Babi na Shidda
A bakin wani hadadden gida da aka mishi ado da flowers tunda ga waje ta ga Barr Mustapha ya tsaya da motan kafin ya danna hon. Nan da nan mai gadin gidan ya bude yana mishi sannu da zuwa, Sai da ya tsaya su ka gaisa sannan ya karasa cikin gidan yayi parking.
Anisa ce ta taimaka ma Suhaiman su karasa cikin gidan. Da gudu Maryam ta fito daga cikin dakin ta Jin muryar su "Welcome home Suhaima" ta fada tana murmushi, Suhaiman ma murmushin ta Mata "thank you" ta furta a hankali. "Sannun ku Anee"
"Yauwa Anty Maryam ni dai yunwa na ke ji"
"Ai Kya bari kiyi Sallah Koh?"
"Nayi a asibiti" ta amsa tana nufan hanyar kitchen.
"Uncle Musty sannu da zuwa" Maryam ta fada cike da tsokana. Harara ya bita dashi "rike kayan ki banso sai yanzu ki ka ganni?"
"Am sorrrrrrrrrry!" sai da ta daidaici saitin kunnen shi sannan tayi maganan da karfi saurin rufe kunnen yayi yana mata nuni da Suhaima da ke Falon. Anisa ta kwala wa Kira ta umurce ta da ta Kai Suhaima dakin da suka shirya mata.
"Ina Haidar" ya bukata
"Sun fita da Hadiza" girgiza Kai kawai yayi "me aka dafa?"
"Ban son Mai hadiza ta dafa ba but let me check"
"Oh ni Mimi ke dai you will never change"
Shagwabe fuska tayi, yasan yanzu zata fara complain da sauri ya katse ta "kawo Mana abincin please Kinga muna tare da patient"
Nodding Kan ta tayi sannan ta tafi kitchen ta iske Anisa na ta zubawa Suhaima za ta Kai Mata.
Kwana Anisa uku a gidan ta koma gidan su saboda zata fara zuwa computer school Aiko ta bar Suhaima da kewa don ita ke Taya ta Hira da abubuwa da dama.
Satin ta daya a da kwana uku a gidan Mai aikin Maryam, Hadiza ta sanar da ita tana da bako a waje. Ba kowa a gidan sai hadizan da Haidar. Barr na wurin aiki Maryam Kuma ta tafi islamiyya. Hijabi dogo ta sa har ta fita tsakar gidan. A Kan bench in kusa da dakin Mai gadin ta hango shi zaune Yana wasa da key in motan shi. Jikin shi ne ya bashi ana Kallon ya dago Aiko four eyes su kayi da ita tana tsaye da crunches a hannu ta.
Tasowa yayi ya karaso har inda take ya ja fararan kujeran da ya gani a wurin ya zauna bakin wani bishiyan da ke ta buso iska. "Bismillah" ya nuna Mata dayan kujeran da ke kusa da ita. Kaman wacce aka dasa haka ta yi ta bin shi da kallo, sai yau ta ke Kara ganin kamanin su da sanda sosai har yanda su ke abubuwa ma Kama yake. "Ki zauna Mana na fanshe ki kice bakuwar bani ba" Zama ta yi akan kujeran still tana Kallon shi "Shine sai yau za ka neme ni" ta fada kasa kasa.
Murmushin Nan nashi yayi Mata har dimples in shi su ka bayyana "am sorry Suhaima na Kara komawa Abuja ne gashi ke baki da waya bare in Kira ki"
"Ya shirye shiryen biki?"
"Lafiya kalau, nace wa Rufaida Zan zo duba biki tace tana Miko gaisuwa"
"Amarya Ina amsawa sosai, ka gaishe ta"
"Kinga tunda da hijab Kika fito mu tafi kawai, we are going out"
Zaro ido tayi tana Kallon shi shiko sai murmushi ya ke Mata.
