Babi na goma sha daya
Ranar yau ta kasance ranar juma'a. Saboda ruwan saman da ake ta shararawa ya sa ba lallai ka gane cewa juma'an bane. Ruwan ma an dade ba ayi shi ba. Da ke ana cikin karshen october hakan ya sa ake sa ran ruwan bankwana ne ake yi, lokacin kaka na gab da shigowa kenan. Yaran gidan gabadaya na makaranta sai su Anisa da Suhaima kawai. yanayin garin ya sa duk su libge akan gado, har wurin Goma da rabi sannan su ka mike, shi inma Mommy ce ta musu waya su tashi su ma Baban su breakfast, zai shigo garin yanzu daga Abuja.
Bai dade da shigo gidan ba su ka gama. Anisa ce ta hada komai ta wuce dashi side in shi.
By 11:37 am, karan siren ya fara tashi. Da ke Unguwa ne da mutane ke hulda akan hanya sosai ba kaman GRA ba, jama'an wurin ne su ka fara mamakin mai ya kawo motocin yan sandan dayawa haka cikin layin? Shin lafiya? Wani mai laifin kuma su ke shirin kamawa. Haka su ka dinga tafiya har kofar gidan Engr Usman alkali, inda duk su ka ja birki. Wani karamin dan sanda ne yayi saurin sauka daga motan farko yayi wurin babban odyssey in da ke tsakiya. Sai da ya sarawa ogan nashi "Sir, how do we get in?"
"Get me the door" ya amsa, dan sanda yayi saurin isa ya bude mai kofan. "Get the boy, dashi za mu shiga" Faroukh ne ya fito daga cikin motan, Yan sandan na bin shi a baya. kai tsaye ya musu jagora zuwa cikin gidan.
Engr na zaune a falon shi yana tsakiyar breakfast ya fara jin siren in Polisawan na tashi. Ba abinda ya kawo a ranshi sai yanzu da ya daga kai, Faroukh ya hango suna faman shigowa cikin gida shi da polisawan kusan biyar. Ai bai san da ya ji kafafuwan shi ba, da kyar ya iya sa takalma yayi waje, domin jin me ya hada danshi da polisawan nan.
Idanuwa ya zuba musu domin gano dalilin shigowar su cikin gidan shi. Faroukh ya zubawa idanu yana kokarin gano wani tashin hankali akan fuskan nashi, sai dai sadda kan shi kasan da yayi bai ba wa mahaifin nashi daman hakan ba.
Hannu babban police in ya mikawa Engr, bayan sun gaisa police in ya gabatar mishi da wani takarda. Engr dai har yanzu a rude yake. Ga faroukh kam har yanzu kanshi na kasa yaki yarda ya kalli mahaifin nashi. Har sanda Engr ya bude takarta, ya ga shaidan kotu ya dauka Faroukh ne ya dauka mishi magana.
Tabbas arrest warrant ne, sai dai ba sunan Faroukh bane a jiki. Suhaima Adam Bello ya gani a rubuce. "An sanar mana cewa tana gidan ka, we need to take her for investigation" Shi dai Engr har yanzu shakku ke ranshi. Shin in ma yarinyar su ke nema me ye hadin ta kuma da Faroukh. Murya ya bude ya kwalla wa Anisa kira. Da sauri ta fito, sai dai tun kafin ta karaso wajen ya ce mata ta kira mai suhaima tazo waje.
Tun daga bakin kofa da ta hango su ta san abinda ya kawo su, ko shakka ba tayi ita su ke nema, balle kuma ma ga Faroukh a tsaye tare dasu. Gabaday jikin ta rawa ya ke, kusan uku ta ke tuntube jiki a sanyaye ta karasa wurin su "Ita ce wannan?" Engr ya tmby, Sergeant maccen da ke wurin ne ta fiddowa Engr hoton da su ka zo dashi domin tabbatar mishi wacce su ke neman ce.
"Suhaimaa" Engr ya kira cike da mamaki a idabuwan shi. Kanta a kasa yake, tana jin zuciyan ta kaman zai fito tsabagen yanda ya ke dukawa da sauri sauri "na'am Baba?"ta amsa.
