Sha biyu
Dukkan wani bayani da ya kamata ace sun samu sun same shi. Abujan su ka tafi da kansu. Sai dai har yanzu ba su gano asalin abinda ya faru tsakanin Suhaima da Almansur ba. Suna dai fatan ji daga bakin Suhaima, daganan a san yanda za a bullo wa zancen. Duk iya kokarin su a ranar ganin Suhaima hakanan ya gagare su. Dole dai Barr Mustapha ya isa station in a matsayin lawyer mai kare ta, tunda ya samu lbrn sun kai case in court.
Abin da ya lura shine, kaman ba gsky a lamarin duba da irin kallon da su ke bin shi dashi. Sai kuma su fara kus kus tsakanin su. Wasa su ka dinga mishi da hankali da dai yaga abun da wata a kasa dole ya koma headquarter insu na nan Abuja yayi reporting abinda ke faruwa.
Ko a can inma, shugaban su ce mishi yayi "Barr Mustapha mai ya kai ka amsan irin case in nan? In zan baka shawara ka ajiye wannan case in mana"
"Amma miye dalilin ka na fadan hakan?" Ya tmby, girgiza kai yayi "yace haba Brr kowa ya kwana ya tashi a kasan nan fa yasan su waye Al-mansur, shin kana ganin za ka iya nasara a irin case in nan da ake amfani da kudi da karfin mulki a ci shi? Kai kasan shari'a, Hujjan da duk ka kafa shi shine abin dubawa. Kai ya kamata ka fadawa mutane cewa dayawan mutanen da ake kai prison ba su aikata abinda ake tuhuman su dashi ba, Aa kawai karfin hujjan akan su ne ya ke kai su inda su ke. Wani irin kudi ma aka yi offering in ka kayi gangancin amsan case irin wannan mustapha?"
Runtse ido Barr yayi, tabbas dukkan abinda ake fada mishi gsky ne. Wannan shi ya ke kara tsorata shi da shari'an. "Ba kudi aka bani ba sir, i personally know the girl ne zan so in taimakeka"
Shiru yayi alamun nazari, can yace "Shknn Barr tun da ka dage, Allah ya bada nasara. Kaje ka same su, zanyi sending note" godiya yayi ma shugaban nasu, cike da farin cikin nasara ya kara nufan station in.
...
Da constable ya bude mata lock in ta fito, ko kadan ba ta kawo komai a rai ba, binshi tayi kaman rakumi da akala har zuwa inda Mustapha ke zaune. Ko kusa ba tayi tsammani ganin daya daga cikin su ba, barin ma a yanayin da aka taho da ita. Kokarin tsagaita tunanin tayi ta fuskance shi da idanunta da su ke bushe kararau har izuwa yanzu.
Kallo daya ya mata ya ji wani irin mugun tausayin ta na ratsa dukkan jikin shi. Ta tsinci kanta ne a cikin wani irin mawuyacin halin. Ko shakka ba yayi gab ta ke da ta cire buri ga rayuwa gabdaya, shiyasa shi kuma ya lashi takobin taimaka ma ta ko ta halin yaya, ko da kuwa bashi ke da Nasara ba a karshen hankalin shi ba zai kwanta ba in har bai kokarta ba.
"Suhaima" ya kira sunan ta yana kara karantar yanayin ta, shi kam a kwana biyun nan har rama idon shi yaga ta mai. Hannun ta daya ta sa kan goshi ta runtse idanuwan ta, a can cikin ta ta keji wani irin radadi na wucin gadi. "Abban Haydar ka yarda dani Wlh ban aika ta ba"
"Kar ki damu, ba wannan bane matsalan a yanzu" ya fada yana kara gyara zaman shi.
