Sha hudu
Zaune ta ke hakimce a kujeran office inta, a hankali ta ke faman juyawa. Ta kura wa news post in da ke gaban wayan ta ido. Wani daci taji ya ziyar ci zuciyan ta, ran ta na wani irin tafasa. "Oh Allah wannan wani irin masifa ne na jefa baiwar nan naka a ciki?" A fili tayi maganan, tana kara jin zuciyan ta na suya. "Allah ya kawo miki mafita, kwarai zan so in cece ki, sai dai hakan nima barazana ce ga rayuwa ta. Asiri na zai tonu, mutane za su daina ganin mutunci na. Duk wani kima da daraja da ake bani zai gushe" ita kadai ta ke magana a cikin rantsatsen office in ta da ya sha haduwa da interiors iya interiors. It looks so serene with simplistic beauty. Yanzu haka dai, tana bukatar wurin da za taje tayi cooling mind inta, inda za ta samu natsuwa da kwanciyar hankali, tana matukar bukatan hakan. Ita haka zuciyan ta ya ke, in dai taji tana son yin abu to cikin gaggawa ta ke aikata shi. Don haka yanzu ma dole ta biya wa zuciyan na ta bukatar ta.
Saurin daukan waya tayi ta dannawa PA inta kira, ba jima wa ya dauka "i need a morning ticket to Seychelles tomorrow" dan jim PA in yayi cike da mamaki, kwata kwata bai jin tana da shirin yin tafiya kwana kusa. Amma kwatsam! Ta kira shi.
"Such a sudden trip" ya fada, yana tsimayin ta mishi bayanin tafiyan na ta. Instead, ce mishi tayi "please do as i said" tayi saurin katse wayan. Ba ta cika son binciken ba, barin ma a wannan tafiyan, da ta ke jin dole ma ne ta bar kasan har sai case in nan ya sarara koma an gama shi gabadaya. She can't do anything for Suhaima now, tunda ta san akwai kason sa hannun ta a abinda ke faruwa da ita. Tana dai fatan wani ya taimaka ma ta. She can't say exactly ga abinda ya faru, dan ba ta sani ba ma. Tuni ta dauki jakan ta, bayan shi ba ta kara daukan komai ba. Landline ta dauka ta danna wa secretary inta kira. "Yes madam" mercy ta fada bayan ta karaso cikin office in.
"Am going for a sudden short trip, make sure, you tied of this place" tana gama magana ta sabi jakan ta tayi waje, ba tare da ta amssa sallaman da mercy in ke mata ba. Mercyn ba ta wani damu ba, domin ta san yan mulkin inta tashi haka ta ke musu, sai dai ba ta jin za ta iya daina aiki da madam in na ta, domin akwai arzikin kyauta kam.
A gaggauce ta isa gida, dan abubuwan da za ta bukata ta hada. Ba wani yawa gare su ba, saboda ita al'adan tane in za tayi tafiya ba ta diban kaya da ya wuce 2 sets, duk abinda ta ke bukata in ta je wurin za ta yi shopping insu. Magungunan ta dai ta hada wuri daya.
Banda secretary in ta da PA, ba wanda ta sanar wa za tayi tafiya. Zama tayi duk wani abinda ta ke bukata ayi in bata nan tayi drafting sannan ta tura wa PA ta Email. A lokacin ta yi booking in hotel in da za ta sauka, a Seychelles in. Bayan nan ne PA in ya sanar mata, an samu flight in amma 6:30 am kuma a airport in lagos. Sannan ba one-way sai round trip. "Its okay, get me a last minute ticket to lagos then"
Karfe hudu na safe driver in ta ya dauke ta zuwa Airport. Har isan ta airport in, fatan ta daya, Allah ya sa ta bar kasan lfy ba tare da wani obstacle ba. Ba su wani dade ba, su ka daga zuwa Lagos.