"Me ke faruwa?" Ya tmby yana kallon ta da kuma yanayin da ta shiga, gabadaya a rikice ta ke sai dai duk da hakan ba ko alaman hawaye a idanuwan ta. Hakan kan shi abun tsoro ne.
Tana shirin ba da amsa taga Ogan nasu ya mika wa maccen handcuff. Kaman a mafarki ta fara jin yanda ake karanto mata marinda right "You are arrested for the suspicion of murder's attempt of Zayd Almansur. You have the right to remain silent. Anything you say maybe used against you in the court of law. You have the right to consult a lawyer, if you can't afford one will be appoint to you if you so desire"
Rayuwa kenan, ashe sa ka wannan abun yana daga cikin kaddarar rayuwa ta, wani irin cunkushe wa taji zuciyan ta yayi lokacin da Yar sanda ke kokarin kamo ta su bar gidan. Kallon fuska Abbah tayi, har yanzu tambayoyi ne a bakin shi, maida idanuwan ta tayi kan Faroukh "Faroukh ban aika ta ba, wlh ban aika ta abinda kake zaton nayi ba, ba ka taba tmby na abinda ke faruwa fa, shine za ka sa a kamani?" Muryan ta na rawa sosai ta ke furucin yayin da yar sanda ke kokarin jan tafita daga gidan. Anisa kam duk ta rude sai faman hawaye ta ke tana kallon Faroukh, taji zancen kuma tasan faroukh in ne yayi abinda ya sa aka kama Anisan, har yanzu dai kasan ya ke kallo. Suna fita daga gidan Anisa ta saki kara ta rushe da kuka, Kallon ta Engr yayi, tsabagen rudewa sai lokacin ya tuna ya kamata ya san station in da za su kaita. Da azama yayi wajen, kusan duk sun gama shiga motan sai mutum daya ne ya rage.
"Station?" Kawai yace mishi. "Ba case in garin nan bane ba, Abuja za a kaita."
"Station in ina a Abuja?" Engr ya kara tmby.
"Wlh ban sani ba, DIG ne ya turo mu" abinda kawai ya fada kenan ya shige motan su ka wuce.
Daidai sanda su ke fita layin motan mommy ya kunno kai. Sai da ta tsaya su ka wuce sannan ta shiga. Isan ta gida kuwa ta iske Engr na ta faman yi wa Faroukh ihu ya ki magana, Anisa ko sai kuka ta ke ta yi.
"Lafiya? " Abinda bakin mommy ya iya furtawa kenan, sai dai ba ta samu wanda ya iya ba ta amsa ba. Engr kokarin kiran connections in shi ya ke domin jin asalin abinda ke faruwa.
"Faroukh ba zaka min magana ba ko? Me ye hada Suhaima da Zayd Almansur"
"Baba fa..." Kaman zai yi magana sai kuma ya kasa yana bin Anisa da kallon gargadi, girgiza mishi kai tayi ta juya wurin Mommy.
"Ku min magana me ke faruwa? Ina Suhaiman?" Mommu ce ta kara magana tana bin ko wanne su da kallo ganin yanayin kowa ya canja, akan Anisa ta tsaya.
"Mommy sun tafi da ita, Yan sanda, Ya Faroukh yazo dasu" Anisan ta fada tana kokarin kore kwallan da ke zubo mata.
"To me tayi mishi?" Wannan tmbyn kam is more like babu wanda ta ke mawa.
"Mommy daman ranar naji suna magana yana cewa sai ya tona mata asiri, ita kuma tace ya tona in daman me ya ke jira?"
"Ko shine ba zaki fada mana ba sai yau? eh?" Tsawan da Engr ya mata ne ya tsorata Anisa sai da ta ja baya. Mai da idanuwan shi yayi kan Faroukh, yace wa Mommy "ki kira Musty shi ya mishi bayani" yana fadin hakan yayi hanyan dakin shi, dan yanda ya ke ji in ya cigaba da tsayuwa yanzu ya kai kasa.
