Babi na goma
Da Anisa, Anty da Suhaima su ka koma gidan Barr, dakin da Suhaima ke zaune Anty da Anisa su ka nufa a tare da ita. Anty tayi insisting dole Suhaima ta dawo nan gidan ta domin ba Yar bauta su ka samu ba Kuma tun an fara samun matsalan dole a kiyaye saboda gaba.
Maryam dai gabadaya jikin ta yayi sanyi sai bin kowa da ido ta ke ta rike haydar a hannun ta, suna shiga gidan Barr ya nufi dakin Hadiza ya kife Mata Mari ta sa ihu, sai da Anty ta Zo ta sa baki ya kyaleta. Rantsuwa yayi sai ta bar mishi gidan shi tana kuka ta hau hada kayan ta. Daman ko Bai sallame ta ba Anty na da niyyan hakan saboda Abbah ya ce a bar Maryam ta zaune ita kadai ta zauna gyara gidan ta in zata iya.
Ba abin ta da su Anty su ka Bari a gidan komai su ka hada su kayi mota, suna waje Suhaima ta fito daga dakin, gata Nan ne dai kawai ba Wanda zai iya fayyace halin da ta ke ciki don ita kanta ba Wai ta sani bane. A falo ta iske Maryam na zaune Kai a kasa idon ta ya ciko da hawaye. Gefen ta ta zauna sannan ta mika Mata hannu, jiki a sanyaye Maryam in ta Mai da Mata "saduwar Alkhairi Maman haydar na gode sosai Ina fatan Zaki yafe min abinda na Miki Wanda na sani da Wanda ban sani ba"
Muryan ta na rawa ta fara magana "Ehm ehm Suhaima ni Zan baki hakuri akan abinda ya faru, ki yi hakuri pls"
"Ban Zan taba iya rike ki ba Maman haydar, kin min alkhairi a rayuwa ta sosai nake godiya, kwanan Ina tunanin tafiya ma bara naje Anty suna jira na" nodding Kai kawai Maryam ta yi gabadaya ji tayi tana regretting action inta, gashi Barr ko Kallon ta Bai sake ba balle Kuma ta San ran zai Mata magana. Tana ganin ya je book shelf in shi ya dauka littatafai, ko bai fada Mata ta San Suhaima zai ba Saboda ita ce ma'abociyar son karatu.
Har Jin jikin motan ya je ya Mika Mata ta sa hannu ta karba hade da yin godiya, idanuwan Nan nashi sun kada sun yi ja, kallo Daya zaka mishi kasan he is hurt sosai, ita Kam Suhaima har wani tausayin ta ke ji. Anty dai ba ta kalle shi ba har ya koma cikin gidan nashi sannan ta ja mota su ka bar gidan.
Dakin Anisa Anty ta Mata masauki ba Wai don Basu da extra ba Aa, a ganin ta za tafi Jin Dadi zaman su biyu akan ace ita kadai ce.
Ko da Dr ya ji labarin komawan ta gidan Antyn, Bai nemi wani ba'asi ba don a tunanin tun farko ma Nan yakama ta ta zauna ba gidan yarinya kamarta ba dole a samu matsala.
Ko da aka fara events In bikin Dr Fahad da Rufaida, sau biyu ta je tare da rakiyar Anisa, faran faran Rufaida da Nabeela su ka Mata karaban hannu bi biyu, Dr kanshi ya ji dadin hakan sosai. Gabadaya he is busy ko da taje gidan bikin duka duka sau Daya ta ganshi shima gaisawa kawai su kayi abokan shi su ka Zo suka ja shi, sai dai ko in ya samu time ya kira ta a waya.
Ranar jumaa ana saukowa Daga Sallah aka daura auren Dr Fahad da Amaryar sa Rufaida hakan yayi dai dai da Lokacin saukan Faroukh daga UK, a Abuja jirgin su yayi landing so gidan su Abokin shi Zaid ya sauka sai da ya jira train in six na yamma sannan ya biyo zuwa Kaduna.
Suhaima da Anisa na shirya warmers Kan table su kaji ihun yaran gidan suna "oyoyo oyoyo ga Yaya Faroukh" Anisa murmushi kawai tayi dan ba wani dasawa su ke dashi ba, ya cika takura Mata komai tayi sai ya kwabeta, at times ji take kaman ya tsane ta ma. Sai da ya fara shiga dakin shi ya ajiye kayan shi sannan ya watsa ruwa. Direct Falon Abbah ya je sanin shi da Anty suna can, zuwa yayi ya gaida su kafin ya nufi wurin kannen nashi.