"Muje Mana da wani Abu ne?"
"Dr Ina zamu je? Kuma ma ai ban fada wa masu gidan ba"
"Munyi magana da Mustapha"
"Toh Ina za mu je"
"Zaki gani kedai"
Bin shi tayi, ba ta gane inda suke ba sai da tagan su a bakin garkuwa hospital, "sorry I have to check on a patient ki bani minti goma"
"Asibiti nawa kake aiki Dr?".
"Many, Zo ki rakani ma" ba musu ta biyo shi. A haraban asibitin su ka hadu da wata Nurse. Ganin Dr Fahad ya gaishe ta ya sa Suhaima tsayawa ita ma ta gaishe tan "Ah doctor Amarya ka kawo Mana ne?" Da fara'a tayi maganan.
"No Dr kanwata ce wannan"
"Oh Allah sarki! Sannu beautiful lady" ita dai smiling kawai ta Mata kafin su ka karasa cikin ward in da zai duba patient in.
Wani Elderly man ne akan gadon, ko da Dr Fahad ya gaishe shi Nodding kawai yayi. A hankali Nurse in da ke tare ya radawa Dr Fahad. "he is not hearing clearly but he pretends to be well" murmushi Dr yayi.
"Baba me ke damun ka right now?"
"naci abinci Mana Dan Nan" da mamaki Suhaima ta bi tsohon da kallo.
"Da kyau, am ina ke maka ciwo yanzu"
"Na ci na ci abinci Mana ba Zan muku karya ba ai ko, Tun dazu abinda kuke tambayan mutum kenan" cike da baccin rai ya karasa zancen. Dafe Kai Dr Fahad ya yi, he have no idea ya zai bullo mishi.
"Where is his guardian" ya tambayi nurse in.
"Sir shi ya kawo shi Amma he left since, he complained about the same thing, shi ma ya fada min Bai Jin sosai, Yana ta tambayan shi Amma Bai fada mishi me ke damun shi"
"So why do you call me? I thought case in field Ina ne"
"No sir, all the doctors here are in the Theater room, Kuma Kai kadai ne Zan kira ka Zo that's why, pardon me sir"
"I have an idea" Suhaima tare da mikawa Dr Fahad hannu.
"Me za kiyi"
"Watch and see, pass me the stethoscope"
"Young lady you are not a doctor"
"I know Kai Dai ka bani" Mika Mata yayi ya tsaya Yana Kallon ikon Allah.
Ear tubes in ta sa mishi a kunne, Sannan ta dago chest piece wurin bakin ta. "Baba ka na jina" kallo tsohon ya bita dashi har da murmushin gamsuwa "sosai ma kuwa"
"Ko za ka iya fada min me ke damun ka?"
"Haba ko kufa da Kun ishe ni akan abinci" murmushi tayi kawai ta mikawa Dr Fahad su ka cika gaba da magana. shi Kan mamaki ma ya Hana shi magana har sai da su ya gama duba patient in tukunna su ka bar asibitin.
"Am so suprised like a wani wuri Kika samo wannan idea in"
"Don't you know I was a medical student you never asked"
" Seriously? I can believe this. Amma kin gama karatun?"
"Nagama, Housemanship ne dai banyi ba"
"Am now more interested in knowing who really are you"
"Suhaima Adam Bello, a lady with full of mysteries. I have a long story by the way"
"I will love to hear..." Ringing in wayan shi ne ya katse maganan tasu, ganin Wanda ke Kiran ya sa shi dole ya dauka. Ummin shi ce sun Dade suna magana ta fulatanci, gabadaya ran shi ya baci kaman zai sa ihu su ka Isa haliems.
Kala Bai iya furta ba bayan ya gama wayan sai ko abubuwan da ya musu ordering.