Bangaren Suhaima kuwa har su ka isa Station zuciyan ta a cunkushe ya ke, ba zafi kuma ba sauki. Ganin abun ta ke tamkar a mafarki, duk da ta san watarana hakan na iya faruwa tunda ta bar Abuja, duk da haka ba ta shiryawa hakan ba. Ba wanda ya hantare a yan sandan, sai dai masu girgiza kai sina kiran "mata akwai iya daukan wa kansu rigima" ba minti talatin ba ta cika a wurin ba su kayi Abuja da ita. Ba wanda tayi wa magana, ba wanda ta ma musu ko kallon banza, ba wanda ta samu matsala dashi har su ka karaso garin Abuja.
A lokacin taji wani nauyi a kirjin ta, Kallon garin kadai yana tuno mata da abubuwa mafi muni da ta aika ta rayuwarta. Shin yanzu kuma wani irin kaddaran rayuwa zai juya mata a cikin garin da rayuwa bai mata adalci ba? Da duk zuciyan ta ta ke jin kiyayyar kasancewa a cikin garin. Ina ma, bai da wani amfani, shiyasa ma ba tayi shi ba tunda mai afkuwa ya riga da ya afku. Sai kuma a fuskanci gaba kawai.
Police headquarters su ka fara zuwa da ita, Wani babban dan sanda ne ya fito suna ganin shi duk suka sara mishi. Kallon ta yayi yace musu "itace wannan?" "Yes sir" su ka amsa mishi. "Yan mata ke ko wani irin masifa ne ya kai ki?" Bai jira amsan ta ba ya girigiza kai "a wuce da ita station a fara investigation" amsa mishi su kayi, ba wanda da suka taho da ita daga kaduna bane su ka wuce da ita. "Wannan ce Almasur su kayi charging?" Wani ya tmby aka ce mishi eh.
"Tabdijam" kawai yace ya juya.
Suna isa aka tura ta wani cell, ita kadai ce a wurin. Tun daga lokacin kuma ba wanda ya kara bi ta kanta sai wani shegen abinci da su ka kawo mata, kamshi shi kadai ya tada mata hankali balle a kai da ganin shi.
A kaduna kuwa zaune Faroukh ya ke a gaban mustapha yana kokarin mishi bayani "Uncle Musty yarinyar nan munafuka ce wlh, Zaman ta a nan ba alkhairi bane, wlh matsala za ta ja mana shiyasa na tura ta inda ake neman ta kawai" harara shi Mustapha yayi "Faroukh ban sa iskanci za ka gaya min me faru ko kuma ince me ke faruwa?"
"Uncle, Maigida na Zayd Almansur ai ka san shi, Wlh shi tayi kokarin kashe wa ta gudu tazo garin nan, i mean na san ta tun a Abuja" kallon shi Mustapha yayi kaman yana nazari, can ya girgiza kai "Ba zai yiwu ba Faroukh, tayi attempting kashe Almansur kuma ta kwana lfy har tayi watanni a garin nan"
"To ni kuma ai ban san me zance maka ba, investigation dai ake yi an fara neman ta, ni kuma na saukake musu wahala na fada musu inda ta ke da suka zo investigation company inmu" shiru Mustapha yayi yana kara karantar Faroukh in "wai to tsaya ka santa tun a Abujan ne?"
"Na santa, ita ma ta ma Almansur in aiki a drink shop inshi. Kawar Budurwa shi ce kafin ta dawo budurwar tashi, i've seen some of her true colors, zaman ta tare damu hatsari ne Uncle"
"Zan binciko dai" Mustapha ya fada hade da mikewa, kallon shi Faroukh yayi a ranshi yana ayyana ya rasa me yarinyar nan ta ke wa mutane, ko ina sonta ake duk da yana kokarin fahimtar da mutane hatsarin da ke gare ta. Ko ma me ta ke musu shi kam bai kama shi ba.
