Sha bakwai

Dr Fahad ne tsaya gaban Suhaima yana faman kare ma ta kallo domin ya tabbatar idanuwan shi ba gizo su ke mishi ba. Wannan ba Suhaiman da ya sani bace, wannan tayi duhu sosai, ta lalace sabili da wani irin mugun rama da tayi, kana ganin ta kaga wacce ke cikin garari da masifan rayuwa. Gabadaya ta canja mai a idanu, wani irin hawaye masu zafi yaji sun cika mai idanu ayayin da zuciyan shi ke faman wani irin suya na masifa. "Ya Allah" ya furta a hankali, shi kam ko lokacin da ta ke asibiti bai ga tayi irin wannan lalace wan ba.

"Suhaima, shin miye labarin Rayuwar ki?" Ya furta a hankali, idanuwan shi a kan nata. Sauke na ta idanun tayi kasa yayin da sautin bugawan zuciyan ta ke kara yawa. Da wani irin rikitaciciyar murya tace "Dr lbr ne mai matukar tsawo wanda ya canci a rubuta shi a cikin littatafai domin koyon darasi a cikin shi, zan baku labarin Rayuwata amma sai a hankali" kanta na a kasan har ta gama gabadaya maganan. Tun da ta shigo bakin wurin, wannan ne karo na farko da Dr Fahad ya sani faman ziyartar ta, ba Wai don bai so hakan ba sai dan daman ba ta samu mishi ba. Ko bai jin komai akan Suhaima, yana ma ta kallon kanwa a gare shi hakan ya sa duk wani matsala da damuwa shi ya ke jin shi kaman na shi. "In sha Allahu Za muyi kokarin fidda ki daga wannan wurin, ko baki fada ba ni kam jikina na bani you are innocent" ba tace komai ba saboda ba ta ma San abun da ya dace tace mishin ba, Dr Fahad na da wani mahimmanci na daban a kadadarorin da ke afkuwa a rayuwan ta.

"Nagode" ta fada a hankali, ita kanta ta san rashin abun cewa ne ya sa ta fadin haka saboda Dr Fahad yafi karfin godiyan fatan baki a wurin ta. Girgiza ma ta kai yayi yace "ki daina min irin haka Suhaima ban so" saurin gyade kai tayi, alaman gamsuwa da kalaman na shi.

"Ina Amarya?" Ta tmby cikin siririn muryar ta. Shi mamaki ma ta bashi, a halin nan da ta ke ciki har ta iya tmbyn wani? Share zance yayi da cewa "ki cigaba da addu'a kaman yanda kike yi sannan ki fawallah wa Allah sauran, mu ma muna yi kuma in sha Allahu za a dace" da kai ta amsa shi, dai dai lokacin dan sandan da ke tsaron wurin ya zo sanar mu su lokacin da aka diba musu ya kare. Murmushin yaki ta aika ma Dr Fahad, ba tare da cewa komai ba ta juya domin komawa inda ya zamar ma ta matsugunni a yanzu. Idanuwan shi na kan ta har ta bace, yana mai cikin dimbin tausayi da son ceton ta ya fito daga station in. Already, sun hadu da Barr Mustapha tun shigowan shi Abujan. Gidan Ummin shi ya nufa domin kai gaisuwa a gare ta zuciyan shi fal tsoron wani irin tarba zai samu, tunda su kayi aure da Rufaida ya ke fuskantan matsaloli daga wurin ta. Har yau kafan ta bai taba taka gidan shi ba, kulan shin da ta kan danyi ma saboda sa bakin Daddyn shi ne. Ranar da ya kawo Rufaida wurin ta kuwa sai da yayi kwallan bakin ciki, ko gaisuwan ta a fizge ta amsa daganan ba su kara ganin ta ba sai kanen shi su Zahra da su kayi ta hidima da Rufaidan. Da yayi tunanin yanda Dada ta ke mishi sai da yaji kaman ya nutse don kunya, amma da ke ita Rufaidan ta sa dawan garin sai Ba ta wani sa abun a ka ba.

...

Eden island,

Seychelles.

