Babi na uku

Yau tunda safe da Rufaida ta fito ta ke tunanin Suhaima, hakanan kawai ta ke jin Yarinyar ta mata. Ta na bata tausayi don ta san ba karamin abu zai sa mutum ya samu raunuka irin wannan amma yaki fadi yan uwanshi ba. Yanke shawara tayi tana zuwa asibitin ita za ta fara zuwa ta duba, kwana biyu ba ta leka ta ba ba don komai ba sai dan Dr Fahad, tana kokarin ganin ko yaushe haduwar su yayi karanci. Da wannan tunanin ta samu karasawa asibitin, tana rubuta suna a registern asibitin na ma'aikata gabadaya ta nufi wurin Suhaiman. Kaman ko yaushe kwance ta ke akan gado sai da wannan karon ko ina na jikin ta rawa ya ke, alamun sanyi na damun ta. Fankan da ke aiki a dakin Rufaida ta duba taga a kashe hakan yasa ta nufi wurin Suhaima domin sanin me ke faruwa. Bargon kadai da Sister Rufaida ta kai hannun ta ya dau zafi, ganin haka ya sa fa fara kokarin budewa. Sai faman karkarwa take hakoran ta har hadewa su ke. "Subhanallah! Lfy Suhaima?" Ta furta tana kokarin kai hannun ta wuyan ta, aiko nan in ma radau ta ji shi. Da alamun dai kwana tayi da zazzabin. Rufaida ba ta son lokacin da ta fiddo wayan ta ba ta fara neman numban Dr Fahad. Shigowan shi asibiti kenan yayi parking yaga kiran Rufaidan na shigowa wayan shi. Mamaki ne yaji mamaye sanin da yayi yanzun guje mishi mq ta ke. Daukan wayan yana tunanin ko dai patient in shi ne.

"Suhaima is..." Iya abinda ya ji ta fada kenan yayi saurin nufan dakin ba tare da ya damu da kashe wayan ba.

"What is the matter?" Kusan a tare ya fada da bude kofan dakin.

"Fever" Rufaidan ta bashi amsa tana kokarin dannawa Suhaima towel in da ta jika da ruwa akan goshin ta.

"Is it that high?" Da Kai ta mishi alamun eh kafin ta matsa ya fara duba ta da stethoscope.

Siririn tsaki ya ja ya juya wurin Rufaida "pls taimaka min da Sphygmomanometer daga ward wurin Vitals" bata ce komai ba ta fita. Mai da hankalin shi yayi kan Suhaimaj da har yanzu ta ke rawan sanyi, ta lullube da bargo fuskan ta ne kawai a waje sai ko kafa da hannun da ke da karayan. Idanuwan ta sunyi ja alamun hada ciwon kai. Hannun shi akan goshin ta, duk da towel in da yazo ya tarar Rufaida na sa mata amma radau yaji shi. Shi daman ya san yawan zaman asibiti ma na sa wa mutum ciwo. A yanda ya kamata, tunda ta fara warke wa ta tafi gida in yaso a dinga kawo ta check up har zuwa lokacin da za a kunce karayan. Sai dai bai jin za iya barin hakan duk da Brr Mustapha ya nuna son tfy da ita in, yana jin cewa ba yan uwan ta bane duk yanda su ka kai da tausayi ba lallai su kula da ita yanda ya kamata domin ko ba su san ciwon ta ba. Komai da ya faru da ita a gaban idon shi ne, yana tunanin ba mamaki hakan yana da alaka da tausayin ta da yake ji na ratsa ko ina na jikin shi. Da komai na rayuwan shi ya ke jin he needs to protect her. Kasa dauke hannun shi a saman goshin ta yayi, bai ko da yi tunanin zai iya kara mata nauyi ba. Addu'a ya fara kokarin mata, bai sanda idanun shi ya sauka akan na ta. Ba wani irin abu ya hango a cikin su da ya sa shi saurin dauke nashi idon, in bq gizo ba ne tabbas shi kam wani haske ya hango mai kashe wa mutum idanu cikin na ta idon. Bai san shigowan Rufaida ba, shi ko takun ta ma bai ji ba sai dai kawai ya ga ta ajiye mishi abinda ya bukata kan table in da ke kusa dashi. Sai a lokacin ya iya daga hannun shi daga kan goshin ta, a hannun da ba karaya ya sa mata abun domin gwada BP inta. Pulse rate inta is high sannan Kuma Bp ma is very high. Ba shakka duk yanda ya so kin yarda da abinda idanun shi ke gaya mishin, Suhaima na fama da hawan jini. Duk sanda ya gwada ba wani canji. Ya kan rasa dalilin da ke sa Yan mata hawan jini sosai a zamanin nan, gabadaya shi kam ji ya ke duk ya fara karaya. A rayuwan shi na likita ya ga abubuwa da dama masu matukar ban tsoro da girgiza, mutum da ranshi amma sai abubuwa da dama su hana shi jin dadin rayuwan. Hakika duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga Uku. "Ki kira lab su turo akwai da tests in da nake so a mata". Wayan da ke dakin Rufaida ta daga ta kira lab in, su ka tabbatar mata za su zo yanzu. Kara sa ta tayi ta hado alluran da yq ke ganinnza su saukar da zazzabin. Rufaida har ta zo tana tunanin yanda za ta fara yi mata. Fahimtan hakan da yayi ne yace " kawo kawai ki ban tourniquet a hannun zan mata. Sai ki rubuta min lab request foam in, za ayi Mp, FBC, widal test, Lipid profile, E/U/cr, Screening na hepatitis da Fasting na sugar. Ai ba ta ci komai ba ko?"

