Hamsin
Ba ta tashi hakan yasa tayi juyawan ta. Ta riga ta gama gane tsanar ta ne ke gudana a cikin zuciyan shi. Hakan yasa ya watsar da ita, ko maganar arziki bai bari ya shiga tsakanin su ba. Bata ga laifin shi ba, don ko ita ada ta kanji ta tsani kanta. Alhmdlh, tunda ta Mika lamarin ta ga Ubangiji take jin komai na dawo mata dai dai ga Kuma wani irin natsuwa da take samu.
"Ina ke kike yawan maganan Uzuri, shin meyesa itan ba zaki mata ba? Kinsan irin halin da ta shiga a sanadiyyan rashin ki? Rashin hankalin naki har ya Kai ki duba tsaban idon mahaifiyar ki, kina fada mata mugayen kalamai? Ba uwan da ta cancanci hakan, ko da kuwa ba ta hanya aure ta same ki ba, ba dai abinda ya Kai wannan ciwo don haka kisan mekike yi" ba ta amsa shin ba, Amma Kuma kalaman shi ya Kai inda ya Kai a kwakwalwar ta. Tabbas ba ta kyau taba, Amma Kuma ita kanta ba ta San me take fadi ba. Hakan Kuma Yana da alaka da alakanta dukkan wani gurbacewan ta da tayi da rashin mahaifiyar ta a tare da ita tun ba yau ba.
Kalan gaisuwan da Sandan kewa Ummi yasa ta gane ba karamin mutunci ke tsakanin su ba da girmama wa. Bayan nan, ko kallon ta bai yi ba ya fita daga dakin. Hakan yasa ta kara shan jinin jikinta.
"Kiyi Hakuri bansan abinda nake fada ba" gyada Kai Ummin tayi "Na sani Suhaima nasan da ciwo Amma bar na Baki labarin abinda ya hada ni da mahaifin ki. Mahaifin ki mutum ne mai tsatsauran ra'ayi kema kinsan da hakan. Sai dai Kuma tun farko ya San ni ban dau hakan ba, shiyasa duk wani abu nashi Zaki ga ba kasafai yake min ba. Abinda Kuma baki sani ba shine, kafin na hadu dashi da Baffan ku na fara haduwa, shiya fara nema na amma Kuma sabo da irin halayen shi na neman mata shiyasa alakan tamu ba tayi wani nisa ba. Baban su Aseem kuwa shine saurayin da na so har sauran kiris muyi aure rabon ku ya hada ni da Abban ku. Bautan kasa ya kawo shi daga Kano, Kuma yayan Hajja ne, su biyu ne kadai wurin iyayen su. Sai Baban Abdallah daya taso a gidan su. Lokaci yayan babana da nake wurin shi a Borno shi yaki aura min shi, a cewan shi gwara Wanda aka sani domin dai kowa yasan baban mahaifinki a jahan borno da yobe. Nima Sai na hakura na aure shin duk da kuwa nasan kanin baffan ne, na dauka ba wata matsala tunda bashi in bane. Muna cikin kwanciyar hankali, ko a lokacin da na hadu da Hajja bansan cewa yayar baban su Aseem bace. Sai watarana da yazo ya iske ni, na shiga wurinta. Ba wani abunda ya hada ni dashi, har lokacin barin ta gidan da zama yaki dadi, ita kam kishiya tasa ta a gaba. Dole ta hakura da auren, har bayan ta tafi we keep in touch. Har lokacin da na haife ki, su kazo suna, yayan nata ya kawo ta. Lokacin already an hada ta aure da baban Abdallah, hukuncin mahaifin su ne. Bansan ina suka hadu da Baffah ba, Amma ya samu Abban ku ya sanar dashi wai saurayina yazo sunar yar shi, don haka ya bincike ni. A tare suka nemi ni lokacin, so sun San juna. A lokacin Abban ki bai dau abun wani serious ba, Amma a hankali ya dinga zuwa yana fada mishi abubuwa. Dalili kuwa har lokacin yana da ra'ayin ya mallake ni, cikin matan