Babi na takwas

Ana idar da Sallan Azahar Dr Fahad ya iso gidan, Sai da ta tabbatar da ta gama abincin da Barr ya sata ta hada musu da abin Sha sannan ta fita, ko da taje fadawa maryam, toh kawai ta amsa Mata ba tare da ko ta kalle ta ba. Jikin ta a sanyaye ta fita wurin Dr.


Gaisawa su kayi kawai ya ja motan su ka tafi. A wani katon super market taga sun tsaya "mu je ko ko ba Zaki tayani zabo kayan lefen bane?"

"Kai za ka hada?" She asked with a suprise expression plastered on her face.

"Mu je kedai kawai ya ce Mata ta ko bishi" siyayya su ka yi sosai na atamfofi, laces, bags, shoes, undies da cosmetics. Maimakon ta ga ya dau hanyar gida sai taga ya bi wani gun Kallon shi ta yi da mamaki yayi saurin ce Mata "shhhh" ai ko shirun ta yi.


Wani madaidai cin gida ta ga ya nufa Yana ta horn, Nan da Nan maigadi ya bude Mai Yana Mai sannu da zuwa. Shiru gidan kaman bakowa hakan yasa ta fara bin shi da Kallon tsoro. "Hey, i don't bite" ya fada Yana dariya. Ba Wai Dan tayi trusting in shi completely ba ta bishi Aa ta dai tsaya ta ga gudun ruwan shi. Sai dai taga yayi sallama taji muryar mace ta amsa sannan hankalin ta ya dan kwanta.


"Ah Fahad har ka iso?" Wata Mata da ba zata wuce 35 ba ta fito tana maganan hade da wata yarinya a bayan ta. Gaishe ta Suhaima ta yi ta amsa faran faran haka ma Dr in.


"Anty ga Suhaima Nan na kawo ta gaishe ki Kinga ita ma ta Taya ni muka karasa siyayyan" murmushi tayi cike da kunya don ko wani iri ta ke ji in Fahad in ya Kira ta da Anty don ta San da kadan ta fishi.


Suhaima dai Kallon da ake ta bin ta dashi ya sa ta tsargu, four eyes su kayi da Zahra Nan da Nan ko kirjin ta ya bada kulululu "Sannu fa kin Sha jiki" Wacce su ka Kira da Antyn ta fadi sai a sannan Zahra ta Mata sannu sai dai da alamun ita ba ta gane ta ba kaman yanda Zahraun ta gane. "Ga sis ita Zahra da nake baki lbr" Dr Fahad ya fada ita ko Suhaima murmushin karfin hali kawai ta sakan Mata cike da mamakin yanda zahran ba ta gane ta ba Amma sai ta barwa zuciyan ta. Sun Dan taba hira sama sama kafin a Kira Zahra a waya tayi saurin dauka tana fadin "F sai yanzu za ka kirani? Nayi fushi" Nan ta ke Suhaima ta gane da Faroukh ta ke waya don ko haka ta ke Kiran shi. Ihun da ta sa ne ya dawo da Suhaima daga tunanin da ta tafi "are you in your senses Zahra?"

"Sorry ya fad, F ne fa yace min In 5 days zai yi Landing a Lagos, nayi missing in shi"

Tsaki Fahad ya ja "I wonder if this guy is even going to marry you kin tsaya kina hauka akan shi" turo baki tayi kaman za tayi kuka "Anty Kinga brother ko"

"Kyaleta Fahad Ikon Allah ne"

"Aa Anty in Sha Allah ma ni shi Zan aura" murmushi su kayi gabadayan su.


Sai bayan la'asar bayan Fahad ya dawo daga masallaci su ka bar gidan, haddadun bokhoor Anty ta bada, zahra Kuma ta Bata bracelet taso ta ki amsa but she insisted, Dr Fahad ko da ya sauke ta a gida wasu haddadun Arabian gowns ya Bata guda biyu da jewelries a cewan shi tukuicin Siyayyan da ta Taya shi ne, ba ta Musa ba ta amsa don ko ta ki ma fada za suyi daga karshe ya sata dole.