Zaro idanu tayi cike da rashin fahimtar manufar maganar shi. Gane hakan da yayi ne yace ma ta "Kin fa san shi kotu hujja kawai ya ke nema Suhaima, kuma banda wurin ki ban gani akwai inda zan samu hujjojin da ya kamata, shiyasa na ke so ki kwantar da hankali muyi magana" saurin girgiza kai tayi tana fadin "ba wannan bane matsala ta Abban Haydar, so na ke kawai ku yarda dani, ku yarda ban aika ta ba. Amma nasan jayayye dasu ba zai wani haifar da da mai idanu ba, toh in ma na samu fita ina zan nufa? Ban ganin ina da wani abu da zanyi fada domin shi ba, banda komai kuma banda kowa"
Zantukan ta ba karamin illa su ka mai ba, sai dai ba ta cikin halin da za ta fuskanci hakan da ba ta karasa ba. Kaman dai yanda yayi hasashe ne, she is giving up akan rayuwa gabadayan ta. Da kyar ya iya hado kalaman da zai fada mata "Aa Suhaima ki daina maganar nan, ai kina da Allah kuma ba gamu ba? Mu dai ba mu ga wani halin assha a tare da ke iya zaman da muka yi da ke, shiyasa mu ka tsaya miki"
Murmushi mai matukar ciwo ta saki "kasan Almansur a kasar nan kuwa? Kasan karfin shaharan su? Ka san yawan dukiyan su? Za su iya yin komai wurin kwato wa Dan su fada duk ko ta hanyan da su ka ga zai kawo musu nasara, ban san saku hadari dan Allah ka bar zancen nan"
"Suhaima please" ya fada yana dakatar da ita da hannuwan shi. "In ba zaki iya bani karfin guiwa ba kimin shiru" a fusace yayi maganan, kusan sanin ta dashi ba za ta iya tuna lokacin da ya fusata irin haka ba sai lokacin case insu da maryam.
Magana ya fara yi yanzu kuma kaman mai lallashin ta yace "Dan Allah ki bani hadin kai kinji? Wlh hankalina ba zai kwanta ba in na bar ki a haka ba zan iya yafe wa kaina ba." Wani iri kunya taji ya kamata, shin ba matsalan ta bane? Amma kuma shi ke rokon ta ta taimaka wurin kare kanta? Shiru tayi ...
"Shkkn" ta fada a sanyaye, sai lokacin yaji sauki ya mamaye shi yace "Kin amsa wani tmby a nan?"
"Ba wanda ya tmbyn, illa ma nuna wan da suka yi kawai nina aikata abinda su ke tuhumata dashi. Wai meyesa mutane ba su da adalci ne a rayuwan nan?"
Shiru yayi can ya kalli agogo "Suhaima zan tafi gobe za a fara zaman kotu domin gabatar da kara, remember you are pleading guilty, try to be yourself kawai kar ki yi wani acting. Sannan za muyi kokarin neman bail ko dan mu samu tattaunawa da kyau."
"Kudin bail in bai da yawa ne?" Ta bukata
Shiru yayi kaman ba zai yi magana ba yace "Sai dai gobe in sun bada zamu ji abinda su ka yanke.
Hannu ta mika mishi ta na nuna takarda da biron da ke hannun shi. Kaman zai yi magana sai kuma ya fasa ya mika mata kawai. Phone no ta rubuta mishi da home address na lagos. Sannan ta mika mishi " Ka kira numban, sunan ta zeenah, tana zaune a gidan yanci a agege da ke garin lagos. Na ma rubuta ma address in, in ka kira kawai kace mata daga kawa Yar baiwa ne. Duk amount in kudin da yakamata ka fada ma ta za ta turo ma ka. In ba ka samu numban ba, in akwai wanda ka sani a lagos ka aike ta wurin shi. Kawa, Yar baiwa fa za kace mata" kaman a mafarki ya ke jin abun da ta ke fada mishi. Gidan yanci kuma? Mai ya hada suhaima da wannan? Gidan karauwai fa kenan, tab da alamun abun ya fi karfin yanda ya ke hango shi.
