Sha biyar
Shiru tayi tana sauraron shi har ya kawo aya. Sai a sannan ta saki nannauyan ajiyan zuciya tace "zan baka gabadaya lbrn kaman yanda ka bukata. Sai dai ina bukatan wani alfarma in za ka iya min kafin in baka lbrn"
Bai ce komai ba sai dai kallon da ya ke mata ya nuna mata alaman ya yarda ta cigaba, shi dai barr har ranshi ya ke jin farin ciki samun nasaran da yayi a akan ta.
"Ina so Dan Allah in na fara baka lbrn nan kar ka katse ni, kar ka fuskance ni a bai bai haka kuma kar ka min wata tmby har sai kaji bayanin komai daga baki na." Kallon shi ta ke tana bayanin, ido gara rau, shi kam har yau yana mamakin rashin kukan da ba tayi ba duk da tsanin tashin hankalin da ya ke hango wa a idanuwan ta.
"Shknn ba matsala, sai dai kafin ki fara ina son sanin nawa zan amsa wurin zeenah" tabe baki tayi hade da girgiza kai.
"Ko nawa ake bukata za ta baka, kawai ka fada ma ta" kallon ta yayi yana mamakin yanda ta ke da tabbacin za a samu duk abinda ake bukata ko da kuwa yawan su. Kokarin furta hakan yayi.
"In ba za su isa ba fa? Akwai kudin da mu ka hada da Dr da baban su Faroukh ba sai mu hada ba? Sincerely speaking kudin nan na da yawa" ko da ya dago ya kasa karantar yanayin fuskan ta, banda yanda idanun ta su ka fada sosai, tayi wani fayau kaman ba ita ba, har rami kasan idanun ta su kayi, zai iya rantse wa bacci ya dade da kaura a idanun ta. Duk da ana ba ta abinci mai kyau, haka kuma wurin baccin ta ma ba laifi kuma ta tabbatar mishi har wa yau ba wanda yazo da niyyan ma ta tambayoyi.
"Abban haydar" ta fada tana kallon shi tace "kar ka damu, Dan Allah dai kar ku taba kudin ku, akwai more than enough a hannun zeenah, ko da an bar su ba za suyi wani amfani ba da yafi wannan in" iya gskyn ta ta ke maganan, shi kam gabadaya zuciyan shi ya tafi da mamakin shin wani irin kudi ne wannan? A ina kuma ta same su? Sai dai da alaman ta bar ma kanta sani. Katse mishi tunani tayi.
"Zan baka labarin sai dai zan fara daga abinda ya fara hada mu da zayd tunda a yanzu shine focus inmu" gyade ma ta kai yayi kawai ya gyara zaman shi yana mai kara fuskan tan ta. Kan ta a kasa ta fara bashi labarin kaman wacce ta ke karatun jarida ko wani littafi.
...
Uzuri, kalma mai mahimmanci da mutane kwata kwata ba sa wa Dan adam a zamanin nan. In ka ga mutum a cikin wani hali na kazanta a rayuwar nan in ba ka mishi fatan shiriya ba to ko tabbas kar ka zage shi. ba wanda ya san rubutaccen kaddarar shi da ta ke jiran shi a cikin littafin rayuwan shi. Kowa da irin yanda tashi za tazo mishi haka kuma da irin yanda zai kokarta wurin cin jarrabawar shi.
Da can a baya na kazanci masu hali irin nawa a yanzu, na yi Allah tur da wadai dasu. Duk a tunani na ba wani kaddarar rayuwar da za tazo in afka cikin rayuwa irin wannan sai dai ina nayi kuskure, jarabawar tawa dole tazo da hakan.
Lagos, Nigeria.