Ko da ta shiga gidan as usual Matan gidan ba ta Nan sai Hadiza da haydar, Yaron har murmushi ya dinga yi ya ganta ita ma ko da sauri ta dauki shi sannan ta bashi tsaraban Bobo in da ta siyo Mai, Nan da Nan ya hau Sha, Yaron har tausayi ya ke bata har ya sa da wuni da yunwa tun Yana karamin shi Yana Shan abubuwan da Nanon Mahaifiyar shi ba da gabadaya ba ta da time in Shi, daga yau tana islamiyya sai gobe kasuwa gata gidan kawa kullum dai da inda ta hara, don da har weekend ta ke hadawa ta tafi gidan Anty sai da Antyn ta hada su da Mustaphan ta musu ta tas tukunna su ka shiga hankalin su. Shi dai ba wai Yana so bane Amma ya tsani abinda zai Bata Mata Rai Yana mugun gudun fushin ta.


Sai bayan magreeb Barr ya shigo tana daki ya kwala Mata Kira don ko kadan bai son abinda zai hada shi da Hadiza, he hate the girl ba ta Mai ba. "Sannu da gida, kin dawo?" Nodding kanta tayi "Ya outing in, hope you enjoy it?"

"Ehmm" kawai ta ce Mai Nan da Nan ya hade Rai "Suhaima na lura har fa yanzu ba ki saki jiki da ni ba come on am your brother" murmushi kawai tayi sannan ta Mika haydar da ke ta kokarin zuwa wurin Baban shi. "Allah sarki my boy mum ta barka da yunwa ko?" Yaron dai sai kananun rigima ya ke don Yana ma da hakuri "Ni ko in tambaye ki, akwai wani abu tsakanin ki da Dr ne?" Kallon mamaki ta bishi dashi sannan ta yi murmushi hade da girgiza Kai "We are just good"

"Em em fa for the first time Naga murmushin ki Sosai daga Kiran Dr ki dai fada min gsky"


"Haba dai bbu komai, aure fa zai yi soon"


"Nasani fa, namiji ne fa ba mace ba infact you are not that easy mutum ya Bari ki kubuce Mai" saurin Kallon shi tayi kafin ta Mai da Kai kasa "Babu komai kawai Allah ya hada jinin mu ne?"

"Then Allah ya samu a danshi shi muma ko a dan da sa damu, he is damn lucky!" Suhaima dai barin kanta tayi a kasa ta kasa magana, maza dai sai a slow ji fa soyayyan da ya ke gwada wa matar shi Amma ya zo zai cika ta da dadin baki.


"And ban fada Miki ba girki yayi Dadi sosai Abokanai na duk sun yaba sunce za su kawo tukuici Amma Bari na bada nawa kafin na sun ya iso" hannu ya Kai cikin aljihu ya fiddo Rafan 2 hundred ya Mika Mata, nodding Kan tayi alamar Aa "kin amsa Mana come on ban son haka fa ni"

"Aa Allah ka bar shi"

"Ranki zai baci fa ki amsa nace maza" cike da fada yayi maganan this time around hakan ya sa ta sa hannu ta amsa hade da godiya, daga Mata hannu yayi da sauri alamun Bai so and she smile. "Ah ah Anty Ashe kin dawo" Hadiza ta fada tana Kallon Maryam da ta saki baki tana Kallon dilemma in da ke faruwa a gabanta. Dukan su Kan one seater da ke kusa da juna su ke zaune sai dai ita Suhaima ta yi gefe. "Mimi kin dawo? Ba ki yi sallama ba fa"

Tabe baki tayi "Daman ya za ayi kaji"

"Sannu da dawowa" Suhaima ta fada

"Sannunki" kawai Maryam ta amsa Mata fuskan Nan a hade kaman zata fashe ta nufi dakin ta.

"Mimi Yar rigima" ya fadi hade da girgiza Kai sannan ya dauki haydar su ka bita dakin.


Hadiza da ke kallo ta matso kusa da Suhaima a hankali ta fara magana "a dai ji tsoron Allah Kar a raba auran so da Allah ya hada" kallo Daya ma Suhaima ba tayi sparing inta ba ta tashi ta dau littafin ta ta bar falon.