A wurin kujerun da aka tanada ta zauna a airport in tana jiran a fara boarding. Don rage time ne ta fiddo magazine in interior decorations tana duba wa, coz akwai aikin da za tayi online very soon a seychelles. Time to time mutane na zuwa su gaisa da ita, wasu har requiring yin photo su ke da ita, perks of being a celebrity, she is an an influencer and blogger online. Cigaba da duba magazine in tayi coz she have to make sure everything is going smoothly.
“What a perfect decoration" ta ji an fada daga bayan ta. Kaman kar ta juya sai kuma kawai taji tana son juyawa taga wanene wannan?
Sanye ya ke da glasses karami da ya matukar amsan shi, frame in gabadaya transparent ne don haka ya hade da lens in ya bada kala daya. Kananan kaya ke jikin, shirt in navy ne ta saman aka yi manya layi ash and red in da aka sa tambarin kamfani. Fari ne sai dai bai yi irin mugun hasken nan ba, kana dai kallon shi kasan harda hutu ya kara mishi hasken da ke gabadaya jikin shi. "Handsome" ta fada a ranta, Kallon ta ya ke da kyakyawan murshi akan fuskan shi "it awesome" ya kara fadi yana mai fadada murmushin shi.
She is so friendly so ba za ta iya gwalase shi ba, ballantana ma itan irin mutanen nan ne da su ke entertaining jama'a, ko dan ma business irin na ta ai daman dole sai da farin jina ga jama'a. "It very nice of you to comment, i appreciate" ta amsa shi da kayattaccen murnushin na ta da ke mugun kara mata farin jini ga jama'a.
"You are an interior decorator?" A hankali ta yi shaking head inta tace "am an event planner"
Gyara zaman shi yayi yace "wow! I like your style, if i figure this well you work with interior decorators, photographers, caterers and many different professionals" a natse ya ke maganan, infact ko man shi a natse ya ke.
"You guess right" ta amsa, bai ce komai ba sai ganin da tayi ya mike yana tafiya ba tare da yace ma ta uffan ba har ya dawo gefen ta ya zauna, sai da ya zauna da kyau sannan ya juya ya fuskance ta "am an Architectural Photographer, i don't know ko za mu iya aiki tare? Am going to seychelles nd you?"
Kallon shi ta dan yi sannan ta juya fuska. Suddenly, taji rashin dadin yanda conversation in su ke shirin komawa formal. Girgiza kai tayi tace "am sorry"
Ba tare da ya nuna wani reaction ba yace ma ta "ba damuwa zan iya samu card inki?" Without second thought ta bude hand bag in hannun ta dauka business card inta ta mika mishi "thank you" ya amsa ba tare da ya duba ba ya sakala a pocket in jeans in shi "see you later" kawai yace da far in ciki bayyana a fuskan shi ya bar wurin ta. Tun tana kallon inda ya bi a cikin airport in har ya bace ma ta gabadaya, tayi tunanin zai yi insisting shiyasa tayi denying offer in shi. Yanzu kam da ya riga ya wuce ji tayi kaman ta je ta jawo domin Sanar mishi she is totally in with the offer sai dai ko kadan ta San ba za ta iya kwatanta hakan ba. Siririn tsaki taja tana mai maida idanuwan ta kan abinda ke gaban ta, duk yanda thoughts in shi ya fitan ma ta a kai hakan ya gagara coz ba ko yaushe ta ke hadu da mutane su yi mata tayin offer tayi rejecting kuma su kyale ta without any persuasion. She pays a lot bayan wannan kuma she is very friendly and accommodating toward duk wani wanda aiki ya hada su, hakan ya sa mutane ke son aiki da ita. Ta fannin ta in dai ka zama mutum mai kula da lura da ai kin shi sosai to ba ka da matsala da ita. Hakanan kawai wani abu ke gaya mata wannan fa ba shi yayi missing offer da ita, Aa, a karon nan alamu na shirin nuna ita ce tayi asaran babban dama da yazo ma ta. Suddenly, sai yaji interest inta ya kara tana son sanin me ya ke bukata a wurin ta. Daga ganin yanayin shi da confidence ya nuna mata shi in ba karamin mutum bane, ba ta bangaren shekaru sai dai ta fannin Naira mai sa mutum suna da daukaka.