uwargidan tasan ya neme ni, hakan yasa kwata kwata bata kauna ta. Daga baya har waya ya fara min, Sai inki dauka. Tsabagen yawan wayan har Abban ki Sai daya San ana yawan Kira na, yace na bashi ya ma mutumin magana yaki saboda ban son ya gane Dan uwan shi ne. Abinda ya fara sa zargi tsakanin mu kenan. Cikin wannan sarkakiyan na haifi Baffah, tun lokacin ya fara tunanin baffan ba dan shi bane saboda irin text in da ake turo mai a kaina. An ganni a can, an ganni a nan, hakan yasa zargin ya kara yawo har yazo yana bibiyata. Kaman shi da Baffah, yasa shin yardan dan shine. Zuwa lokacin na riga da nasan aure na ya fara samun gargada. Wani Ikon Allah, ban dade da fara koyarwa ba, aka kawo Baban su Aseem University in da nake, ai Kuma lokacin abun ya tsanan ta. Domin dai rahota ake Kai mishi akan ana ganin mu tare dashi, Wlh Suhaima ko gaishe shi banyi saboda gudun matsala. Ya nemi in daina zuwa ko ina, ni Kuma naki. Baban su Aseem kuwa Oga nane, hakan yasa duk yanda naso guje mishi Sai wani abu ya hada mu. Bayan Baffah, na kara Samun wani cikin Amma haka mahaifin ki ya rantse ba nashi bane, muka hau muka fado Amma Ina yaki zancen, daga karshe dai tilasta ni yayi Sai da aka cire cikin nan. Nayi kukan bakin ciki, nayi takaici amma na zabi kare martabar aure na. To Sai dai shi aure ba ayin shi da zargi. Akwai wani zuwana maiduguri, Baffah na kai asibiti Abban ki ya sani zama gidan Baffa duk da ban son haka. Wlh cikin dare ba kunya mutumin nan yaso ya far min, ikon Allah ne ya cece ni a wannan daren. Amma ya min alkawarin ganin bakin ciki mara misaltuwa. Yanda ya fara kuwa shine da amsan Baffah, duk da nasan daga shi har matan shi ba Wanda zai kula min da da, nayi kuka na, nayi bakin ciki Amma hakanan aka Kai shi. Sai Kuma na samu cikin Mai Jiddah, lokacin Kuma bala'i ya taso gadan gadan, domin dai Abban ki cewa yayi Sai dai na kara cire cikin, ni Kuma nace ba Wanda ya isa ya sani kaf duniya. Muka dinga hawa muna sauka, har na haifo ta. Yaki yarda yar tashi ce, musamman ganin ba kamannin. Lokacin ya fara hada ni da yan uwana, har nasiha suke zuwa yi min in rasa abun ce musu. Daga karshe ce min sukayi in na kashe aure na kar na sake na waiwaye su, domin dai labari ya zaga cikin shege nayi da aure na, na haihu. Ban iya zama ana shegan ta min ya, don haka na nemi mahaifin ki da ya gyara abinda ya hada ko Kuma in Kama gabana. Yaki, Sai ma ya kafa min bala'i, wai zai iya hakura ya zauna dani Amma ba tare da Maijiddah ba, in San inda zan kaita, in ko nace zan zauna da ita a bakin aure na. Na gaji da auren zargi, don haka na sama ma kaina mafita domin auren dai ba inda zai Kai ki na zauna tunda ba yarda a tsakanin mu. Labari ya Kai gun yan uwana mun rabu dashi, kowa yace in Kama gabana. Ko na gaya ma Goggo da Goggon Adama illa iyaka za suce nayi Hakuri na zauna ne, ni Kuma ba Zan iya ba. Don haka na hau shirin tafiya, a lokacin Kuma mahaifinki ya sanar min in har na tafi kar na sake na kara tako mai gida, sannan Kar na sake na daukan mishi ya'ya' bai amince ba. Ko ya fadi hakan ne ya na tunanin