"Na dai same ta tana rawan sanyin ne" Rufaida ta fada bayan ta ja wa request foam in tana kokarin filling.

"Have you eaten?" Suhaima ya tmby, girgiza kan ta kawai tayi dan yanda ta ke jin kanta ba za ta iya magana ba, she is feeling out of the world kawai.

Daura tourniquet in yayi a hannun ta ya fara mata allura bayan ya samo jijiyan ya gogo spirit. Allura ne kusan guda uku hakan ya sa shi Using babban Syringe saboda ya mata duka a lokaci daya kawai. Sai dai me? Yana zare alluran sai ga amai ya zo mata ba shiri. Saurin tallabo ta yayi ai ko gabadaya aman ya bata mishi jiki. kokari ta ke ta janye jikin ta amma ya ki bata daman hakan, jikin na ta ba karfi haka nan ta kyale shi. Rufaida sai sannu ta ke mata tana kokarin karasa filling foam in. Dai dai lokacin Mr Edward ya shigo tare da wata IT student a bayan shi. Sannu ya ma patient da shi kan shi Dr in jaje ganin yanda jikin shi ya baci. "Mr Edward kawo kawai na debi jinin"

"Anya Dr ba za kaje ka gyara jikin ka ba kuwa?" Murmushi ya mai yace "bakomai ai in na je sai in gyaran" bashi syringe in yayi, vacoutiner needle ne ma, da yawa ake son jinin saboda yawan tests in. Sai da Dr Fahad ya mata sannu sannan ya kara daura mata tourniquet in amma ba inda yayi alluran ba. Bottle kusan Four ne yayi kokarin ganin kowanne an samu, gudu samun matsala a result in. Rintse idanu Suhaima kawai tayi, har ranta ta ke jin zafin alluran da ke cikin jikin ta, ita kam da lfy lau ma ba zata taba bari ayi da saukin kai ba. Gane hakan da Dr Fahad yayi ne yasa yace mata "sorry ko" bayan ya gama jan jinin, Mr Edward ma sannun ya mata yana amsan bottles in "Please Mr Edward ina son tests in as soon as possible"

"In Sha Allah za ayi kokari likita" ya fada yana amsan bottles in, Mika wa IT student in request foams in Rufaira tayi sannan su ka wuce.

Kokarin magana Suhaiman ta ke yi tana son bashi hakuri yayi saurin girgiza ma ta kai. Kallon Rufaida kawai yayi ta tashi ta kawo mishi ruwa ya dan dauraye jikin shi sannan ta amsa ta taimaka wa Suhaiman, Sai da ya fita dakin ya Kira cleaners domin su gyara wurin shi kuma ya tafi gida domin gyara jikin shi.