Duk yanda ta so ganin shi abun ya gagara, duk da ma ba wani yunkuri da tayi bayan wuce war shi amma ta so kwarai ya dawo ta inda ta ke ta samu daman mishi magana. A haka aka kira boarding, sai a lokacin ta ke tunanin tabbas Seychelles ya ce mata za shi, duk da haka ba ta ganshi ba.
Da ke Ethiopian airline ne flight in, ticket in business class ta siya daman. Settling tayi a seat inta sannan ta fiddo magazines inta tana kara dubawa, a gefe daya tana calculating events in da ke gaban ta duk da ba ta country in. Har aka tashi abinda ta ke ta faman yi kenan, ba laifi tayi progressing sosai. Ajiye su tayi ta dauko English novel in Danielle steel, the cast ta fara karanta wa, it part of her in dai za ta shiga plane to tabbas da novel a hannun ta, tana enjoying karatu sosai a wannan lokacin. She is engrossed in the novel da ba ta ma lura da environment inta, novel like this are so wonderful and lovely to her, sosai novel in ke inspiring mutum. Ba abun da ya dau hankalin ta kaman novel is not centered around budurwa da saurayi, Aa, it talking about babban mace that already yaran ta sun girma sun kama gaban su kowa ya fuskanci future in shi but still the writer got something to share on the mothers life and it amazing.
Kaman an ce ta dago kanta, ta hango shi can gaba da ita. Hankali kwance ya ke operating system da coffee cup a gaban shi a hankali tana sipping.
Seconds ta dauko tana kallon bayan shi sannan tayi saurin dauke kai ta mai da attention in ta kan novel inta.
Awanni masu yawa ya kai su Seychelles international airport da ke mahe island. Aljannar duniya, kirarin da ake ma kasar kenan. Haddaden kasa ne da Allah ya wadata da wadataccen ruwan teku, duwatsuna da tsaunu ka sannan ga bishiyoyi iri iri da ke zama a bakin teku da tsibiri (island) kala kala da su ka cika Kasan. Gabadaya, sai su ka hadu su ka bada wani ni'imtaciyyar ni'ima da annshuwa da ke wadata natsuwa da farin cikin. Sau dayawa za ka iske sabbin ma'aurata da masu yawan shakatawa a kowani sashe na Kasan.
Tun da ta sauko daga cikin jirgin ta ke jin wani natsuwa na daban na mamaye duk ilahirn jikin ta. "Alhamdulilah" ta samu bakin ta da fadi tana mai godewa ni'imar ubangiji ta da ya wadata mutane da wannan Kasa mai cike da albarka. Da lugagges da ba su da wani tawa ta fito daga cikin airport in domin neman taxi in da zai kai ta Victoria, inda za ta karasa Eden island, a nan hotel in da tayi booking ya ke.
Hango shi tayi a can gefe guda shi kadai da camera a hannun shi tana kokarin capturing view in da ke wurin. Murmushi tayi, domin ita kanta ta San da photographer ce ba abinda zai hana ta daukan wurin nan, haka da ita marubuciya ce samun wuri za tayi ta rubuta duk wani yanayi da ta ke ji sanadiyyan ni'imtacciyar Kasan nan kafin ta kara gaba.
Tana cikin wannan tunanin ne ta ga tana kokarin karaso wa inda ta ke, standstill tayi har ya karaso da camera in shi rataye a Wuyan shi yayi folding lips in shi. Irin su ne mazan da mata ba su iya resisting kallo, in kaji ana dream guy, to wannan irin shine gabadaya, wato abinda ake cewa jinin burga, da ka kalle shi zai tafi da kai ga kuma kwarjinin da ke sa ta kasa zuba mishi idanu tana kallon halittan Ubangiji.