Zaune ta ke daga gefe guda a open restaurant in da ke kusa da pool in hotel in. Wannan karon ne ziyarar ta na biyu zuwa kasan da ta kira da kasar baiwa, sai dai ta kasa daina kallo da jinjina ni'iman ubangiji da yayi shi cikin tarin ni'imomi. Mafi yawan bakin da ke wurin wandan da su kazo honeymoon ko kuma dai masoyan da su kazo shakatawa. Yeah, the weather is totally good for them, kaman dai abinda ake cema weather for two. Haka kurum ta ke jin wani iri da ya kasance ita daya ne a irin wannan wuri ba tare da kowa nata ba. Wani irin kadaici ta ke jin ya mamaye yayin da ta ke kokarin danne shi da cocktail in da ke gaban ta, a yanda ta ke jin ta she seriously need someone to share those nice moment with her. Har ga Allah, ba za ta tuna when last taji abinda ta ke ji ba, ta dade da cire namiji daga cikin rayuwan ta, ta kulle su daga babin tarihin rayuwar ta gabadaya. Namiji y riga da ya mata illan da ba zata taba iya warke wa ba, shiyasa ta yakice su daga alamuran ta.

Tana cikin tunanin na ta ne ta hango shi yana taho, cikin tafiyan shi mai burgewa. Za ta iya cewa ita kadai ce yar Nigeria ba haushiya a wurin amma kuma duk da hakan tana da tabbacin ba ita kadai bace idanuwan ta ke kanshi. Yau ma sanye ya ke cikin kananan kaya, gabadaya navy blue sai dai rigan yan da touch of white, hoodie ne wanda ta alakan ta hakan da sanyin da ke garin,  sai facing cap in da ke kanshi da ke da touch of red. Kayan sun matukar amsan shi sai dai tunani ta ke kaman akwai abunda is omitted a shigan nashi.

"Hello dear, kina ta jira na ko" yana jawo kujeran da ke facing inta yayi maganan, ba tace komai ba sai murmushin da ta dan yi. Sai da y zauna daf da ita sannan ta gane glasses da ba bata gani bane ya sata tunanin he omit something. Fadada murmushin nashi yayi yace "Ya sabon yanayi kuma? Do you cope well?"

"I love the weather" ta amsa shi tana kara sipping in coffee in da ke gaban ta.

"Nice to hear, shi ya sa na ganki da katon jacket kenan da hulan sanyi" dariyan tsokanan tayi tace "It so nice duk da haka kaga da zafi ne mutum rasa in da zai sa kan shi zai yi"

"Kuma da gsky, as a Nigerians we have to appreciate this daman ai, so let talk about the business, are you in" dan shiru tayi kaman tana tunani, sai can tace mishi "wani irin business ne"

Dan dariya yayi hade da girgiza "mata mata dai, har business inma sai an ja wa aji? Don't tell me you are getting customers a haka" yana maganan hannun shi na kan gemun shi yana wasa dashi, idanuwan shi kar akan ta ya ke maganan. Hakan da yayi ba karamin kara tafiya yayi da ita ba tace "no ai ba maganan jan aji a business, i just want to know what am getting myself into"

"Are you not an event planner? Ai ba zan nemi wani abu out of your field ba. Do you have event center back in Nigeria" gyade kanta tayi tana realizing yanda ya ke maganan shi natsuwa da ma'ana. "Vows a Abuja" ta fada tana ajiye mug in coffee inta da ya kare.

"You own Vows?" Mamaki ne sosai a kwance a fuskan shi, itan ma mamki ne a na tan saboda a zamanin na social media ba tayi tsamman akwai wani matashi da ke cikin Abuja da bai santa ba.

"Dole kika ja min aji, let do this please" ya fada yana dan marairaice fuska "okay" ta fada simply tana jiran me zai ce.

"My Friends are getting married here. Dukkan su biyu University mu kayi tare a Egypt, am more like the middle kingane ta dalili na su ka hadu. Dukkan su Nigerian ne sai dai ita a kasan Oman ta taso tun secondary school days inta. Har gwara ita ma saboda shi a Saudia aka haife shi bai ma taba zuwa Nigeria ba. This is her Dream place, so they decide ana daura aure a oman ranar za su taho nan ayi duk wani events in bikin su. The issue is they want a wedding of their tradition sai dai they have no any idea da zai sa yayi working, shine fa su ka taso ni a gaba na taho a cewarsu in bincika tunda am living a country in sai nazo a fara shirye shirye" murmushi sosai Umaimah tayi, kana kallon ta kasan tana cikin farin ciki. Ba banza ba jikin ta ya dinga bata zata yi missing opportunity in ta share shi, this is a good idea, shi kan shi sai da ya gane ta ji dadin bayanin da ya mata.