zan hakura na zauna, bai San na riga da nayi nisa ba. Wannan shine sanadiyyan rabuwan mu, Kuma direct Kano na tafi na kai ma Hajja kuka na. A wurin ta na gama idda na, har na cigaba da zuwa makaranta baban su Aseem bai ma sani. Sai da nayi shekara biyu ma a wurin ta sannan ya San Ina nan. Auren mu Kuma Sai bayan an mishi transfer Egypt, shi ma ikon Allah ne kawai saboda na hakikance na gama aure a rayuwa ta. Ban Kara waiwayan Damaturu ba, Amma kullum kina raina, dake bake kwana nake tashi. Kullum addu'a ta Allah ya raya min ke. Na barwa Allah ikon shi, nasan Kuma duk abinda ya same ki kaddarar kice Suhaima. Ko Ina tare dake kuwa zai faru, a sannan bakin cikin ma zai fi yawa. Sanda ke kawo min feedback akan ki, har zuwa lokacin da yayi loosing contact dake. Lokacin daga ni har shi mun ahiga tashin hankali, saboda yana da niyyan tun kan ki shiga University ya aure ki ya taho dake nan. Amma yasan baban ki ba zai amince ba, ba mu so ya fahimci wani abu bayan nan Kuma ga Goggo. Ya dade yana neman labarin ki, tukunna ya samu a lagos bayan ansan case akan company in da kike aiki. Tanan ya samo ki, don haka ina fatan Zaki yafe min duk wani abinda kike ganin na Miki" da kuka idanun ta, ta rungume mahaifiyar tata "Ina son ki a kullum Ummi na" rungume ta tayi ita ma, cike da farin cikin dake zagaye su ta ko ina.
Washegarin ranar, Jiddah tazo ta tmbyn ta. Wai brother yace ta bashi Email address inta. Material ya turo mata na license exams da zata yi, da foams ta cika. Har yanzu dai tana mamakin wai ya so auren ta ada, to meye sa bai taba mata magana ba? Ko dai kawai don Ummin yake yi ne daman? Yanzu ta gane duk sakon da yake cewa an bashi ya bata, daga Ummin suke fitowa.
Ga mamakin ta kaman da haka ya koma mata tambayoyi akan karatun ta. Ba ta San Ina ya amshi numban ta ba, Sai dai Kawai taga mssg Yana tmbyn ta, tana dai karatu ko? Lokacin ya riga ya koma Abuja. So ta chat yake bata feedback kan duk wani abu dake tafiya akan Exams in nasu. Ta dade ba tayi karatu ba, hakan yasa take dan Shan wuyan abun. Daga karshe dole sai ta ajiye catering school in da take zuwa, tayi focusing gu daya. Islamiyyan dai har yanzu tana da zuwa. Ko fuskan tan tana Shan wuyan yayi, kawai sai gani tayi ya turo mata application in online course, Wanda duk yayi covering akan Exams in nata ne. Cikin ikon Allah Sai abun ya fara mata sauki, domin dai sosai ake warware musu komai. A haka ta cigaba da fafatawa har Exams in ya gabato. Ana three days to exam, ta shirya tafiya Abuja. Ummi dai ba wani son tafiyan nata take ba, saboda tana jin kar ta ki dawowa Kuma.
"Kin kwantar da hankalin ki Ummina, in dai nine Sai kin kore ni" hararan ta Ummin tayi "Kaji min yarinya, auren fa?" Dam! Gaban ta ya fadi. Da kyar ta iya basarwa suka cigaba da magana. Sai dai har ga Allah zancen nan Yana damun ta, shin akwai ma Wanda zai iya auren ta kuwa? Ta riga da ta sama ranta, kilan hakan na daga cikin kaddaran tane kawai. Har a jirgi tunanin da ta dinga yi kenan, Sai da kyar ta samu ta kauda shi tukuuna ta iya focusing kan abinda ke gaban ta.