"Hey, we meet again" ya fada bayan ya karaso inda ta ke. Siririn murmushi tayi wanda ya kara fiddo da kyan ta, ba fara bace ita amma her skin color is just wow, musamman da ta ke glowing in su da hadaddun creams. Tana kyau iya Kyan ta barin ma in tayi murmushi. Ba siririya bace, sai dai yanayin jikin ta ma kyau ya ke kara ma ta, sai dai kallo days za ka mata kace she is bossy.
Ganin ba tace mishi komai ba yasa yace "Am Faroukh Machina nd you?" Kasa kasa ya ke magana kaman mai rada yana kallon fuskan ta.
"Umaimah Amin" ta amsa tana dan juye juye da kan ta.
" Beautiful lady with nice name, are you heading toward Victoria?" Ya tmby saboda yanda ta ke nuna ba ta son tsayuwan.
"Eden island" ta fada
"Mu je mana, am going there" ba tace komai ba ya kira musu mai taxi su ka shiga. Da farko ba su yi wani magana ba, da ke duk a baya su ka zauna sai lokacin ta ke ganin camera in shi da ya ajiye a kasa da kyau, latest Nikon ce ko shakka babu wannan dan wani kusan ne a Nigeria saboda dai irin harkan sai su.
"Wani hotel za ki" ya kara tmbyn ta.
"Eden bleu" ta bashi amsa, dan cizan yatsa yayi yace "bansan za mu hadu ba da na mana booking a apartment in da zani, nasan you will love it"
"I can come visit" ta fada tana kallon shi alamun is he okay da abinda ta fada. "Sure" ya amsa dukkan suna murmushi cike da annashuwa har su ka karasa destination insu.
...
A daya barin kuwa, kafin safiya. El-yas bai samu zuwa apartment inda Barr Mustapha ya ke ba sai bayan isha'i. Zallan bakin shayi ya iske shi yana sha, suna gama gaisa wa yayi offering in shi shayin, ba musu ya amsa. He looks so calm and cool, shi daman Barr ya mugun yaba wa da El-yas in tun a farkon ganin shi.
"Sorry fa na neme ka kana wani abun" barrister ya fada bayan yayi sipping shayin da ke hannun shi.
"Bakomai Uncle Musty" dan shiru El-yas yayi, yace "naga kai ke kare jewel in mu ai"
Widening eyes in shi mustapha yayi yace "jewel?"
Siririn murmushi El-yas yayi "Oga Zayd calls her that"
"To Amma me ke tsakanin su?" Mustapha ya bukata. Kai tsaye El-yas yace "Employer and employee, then he so much adores her"
"Kana nufin budurwar shi ce?" Girgiza kai El-yas yayi "Probably, amma am not sure. Everybody adores her ai but Faroukh is an exception."
"Kowa ya san tana da halaye mai kyau kenan?"
Gyade kai El-yas yayi "she is so friendly though ba ta cika magana ba, she is kind with everybody. Sai dai wasu na mata kallon mai girman kai, mostly mata ne. amma na fi dangan ta hakan da rashin kula su sosai a zauna ana hira. Faroukh bai taba yarda da ita, ya kan ce min akwai mugun manufa tattare da ita. Bai taba fada min dalilin shi ba kowa da kuwa na tambaye shi" sai dai barr ya gama sauraron bayanin nashi sannan ya fara wani tunani. Ya san abinda zai tmby Suhaima ranar da ya kara koma wa wurin ta.
"Ban san mai ya hada ta da Faroukh ba kam" Barr ya fada, more like kan shi ya ke wa magana.
"On 31st July, wasu daga cikin ma'aikatan ku sun je apartment in da ita Suhaiman ke zama a Asokoro kana daga cikin su?"