Sai bayan 2 hours ya dawo dakin ya samu Maryam, Barr da Anisa sun Zo duba ta ita ko ma bacci take. Sun gaisa ya musu bayanin zazzabin da ta tashi dashi Wanda yafi danganta shi da yawan tunani ne hade da sa damuwa a rai. Ba ta dade ba ta farka, Dr na ganin yanayin ta ya san an samu canji sosai ba kaman dazun da yazo ba. Yanzu kam murmushi ne ma ke kan fuskan ta wanda dai tana yi ne kawai ba don ya kai zuci ba. Kokarin zama ta ke son ganin haka Anisa ta je taimaka mata. Kallon Anisan ta ke sosai tna tunanin akwai inda ta san Fuskan, Dr ne ya lura da hakan yayi mamaki saboda a yan kwanakin da tayi a asibitin ya sa kurawa mutum ido bai daya daga cikin halayen ta. Ita kanta Anisa sai da ta tsargu amma kuma sai tayi kokarin basarwa. Sun dan taba hira kadan har zuwa lokacin da result in lab ya iso sannan su ka mata sallama su ka wuce.

"Am sorry Dr abo..." Ba
p. ta karasa ba yayi saurin katse ta da hannu.

"Shhhh Dr ma ai ya San lalura right?"

Nodding kanta tayi in affirmative

"To a bar zancen ban so" Kan nata dai ta Kara Nodding still.

Duba result in Dr Fahad yayi, ya jin dadin ganin sugar level inta is normal haka kuma ba hepatitis.

"Suhaima" ya kira, dago kanta tayi tana kallon shi. Four eyes su kayi dashi ba ko shakka wannan karon ya tabbatar da abinda ya ke zargin ya gani dazun a cikin idanuwan nata. Dauke na shi yayi.

"Meyesa kike yawan tunani da sa damuwa a rai"

Dagowa tayi tana kallon shi, ta bude baki tana shirin musa wa ya girgiza mata kai "i know you are doing it fa"

Shiru tayi don ba ta ma san me za tace mishi ba, to ta ina ma zata fara? Ita kam ba ta jin za ta iya fadin komai akanta. Nothing is worth saying out ma.

Karkada Kan shi yayi alaman gamsuwan ba maganan za ta mai ba "Whatever, ki yi kokarin rage damuwa coz Yana affecting health inki negatively" Kallon shi ta ke yanda ya ke Mata magana cike da nuna kulawa sai kace wani dan uwanta na jini, Most of the times ya na tuna Mata Wanda ta sani. Halayen su da maganganun su kan mata shige. Wannan dalilin ya na daga cikin

abinda yasa ta yi saurin sakewa dashi, tana ganin kaman wancan inne a gaban ta.

He makes sure ta Sha magungunan ta sannan ya bar asibitin bayan ya kafawa Nurses in dokon kula da ita, ba Wanda ya gani a cikin Nabeela da Rufaida Bai Kuma tambaya ba ya Kama hanyar gaban shi.

Sosai ta fara gajiya da kwanciya ko yaushe akan gado fuskan tan hakan da Rufaida tayi yasa ta kan taimaka mata ta sauko kan wheelchair inta ta dan huta, duk ma har yanzun ba wani hira su ke ba amma Suhaiman na jin dadin zama da ita, ta san cewa Rufaida na daya daga cikin wadanda su ke taimaka mata sosai a yanzun, ta na kuma mahimman ta hakan. Musamman ranar sai ga Maman Rufaidan da kanwar ta sun zo duba ta, matar na da kirki sosai kana ganin ta kaga bafulatana, ai ko fulatancin ta ji suna yi dukkan su. Wani abu da su ka fada ne yasa ta dariya, ba ta ma san sanda tayi shi ba. "Haba ashe yar tawa bafulatana ce daman na zargi hakan" Dada, kaman yanda taji su Rufaidan na kiranta ta fada, dariya kawai ta sa ke yi. A nan Dr Fahad ya zo ya same su, da fara'an shi ya durkusa yana gaida Dadan kanwan Rufaidan ta gaishe shi tan fadin "Hamma Fahad"

"Kai kan asibiti ya boye mana kai kwana biyu ko fahad"

Da sauri yace "yi hakuri Dada ai yau ma dole in zo gida, Aliyu ya dawo ko?" Tun lokacin sau da dama Rufaida na kawo mata abubuwa tace Dada ta bada a kawo mata. Zaman ta a asibitin nan ya sauya tunanin da dama akan yanda ta dauki mutane da zaman takewan rayuwa.