Ko da Mommy taji abinda Faroukh ya fada wa Mustapha, Fada ta hau mishi sosai akan meyesa tun tuni bai fada musu ba, shin in ma wata muguwan ce da ta musu wani abu kenan. "Amma Faroukh da ta yarana wani abu da ka cuce ni wlh" ta fada tana mai aikawa Faroukh kallon banza. Mustapha da Anisa ko mamakin wannan furucin na ta su kayi. "Mommy Suhaima ba abinda za ta ma kowa, ni na nasan ba ta aika ta abinda ake zargin ta dashi ba wlh" da kuka ta karasa zancen nata.
"Kaniyar ki Anisa kinji, ba ki da hankali ne? Yarinyar da ake zargi da kisa? Kuma baki ji abinda Faroukh yace ba? Tuntuni daman ba da zuciya daya ta ke zaune da zayd in ba? Wacce aka ce ta kwace wa kawarta Saurayi. Ke baki san dan Adam ba ko? Ba kisan munafunci mutane ba ko? Tun farko meya hana ta fada mana asalin wacece ita?" Yanda mommy ta ke magana da yanayin fuskan ta zai tabbatar ma ka gaskiyan abinda ta ke fadi har ranta, tana jin zafin barin ta da Anisa da ta dinga yi da sauran kannen ta, daman duk karatun da ta dinga koya musu duk pretending ne kawai.
"Bakomai in sha Allahu Anty tunda ba ta musu komai ba. Yanzu dai shari'ah za ta tabbatar da gskyn matsalan." Mustapha ne yayi maganan. Shi inma da hararan ta bishi "Eh lallai yanzu na gane dalilin da yasa ba ka taba gano matsalolin matarka ba sai da ka san yarinyar nan. Gashi nan daman halin ta ne raba masoya ai. Nima ban san meye riban ta ne zama damu ba, tabbas tana da dalili. Ba kaji mai Anisa ta fada ba ranar? Tace wa Faroukh ta san me ta ke, ba hakanan banza ta zauna a gidan su ba?"
"Amma Anty baki ganin shima Faroukh in ya hada da wani ganin dama tun can bai son yariny..."
"Ya ci riban me ke nan? Kaga lil bace min daga gani, akan macce kana kokarin aiba ta min da ko?" Kwafa tayi sannan tayi hanyan dakin ta ba tare da ta bashi daman kara magana ba. Inji masu magana su kace wai mai da wawa.
Mustapha na fita daga gidan ya kira numban Dr Fahad domin sanar mishi abinda ake ciki. Sanar mishi yayi inda za su hadu suyi magana. Open spaces ne wurin, bai dade da isa ba sai ga likitan nan ya iso. A daddafe su ka gaisa kafin Mustapha ya fara koro mishi bayanin abinda ke akwai.
Shirun dole Dr Fahad yayi, gabadaya ma ji yayi notunan kanshi sun kwance. Ko da Faroukg ya taba tare shi ya mishi magana bai wani kowa komai ba akan abun. Kawai ya dauka rigima ce tasu ta matasa ko wani banzan ra'ayin shi na daban, shi har ga Allah ma yafi zaton ko al'amarin ne na kishi, yana son ta.
"Me kake ganin za mu yi Dr" Mustapha ya katse mishi dogon tunanin bala'in da ya shiga. "Al'amarin ne da daure kia Barr, barin ma da bamu san komai akan zancen ba"
Wani dan Nazari Barr yayi sannan yace "Ni ina ganin kaman akwai abunda Faroukh in ke boyewa ne gsky"
"Da gskyn ka ma, Amma yanzu ina ganin abunda yafi dacewa shine mu fara sanin inda ta ke sannan mu ji daga bakin Yan sandan. Kotu za a shiga ko miye?"
"Nima nayi tunanin nan Dr, Ina so inyi magana da Engr ne inji yanda zamu fara bullowa abun, saboda zai fi ni connection."