"What is the couple name?" Ta bukata

"Rawan nd Adam"

"You are in the right place" ta fada, already har ta bude system inta ta fara danne danne, shi dai bin ta da kallo kawai ya ke, he likes her fierceness, no wonder events in Vows is always unique. He sees determination in her.

"Tana da outfit ne?" Ta fada still tana ta faman danne danne.

"No, we are planning ayi ordering ready to wear"

Girgiza kai tayi saurin yi tace "we are ordering Bespoke, yaushe ne wedding in?"

"In Three weeks time" shi dai amsa ta kawai yake yi yana kallon yanda ta juye lokaci daya ta koma kan aiki.

"We have enough time, ina da Fashion designer in da za ta iya min a takaitaccen lokacin, i want to talk with the bride saboda in san test inta exactly, then she need to come with a makeup nd henna artist, kayan za a mana delivering ta jirgi. Sai caterers, i will guide them by getting the necessary ingredient so your only job now is to find an interior decorator da kuma caterers in but i want to try talking to Nigerians da su ka zo nan for tourism, experience is the best"

Sosai ta burge shi ganin yanda nan da nan ta hau aiki, kuma da alaman kware da mai da hankali a dukkan abinda ta ke yi "we didn't even talk about the pay"

"This is a great opportunity for my career zamu yi maganan wannan daga baya"

Folding lips in shi yayi yana kare mata kallo "Rawan will be crazy in ta samu labarin ki, she madly wanted her crazy ideas to work sosai don kowa kallon craziness ya ka mata"

Dan ware idanuwan ta tayi tace "ni kuma i like her because she know what she want"

Dan dariya yayi yace " sai dai she can't talk in hausa and her English is not clear sosai, Arabic accent inta keeps affecting"

"Ba matsala" ta amsa.

"So let go for the shopping?" Da ido ya ke jiran amsan ta, lumshe idanuwan na ta tayi cike da tsantsan farin ciki ta mike tsaye "let go then"

...

"Tun daga ranar ba mu kara haduwa da su ba Faroukh ba sai Abuja, hatta Zayd ranar ya koma, bai wani kira ni ba ni ma kuma ban bi ta kanshi ba, don har na fara tunanin ko ya hakura da bukatan shi a kaina ne" Suhaima ce tsaye a gefen barrister tana cigaba da bashi lbrn da ta fara, yau duk yanda ya so ta zauna hakan ya faskara, sam ta ki zama. Hannun ta tasa duka biyun ta riko karfen da ke gaban shi

No 5 Maitama, Abuja.

Brown polkadot armless straight gown ne sanye a jikina, light brown Bf jacket na daura a saman gown in sai veil da na daura a kaina. Ko kadan ban damu da rashin yafa babban gyale da Zai rufe min jikina ba. A gate in vows nayi horn, nan da nan aka bude min gate in na kutsa. Bayan nayi parking a lodge, direct na nufi side in da office building in su ke.

Cikin natsuwa na ke tafiya ta, da ke tuntuni daman ni ba ma'abociyar heels bace, kullum ka kafata sanye na ke da flat shoes. Gaf nake da karasawa wurin elevator na hango shi tafe yana karasawo inda nake. Da sauri na budi ban dakin da ke wurin domin rakubewa, Sam Sam na manta cewa ban dakin maza ne a wurin.

Ajiyar zuciya na saki ina mai rokon Allah ya sa ya wuce da sauri "Baiwar Allah lfy?" Muryan Namiji da naji ya sani saurin juyawa cike da tsoro. Daram! Na ji a gabana sanadiyyan Wanda na gani tsaye a jikin zinc yana wanke hannu. Tabbas, wannan shine anyi gudun gara an fada gidan zago. Faroukh Usman ne employer in Zaid Al-mansur. Abinda zai baku dariyan shine El-yas na hango na ke ta ma wannan gudun.

"Sistern oga ko bake bace?"

Nodding kaina yi da sauri "Sorry Faroukh, am pressed ne gabadaya na manta ban dakin maza ne nan" ba tare da wani reaction ba yace "Eyyah, You can use the restroom tunda you are pressed bara in fita." Bai kara cewa komai ba ya nufo kofa, matsa mishi nayi ya fita. Gabadaya jiki na rawa ya ke tsabagen tsoro, da kyar na iya kara yan mintuna kafin na fita.