"Sorry Fa, actually cinema na kawo ki kiyi kallo, you must be bored indoors always"
Nodding Kan ta tayi in affirmative "surely, nagode sosai but let's go back, you are not in a good mood" ba ta jira me sai ce ba tayi saurin Mikewa. Bai San sanda ya rike hannun ta ba, laushin Mai hade da shock in da yaji ne yasa yayi realizing abinda yayi "am sorry please Amma ki zauna" saurin zaman tayi tana Kallon shi.
A hankali ya fara Magana though jikin shi har rawa ya ke. Ruwa Suhaima ta Mika mishi ya Sha kafin ya cigaba.
"Ban San meyesa nake sharing personal life Ina da ke but whenever I do I felt comfortable" Dan Jim yayi kafin ya cigaba Ina son in fasa auren Rufaida Amma I can't saboda parents inta ga Kuma Ummi na on the other side. I need an advice from a lady this time other than Ummi and Dada, I got attached Suhaima I think I've start to like you. Ki bani shawara even though ban sanki ba ban San kowa naki ba still zuciya ta ta aminta da addini da kyawawan halayen ki, Am sorry if I may sound offended but I think i have a strong feelings for you"
Turus tayi tana Kallon shi cike da mamaki, seriously she never expect this from him. How can't he even love her? Ba shakka halayen ta ke rudar shi da Kuma situation in da ya ke ciki. Dr Fahad a yanzu ko shakka bbu wani jigo ne a rayuwarta sai dai Kuma ba ta wannan fannin ba domin kuwa zuciya ta a rufe take da ko wani irin soyayya na Dan Adam illa mutum dayan da ta ke da tabbacin ba zai taba iya fita a cikin ta domin an halicce sa ne domin shi.
Shirun da tayi ne ya bashi daman cigaba da maganan shi ko ince labarin Rayuwar shi.
Mahaifin Rufaida wan Mahaifi nane uwa Daya uba daya. Mahaifin nata da muke Kira Baffah yayi aure Mahaifiyar ta wato Dada shekaran su Biyar da aure Amma Allah Bai azurta su da haihuwa ba. Dada bafulatanar Gombe ce, mace ce Mai mutunci, kirki, hankali da sanin yakama ta, kyawawan halayen ta shi ya jawo Mata soyayya a cikin dangin mahaifan maza kowa alfahari ya ke da ita. A shekaran da su ka cika biyar da auren Abba wato mahaifina ya auro Ummi. zuwan shi Yobe service ya hadu da ita. Ummi na mace ce Mai zafi ga Kuma zuciya irin ta bafulatanin mutum. Still tana da kirki Amma sai dai ba ta Kama kafan Dada.
Zaman lfy ne tsakanin su da Dadan da dukkan dangin Abba na. Bayan shekara daya ta samu ciki na. Tun Ina ciki Abba ya yanke Shawaran bawa Dada da Baffah ni ba Dan komai ba sai dan irin tausayin Dan uwanshi da yake, mutum ne Mai matukar son haihuwa Amma Allah bai bashi ba. Duk Yana wannan Shawaran ne ba tare da ya sanar da Ummi ba sai bayan an haife ni ya sanar Mata, Nan ta ke Ummi ta ki amincewa, Tace ba yanda za ayi a rabata da Dan ta na fari domin ko Ummi ko kunyan Dan fari da fulani ke ji ita ba tayi. Ba ta yadda cewa Abba dagaske ya ke ba sai bayan an dawo Dani daga Yobe, can ta Kai ni yaye wurin mamanta har sai da nayi shekara uku aka maido ni. Wata na daya a gunta Abbah ya Kara tuna Mata kudirinsa. Fir Ummi ta nuna ba ta San zancen ba don haka Abba ya share sai bayan kwanaki ta fita Unguwa ya hada kayana gabadaya da ni ya kaini gidan Baffah inda ya sanar mishi kudirinsa. Dan farinciki Baffah har kukan murna yayi haka ma Dada har sujada tayi ta gode ma Allah, yanda ta rungume ni ko kaman za a kwace ni daga gun ta.