Tana fitowa daga airport in, ta hango shi a haraban wurin yana tsaye kawai yana wasa da key. Kawai sai taji ya burge ta, musamman irin yanda yayi tsayuwan nashi hankali kwance idanuwan shi Kuma na kallon camera in dake hannun shi. Zuwa yanzu tasan his love for photography, saboda duk inda zaka ganshi Yana makale da haddadun camera. To In Sha Allah, Sai ya samu wani abu crearive ya dauka tukunna hankalin shi ke samun kwanciya. Lura da yayi ana kallon shi yasa ya dago idanuwan shi, Sai da jikin ta ya bata wani yarr sanadiyyan haduwan kwayoyin idanun nasu. A kunyace ta saukar da nata, kafin ta ankara kawai sai flash in camera ta gani. Da sauri ta dago, murmushi ya sakan mata "let go" yace yana amsan trolley in dake hannun ta. Ba wani magana tsakanin su har suka Kai mota, Sai da ya fara driving tukunna tace "Ya Sanda ina wuni" da sauri ya taka birki ya fasa tafiyan.
"Kar in Kara ji" ya fada da kakkauran murya, Sai dai taso gane wasa yake ko Kuma da gaske Amma ba alamun hakan.
"Baki San sunana bane? Don't ever call me that again, am Umar Faroukh of you have to know again" dariya ya so bata, Sai dai yanayin saitin muryan shi ya tabbatar mata har ga Allah da gaske yake.
"Am sorry" in short ta amsa. Ai kuwa a sittin ya ja motan. Straight bai tsaya ko ina ba ya dau hanyan barin garin. Ta so yin shiru Amma Ina yunwa da ke nukurkusar ta yafi karfin da haka.
"Brother Ina jin yunwa please" kaman ba zai tanka ba Sai Kuma ya Kai u-turn ya juya. A wani restaurant ya tsaya, da saurin ta kuwa ta fito tabi bayan shi. "Take away Zaki yi mu tafi fa, kinsan ai hanyan Abuja-kaduna in yamma yayi bin shi is risk" dole tayi hakan duk da ba ta kauna cin abinci a mota yana tafiya Kuma wai gaban shi. Tana cikin cin abinci taji an rufe mata idanu, it appears so odd to her, like yanzu wake wannan? Kaman dai yanda ake yi sai taga an miko mata hannu, thank God na mace ne. And she can't forget it da sauri ta juya tana fadin "Anty Nainerh" side hugging juna suka yi, tana daga idanun ta taga Zayd Al-mansur a gefe ya zuba mata idanu. Rasa abun yi tayi for some second suna exchanging looks. Ta ma manta Umar na kusa da ita. "Suhaima" Zayd in ya fada a hankali still idanun shi akan ta. Cike da kunci tace " I need to know about Amal please" abinda ke ranta kenan, abun da ya kasa ko da almaan bata a kwakwalwar ta.
"We need to talk then"
"Muje ko?" Umar in ya fada bayan an Mika musu order insu. Sai lokacin suka gane tare suke, da sauri Zayd in ya Mika ma Umar hannu su ka gaisa. Hakanan dai suka yi sallama bayan Zayd in ya mata alkawarin zai neme ta.
"Ke kinga tsohon saurayin ki ko?" Abinda yace mata kenan, Sai dai shi kanshi y rasa dalilin fadan haka.
"You should be careful, ban son ki Kara shiga matsala Kuma" dole ta saki murmushi a hankali tace "Thanks" yaji ko bai ji ba, bai dai amsa ba.