A dai dai lokacin su kuma su ke wurin exit in building in. Elevator in na danna domin karasawa office in da ya kawo ni wurin. Umaimah Amin, Director's Office. Shine a rubuce a jikin office in da na shiga.

"Hello cutee" secretary in ta fada tana gani.

"Mercy merci, the beautiful lady" dariya tayi tace "kwana biyu, my madam just call ko kin iso" cikin hausan ta da bata gama gwanancewa ba tayi maganan.

"Eyyerh, na dan tsaya kasa ne" na fada ina karasa bude office in director in.

Zaune ta ke akan office chair in tana ta fama rubutu. Sallama nayi ba tare da ta dago ba ta amsa. Wurin couch in da ke office in na nufa na zauna. Ba ta taso ba sai da ta kira mercy ta sanar mata ba ta son ganin kowa for 30 to 45 minutes.

Plain black bubu gown ne ke jikin ta, kwata kwata ba a mishi kwalliya ba, Kullum in ka ganta irin shigan ta kenan, ko atamfa ne kuwa in ba ta mishi bubu to play gown ne. Cikin kasaitar ta taso zuwa inda nake da kwantaciyyar murmushi akan fuskan ta, tafiyan ta kadai abun kallo ne. Kafin akai zuwa kyau da kwarjinin ta kuma. Irin dirarrin matan nan ne da komai yaji, jikin ta ya matukar amsan yanayin ta. Irin matan nan ne da ba kasafai ake taran su a musu magana ba. Kullum ka ganta she is always smiling. Umaimah Amin kenan, mace mai kamar maza ko ma ince wacce ta taka mazan kwazo da kokarin neman na kai. Babban Event planner ce da tayi kaurin suna sosai, The Vows, shine sunan event center inta. Event halls uku manya sosai da maidaidai ta guda biyu ke cikin vows. Bayan su akwai fili sosai, wanda ake organing event a open space a wurin har da ma wurin da ake na tent. Ba wedding event kadai ta tsaya ba, duk wani event in da ya taso ana booking a wurin ta. Yana yanda ta ke fidda decoration inta is always unique, she can be traditional ko kuma ta juya modern. Duk irin yanda kake son tsarin ceremony, in dai kama ta bayani to ko zaka sha mamaki. Tana aiki da different photographers, Videographers, MC, DJ, interior decorators and architectures. Banagaren abin ci da sha ma tana aiki da caterers da ma bakers kala kala. Akwai wanda suna karkashin ta ne tayi employing insu akwai kuma wanda suna zaman kan su ne, appointment ta ke signing. Aikin ta dai ta tabbatar event in ka is well organized. Bayan haka kuma influencer a social media, haka ya matukar kara mata suna kuma ya kara ma business inta farin jini. Ga ta akwai taimako, tana sponsoring yan uwanta dayawa.

Gefen kujeran da nake ta zauna, har yanzu dai da shu'umin murmushin a fuskan ta take kallo na. Bude hannayen ta tayi inviting me for friendly hug. "Baby na nayi kewan ki dayawa"

"Anty na kenan, nima nayi kewan naki ai"

"Allah baby?" Ta fada hade da rungumo ni for seconds sannan tayi pecking ina akan forehead.

"Na fa ga El-yas a kasa" ba a wurin Zaid na fara Sanin El-yas ba, shine dai bai sanni ba. Nan na bata labarin abinda ya afku a kasa. Kallo na tayi sannan ta kwashe da dariya "wannan ai ke zaki tona asirin kanki da kanki, Ya San me ya kawo ki nan? Ai da sai ki Fuske"

"Kin sanni akwai rudewa ne"

"El-yas ba mu da matsala dashi na sani amma sai dai Faroukh in, yana da surutu ne"

"Kai anya?" Na fada hade da girgiza kai.

"Faroukh Usman, zan yi bincike akan shi. Kinsan karamin obstacle sai ya zamo maka babba kafin ka ankare"

"Faree ta kira ni" ta cigaba "So ya ake ciki?" Lbrn gabadaya abinda ya faru tsakanina da Zaid na bata.

"Yanzu kun bar Lagos in gabadaya kenan?"

"Offer week POP in Amal, za ta koma Sunday ita kadai daga baya zanje sai mu dawo tare gabadaya"

Jinjina kai tayi tace "Gsky babe in nan tana ji da ke dayawa baby, anya kuwa? Can i trust her?"