Yau ma kaman kullum zaune na ke a katafaren gidan rawan (club) in da ke birnin lagos a ikeja. Hankali kwance ba tare da nayi la'akari da daren da ya ja sosai ba. Kaman ba nice Watannin baya da su ka shude kafin yau in na ke dar dar da zaman wurin ba gabadaya na kasa sakewa. Kallo na kara bin gabadaya wadanda ke wurin da ke ta faman rawan su hankali kwance ba tare da an damu da cudanyan da ke tsakanin maza da mata ba kaman yanda ake yi a arewacin Nigeria. Amma nan al'adan su da dabi'un su ya sha banban domin daga musulman har arnan hade su ke hankali kwance suna shan rawan su mai hade da kida da ke matukar tashi, rawa ne na musamman da ya zama jiki anayi duk dare, mawakan su dayawa na halattar wurin. Kalolin giyan da ke wurin ko ba a magana balle kuma a kai da irin rawan shafa jikin da ke gudana tsakanin mace da namiji. In har budurwa ba ta zuwa irin wadannan wuraren to ganin mai duhun kai a ke mata shiyasa kowacce ke kokarin halarta wasu ma kawai don su faranta wa samarin su ne. A arewacin Nigeria ne za kaji wai don saurayi yaga budurwa a wurin rawa zai dauke ta yar iska ba zai iya auren ta ba ko da shi in ma yana zuwa. A can ko hankalin su kwance duk abinda zai gudana tsakanin su da mace ba zai hana su auren ta in dai suna son ta. Kawai dai sai dai ace auren ba Albarka sabida ba a gina shi akan turba mai kyau ba. Yau a irin yanda rayuwa ta juya min kenan. Na ruga na sawa raina ba abinda zanyi yanzu in canja hakan, kwalban da ke gaba na na dauka na cigaba da kwankwadan abinda ke ciki. Tunanin kowa a wurin giya ce na ke sha sai dai abinda ba su sani ba har wayau shine na kasa sabawa da shan shi duk barikanci na, ko dandanon sa tada min zuciya ya ke. Barni dai da duniyanci amma shan giya kwata kwata na kasa iya sa.
Tsit naji wakan ya tsaya a sandiyan salon kidan da aka canja zuwa wani slow motion, ai ban san lokacin da na mike a hankali na nufi tsakiyan filin ba. Ihu kake ji yana ta faman tashi a wurin yayi da bakin su ke faman furta "Pul-chri-tude! Pulchritude! Pulchritude!" Cike da farin cikin ihun support in da na ke samu na karasa tsakiyan filin. Cikin da natsuwa na fara juya kugu na ina wani irin rawa na daban da ba kowa zai iya shi ba a wannan wurin. Rawan ne na musamman da masu irin jiki nawa kadai ke iya wa, wanda shi ne asalin sunan da na samu wato pulchritude "physical comeliness" saboda irin tsarin kyaun halittan jiki na. Tafi ne raf raf ke faman tashi a cikin mashayan nan yayin da na ke ta faman canja salon rawa na na daban kidan na kara shiga na. Ba wanda yayi kokarin shiga sanin yana shiga zai katse min juyin da nake, haka tsari na ya ke ba wai na cika rawa da kowa bane. Carab naji an kamo hannu na ana kokarin juyawa da nayi. A harzuke na dago idanun inga wani ishashen ne ke kokarin min katsalan da a harka na. Ina hada ido dashi duk wani ruwan bala'i da na tara zan sauke mishi ya kau, sai ma replacing in shi da nayi da wani kayataccen murmushi cike da kunya na dukar da kaina kasa. "Can i dance with you jewel?" A kunne na ya rada min maganan. Ban amsa mishi hakan ya bashi daman kara jawo ni jikin shi, a bisa dole na biye mishi mu kayi rawa. Fahimtan da yayi na kasa sakin jiki in yi rawan da shi ya sa ya jawo ni mu ka bar filin tuni ko wurin ya dinke da mutane "ina kawar ki?" Ya fada yayin da idanun shi ke scanning hall in yana neman Amal. Can na hango ta gabdaya hankalin ta da natsuwar ta zuwa yanzu ya fara gushewa. Da gudu ya isa gare ta tun kafin in gama nuna mishi inda ta ke. Kaman jaririya haka ya dauke ta a hannun shi muka nufi mota. Mika min makullin yayi ya shiga baya tare da ita, ni kuma na ja motan mu ka nufi Apartment inta da ke banana highland.
Wannan daren shine mafarin komai kuma shine sanadi da ya kawo aya a walwala da farin cikin sabuwar rayuwar da na shiga. Tun a mota na lura da irin kallon da Zaid ya ke jifa na dashi kadan kadan yana dauke kan shi.
Daki na na nufa kai tsaye sanin duk ranar da Zaid ke gari ba a gane kan Amal. Duk wani hiranmu sai ya tafi za ayi shi. Na fito daga wanka kenan da towel a jikina ina goge kaina da head towel naji knocking a kofa. Kusan knocking in da bude kofan duk a tare yake don haka ban samu daman suturta jiki na. "Ouch! Sorry ashe dressing kike" ya fada yana kare min kallo. Kallo na ya ke sosai bbu alamun daukewan idon shi, wuri ya samu ya zauna akan sofa in dakin yana cigaba da karemin kallo. "Ki sa kayan ki mana" ya fada yana maida hankalin shi kan wayan da ke hannun shi yanzu. Da ke gown ne nightie in ta sa ma kawai na sa shi sannan na zare towel in.