Kaman ya share numban da ta bashi, sai da su ka hadu da Dr Fahad a guest house in Abban shi likitan ya labarta mishi yanda su kayi da Suhaiman. Shi kanshi Dr in sai da yaji faduwar gaba amma sai yayi kokarin ba wa Barr karfin guiwa. "Mu neme ta kawai, kilan ta zamo wani hanyan taimaka mana ma bayan kudin" Shawaran ko su kabi. Sai dai kusan sau bakwai suna kira numban ba a daga ba, duk jikin su yayi sanyi. Dr Fahad yayi kokarin daga wayan shi ya kira wani abokin shi da ke garin lagos in kuma ba laifi ya dan yi harka da gidajen kafin daga baya Allah ya shirye shi bayan yayi aure. Bai wani tsaya dogon gaisuwa ba ya sanar taimakon da ya ke nema a wurin shi.
"Haba bokon turai kar ka sa ni jin kunya mana? Kai da kanka yau kuma?" Da shekiyan ci ya mai maganan, Dr Fahad ya gane hakan ne saboda wa'azin da ya kan yi mai lokacin da su ke service.
"Pls mana its urgent, wani case ne" ya fada sounding more serious.
Har wurin magriba suna jiran jin labarin. Sai bayan anyi sallah yayi receiving call in friend in nashi, ba lbr bane mai dadi. Zeenah tayi tafiya yau kwana biyar kenan kuma ba wanda ya san ranar da zata dawo, ba wanda ya san takamaiman inda taje kuma. Ba suji dadin lbrn ba amma sai suka share su ka fara neman mafita, sanin ko an basu bail in tofa ba karamin kudi za su ciro ba. Amma ganin su biyu ne ga kuma Engr is more than ready to help sai su kaji dan dama dama.
...
Safiyar litinin da karfe sha daya da rabi na safe aka shirya sauraron karan. Dukkan su da wuri su ka halarci kotun suna jiran kiran karan su. Ba abinda ya daure wa Barr Mustapha kai sai Jaridar da yaga ana ta sayarwa lokacin da ya isa court house. A young lady charged for murder of the Famous Almansur son. Hoton Suhaima ne a jiki da handcuffs a hannun ta lokacin da ake kokarin shiga da ita police headquarters na Abuja. Abin daurewan kan shine: Atleast case in nan zai yi wata uku da faruwa, shin meyesa ba su taso dashi ba sai yanzu? Sannan a sunan da Almansur su kayi a kasan da mamaki ace dansu yana cikin wani hali na rayuwa mutuwa har na wata uku ba wanda ke da information akai.
Sha daya dai dai gabadayan su suka gabata cikin kotun. Reporters kala kala Suhaima da police su ka tarar dasu a bakin kotun sai dai ba wanda ta ba wa attention balle yayi tunanin tana da niyyan amsa shi. Tayi kokari sosai gun bin abinda Barr Mustapha ya fada mata, kanta ba a kasa ya ke sai dai duk da haka ba wanda ta ke kallo har a ka isar da ita gun inda ake bukatan ta tsaya. Bakin abaya ke jikinta sai farin baby hijab akai, musamman Barr in ya aika ma ta saboda gabata a gaban kotu. Kana ganin ta kaga wacce ke cikin matsanancin tashin hankali, addu'a ta ke ta fama yi a hankali za kaga bakin ta na motsawa.
Judge Yusuf Ibrahim, shine sunan alkalin da zai saurari karan. Sai da yayi yan rubuce rubucen shi sannan ya dago, kan Suhaima ya fara sauke idanuwan shi. Bai wani dade ba ya dauke ya maida kan lauyoyin da su ke zaune a wurin.
"Lauyan Gwamnati, ina sauraran ka" Alkalin ya fada, idanun shi akan lauyan.