A cikin daki Mustapha ya kura wa matar shi da ke ta faman kuka Ido, abin ko ba karamin Kona Mata Rai yayi ba da da dane ya dinga rudewa kenan Yana tambayan ta damuwan ta. Da kanta tayi shiru ta fara shesheka "tashi ki wanko idonki muyi magana" ba musu ta tashi ta yi abinda ya ce in ta dawo ta zauna "tell me me ke damun ki"

"Kai ne Ya Musty"

"Me na miki Mimi?"

"You love her right?"

"Wai Suhaima?" Murmushi ya saki "haba Mimi har Zaki zarge ni don na fada son wata macen bayan ki after all you gave the room for that to happen"

"Okay dan nayi taimako shi ne laifina ya Musty?"

"Meyesa da nace ki kaita gidan Anty Kika ki"

"I want to help myself and I trust you" ta fada tana Kara fashewa da wani kukan, yayi lallashin har ya gaji ya kyaleta. Tun daga ranar ta fara daure dauren fuska a gidan, sai ta wuni a waje sai dare ta dawo, haydar ko a gida ta ke barin shi, a cewarta ta bar mishi dan yayi abinda zai yi tunda ta San ya tsani hakan, tsakanin ta da Suhaima sai Kallon banza, baiwar Allah duk ta tsangwame kanta, she is feeling guilty ga Barr sai faman kara shige Mata ya ke ya dinga Jan ta da hira kenan tana kaucewa, Maryam ko ko bi ta kanta Bai yi ta Kai ta kawo ma kowa a dakin shi ya ke kwana.


Da dai ta lura da gasken Fushi ya ke da ita sosai,  ita kuma ba ta saba da fushin shi ba kwata kwata sai ta fara karaya. A hankali ta fara jure zaman gidan, ba ta cika fita sai dai duk da hakan zaman bai sauya zamani ba saboda wuni ta ke tana kallon series, wanda daman a gidan kawayen ta ta ke kallo saboda ya ki mata subscription tun asali ganin ba ta da aikin yin sai kallon a gidan shine fa ta dauke kafan ta gabadaya daga gidan dan zaman da ta ke ma ta daina. Yanzu kam da kanta ta je ta yi subscription in DSTV in ta zo ta cigaba da kallon ta. Mustapha yayi tunanin sauya wa tayi da yaga ta fara zaman gidan amma sai ya zuba mata ido ya gani. Ya ko gani in,  ba ta sisin fari ko baki a gidan nan banda ta yi bacci,  chatting, ta ci abinci sai ko kallo. Don ko haydar in ba nono za ta bashi ba to hadiza ta ke ba ma wa, aikin gidan kam Suhaima ke fama in ta gama ta karbi haydar.


Duk cikin su ba mai jin dadin zaman gidan hatta ita maryam in,  ba ta saba zama da sabon halin da barr ke ma ta ba wanda ta ke tunanin duk akan Suhaima ne. Daman dai kawayen ta sun sha gaya mata ba a yarda da namiji dari bisa dari sai yau ta yarda da hakan. Shi ko Mustapha lallabawa yayi ya dauke key in motan ta ya ma tafi dashi office ya boye gabadaya don a ganin shi zama kallon series in yafi mishi yawon gidan mutane. Ya ko kara sa Mimin nashi a wani hali,  dan fitan da ta ke yi ma ya zama bbu. Gashi ita kuma tana ganin kaman raini ne kaman ita a ganta a napep, anya har yanzu barr na sonta kuwa? Girman kai ya hana ta mishi maganan dauke ma ta key in da yayi, ba ta son ya zamana ita ce ta fara karaya. Tsakanin ta da Suhaima kam abun yanzu ba kyau, ta na dai amsa gaisuwan ta shima darajan yaron da ta ke kula mata dashi, kunsan ance mai da wawa saboda haka ta ma fi daura laifin kan mijin ta akan Suhaiman.