A hankali ta fara cin abincin ta, har ta gama ba abinda yace mata. Sai da ya bari ta Sha ruwa tukunna yace "When are you planning on getting married?" Dole gaban nata ya kara faduwa. Ganin Yana jiran jin amsan ta yasa tace "Lokacin da Allah yayi" juyowa yayi ya harare ta "You are not serious, ni da nake tunanin kafin ki fara housemanship ma"
Rasa kan zancen nashi tayi amma Kuma Sai tace "Ban ma fa da tsayaye ni ko saurayi yanzu banda shi" da mamaki kan fuskan shi ya juyo yana kallon ta, kika yi saurayi ai sana ji dalili. Batun tsayaye Kuma, who have i been waiting for?" Sai da notin jikin ta ya kunce baki daya jin kalaman nashi. Bai tsaya la'akari da yanayin da ta shiga ba ya cigaba da cewa "Daman na dade da sanin am alone on this. Kin sani sarai fushi nake dake Amma ko Hakuri kika gaza bani" ta gane in da zancen nashi ya dosa, in akwai abinda ta tsana taso dashi don haka tace "Am sorry to, nasani ban kyauta ba" da Kai ya amsa mata Sai Kuma yace "am not getting any younger, abokaina ba Wanda bai yi aure ba, sun min tsiya har sun gaji, tun abun bai damuna har ya fara. But now tunda you are here, ba Zaki koma Damaturu ba Sai naje wurin Abbah, nd rana kawai za a sa"
Mamaki biyu ya hade mata "Abban zai amince ne?"
"Ai ya dade da bani ke, kuma har gobe alkawarin mu na nan dashi. Saura ke"
"You never told me anything about it" dariya yayi "In Zaki ma kanki adalci Sai na ce wani abu? Shin action ina basu nuna Miki komai ba? Ba abinda bki sani ba so I don't have any more times to waste" shiru tayi, tana hesitating abinda za ta fada mishi. Can dai ta fuske "ba abinda ba ka sani a kaina ba Ya Umar, why do you still want to marry me?" Murmushi yayi mai ciwo "Waya gaya miki soyayya tana ba mutum zabi? Halan baki taba shiga cikin ta ba? Akwai ta da daci, irin dacin da ba ka iya tauna haka Kuma in taso Zaki you can't resist it. Sannan ban so ki Kara irin tunanin nan, ban lamunce Miki ba. Ko ba don ke ba, Ummi za ta iya sani yin komai in mata. In Baki manta ba, na taba Baki labarin abinda na aika ta a garin Kano, na yima wata yarinya fyade. A wannan lokacin hatta mahaifiya ta, ta juya min baya. Sai Ummi, ita ta jawo ni ta nuna min kuskure na, da kuma yanda ya kamata in bi dashi. Ita ta ceto ni daga cikin kangin wahalan da na shiga ta Kuma nuna min madaidaiciyan hanya. Ko wannan kadai ya isa in aure ki Suhaima balle Kuma ke kadai ce macen da zuciyata take muradi a kullum. Tabbas nayi takaicin rabuwan da muka yi a baya, da Kuma irin rayuwa da kika jefa kanki bayan nan. Amma na dauki hakan daga cikin kaddara na, abinda na yima yarinyar nan kuwa shike bibiyata. Hakan na daga cikin dalilin abinda ya same ki a ajeyari. Allah ya yafe mana baki daya" da Ameen ta amsa cikin kankanuwar murya. Tabbas, rayuwa kowa da irin tashi jarrabawan, ita kam irin nata kenan Sai dai tana mai gode ma Ubangiji da ya kawo mata yusrah a cikin dukkan tsanani.
Gidan Yan uwan su Hajja ya kaita a Kano, kullum Sai yazo ya duba ta yaji ko tana bukatan wani Abu. Bai so da aikin gaggawa ya Kira shi Abuja, dole ya tafi ya bar ta, dan ma yasan unda ya Kai ta bai da matsalan wani tunani, domin ya San za a mata duk wani abinda ake bukata.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top