"I promise babu komai Anty na"

Mun dade muna magana, wanda duk tana fada min yanda zan bi da lamarin Zaid Al-mansur ne. "Baby ki fa tabbatar tarkon ki ya danu kafin ta dawo Abuja"

Gyara zama nayi na sa kaina akan cinyan ta "ba ki da matsala dani Allah, komai zan iya miki Anty na" hannun ta dora kan kai na, sannan ta zare veil in, kanana kalaba ke kaina ta tusa yatsunta tsakanin su tana wasa da su. "To yaushe zaki zo wuse, dagaske nayi kewan ki fa"

"Zan zo ai amma sai Amal ta koma Lagos"


Al-mansur

Drinks shop.

Tun bayan gamuwar mu da Zaid a Lagos, ranar da Amal ta ke buge ba mu kara wani haduwan ba. Yau zaune na ke a specific office ina da ke cikin Drink shop in, kwanan mu uku kenan da relocating wurin gabadaya. Ban da wani aiki sai supervising in workers in domin tabbatar da komai na tfy dai dai. Sai kuma Satandard recipes da ne ke forming, inyi guiding in su. Sai na kasance kullum cikin browsing to gather more knowledge akan drinks in.

Knocking naji, kafin in amsa an bude kofan. Ban dago ba amma nasan Zaid ne, tsarin shi ne wannan. Balle ma ga sanyayyen kamshin turaren shi na kullum da kullum da ke tashi.

"Baiwar Allah barka da war haka" daya daga cikin kujeran da ke gaba na ya jawo ya zauna.

"Barkan mu dai Yayana" harara ya aika min mai tattare dace wa zaki sani.

"Babe ya maganan mu" tsare ni yayi da idanu sosai yake kare min kallo.

“Ai na dauka mun bar wannan zancen kuma yayana, ba zan iya ma Amal haka ba” murmushin da ke kan fuskan shi ya bayyana cewa yasan za ayi hakan.

"Zan so ki bar batun Amal domin mu fara fuskantan abinda ke gaban mu. Suhaimaa" jin yanda ya kira sunan ya sani dagowa muka hada ido, kaman kullum yau ma nice na yi kokarin janye nawa idon. Ban ni da rashin kunya na amma ina tsoron sharri kallon cikin kwayan idon mutum. idanuwa na dauke da wasu sirri na daban,  yana fallasa mutum sau da dama ko da so boye abun da ke zuci.

"Kin ganni nan wlh ban iya sa abu a rai, in har na sa kuwa ina bin duk wani hanya da ya zo min domin samun wannan abun. Matsayina na ke so in sani a wurinki kawai domin shine muradi na a yanzu"

"Dan uwa na" nayi saurin fada, ina kokarin kara karantar yanayin shi. Ba kaman dazu ba yanzu murmushin ma kin fitowa tayi, “i need more than that please Suhaima" bance mai komai ya mike a hankali har ya karaso inda nake, gab dani sosai ya tsaya har ina iya jiyo sautin fitan numfashin. Dan durkuso wa yayi ya sa kan shi kan table in da ke wurin, hannuna da ke da kan table ya kamo da hannun shi ya rike tam yana murza tafin hannun namu a tare "ina so kisan ba wasa na ke miki ba jewel, i so much love you" a saitin kunne na ya ke magana yana kara manne jikin shi kusa dani. Wutan kai na gabadaya dauke wa yayi a lokacin, ina so in ture shi sai dai kuma nasan this is an opportunity. "Stop this please nifa kawar Amal ce" a hankali nayi maganan sounding so vulnerable.

"Kar ki damu nasan da hakan, for now ina son sanin matsayina a wurin ki kinji" a hankali yake magana yana kallon fuskana, idon shi duk ya marairaice, na kasa tantance gskyn shi a wannan lokacin. Basar nayi saboda ba wannan bane matsala a yanzu nace "recently, banjin wani abu da ban san shi ba akan ka" kara marairaice wa yayi jin amsan da na bashi yace "to ai nasani mana jewel, ni chance kawai na ke so ki bani mana"

Girgiza kai nayi nace mishi "but we don't have to do this"

"We have to when i can't control it" sai a lokacin ya raba hannu na da nashi, da hannun yasa ya dan shafo fuskana yace "my beautiful babe, we shall talk later"












Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top