Yau ma in dai kaman kullum zaune ta ke a falon daga tana kallon Indian Series in da ta sa a gaba. Gabadaya ya dauke mata hankali,  sam ba taji sallaman mustapha ma da ya shigo gidan ba. Maimakon ya kalle ta gani tayi yayi cikin gidan da sauri. Ita ma in sai a lokacin taji kukan haydar da ke ta tashi, tabbas taji shi yana kuka sai dai cewa tayi ba ta da lokacin shi in ya gaji yayi shiru. Bin bayan Mustaphan tayi har zuwa corridor in da ta jiyo kukan yaron. Yana hannun suhaima tana faman jijiga shi, fuskan shi yayi ja tsabagen kuka har shidewa ya ke domin da alama yau kam ya ki jin lallashi. Ko da baban shi ya mika hannu kin zuwa yayi yana tirje wa "wai me ya same shi haka Suhaima?" Sai a lokacin ya ga hadiza da ke ta faman sinne kai alamun rashin gaskiya. "Wlh fa fadi yayi a hannu na ban sani ba shine ya buge kai" tsaki barr yaja yana girgiza kai

"saboda ke mahaukaciya ce yaron zai fadi a hannun ki ba ki sani ba ko?" Maryam ce ke maganan tana shirin yin wani ya mata wani kallon da ya sa ta yin shiru "Ki amshi danki" kawai ya ce ya kama hanyan bari wurin. Ai ko yaro da saurin shi ya zo wurin mamanshi yana kara kankame ta. Saurin zama tayi ta sa mishi nono a baki,  wannan karon kam kin amsa yayi ya janye kan shi, sai ta lallashe shi tukkuna ya amsa hat da sakin ajiyan zuciya, ita kanta tabbas ta san tana shiga hakkin yaron sosai.


Mustapha kam falon ya nufa direct ya cire DSTV in yayi disconnecting ma gabadaya har TV in. Mota ya nufa ya ajiye ya bar ma gidan gabadaya, tun maryam tana tsammanin zai dawo har ta gaji ta hakura. Shi ko ranar har kukan bakin ciki yayi, bai yi zaton za ta iya saka mishi da abinda ta ke mishi yanzun ba. A ganin shi ya fi karfin abinda ta ke mishi a wurin ta. Sai wuraren goma ya dawo gidan, ya samu haydar yayi bacci ita ko sai faman chatting ga ke a wayan ta. Wani irin nauyi yaji kanshi ya dauka, shin ba ta idan zai bullo wa alamarin maryam yayi nasara ne? Shi kam lamarin ta ya fara kai shi makura domin a kwanakin nan har aikin shi ya fara affecting. Har ya gama abinda zai yi ba ta mishi magana ba,  hakan ya kara tunzura shi. Yanda ya ke ganin ta bakikirin hakan ya ke jin zuciyan shi bakikirin, shi kanshi bai san inda ya ke nufa ba sai da yaga kanshi a gaban ta. Tsabagen chatting sai da taji mutum a gaban ta sannan ta ankara da shi, tun kafin ta gama gane yanin shi yayi nasaran wafce wayan a hannun ta. Kafin ta gama bude baki domin furta magana,  wani kara ta ji a cikin dakin. Saurin mai da idanun ta tayi kan wayan da ya wulla jikin bango da dukkan iya karfin shi sannan ya fado kasa. A rikice ta nufi wurin wayan, a bushe ta ke jin zuciyan ta ita ma. Kallon arziki ba ta yi wa wayan da ya dagargaje ba illa ma sims inta da m card da ta dauka kawai ta sama musu ma'adana ta nemi wuri tayi kwanciyan ta, a ranta tana fadin "Sai me? Kaine dai zaka kara siya" Tabbas ya san halin mimin da taurin kai amma bai zata za ta iya mishi abinda ta mishi yanzun ba. Da dukkan sakwanin duniya tana kara tabbatar mishi itan ba ta dauke shi a yanda ya dauke tan ba. A daren da kyar yayi yaki da zuciyan shi wurin ganin bai sa hannu a jikin ta ba domin haka ba halin shi bane. Kallo daya ya mata yana jin dukkan zuciyan shi na mai ciwo ya dauke idanuwan shi,  saurin barin dakin yayi domin yanda ya ke jin shi in har ya cigaba da kallon ta a ranar ba abinda zai hana bai fidda ma ta jini ba. Ya san yana da mugun hakuri amma kuma zuciyan shi tabbas ba abu bane mai kyau ba, ya kan dau lokaci kafin yayj fushi amma in yayin shi kan shi yana tsoron abinda zai iya aikatawan. Daren ranar kam bai runtsa ba,  saukin shi washegari weekend don haka yana sallan Asuba ya samu wani bacci mai karfi ya kwashe shi. Ringing in wayan shi ne ya tashe shi daga bacci,  da kyar ya iya bude idon yana dubawa ko yaga anty ne.