Ita kadai ke zaune a dakin, a zahiri TV ta ke kallo sai dai Kuma hankalin ta bai Kan film in kwata kwata. Ganin haka ya sa ta fiddo Qur'anin da Dr Fahad ya bata ta fara muraja'a cike gwanance tare da ba ma kowani lafazi hakinsa. Ta kai minti arbin tana karatun kafin ta rufe Qur'anin ta fara addu'ointa tana me tuno mutumin da ya bada gudun mowa babba wurin karatun nata.

Wasu zazzafan hawaye ke fita daga cikin idanunta domin tunanin makoman ratuwar ta bayan ta warke. Shin Ina za ta? Baya za ta koma ko Kuma gaba za ta ci. Dr Fahad ne ya katse mata tunanin nata, tana ganin shi ta yi kokarin goge hawayen da ke idanun ta gudun ya fahimci kuka ta ke yi. Sarai ya ga hawayen amma sai ya basar ganin ba ta so ya ganin. Ya na matukar son sanin damuwan, yana son ko akwai gudumuwar da zai iya bata komin kankantan shi amma still bai son takura mata.

"Sorry an barki ke kadai ko?" Murmushi ta Mai kafin ta amsa da bakomai.

"Kin gaji da Asibitin namu ko?"

Wannan karon ma ba tayi magana ba sai shine ya Kara fadin "sai hakuri, Allah dai ya baki lfy" sai a sannan ta amsa mai da Ameen. A ranta faduwan gaba na ya ziyarce ta, a yanzu ta san zaman asibitin ke rufa mata asiri ba ta san me kaddara zai yi da rayuwan ta ba kuma.

"Mu fita waje ki Sha iska" da sauri ta daga mishi Kai yayi murmushin da sai da har dimples insa su ka lotsa.

"Gsky Suhaima kin gaji" ya fadi yana tura wheel chair in nata waje. Wani ajiyan zuciya ta saki bayan fitan ta su daga dakin after kusan 1 month she is finally out.

Za a iya kiran wurin da ya kaita Garden saboda shuke shuken da ke wurin ya karawa mishi Ni'ima, wani iska Mai Dadi Ke hurowa hade da kukan tsuntsaye in kana wurin ba za kaso ka bari ba. Wurin wasu beautiful adorned flowers ya Kai ta, kamshin su sai blowing ya ke. Lavender, lilac and pink lilies ne gabadaya a wurin cikin pot in su making the place purple and pink, she likes the combination. Pink was her favorite color but as she grow up she changed to purple kaman yanda life in ta ke canjawa eventually haka ma likes and dislikes inta dama komai na ta gabadaya inka cire abu daya, she can't never move on if it comes to that.

Kura Mata idanu Dr Fahad yayi Yana smiling ganin mode in da ta shiga sai dariya ta ke tana smiling as she is touching the flowers tana scenting fragrance insu, kwalla ke zubo daga idon ta tana goge da handkerchief in da Dr in ya bata. Abun mamakin shi ba yanda ya kasa lallashin ta illa bin ta da idanu da yayi cike da sha'awa. abubuwa dayawa ke running a mind in shi, wani irin tausayin ta da Kuma tausayin Kan shi ya ji Yana ratsa shi. Bai San me ke damun ta amma zaman da yayi da ita na yan kwanakin bayan ta yi regaining concious ya tabbatar mishi da ta na cikin wani hali wanda Addu'a ne kadai zai cire ta daga ciki. he is very sure ba health condition inta bane saboda ba ta ta da hankalin ta akan shi ba kwata kwata. Deep down inside him Yana son sanin labarin ta but yasan she can't open up to him hakanan.

Ita ko Suhaima moment in wani moment ya ke tuno mata wanda ya shude a rayuwarta, she misses and fansy that moment sanin ya riga ya wuce har abada ke sa ta kwalla. If only wishes were horses...

"Earth to Suhaima" clapping hannun shi yayi saitin fuskan ta ganin yanda tayi zurfi sosai cikin tunani.

Kanta ta yi saurin ja baya a firgice kafin ta dago ta kalle shi yana mata dariya.

"Shine ka tsoratani Koh?" Ta fadi kaman ta yi kuka.

"In tambayeki" nodding kanta tayi in affirmative.

"Ke Yar wani gari ne"

Zaro idanu tayi "me ye sa kake tambayana?"

"Isn't it obvious? Hausanki is not clear"

"Yobe state" yanayin fuskan ta gabadaya canja wa yayi, she looks pale and pathetic.

