Babi na daya

4:00 pm

1st August, 2016

Kaduna, Nigeria.

Hadari ne ya mamaye garin gabadaya, daidai lokacin aka fara wani iska Mai karfi kafin kace kabo garin yayi bakikirin alamun ruwa Mai karfi na dab da saukowa. Dole ya sa motocin da ke kan titi su ka fara driving a hankali saboda da kyar su ke ganin gaban su.

Agogon hannun shi ya duba sannan yayi concentrating akan driving in da yake da kyar ma ya ke iya ganin gaban shi.

Roundabout in Oando ya bi ya shiga constitution Road, kaman ance daga kanka ya hango wata budurwa na kokarin tsallaka express in ko duba gaban ta ba tayi kaman ma hankalin ta ba ya jikin ta. Motan da ke gaban shi ma da budurwar ta shigawa gaba gudu yake sosai kaman zai tashi sama kafin ya ankara yaji wani irin kara daya sa shi yin parking ba shiri. Sai hango wanna budurwar yayi tayi sama sannan ta fado akan glass in moton ji kake tas tas glass in motan ya dagar gaje rolling budurwar ta Kara yi sannan ta kife akan kwalta daidai lokacin ruwa Mai karfi ya sauko kam da bakin kwarya, salati ya ke a fili ci ke da shock in abinda ya faru right a gaban shi.

Ko kafin ya je har mutane sun fara taruwa suna wa Wanda ke cikin motan masifa ganin ba a fito ba, Tinted glass ne hakan ya sa ba a gane Wanda ke ciki ba.Ganin karfin ruwan ya na karuwa ya sa dayawa daga cikin mutanen su ka ja baya sai sannan ya samu ganin budurwar da gabadaya jini ya gama bata Mata jiki. Tsaki ya ja da karfi hade da girgiza Kai "ko miye amfanin rufe ta da suka yi suna Kallon ta?" Ya tambayi kanshi. In ma ba karya idanuwan shi su ka mishi ba to tabbas ya hango masu kokarin daukan incident in a waya, girgiza Kai yayi Yana fadin "Allah ya shirya Mana wannan zamani namu" a kasan zuciyan shi.

Sai sannan Wanda ke cikin motan ta samu fitowa abin mamaki Mace itama da ba zata wuce 25 Years ba hade da danta a hannu, Yaron sai kuka ya ke ba ta bi ta kanshi ba Saboda ita ma kanta jikin ta rawa ya ke kaman za ta fadi kasa.

Cinciban yarinyar yayi ya bude bayan motan shi ya sa ta sannan yayi wa motan key, Wanda ke wurin su kayi yo kanshi suna tambayan Ina za shi da ita? Ko Kallon su Bai yi ba ya sa wa motan key ganin haka ya sa su kayi baya.

Komawa motan Matan ta yi ita ma ta bi bayan shi da sauri.

Unguwan rimi ya nufa direct ya dau hanyan nursing home, Barau  dikko yayi parking. Yana isowa nurses su ka fiddo yarinyar su ka daura ta kan gado Emergency aka tura ta zuwa cikin asibitin da sauri.

Da sauri ya bi su cikin asibitin ita ma Matan saurin binshi tayi rike da danta a hannu sai a sannan ya juya ya kalle ta gabadaya ta rude tafiya kawai ta ke ba wai hankalin ta na jikin ta bane.

Wayanta ne ya fara ruri tayi saurin dauka. "Lfy har yanzu ba ki Kara so ba?" A ka fada daga dayan bangaren

Ba ta San lokacin da ta saki kuka ba Jin muryar shi "Lfy me ke faruwa" ya fada a rude.

"Ka zo Barau Dikko " kawai ta fada sannan ta yi ending call in.

Accident and Emergency room aka nufa da ita da sauri ya je ya canja kayan surgery su ka shiga operation room tare da wasu Yan uwan shi doctors da nurses. Cike da kwarewa su ka fara aikin nasu.

Ta ka sa zaune ta kasa tsaye sai kai wa da kawo wa ta ke zuwa yanzu har yaron nata ya fara kuka. Bayan Yan mintuna Wanda su ka yi wayan ya karaso a rude "Mimi na lafiya me ya faru?" Ya tmby ganin yanda ta rude gabadaya.

Habawa tana ganin shi ta saki kuka Mai karfi "accident nayi na buge wata" ta fada cikin sheshekar kuka "Subhanallah yanzu Ina ta ke?"