Abbah ko kwata kwata ba su wanye ta lfy da Ummi ba har ya kai da Rantsuwa ta yi sai ta je ta dauko ni, cikin fushi Abbah ya ce Mata matukar ta je gidan wan shi da niyar dauko ni shi Kuma a bakin auren ta. Rigima su ka you sosai Amma Bai hana Washegari Ummi ta je gun Dada dauko ni ba. Ba irin kwantar Mata da hankali da Dada ba ta yi ba Amma Sam Ummi ta ki ji, Dada na kuka ta dauke ni ta Bata saboda Ummi ba rashin kunya ta Mata kawai dai ta bukaci a Bata nine Mu koma gida.
Hakan yayi sanadiyar Rabuwan auren su. Dani Ummi ta tafi kolere Amma fir iyayen ta suka ki su ka maido ni wurin mahaifina Wanda ya maida ni gun Dada. Tun daganan Ummi ta fara kin Dadan sanadiyar raba ta da Danta da Kuma auren da ta ke matukar so. Abbah ya Sha so ya maida ta Amma fir taki amincewa a cewarta sai dai in ya yarda zai maido ni hannun ta.
Ba karamin gata na samu gun Dada ba, ba irin kaunar da Bata nuna min ba fiye ma da Ya'ya'n da ta Haifa. Ina Five years ta haifi Aliyu bayan shekara biyu ta Kara haifan Sadiq tun daga Nan Kuma sai bayan wani five years in ta haifi Rufaida. Allah yayi ni da son kanwa mace saboda haka tunda na kyalle ido Naga Rufaida a gida mu na ke matukar kaunar ta, tare ma mu ke rainon ta da Dada" dan dakata wa yayi yana murmushi da alamun ya tuno Lokacin ne sannan ya cigaba. "Kusan Nina raini Rufaida don kullum tana wuri na. Ko da ta fara magana da suna na ta fara bude baki. Ya fad, Nina sa Mata Faidah saboda a cewata yafi kama da suna na. Ko bayan da aka haifi kannen ta Mata still na fi shakuwa da ita duk abinda na samu to tabbas rabi da kwata na Rufaida ne. Gabadaya yaran gidanmu tsoro na suke ji saboda bana musu wasa har ko su Aliyu da Sadiq Amma Banda Rufaida don in har suna son abu guna ma ita su ke aikowa."
"Ta San cewa ba iyayen ta bane su ka haife ni saboda yawancin hutu Ina zuwa hutu kolere har bayan Ummi ta yi aure a Abuja ban daina zuwa ba daga Yoben har Abujan. Ina tausayin Ummi na saboda irin son da ta ke min fiye da duk wani da da ta haifa a duniya. Musamman ta ke zuwa Taraba ganina Amma ba ta zuwa gidan Dada sai ta je gun Goggo Fatume kanwar Su Baffah ita Kee zuwa ta dauko Mata ni har sai ta tafi a maida ni. Tun Ina karami Dada ta sanar dani ita ce Mahaifiya ta hakan ya sa Nima na taso da soyayyar ta a raina. Ba abun duniya da Ummi na ba ta min har bayan mun dawo Kaduna a sanadiyar transfer inda akawa Baffah, Abbah ko daman ya Dade Yana aiki a Abuja.
Ina final year a secondary school Iyayena su ka dawo da auren su bayan Allah yayi ma mijin Ummin rasuwa. Ya'ya'n su biyu duka Mata, Shaheeda da Zahra sai Kuma bayan ta koma gidan Abbah ta haifi Fu'ad, Mukhtar da Rukayya. Akwai Matan Abban da mu ke Kira da Mami ita Kuma Ya'ya'n ta uku. Sulaiman, Abdallah da auta Mamah.
Ko bayan Nan Ummi ta nemi in koma Abbah ya ki zancen ba dan ta so ba ta hakura.