Kai tsaye Barr in ya mike tsaye. Lauyan da ke aiki karkashin gwamnati ma'ana (prosecutor) aikin su suyi proving zargin da ake ma criminal, su gabatar da shaidun da zai nuna guiltiness insu. Irin lauyoyin nan ne da suka yi kaurin suna a sana'ar su kuma suka taka mataki daban daban a fannin shari'ah. Maye ne, dalili kuwa ya matukar kwarewa wurin iya samo hujjoji da kure mutum, ya na yawan samun nasara a dukkan shari'ar da ya sa gaba. da karfin guiwan shi sosai yace "Ya mai girma mai shari'a sunana Barr Sadiq Lawal Funtua. Wacce ake kara tayi yunkurin kisan Zayd Almansur ta hanyan sa mishi guba a abinci, sannan ta tada gobara a gidan bayan ta tabbatar da yaci abinci. Tayi hakan ne saboda wani tunanin na ta na ganin ba za a zarge ta ba. Bayan ta gama kuma sai ta sa kafa ta bar garin har na wata uku sai a kwanan nan aka samu lbrn ta a jihar kaduna a bakin wani Ma'aikacin Zayd Almansur in. Yanzu haka victim in bai san inda kan shi ya ke ba." Cikin natsuwa ya ke bayanin yana kai kallon shi kan alkalin domin kokarin ganin inda zancen nashi ya ke kaiwa. Yanayin maganan shi kadai zai fahimtar da kai an dade ana damawa dashi.
"Wannan case in ba karamin bane, bayan guduwan da tayi ta ba wa yan sanda wahalan bincike" farat daya muryan shi ta canja irin na wanda aka cuca ta "Don haka ina mai rokon wannan kotu mai alfarma da ta hana bailing wannan yarinya, sake ta daga hannun hukuma babban risk ne, za ta iya kara bacewa wani wuri kuma tazo tana wahalar da shari'ah." Sunkuyar da kan shi yayi sannan yace "ina mai fatan wannan kotu zata fahimci inda na dosa, nagode" ya karasa sannan ya samu wuri ya zauna.
Alkalin ya dade yana rubuce rubuce kafin ya dago yace "lauyan wanda ake kara, bismillah" da izza Barr Mustapha ya tashi ya gabatar da kanshi "Ya mai girma mai shari'a zan so wannan kotu mai Alfarma ta fahimci cewa da wacce ake kara guduwa tayi da yan sanda ba su same ta cikin sauki ba. Ko cikin report insu har cikin gidan da ta ke da zama su ka je kuma su ka same ta, haka kuma ba wani gargada ta mika wuya." Shiru Barr ya danyi na seconds yana kallon yanayin Suhaima sannan ya cigaba "zan so wannan kotu tayi la'akari da cewa wacce ake kara ta san cewa gidan da ta ke zama akwai wanda ke aiki karkashin wanda ake ikirari tayi yunkuri kisa. Da taso guduwa ba zata zauna a wannan gidan ba bayan ta san hatsarin da ke ciki. Ina fatan wannan kotu mai adalci za tayi duba cikin lamarin nan ta ba mu beli, nagode ya mai girma mai shari'ah" shiru kotun ya dauka kafin alkalin ya dago kanshi.
"Muna bukatar hujjoji akan abinda ka gabatar Barr Mustapha. Za a daga wannan karan zuwa 7 ga watan November, nan da sati biyu masu zuwa. Yan sanda na da ikon cigaba da tsare wacce ake kara har zuwa wannan ranar. Kotuu" alkalin ya karasa da bugu yar guduman shi.
Zufan azaba ne ya fara zubo ma Suhaima daga ko ina na jikin ta, yanzu a wannan kazamin wurin ake so ta cigaba da rayuwa har nan da sati biyu masu zuwa.To kika san inda makomar ki za ta kare bayan shari'an? Wani zuciya ya tunatar da ita. Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata a makogaro. Shin wannan wani irin mugun kaddara ne rayuwa ke juyi da ita ta ko wani fanni. Tabbas yanzu kam ta gama yarda rayuwan ta ba ta da wani amfani. Kaman mutum mutumi haka ta ji lokacin da police in ta ja ta zuwa motan su, gab fita kotun ta hadu da Barr Mustapha da Dr Fahad. Police in ba ta wani bata daman kallon su da kyau ba amma duk da hakan bai hana ta hango zallan tausayin ta a idanuwan su ba. Tabbas Allah bai hada ma ka zafi biyu a rayuwa, ita kam haduwan ta da wadannan mutanen ne sanyin da ta ke fuskan ta acikin dukkan wani kunci. Tana ji tana gani su ka kara janta zuwa Cikin tashin hankalin da ta ki jini da dukkan wani nau'i na jikin ta. Hakika an cuce ta a rayuwa, cutan da bashi da iyaka kuma ba mai iya rama mata sai Allah SWT.