"An shiga da ita operation"

"Okay calm down Allah zai rufa asiri and please ki daina kukan nan Kinga dai asibiti mu ke ga jama'a" ya karasa tare da amsan dan da ke hannun ta wanda har ya gaji da kukan ya fara bacin wahala.

Lallashin ta ya dinga yi har sai da ya samu ta yi shiru sai ko ajiyan zuciya da yi karewa, hannun ta ya riko ya na cigaba da bata baki.

Sunfi 3 hours suna jira dole sai da aka Mata dressing hannun ta coz hannun na Kan sitiyari Lokacin da budurwar ta fado glass in ya fashe ya zube Mata a hannu, Dan nata ne ba abinda ya same shi saboda yana Kan kujeran Mai zaman banza a baby suit in shi. Sai gab da magreeb aka fito da ita daga dakin tiyatan aka tura ta zuwa wani dakin na daban.

Suna kokarin Mikewa su bita domin gano halin da ta ke ciki, Dr in da ya kawo ta asibitin ya fito, ganin shi ya sa Namijin tsayawa domin samun bayani daga wurin shi. shi ma dai Kai tsaye wurin su ya nufo, Harara ya fara Kai wa Maryam sannan ya juya ya ba mijin ta hannu.

Zai fara magana likitan ya dakatar dashi "Sorry sir, mu je muyi Sallah please ko"

Ba musu ya bishi bayan ya ce wa matar shi " ta kwantar da hankalin ta pls kafin su dawo"

Har sun fara tafiya likitan ya juyo "Ki samu Nurses in can su baki ruwan Sallah" ya fadi Kai tsaye ya Mata pointing wasu nurses biyu kafin su ka wuce Masallacin.

Yanayin gari na ruwan sama ya sa a kayi walda a Masallacin. Dalilin da ya sa Maryam ta ga dadewan su kenan duk ta kagu.

Akan hanyar su na dawo wa daga Masallacin Likitan ya farawa Mustapha (Mijin Maryam) bayani "Abokina am sorry to say but your wife is at fault even though ita ma yarinyar da laifin ta Amma ko dan darajan ruwan saman da ke kokarin saukowa a lokacin ya kamata ace ta rage speed inta" shiru Mustapha ya mishi har sai da ya Kai aya sannan.

"Then its my fault not hers, dawo wa na kenan daga tafiya ita Kuma tana school, ba ta son bari na a gida nikadai shiyasa ta ke speeding sosai haka. We accept that is our fault so we are sorry please, ya condition in yarinyar"

Murmushi likitan yayi, yanda Mustapha ke kokarin kare matar shi ya matukar burge shi "let just hope she could make it" Dr Fahad ya fada yana shrugging shoulders in shi sannan ya cigaba "Kanta ya bugu sosai so sai anyi scanning a duba ko da wani matsala sannan Kuma ta samu karaya a kafa da hannu da Kuma karamin Dan yatsan ta na hannu sai Kuma raunuka da taji externally"

Shiru Mustapha yayi gabadaya jikin shi yayi sanyi da kyar ya iya furta.

"Allah ya kara tsarewa, Yanzu ya ake ciki kenan?"

Dan Jim Likitan yayi yana Kallon Mustapha "anyi treating in abinda zai yiwu yanzu the rest sai a hankali she is still unconcious, so an sa mata oxygen. Karayan sai ta farfado za ayi treating in shi. Zuwa gobe dai in sha Allahu za a duba komai"

"To shikenan Allah ya kaimu"

"Ameen" ya amsa

A reception su ka tadda Maryam na jiran su, ta na hango su ta taso. Likitan shigewa yayi ya bar su suna tattaunawa.

Sai can su ka shiga cikin asibitin, a haraba su ka samu likitan fitowan shknn daga dakin patient inta su. "Sorry please Dr za mu iya ganin ta" Mustapha ya bukata.

Kallon su yayi "Of no use, har yanzu ba ta tashi Kuma she will take a while but Bismillah" ya karasa zancen da murda handle in dakin, a tare su ka shiga gabadaya.

Ganin ta a kwance kaman ba ta motsi ya matukar tadawa Maryam hankali, she is feeling guilty sosai, she can't believe she cause it all.

"Yanzun za a samu Mai kwana da ita ko?"

"No need, Nurses inmu na nan in case inta tashi cikin dare, You can leave now"

"Thank you Dr, may i know your name?"

"Fahad"

"Nice meeting you Dr Fahad" ya fada yana smiling.