"Ehmm hakan za ayi, ni ma dai zanyi kokarin yi wa Abbah na maganan da ke shi yana ma can Abujan ne" tattauna wan mafita su ka cigaba dayi kafin can Barr yace "abin nan da mamaki, a halin Suhaima da na fuskanta ba alaman za ta iya hallaka ko dabba ma balle mutum. Sai dai ance kar kayi saurin yarda da mutum"
"Tabbas abin akwai daure kai. Amma ni kam ina tunanin ko hakan ya faru to tabbas ba banza ba, Ruwa fa ba ya tsami a kasa. Kila wani abun shi Al-mansur ya mata and she try protecting herself, i mean self defence. Lokacin da accideny in da mai dakin ka ai nayi witnessing. Is like ba ta san inda kanta ya ke ba shigowa titin kawai tayi ita kuma tana gudu"
Barr na shirin responding call in Engr da ya shigo ya katse shi. "Bara nayi picking call in nan please, Engr ke kira" nodding Dr yayi, yana jin gabadayan shi wan iri, labarin da barrister ya bashi ba karamin girgiza shi yayi ba.
Mustaphan kam bayan ya amsa wayan Engr, shi ma dai maganan ce ta Suhaima "na samu daman yin magana da Commissioner of police na nan Kaduna, Ya sanar min bai san kan abun kwata kwata amma tabbas Zayd in bai da lafiya, suna asibiti a indian shi da mahaifiyar shi. In dai ya binciko zan kara waiwayen shi"
"To shknn Uncle, mu ma nan muna kokarin binciken ne. Yanzu haka muna tare da Dr in da yayi treating inta bayan accident in" yanda ya sunkuyar da kai ya ke maganan zai tabbatar ma yanda ya ke ganin girman wanda su ke maganan. Magana daya biyu su kayi kafin yace mai "Antin is so scared, ka san su yan boko halin su daban yake, tana insisting wai mu bar maganan kawai tunda asirin yarinyar ya tonu. Don haka ka guji maganan a gabatan, we can't just leave the case bayan ta zauna a wurin mu, it can even implicate us balle ma Faroukh is somehow involve ai"
"To shknn Uncle ba wani matsala in sha Allah"
"Allah ya dafa mana" Engr ya fada kafin su kayi sallama akan inda wani abu su nemi juna kawai.
Labarta wa Dr yayi progress in da aka samu akan zance sannan ya ce "Tunda abu ina tunanin kaman court case ne, zan yi kokarin tabo wasu collegeau ina da ke can Abujan
Na'am Dr yayi da shawaran, sun dan jima suna kara tattaunawa akan al'amari. Dukkan su dai abun ya rikita su barin ma Dr Fahad, da su kayi shakuwa na musamman. Duk da ko case in ya shafi yaron babban mutum kaman Al-mansur amma ba su jin za su iya barin shi, sai dai in dumu dumu aka kama ta da lafiya, ba ma sa fatan haka, suna mata kyakyawan zato. Mutum irin Suhaima akwai dadin Zama.
Hatta Maryam da ta ji zancen sai da taji wani iri, barin ma da taji case in da Al-mansur " Hmm ehm in dai sharri ake mata Allah ya fidda ta" ta fada cike da jinjina zancen "Ashe barin ta nan alkhairi ne da kilan harda mu za a kama" hararan ta Barrister "ke dai mimi akwai matsala, ko da ma wani abun ne shin ba gidan yayanki ta ke ba? Kuma ba ke kika fara insisting ta zauna damu ba? Kuma ke kika fara kade ta tun farko. Kinga ko a tsarin shari'ah a ma ke ma suspect ce"
"Ah haba Dan Allah bari mana" yanda ta zaro idanu waje cike da tsoro ne ya ba mustapha dariya, dole sai da ya dara yace "See you mijin ki na lauya kina tsoron shari'a. Yanzu dai kawai mu taya ta da addu'a kuma mu mata kyakyawan zato tunda dai ba ta nuna mana wani kofa da xamu iya gasgata abinda ake zargin ta dashi ba"
"In sha Allah" maryam in ta amsa.
Ita kam Rufaidah ko da aka sanar mata cewa tayi kawai "Allah ya raba mu da munmunar kaddara" da ke ita ba gwanar surutu ba ce.
Slm, how are you guys? Ina fatan kowa lfy, Alhmdlh. So sorry i got so many issues da dole na tsaya fixing. Also sorry about the last update, it more of a mistake and i have to change it.
Nagode
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top