"Wani gari infact ma wani yare yarukan yobe ai suna dayawa"

Za ta yi magana kenan wayan shi ya dau ruri, da hannu ya nuna mata alamun Yana zuwa, saurin daukan wayan yayi sannan ya sadda Kan shi kasa alamun da Babban mutum zai yi maganan.

"Hello Ummi Nyalli jam?" Ya fadi leaving Suhaima tongue tied, she can't believe Dr Fahad bafulatani ne ko tace ya iya yaren ganin ranar da Dada ta zo shi Hausa su kayi. Ba wai bai yi Kama dasu bane No ba tayi zaton zai iya speaking fluently haka ba sai gashi ko har ya gama waya da Mahaifiyar shi fulatancin su ke yi.

Sai da ya gama ya juyo ya kalle ta

"Ãn a fullo na?" Ta tambaya leaving him tongue tied, he is beyond shocked, For sure yasan ba bahaushiya bace Amma ko da tace Yobe he expects some tribe like Bolawa ko Kuma badawa, for sure yasan ba kanuri bace.

"Which of the fulani local government are you from in Yobe"

"Damaturu"

"Ummi na Yar Kolere ce"

Runtse idanu tayi cike da takaici jin sunan garin da ya fada bayan hakan ma yanda ya kira mahaifiyar tashi ya sata shiga wani yanayi, a can kasan zuciya ta ke jin ai she is already over this kuma. Da kyar ta furta "Ummi na ma haka"

"Baffa mada no fullo?" Ta tmby shi, nodding Kan shi ya Mata "From jalingo"

Sun Jima suna hira a wurin inda kowannen su ya ke jin dadin hira da dan uwanshi, gabadaya ma juye harshe su ka yi zuwa fulatancin. Da wannan daman yayi Using a siyasance ya mata fadan kuka da tunanin da ta ke yawan yi. "Hawan Jin kawai xai Kara miki Suhaima Allah ne kawai zai miki magani" Nodding kan ta tayi a zahiri Amma fa deep inside tasan cewa she have face a lot... So abu ne mai matukar wuya ta daina tunani wannan tunanin.

Nabeela ce ta Kira shi tana tambayan ko ya tafi gida ne, Eh kawai ya sanar Mata. Tsab ya fahimci Karatun da Nabeelan ke son ya gane shiyasa ma kwana biyu ya ke kauce Mata domin matsalan da ke gaban shi ma ya ishe shi.

"Me kike so in na koma gida insa Rufaida ta taho Miki dashi in za ta zo, gidan zan wuce kawai direct" ya fadi Yana duba agogo.

"Wala dume ma" ta fada kafin ta Kara mishi wani tambayan.

"Are you cousins?"

"And fiance"

Kallo ta bishi dashi with a wider eyes.

"Really? I can't believe this" shaking kanta tayi cike da shakku "You guys hardly talks"

Murmushi yayi dimples in shi ya shige cike sosai "Suhaima kenan, Can't you see kawar ta ki miskila ce? And its kind of arranged marriage kin San Fulani"

"But she is nice and you look good together"

Murmushin na shi ya Kara yi Wanda ke tuna Mata da mutumin da kullum Yana ranta "I may not be interested fa Kuma ma I think I've just find my girl"

"Ku dai kun cika ruwan ido Allah, yanzu miye laifin Rufaida? ba abinda ta rasa" cike da fada tayi maganan wanda ya sa shi dagowa yana kallon ta.

"Na sani Kuma ba ruwan Ido bane"

"Shine mana"

"Bazaki gane bane" ya fadi Yana kokarin turo wheel chair in nata.

A bakin dakin su ka hadu da Maryam tare dasu Anisa da muhibba don haka kawai ya Mata sallama ya wuce.

Sun dan taba hira sama sama da ke ita in ba mai yawan surutu bane, sai dai yau ma kara Kallon Anisa ta ke da kyau ganin dai da kyar in zargin ta bai zama gsky ba. Ganin dai Anisa ta fara tsarguwa ya sa ta dauke idon ta. A nan Rufaida ta zo ta same su, sai da ko Dr Fahad ya aiko mata da abhbuwa duk da bata fada. Ta kan jinjina irin sabon da tayi da Dr, ko dan ya damu da lamarin ta ne?

Nyalli jam? : an wuni lafiya?

An a fullo na?: Daman Kai bafulatani ne?


Baffa mada no fullo?: Babanka ma bafulatani ne?


Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top