"Little come home now and ka taho da Suhaima"


A rude ya tambayeta "Anty lafiya?"


"Just come yanzu nan fa, it's urgent" da sauri ya tashi ya dauki key in mota kafin ya kwalawa Suhaima kira "ina haydar?" Ya bukata


"Yana bacci"


"Maman shi fa?"


"Ai ta fita "


"Oya dauko shi maza we are going out" ganin yanda ya ke a rude he didn't give room to intrude ya sa ta dauka haydar in kawai su ka nufi mota.


Sallama su kayi a Falon aiko four eyes Barr ya yi da Maryam da ke zaune gaban Dad insu Aneesa, kallo Daya ya Mata ya gane ta Sha kuka don ko idanuwan ta har sun kada sun yi ja.


Sai da suka zauna sannan su ka gagaisa, bawan Allah haydar ya hango uwarshi tuni ya fara kiciniyar zai je wurin ta ita ko Kallon shi ba ta yi ba kanta a kasa.

"Kawo shi Suhaima" Dad insu Aneesan ya fada, Anty ta Mika ma wa sannan ta ba wa Dad in "Maryam amshi danki Mana ko ba ki ga Yana son zuwa wurin ki bane" kaman za ta fashe ta amshe shi ai ko lafewa yayi a jikin ta. "Tashi ki je ki bashi abinci ya Sha ki dawo muna jiran ki" Toh kawai ta ce sannan ta tashi ta basu gu, sai bayan 5 minutes ta dawo kaman yanda ta bar su haka ta iske su, bawan Allah ko da ya koshi bacci yayi abin shi sai kawai ta kwantar dashi.


Addu'an bude taro Dad in yayi sannan ya juya ya kalli Mustapha "Massa me ya hada ka da matar ka tace ka daina kulata more like gaba ma kuke kawai" with a blank expression ya ke maganan cike da natsuwa. Barr Sunkuyar da kanshi kasa yayi a hankali yace "Abbah tace na Mata wani Abu?" Yanda yayi maganan kadai ya Isa tabbatar maka da yanda ya ke girmama Wanda ya ke maganan dashi bai ma iya dago Kan nashi ba.

"Shiyasa na nema ka ai don inji dalilin gaban da kuke da junan ku a cikin gidan ku na sunna"

"Ni ban gaba da ita Allah, ita ce dai Naga tana fushi dani ko na Mata magana ba ta tanka ni shiyasa na fita harkar ta for some time"


"Saboda duk ku taru ku Zama Daya ko? Haba lil sai kace ba namiji ba?" Wannan karon Anty ce ta yi maganan.


"Allah ba fa abinda ya faru ba kenan Abbah, ya fadi gsky man kullum fa samun shi na ke Yana hira da Suhaima infact komai yanzu ya ke bukata ita ya ke cewa ta Mai har fita tare su ke yi har kudi ya ke Bata hakanan yayi ta siyo Mata abubuwa Kuma duk bai fada min." da sauri Mustapha dauke Kai.


"Toh Maryam tsakani ga Allah in zai yi kyauta dole sai ya fada Miki? A takaice dai Kishin ki na Mata kike right?"


"Abbah ba Haka bane gsky ne fa Yana faruwa"


"Naji ai ko ma Yana faruwan shin tun farko Antyn ku ba tace Miki Kar ki tafi da ita gidanki a barta a Nan Kika ki? Ke Mai taurin Kai ko?" Rau rau tayi da Ido kaman za ta yi kuka.


