole ya fara shakkun anya za a sami wadannan kudaden a gun su Suhaima kuwa? Har zai kira Dr suyi shawara sai yayi tunanin bara dai ya gwada au ya gani.

A wani restaurant su ka hadu Zeenah da dare. Sai falli ta ke ta faman mishi, shi kam dai bai tanka ya fara fado ma ta bukatun shi. Da ya kira yawan kudin, duk a tunanin shi za ta girgiza. Sai dai maimakon hakan sai ce mishi tayi "i will write the cheque in ba ka kafin na bar Abuja" ba wani alamun mamaki a fuskan ta, sosai ya ke jin yana son tmbyn ta dukiyan na wanene sai dai bakin shi ya kasa furta hakan.

"Zeenah" ya kira ta a hankali yana kokarin tattaro tambayoyin da ya ke son mata. "Ya kuke da Suhaima?"

Sai da tayi wani fari da ido ta saki mugun murmushi mai cike da ma'anoni tace "kawa ta ce fa, kaman na taba gaya maka ai. Ba kaji kawa mu ke ce wa junan mu ba?"

Tabe baki ya danyi, yana ganin kaman ba zai wani samo abin arziki a wurin ta ba yace "nasani, amma za ki iya fada min inda kika san ta har kuka shaku?"

"Gidan magajiya da ke agege" ta fada kai tsaye tana kara sautin karan chewing gum in da ke bakin ta. "Ka gane akwai yarda da aminci a tsakanin mu duk ba wani zauna tare da ita na dogon lokaci ba, ta kan nemi ni bayan ta bar gidan akai akai kuma..."

"Ita kadai ta zo wannan gidan?" Ya bukata, girgiza kai tayi tace "wata Aminiyar ta ta kawo ta"

Gyade kai yayi yana wani nazari yace "tana ina Aminiyar na ta?"

"Ta dade ba ta kasan nan gsky, banji ta ma san abinda ke faru yanzu haka"

"Okay" yace yana kara sa abun a kwakwalwar shi. "Me za ki iya fada min game da halayen ta?"

Murmushi tayi sosai sannan tace "akwai kirki ga wanda ya zauna da ita ya fuskance ta fa amma don har yau akwai ma su ma ta kallon mai girman kai a gidan namu, ba ta cika magana, a fuskan tan da na mata yana daya daga cikin dalililan da ya so ba ta cika shiga harkan mutane ba. She is a good listener, duk shirman da na zo ma ta dashi tana za ta saurare ni har ta bani mafita. Sannan zan iya ce maka bayan wacce ta kawo ta dani kadai ta ke mu'amala bayan ta bar gidan"  tsab ya ke sauraran ta yana kokarin sa lissafin sa a duk bayanan da ta mai. A ko ina da ta zauna, ana mata kallon mai girman kai, ko meyesa haka? Amma a kaduna duk da rashin surutun ta, ba mai mata wannan kallon. Is she just acting ne?

Shi tun da ya bar wurin ta ya ke tunanin lbrn da ta fara bashi, in akwai abinda ya fahimta game da lbrn abu daya ne, bayanan Faroukh ne kawai su ke kokarin zama gsky. Amma zai mata Uzuri, kaman yanda ta bukata.

"Meye sa ta barin gidan Yancin?" Ya tmby zeenah, da ta kalalo idanu "ban san dalilin ba saboda ba ta fada min. Sannan ita ba mai son a dinga ma ta yawan shishigi bane shiyasa ban bukaci sanin ba, amma mutane dayawa na cewa wani mai kudi ne da su ka hadu ya tsaya ma ta har ya kai ta da barin gida" hmmm, komai dai kara daure mishi kai ya ke, duk wani da ya ke samu a kulle su ke zuwa mai, kowanne yana bukatan a warware shi sosai, daga haka ya yanke shawaran sauraron lbrn da ta fara bashi, wanda ya ke tunanin ana za a samo mafita gabadaya.

Godiya ya ma zeenah, ya mata alkhairi sannan kafin su rabu ya sanar mata in yana bukatan wani abu daga gare ta, zai nema ta.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top