Alaka ta da Rufaida ko sai abinda yayi gaba, shakuwar mu ko har ta wuce misali kowa kwatancen mu yake. Ban son Lokacin da na fara son ta ba" da sauri ta dago ta kalle shi, daga Mata Kai kawai yayi sannan ya cigaba "Tun Ina karami ake tsokana ta ko Yar gida za ayi ne? Sai dai kawai inyi murmushi. Tun ana fada Ina murmushin har ban son Lokacin da na fara Jin maganan nasu na Zama a kwakwalwa ta ba, har ya ke da na sawa Raina ba ni da wata Mata a duniya inba Rufaida ba. A bangaren ta ko a nawa shirmen gani nake banda matsala domin nasan ba za ta ki ni ba. Aliyu kadai yasan da wannan sirrin nawa domin duk wata shawara wurin shi na ke nema duk da na girme mishi Amma shi mutum ne Mai matukar hankali da sanin Yakama ta just like Dada, sosai ya dauko ta ta wannan fannin.
A India nayi karatun likitan, gabadaya Baffah yayi sponsoring karatuna da komai da komai. Tsakani na da Daddy ko sai dai kyautatawa Amma komai nawa Baffah ya tsare min. Bayan tafiya ta Rufaida har ciwo ta yi, ba ta wa kowa magana sai da Dada ta Kira ni na dinga lallashin ta kuwa. Still kullum sai na Kira Dada da murnar ta za ta amshi wayan mu yi ta hira da ita, musamman saboda ita na ke dawowa hutu duk shekara haka kuma tsaraban ta sai yafi na kowa yawa.
Bayan Naga karatuna sai da na tsaya one year nayi wani course kafin na dawo Nigeria Housemanship. A ABUTH shika nayi. Duka duka ban cika 1 month da farawa ba Ummi na ta fara min maganar aure, Kai tsaye nace Mata Kar ta damu kwanan zan je Abujan mu yi maganan. Ni fa duk ana wa zaton Zan jira Rufaida ne ta gama secondary School muyi aure, Lokacin ta na SS3 ma ne.
Tana gama secondary da kaina na siya waya Mai kyau na bata as gift. Ba karamin farin cikin samun wayan tayi ba Saboda Baffah Bai taba barin ta ta rike waya ba. Ba dadewa ba ta samu admission a ABU Zaria su ka bata Nursing, Ni na Mata registration da komai da komai hakanan Lokacin na kusan gama Housemanship Ina Saboda haka na yanke Shawaran yi residence ina a Nan ABUTH.
A Lokacin Ummi ta fara matsa min da batun aure abun Kuma kaman hadin baki Baffah, Dada da Abbah duk su ka fara min maganar duk da dai shi Abbah hanya hanya kawai ya ke min Bai fito fili ya fada ba.
Ba Wanda ya San abinda ke zuciya ta a Lokacin sai Aliyu yayanta saboda haka Kai tsaye na tunkare shi da zancen ganin Rufaidan har ta fara University.
"Haba Ya Fad ai Nasha ka fasa ne" ya fada cike da tsokana, harara na bishi dashi ba shiri ya natsu.
"Afuwan Yaya Fahad Amma ni ai da Naga har ka Bari ta fara makaranta ba Ka yi zancen ba na dauka ka canja ra'ayi ne. Gsky gwara ka tunkare ta tunda wuri kafin wani ya hure Mata kunne ta ki sauraran ka" wani irin tsoro naji saboda maganganun Shi, a Lokacin na nufi zaria. Tun akan hanya na sanar da ita Ina nazo za muyi magana da ita, ita ma ko cike da murna ta ke fada min akwai labarin da zata bani. Nan ta ke naji gaba na ya fadi...