Suna zaune gabadayan su a Falon wasu na kallo wasu na assignment. Da gudu Kulsoom ta nufi wurin shi Aiko daga ta sama sannan ya ajiye ta, twins Kam sai murmushi su ke suka Mai sannu da zuwa, muhibba ko gefen shi ta koma ta zauna ya riko Mata hannu suna Hira. "Sannu da hanya Ya Faroukh" hararan ta sannan ya ce "ban so rike kayan ki" kala ba tace ba har ta gamawa Arif assignment da ta ke mishi sannan ta Mike ta nufi daki. Good five minutes ba tayi ba Kulsoom ta shigo dakin, Suhaima littafi ta ke karanta wa abinta. "Anty Anee ya Faroukh ki Kai mishi abincin daki" nodding kanta kawai tayi Amma kasan zuciyan ta mamakin takura Matan da Ya Faroukh in yayi ta ke duk da lokuttan da ya so Wasa ya Kan ja ta dashi. Dinning ta nufa ta hado abincin nashi ta nufi dakin.
Sallama tayi ya amsa Mata, waya ya keyi ga dukkan alamu Kuma da budurwar shi ce, ita dai ajiye abincin tayi ta yi gefe don ta San ko ta fita kwala Mata Kira zai. Ka ta hakura har ya gama wayan shi sannan ya juyo gare ta "Zuba min abinci Mana Anee Naga alaman ko murnar gani na ma baki yi right?" Ba abinda ta ce har ta gama zuba abincin ta Mike mishi, ga mamakin ta ko har da godiya ya Mata.
"Da gaske wancan yarinyar ta dawo gidan Nan?" Da mamaki ta kalle shi sannan ta ce "Ya Faroukh wa?"
"Ban sani ba yarinyar da ke gidan Uncle musty Mana"
"Wai Anty Suhaima tana Nan mana"
"Wani daki ta ke Zama?"
"Room Ina"
"You have to leave the room for her then" da mamaki ta dago Kai tana Kallon shi.
"Ko ma da yake bara na bi abin a hankali, Wlh ki kiyaye kanki da ita Kar kice Zaki dinga shishige Mata you never know who truly she is, tashi ki tafi" Bai Bata room in yin magana ba hakanan ta tashi ta Mike jiki a sanyaye.
Kwanan Faroukh biyar a gida Amma ko sau Daya ba su hadu da Faroukh ba sai ranar. Anty was so surprised da Suhaima ta fada Mata she is already a graduate of medicine, tayi tunanin enrolling to islamiyya sai dai Kuma Alhmdlh taji ta San addinin ta sosai, ga girki ma ta iya recipes kala kala and suddenly Anty become interested in knowing her story. Ranar tana tsaye a kitchen tana girki, Anty ta fita Anisa ma Kuma ta wuce computer school unknown to her Faroukh na gidan. Sai dai kawai ji tayi alamun mutum a bayan ta na Kallon ta, karfin halin juyowa Aiko su ka yi four eyes. Ganin yaki dauke idon shi cikin nata ya sa tayi saurin Mai da na ta kasa. "Sannu" kawai ta ce mishi ta juya ta cigaba da aikin ta. As she expected Bai amsa gaisuwan ba instead sai ya fara magana "Suhaima ba ki ji ko? I've warned you kin ki dauka" ganin ba tayi magana ba ya sa ya cigaba da nashi maganan "since ba ki dauki abinda na fada Miki ba let me tell this, am sorry but i have to expose you" cak ta tsaya sannan ta juyo ta kalle shi "I expect to did it soon Faroukh, I don't even understand me ye sa har yanzu ma ba ka dau action"
Tafa hannun shi yayi in an amazing way "Suhaima kenan wato ba Zaki taba canjawa ba Koh?"