A hankali Barr ya fara magana "Abbah maganan fita da ita wlh sau Daya ne ku Nan mu ka Zo da dare ranar Zan fito haydar ya sa Kuka nace ta dauko shi mu zo, Zan iya Rantsuwa Banda kudin da Kika Zo ranar Kika ga Ina ba Suhaima ban taba Mata kyautan da baki sani ba Mimi" shiru yayi saboda takaicin abinda zai fada but this is his only choice, a hankali ya fara magana da kaji kasan Yana Jin zafin abinda ya ke fadan "Abbah miye laifina don na bukaci abu gun wacce da na sa za ta mun, Abbah kaga Mimi fa ba ta San ta tashi ta dafa min abinci ba Aa sai dai Mai aikin ta ne za ta yi in na ga dama in ci ko in barshi ba damuwan ta bane, ba ta San ci na ba balle Kuma batun sutaran na a tsaftace min su, ba ta San ta gyara gidan ta in ma Mai aikin Bata Nan sai dai a bar shi kaca kace Bai dame ta ba indai za ta gyara jikin ta, dakin ta ma ba ta gyarawa balle Kuma nawa duk sai dai Mai aikin ta tayi har kananan Kaya na fa sai taba Mai aikin ta ta wanke da na gane na fara wanke abu na, Abbah Mimi ce a matsayin ta na matar aure ina fita zata sa kafa ta bar gidan ita ma har in dawo ba ta Nan sai isha'i ta ke dawo min gida a matsayin ta na Matan aure ta bar min yaro a gidan Yana wahala sai dai ta sa a bashi kunu ko Madara ita Kam ba ta da Lokacin Dan da ta Haifa to shin miye laifina don nasa Suhaima ta min abu ta min Kuma alhalin ke ko nasa ki ba yi za ki yi ba Saboda Sam Sam ke ba ki gudun baccin rai na sai dai ni ne ma ke gudun naki kuma har kalaman Nan za su fito daga bakin ki Mimi ba ki min adalci ba ai yau ko auren Suhaima nace zan yi a ganina ba ki da bakin yin magana Kai wlh Ni ko ba ita ba Mimi in dai haka Zaki cigaba Ina Mai tabbatar Miki ba abinda zai hanani Kara aure kwanan, sannan Kuma ban tsamman Zaki Zo ki hada min sharri ba, you are more than this haba,  Abbah fa banda yawo,  kallo da chatting ba abinda ta ke tsinana wa a gidan nan." gabadaya jikin su yayi sanyi, Ganin yanda Mustaphan sam bai son laifin matar shi har ya iya bude baki ya fada da kanshi Kam abin ba karamin Kai shi makura yayi ba.


Ita Kam Mimi tun da ya ambato kara aure jikin ta ya fara rawa "Ni ni fa ba sharri na maka ba ba Hadiza ba ce ta fada min?" Gabadaya jikin ta karkarwa ta ke yi.


"Ke kuma sai Kika ga yadda, Nagode Amma wlh yarinyar can sai ta bar gidana Kuma ban son wata Mai aikin cikin gida Kam in ba za kiyi ba zanyi abu na"


"Ya Isa dukkan ku kuyi shiru" tsit ko su kayi dukkansu kafin Abbah yayi wa maryam ta tas, da kanshi ya umurci in har ba ta gyaran ban ya Zo ya fada Mai aure ko ba fashi, sannan ya sa Mata dokan rashin fita kwata kwata In ba da wata kwakwaran hujja ba har Islamiyyan ko sauke ta yayi don a cewar shi bai ga amafanin Islamiyyan ba tunda ba ta yi koyi da yanda ya kamata a yi zamantakewar aure a musulunce ba. Sai kuka ta ke tayi shi dai Mustapha Kan shi a kasa zuciyan shi sai zafi ta ke yi. A hankali ya fara tuno tun farkon soyayyan su da maryam abinda har ya Kai su da aure.


Am still not seeing ur comment fa? Please share your thoughts.

Nagode.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top