...
Su Dr Fahad kam da bakin ciki rashin nasarar da su kayi su ka bar wurin. Barin ma Dr da ke jin kaman ya tsaga zuciyan shi kawai ya fito da ita saboda azaban kunan da ya ke ji a wurin. A cikin yan kwanakin da ya san Suhaima ya mugun sa ta a ranshi da ma rayuwar shi gabadaya, shiyasa duk wani damuwan shi ya ke jin ta kaman nashi ne. Duk wani abinda ya shafe ta ya shafe shi, abinda ya ke fada ma ta kenan kuma har ran shi yana jin gskyn hakan a yanzu.
Tilas Barr ya dau hanyar kaduna saboda a yanzun hakane ya zame mashi dolen dole. Ko Faroukh bai so sai ya sanar mishi dukkan abinda ya sani in details saboda hakan ne kawai zai samo mishi mafitan da ya ke bukata. Gidan Anty ya nufa yana shiga Kaduna, tana ganin shi ta hade rai da kyar ta amsa gaisuwan da ya mata ma.
Marairaice fuska yayi zuwa gare ta, abunda tayin bakon abu ne a wurin shi. Alakar su da ita na daban ne, duk wani matsalolin shi a rayuwa ita kadai ya ke iya tunkara da. Ya santa farin sani don ko mahaifiyar shi bai ma sanin da ya wa Antyn nashi ba. Akwai ta da mugun son ya'ya'nta duk da ta kan dage wurin tsawatar musu. Sai dai ba ko yaushe ta ke karban laifin yaran nata. Yanxun ma ya san matsalan akan furucin da yayi akan Faroukh. "Haba Anty na da lil inki zaki yi fushi kuma?"
Hararan shi ta juya kai "Ka tashi ka tafi kayi abinda ka sa a gaba" ganin dai da gaske fushin ta ke dashi ya sa ya dage yayi ta bata haushi, dolen dole ta sauko tace mishi "ban san ka da taurin kai lil, shin meye sa ba zaka bar case in nan bane wai? Kasan me kake jefa kanka a ciki kuwa? Eh! Akan yarinyar da ba ka santa ba, ba kuma ka san asalin nufin ta ba."
Dukar da kai kasa yayi cike da ladabi "ki yi hakuri Dan Allah Anty. A fahimta ta Suhaima na cikin wani hali da ta ke matakur bakutar taimako. Hakan yasa na ke son yi kokari akan ta. Yarinya ce duka duka amma ba ta da kowa da ya tsaya ma ta a rayuwa, shin ba kya tunanin wani bala'i ne babba ya afku da ita har yasa ta barin kowa nata? Nikam ina tausayin ta sosai wlh haka kuma ina son sanin Labarin Rayuwar ta" shiru Anty tayi tana sauraron shi har ya gama sannan tace.
"Amma ba ka tunanin bala'in da zai raba budurwa kaman wannan da iyayen ta ba karami bane? Ba ka gudun wannan ya shafe mu? Har ga Allah da fari na yarda da ita na bata benefit of doubt amma tunda wannan abun ya faru hankali na ya ki kwanciya da lamarin. Kuma kasan shi Dan adam wani abun kwata kwata ba kama. Amma tunda ka dage Allah ya bada saa" ta na fadin haka ta tashi ta bar falon, bin ta yayi da kallo yana wani nazari kafin ya nemi ganin Faroukh, ba ya gidan don haka ya kira shi ya same shi a gidan shi washegari da safe.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top