Juyowa tayi Wannan karon tsab tana Kallon shi kaman yanda ya kura Mata idanu "a tunanin rashin wurin zuwa ne ya sa na ke zaune da ku F... ? As brave as you are ban yi zaton za kiyi wannan tunanin ba. Let me tell you F... Na tsaya ne saboda ayi ta ta kare, am tired of the game, enough is enough, na gaji hakanan saboda haka Ina Mai rokon ka Dan Allah Faroukh ka shigar da Karan Nan Haka Nan, in ma tausayi na kake ji please ka daina, don't you get it? Am tired of the whole world" ko kadan Faroukh bai yi mamakin kalma daya daga cikin zantukan ta ba because he expects it, sai dai bai tabbatar ba sai yanzu da ta furta da bakin ta.
"Kar ki damu, daman duniya ma ta gaji da mutane irin ki..." Jin da yayi kaman ana Kallon shi yasa yayi saurin juyowa four eyes yayi da Anisa ta kwalalo ido tana Kallon shi. "In ma kinji conversation inmu inji a bakin wani ki gani" ya fada tare da kwafa kafin ya bar wurin. Suhaima ta juya ta cigaba wa Kallon tsoro hade da mamaki, murmushin karfin hali ta kirkiro sannan ta ce "Anee kin dawo?" Nodding Kan ta kawai tayi kafin ta wuce daki.
Anisa kept giving them weird glances, sosai ta ja baya da shigewa Suhaima don gabadaya tsoron ta ma ta fara ji, ita kanta Suhaima ta lura da haka hakan ya sa tayi confronting in ta a daki. "Anee ki daina Jin tsoro na, I don't bite" girgiza Kan ta tayi sannan ta ce "Anty Suhaima me kike expecting Zan yi bayan ji abinda kuka tattaunawa ke da Ya Faroukh? Kin San shi ne Daman"
"I used to live in Abuja, a can na San shi"
Nodding Kan ta tayi alaman gamsuwa sannan ta ce "toh wani Abu ya shiga tsakanin ku ne"
"Kinga Anisa kwantar da hankalin ki ba abinda Zan Miki, you will know my story when the time is due."
Haka dai aka cigaba da rayuwa a gidan, Faroukh na can Yana kulla abinda shi kadai ya sani, Suhaima ko a kullum cikin shiri take Tana sauraron ita baiwar Allah Anisa gabadaya ta daburce Tana mamakin sai dai ganin yanda dukkansu biyun ko a jikin su yasa abin ke kulle Mata Kai. Shin mai Suhaima ta yi haka har yayanta ya ke threatening kulle ta? Ita dai ta San Suhaima is very nice, ga addini ga tsafta gashi Bata kiwuya ko kadan ba kaman ita ba. Da safe bayan sallahn asuba za tayi karatu ta hada breakfast sannan ita zata ma kulsoom da twins wanka ta taya su shiryawa, all these while Anisan ba ta San ana yi ba ma saboda da tayi sallah ta ke komawa bacci. Kyawawan halayen ta ne yasa ta shiga ran Yan gidan gabadaya cikin kankanin lokaci har ma ko da Abbah, Anty ko ji da ita ta ke sosai.
Anyi three weeks da case in Maryam tun bayan nan Bata Kara zuwa gidan ba sai a Daren ranar Shima a dalilin tafiyan da za suyi Kano washegari da safe ne. Har daki ta zo su ka gaisa da Suhaima gabadaya ta sauya da dukkan alamun kishiyan da aka ce za a Mata ne ya saita ta. Fararan su ka gaisa ta amshi haydar sannan ta fita ta gaida Barr, murmushi ya dinga Mata Yana tambayan ta ya take? Faroukh ko sai harara ya ke aika Mata. Ita Kam Maryam ba yanda za tayi ne yanzu mustapha dai dai ya ke da ita Amma its so obvious he is interested in Suhaima. Sai dai Suhaiman na kokarin kaucewa hakan, musamman ta ke sa wayan ta a flight mode saboda shi in da Kuma Dr, haka kurum duk da auren su su jawo Mata bala'i gun matansu da su ke mutunci, barin ma maryam har gwara Rufaida akwai shariya ko da ta gane hakan. Haka ranar Dr Fahad ya matsa sai ta je gidan shi ba yanda ta iya sai dai da Anisa da Muhibba duka suka tafi a motan gidansu don ba ta yadda ta Kara shiga motan Dr ba tun bayan abinda ya faru a case in maryam, bata wani Jima su ka tafi Dan ma Rufaidan ta amshe su hannu bibiyu, its was so obvious Yana son tattauna da ita sai dai ba dama. Ta San sun Mata mutunci sosai Amma Kuma ba ta fatan tarwatsa musu Family.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top