"Bestie ta ja min kadaici bayan ta sani zuwa tun daga Abuja" idon shi a saita kan fuskana ya ke maganan. Furucin na shi ya dan so ya bani mamaki, duk sanda ya iso garin yawanci a irin halin nan ya ke samun Amal don haka shima ya ke biye mata ya sha sosai a haka su ke kare daren. Tun asali ma shi ya daura ta a hanyar duk wani abinda ta ke sha a yanzu haka.
"Eyyerh sorry" cike da duniyanci nayi magana saboda haka yayi kokarin sauya akalan zancen.
"We miss your drinks fa, Ya kamata ki koma Abuja hakanan"
"Next week zamu je da frnd ai"
"Jewel let talk about you mana. Kinsan kina da kyau sosai kuwa? Slowly am realizing how the word pulchritude describes the entire you"
A duniyance na aika mishi da wani irin kallo "Allah koh?"
"Am been serious here Babe Don't tell me ba ki taba lura da irin kallon da na ke yawan aika miki ba" tabe baki nayi ba tare da na juya na tanka shi ba.
"Ina son ki fada min alakar ku da Amal domin ban yarda cewa Ku yan uwa bane kaman yanda ta fada min. Amal ba ta min karya ban san meye sa ta min akan ki ba"
"Ba sanin alakarmu bace abu mai mahimmanci Zaid. Ina ganin sanin dalilin yin karyan shi yafi kamata ka bukata"
Kasa maganan yayi sai dai murmushin da ya ke jifa na dashi ta isa tabbatar min ya fahimci rainin wayau na ke mishi. Kaman wanda aka tsikara yayi saurin tashi daga kan sofa, ido ya kura min sosai sai kace cinye ni zai yi. Sai kuma ya hawo kan gadon da nake zaune yana mai saurin nade kafafuwan shi ya iso gab inda nake. In duniyan ci ne zuwa yanzu ba wanda ban gani da idanuna ba, Hakan ya sa ko dar ban yi ba na tsaya in ga gudun ruwan shi. Wannan karon direct tsakiyar idanuna ya ke kallo, ni inma kurawa mishi na mujiyan nayi ina son gano manufar shi sai dai duk yanda na so karantar idanuwan shi na gaza fahimtar me ke damun shi. Ganin abun ba na kare bane ya sa nayi saurin janye nawa idanuwan. Wani rauni naji ya mamaye zuciyata, Tabbas akwai wani abu da ke cikin idanun dan adam da kallon shi ke haddasa fitina. "Meyesa kika dauke idanuwan ki? They are so lovely" yana maganan ya jawo hannuna yana wasa dashi. Kasa ce mishi komai nayi, ban san dalili ba naji jiki na yayi wani sanyi.
Akwai girmamawa da mutunci sosai tsakanina da zaid Almansur da ba zai barni in aikata abinda na zuciya na ke ayyana min ba a halin yanzu. Sai dai abinda ya min ya zo min kwata kwata a baza ta. Jawo tafin hannuna yayi ya sa yatsan shi yana wasa da shi, pecking yayi a hankali yace "what a skin! So cutee" da idanunwan shi da yayi lum lum kaman mai jin bacci ya dago ya zuba kan fuska ta, alamun shi ya nuna aminci ya ke nema daga wuri na. Cikin natsuwa na girgiza mishi kai. Kaman dutse haka na ke jin zuciya ta, Sam ban ji alamun tsoro sai dai duk da hakan har raina banji zan iya barin shi aika ta abinda ya ke kokarin yi, ko don saboda Amal, i so much respect both of them. Kara jawo hannun yayi wannan karon ta gaba, kaman mai karantar wani abu a wurin... "Ya zai..." Sumbar da ya kai wa hannun ya katse min maganar da na ke shirin yi. Kissing wurin hannun ya ke sosai, kaman an zare min lakka haka na ke jina. Fara kokarin kwace hannun nayi ganin abin ba na kare bane. Sai dai duk iya karfin da nasa na kasa raba hannuna da bakin shi. Daya hannun na sa akan shi ina kokarin dago shi, sai dai hakan ma yaci tura. Kaman karamin yaro ana kokarin raba shi da abin wasa shin haka ya ke claiming hannun yana ciga da kissing. Rau rau nayi da idanuna "Ya zaid please leave me Dan Allah" ganin reaction ina da gaske na ke kin abinda ya ke aikatawa a gare nin ya sa ya dago a hankali.
"Am sorry jewel ba abinda nayi niyyan miki Allah, wannan inma i couldn't help it ne" harara na watsa mishi "i respect you please kayi kokarin girmama wannan"
"Shknn naji nagode"
"Then get out please" pointing kofan nayi da yatsa na.
"Zan fita But you need to here me out" ganin he is serious ya sa na maida hankalin nawa gare shi.