"Kwarai kuwa" El-yas ya amsa. "Mun je gidan kusan mu goma a wannan rana bisa ga Umurnin Oga Zayd. Abin da ya faru shine: Suhaiman tayi kwana kusan bakwai ba ta zuwa gun aiki. Oga zayd in ya matukar damuwa da rashin ganin ta a yan kwanakin, to dama a ranar akwai meeting in da za muyi sai ya kira ni, yace min dukkan mu mu same mishi a can gidan. Da ke asali guest house in shi ne. Two flats ne a ciki, daya inda Suhaiman ke zama daya kuma wurin da ya kan hadu da bakin shi. Wato abinda na lura a wannan ranar kaman sun samu wani matsala ne tsakanin su. Ganin mu ya sa ta dole fitowa aka yi meeting in da ita, daganan sai muka zauna hira. To ni dai wani uzuri ya taso min, a gidan na tafi na bar su"
"Ko akwai wanda ya shiga kitchen in gidan ranar?"
Citse lebe El-yas yayi kan shi a sama kaman yana tunani yace "Gsky ba wanda bai shiga ba, ai gidan kitchen daya ne. Tunda na ce maka guest house ne kaga kenan ba lallai kitchen ya zamo daga cikin lissafi ba, duk an shiga, kuma daga masu soya kwai, dafa indomie, sai masu tafasa shayi. Halin Oga Zayd ne haka, he treat all his employers as friends."
"Amma banda Faroukh, ba wanda kake tunanin suna da matsala tsakanin su da Suhaima?"
"Babu ai nace ma ka ba ta cika shiga harkan mutane ba, iya sanina gsky bbu kam."
Banda daure kai ba abinda Barr ya samu wurin El-yas. The more yana kara bincike, the more lamarin yana kara shigar da Faroukh ciki. Kowa ya san Faroukh ya ki jinin ta, to amma miye dalili? Ko da ya san Faroukh in na da baudadden hali amma its unlike him ya dauki tsanar duniya ya daura wa Mutum. Dole ma ya koma wurin Suhaima su tattauna tunda Faroukh in yaki fito mishi a mutum.
"Faroukh yace min asali kawar budurwar shi ce?" Barr ya tmby.
"Eh hakane saboda da ma a gidan su ta ke zama"
Jinjina zancen Barr yayi tayi a zuciya yana mai neman mafita. Sai dai mafita daya ta ke bashi, amsa na wurin suhaima. Kuma in dai tana son fita daga kangin rayuwan da ta ke ciki, ya zama tilas ta buda mishi cikin ta gaba ki daya.
Yana shirin bacci, call in zeenah yayi obstructing in shi. Dole ya dauka, bacci ne sosai a idanun shi, har rufe su ke yana kokarin bude su gabadaya sun mishi wani mugun nauyi ga ya hade mishi da kai. Ita ko zeenah sai faman bashi wani lbr da ba kai ta ke, it doesn't even make sense to him. "Yanzu nan rabuwan dashi, night flight gare shi zai koma jigawa inda iyalan shi su ke. Kaga bakin ciki da ke ranshi? Ga dukkan alamu iyalan na shi ba ma su kula bane kuma ma throughout da mu ke tare dashi ba wani wayan kirki da suka yi, in kaga sun kira to abu ne ya kare a gidan ko kuma suna bukatan wani abu. Ai mata dai..."
"Zeenah please" yayi saurin interrupting saboda shi gabadaya labarin ma ba wai ya wani fahimta bane don bai jin ta.
"Oh sorry, you sound sleepy gobe xan neme ka sai muyi magana, ai kawa tafi karfin komai a wurina kar ka wani damu domin hadin kai..."
"Nagode, zan kira ki goben" yayi saurin fada sannan yayi ending call in. Shi kam bai taba ganin mace mai surutu ba ma kaman zennan. Ko ta ya ma aka yi su kayi abokanta ka da Suhaima? Bayan itan she is too silent. Shi dai kam wannan sarkakiya na Suhaima na mugun daure mai kai, dole ta samu ta warware mai ko da kuwa itan ce ba ta da gsky ta aika ta abinda ake zargin na ta dashi. Dole daman shi lawyer inta ne ya kare ta ko da cikin wani hali, duk ma bai ganin za ta iya kwatanta aikata hakan.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top