Da la'asar na isa Zaria, Kai tsaye na wuce samaru. Sai da na tsaya nayi Sallan la'asar kafin na nemi Rufaida. A mota na dauke ta Mika wuce wurin Dam in da ke cikin ABU in, Dama tun can ni Allah yayi da so wuraren shuke shuke, they always gives me comfort. Sai da muka gaisa sannan na taso Mata da zancen da nace Mata zamuyi. "Oh! Ya fad am dying to tell you this" da mamaki na bita da kallo, Kar de itama tana Jin abinda na ke ji but she gave the suprise of my life "Ya fad na yi saurayi har yace Yana so ya je samu Baffah" hmm! Ji nayi gabadaya numfashi na ya dauke for some seconds kafin ya dawo, har na fara hada gumi Lokaci da ya annurin fuskana ya dauke. "Are you not happy? Am getting married fa"
"Faidah am not" Kai tsaye na fada mata "am disappointed rather"
"Ya fad ba Ka son inyi aure ne?" Kaman za ta yi kuka ta ke magana "Ya fad Yana Sona fa and he even promised to take good care of me, I mean he is very nice and I love him too" Ya Isa! Na yi saurin dakatar. "Haba Faidah, are you telling me baki taba sanin Ina son ki ba? I thought its even a mutual feeling" fara'ar fuskan ta gabadaya daukewa yayi tana dubana da mamaki "Kana so na fa kece? Haba ya Fahad you are my brother"
"And? Ai kinsan ba haram bane right?"
"But ya Fahad I can't marry you, Kallon yayana ya ke maka who is always there for his little sister and nothing more." To say i was dumbstruck is an underestimate wlh. "Meaning?" I asked her.
"I love someone else and we are even talking of taking our relationship forward" kasa cewa komai nayi for I can't still believe I was rejected on the first trial, Rufaida rejected me.
Miyan baki na gabadaya kafewa yayi, a hankali nayi yunkuran jawo ruwan da ke kusa Dani nayi gulping. And can you believe that Rufaida kuka ta ke, I feel like slapping her don ji nake dama ni na samu nayi wannan kukan nata da nagode. Kala ban kara ce Mata ba har tayi kukan ta ta gama sannan na Mike nace Mata ta tashi mu tafi. Har na sauke ta a hostel ba maganan da ya shiga tsakanin mu sannan na koma hotel in da na sauka. Da da dare ta turo sms Wai tana bani hakuri claiming that she is taken. Wlh ban taba tunanin Faidah za ta min haka ba. Abinda yayi shattering kyakyawan alakan mu da ita kenan. Da safe na koma Kaduna, Aliyu ya fahimci halin da na ke ciki don Haka na warware mishi halin da ake ciki. He insists on talking but still yarinyar Nan ta bijire. Har ta gama University Saurayin nata Bai turo ba, kullum sai an dauko magana sai ya rushe tunda ga Nan na gane yaudaran ta ya ke you but I can't tell her saboda gabadaya ma maganan arziki daina shiga tsakanin mu yayi sai ko in ya Kama, Kai gaisuwa ma sai ta ga dama ta ke min saboda gabadaya harkar ta na fita na daina sakan Mata fuska, I was so disappointed in her. I can't still get to tell her he is getting married in two weeks time. Recently, Dada ta samu labari which I believe Aliyu ne ya fada Mata, ita ta gaya wa Baffah and they arranged the marriage. Ina so ince musu na hakura but Baffah ya rantse sai anyi sai dai ko mu mutu, that's why I give in but I still don't think ina son Rufaida kaman da even though we agreed on making it work.
So Suhaima this is my story. can I hear yours?. Kiran Sallan magreeb ya ji. Murmushi su ka saki a tare "I guess it will be for another day then, mu je in ajiye ki gida ko, are you even comfortable living with them" nodding kanta tayi "okay remember am just a call away and thats remind, I bought you a phone, I will send it tomorrow"
"You shouldn't have done that"
"Shhhh" ya fada making her chuckled "remember you are my sister" and he never talks about the confession he makes earlier on....
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top