Hannun shi ya daura kan cinyen shi ya kara fuskanta na da kyau "i have a wife, sunan ta Amina. Cousin ina ce, tun muna kanana aka mana aure a lokacin muna ganiyar soyayyan mu da Amal, na sota sosai sai dai a wannan lokacin fir iyayena su kaki yarda suna nema min auren ta. Daga baya bayan mun kara girma still na nemi auren Amal, wannan lokacin kuma iyayen ta ne su kaki yarda da auren, ba yanda ba muyi ba still they objected. Su ka raba mu amma as you can see bamu rabu ba. Amma kin san abinda na ke ji yanzu?"
Kallon shi kawai na ke ban ce kala ba shi ma kuma bai jira amsan nawa ba ya cigaba "Wlh yanda na ke ji akan ki, kaf duniya ba abinda ya isa ya raba ni da ke. Ko iyaye na ko naki ba wanda ke da wannan ikon. Ban taba jin abinda zuciya na ya tafi gabadaya akan shi ba kaman ke. Tun ranar da na fara daura ido akan ki na ke jin zuciya ta na doka miki, ina miki irin soyayyan da ban taba wa wani mahaluki a duniya, babe i so much love everything about you and i can fight the world for you. No one can stop me not even Amal or Amina"
Garau rau na ke kallon shi. Ko kadan ban yi mamakin abinda zuciya na yaji min ba. A dan sanin da nawa maza wannan ba wani abun rashin kunya bane a wurin. Abu daya na sani tabbas ba za ayi wannan rashin kunyan da ni ba. Wannan karon tashi nayi da kafa na, inajin saukan idanuwan shi a kaina har na isa bakin kofa. A hankali na bude kofan gaba daya. "Please get out" na fada ina nuna wajen. Murmushi mai ciwo yayi sannan yace "kar ki damu am going out"
Amal Idriss Hayatuddeen, diyar wani mashurin mai kudi ne da ya ke zama a garin Abuja. Mahaifin ta ba dan siyasa bane sai dai duk da haka siyasan ba ta damawa sai da irin shi. Mai kudin ne na gasken gasken domin yawancin estates in da ke birin tarayya da ma lagos da sa hannun kamfanin shi a ciki. Yana da kudi na ban mamaki, wanda shi kanshi ba zai ce ga sirrin dukiyar na shi ba domin kuwa ba iya gine gine kadai ya sani ba. Duk wannan dukiyan na shi yara uku kadai Allah ya azurta shi dashi tare da matar shi daya uwar yaran.
Salim ne babban dan shi sai Amal sannan Aliy. Shi jarrabawar ta shi akan yara ta fada mishi. Salim yayi auren har da yara sai dai kuma hakan bai hana shi bin mata, yanda ran shi ya ke so ba. karatun ma da kyar aka samu ya karasa saboda shaye shaye da ya sa a gaba, an sha koran shi makarantu da dama da kyar ya hada harda masters ba tare da wani result in azo a gani ba. Baban ne ya mishi komai na aure hatta gida da abincin da zai ba iyalan shi shi ke daukan nauyi. Da gan gan ya neman mishi aiki a karamin ma'aikata da niyyan sai yayi hankali zai bashi aiki mai kyau, kiri kiri ya nuna albashin ya mishi kadan yaki aikin, natsuwan ma ya kiyi, har wayau baban nashi ke ciyar da iyalan shi.
Amal ko mace ce mai rauni ga dan banzan kyau mai jan hankali, sai dai ba ta bin mazan bar ta dai da bin club club tana rawa da shan dukkan abinda ya zo gaban ta. A kullum shaye shaye kara karar da ita ya ke. Son duniya Wa Zaid ta ke ma wa duk dai iyayen ta sun sha alwashin ba za ta taba auren nashi ba, a cewar su halayen shi ba su da kyau ko su ba su yi la'akari da irin nasu yar bane.
Shi kam Aliy kan kat dawowa kasan ne ya gagara, shi kam ba irin karatun da bai yi ba, degree kala kala a fanni daban daban. Kusan shi ya biyo baban shi ta fannin iya neman kudi, he is creative on his own yana earning kudin shi sosai, ko da yana shan abu to tabbas ba addiction. He is so responsible sai dai ko kadan bai son maganan dawowa Nigeria, he is so used to the outside countries. Ko kadan bai damu da sha'anin iyayen ba balle yaji halin da su ke. In za ayi watannin in ba su neme shi, he never care to check on them.
Abinda zai baki mamaki shine yanda gidan su ke ciki da mutane, yan mata da samari, Yaran yan'uwa da abokai kala kala ba wanda bai zama a gidan nan. Shi kanshi he can't count the no of mutanen da ya ke sponsoring a Nigeria da outside countries. Kai har friends in yaran shi na zuwa su zauna a gidan son ransu.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top