Shi ma Dr Fahad in murmushin shi ya mishi "see you tomorrow, am kinda busy now"

"Okay"

Cikin dare ta farka a firgice, jikinta gabadaya rawa da kyar ta samu ta bude idanunta, dakin ta fara bi da kallo a hankali, kaman Kuma wacce ta tuno wani Abu tayi saurin rintsa idon, wani irin uban Kara ta saki tana girgiza kanta.

Ihun na ta ne ya jo hankalin Nurses in da su ke da night duty a lokacin, da sauri mutum uku su ka nufi wurin ta ganin irin warning inda Dr Fahad ya musu kafin ya bar asibitin zuwa gidan shi da ke kusa da asibitin.

Samun ta su kayi tana Fisge Fisge har tayi nasarar cire drip in da ke hannun da ya karye ta jini sai zuba ya ke, kokarin controlling inta su ka shiga yi Amma Ina nema ta ke ta fi karfin su, cikin dabara sister Nabeela ta samu ta Mata alluran bacci sannan jikin ta ya sake su ka samu su ka gyara Mata drip in da ke hannun ta da Kuma kwanciyar ta. Sun so Kiran Dr Fuhad, Nabeela ce ta Hana a cewar ta shi ma ya gaji dayawa, why not a bari sai da safe in ya shigo ya ganta.

Washegari, karfe 8:30 dai dai ta mishi a haraban asibitin, yayi parking kenan ya hango Mustapha ya fito daga motan rike da Dan shi a kafadan sa, Maryam ko tana tsaye a bayan shi.

Hango shin da suka yi ne yasa su ka jire har sai da ya karaso, hannu ya mikawa Mustapha su ka gaisa Maryam Kuma ta gaishe shi, a hankali ya amsa sannan su ka nufi cikin asibitin.

Direct dakin da aka yi admitting inta su ka nufa. Nurses biyu su ka tarar zaune a daki suna hira.

"Good morning Dr" ta fada tana murmushi.

Shi ma murmushin ya maida Mata "morning sister Nabeela, na same ku lfy?"

Amsawa tayi ita ko sister Rufaida tabe baki tayi sannan ta gaida Dr kaman an sa ta dole, Sannan su ka gaisa da su Maryam.

"Ya patient in?" Sister Nabeela yayi ma directing question, shi ma kaman yadda Rufaida ba ta cika son mishi magana ba shi ma bai shiga harkan ta duk da ko ba a asibitin su ka fara sanin juna ba.

"Ta farka cikin dare tana ihu, tayi ta Fisge Fisge har ta cire drip in hannun ta sai da muka Mata alluran bacci'

Shiru yayi alamun tunani kafin can yayi magana "Ya Salam! But meye sa ba ku kira ni ba?"

"Dr Wai Naga kayi aiki ka gaji ne shine nace a bari sai yau kawai tunda za ka shigo da wuri"

"You should have called me Nabeela" ya fadi Yana Kara duban bugun zuciyan ta da sauri ya maida Mata oxygen in da su ka cire ganin numfashin ta na son ya fara seizing. Wasu dube dube ya kara yi.

Wasu zafaffan hawaye ya fara fitowa daga idon Maryam ganin halin da patient in ke ciki har yanzu,  she can't believe she cause it. Gabadaya jiya kasa rintsawa tayi tana tunani, Mustapha ne ya fara kwantar ma ta da hankali.

Juyawa Dr Fahad yayi ya kalli Mustapha "sorry Dan Allah, akwai abinda Zan Dan yi yanzu sannan zan dan duba patients in da na yi bedridden, I will be back soon"

"Ba matsala" Mustapha ya amsa.

Hankali Rufaida gabadaya ya koma Kan Babyn da ke hannun Maryam, ita haka Allah yayi ta da son yara sosai, burin ta kullum ta ga danta.

Mika mishi hannu ta yi tana smiling, ba musu Yaron ya tafi wurin ta da alamun bai da kiwuya ko bai Kai ya fara kiwiyan ba ne?

"Ya sunan shi?" Ta tambaya

"Haidar" Maryam ta amsa da kyar.

"Wow! Ki ce baba nane, Ma Sha Allah he is cute"

Murmushi karfin hali Maryam tayi saboda yanda Rufaida ta yi complementing Dan ta in a nice way "Thank you" ta fada a hankali.

Nan fa Nabeela ita ma ta fara kokarin amsan Dan, sai da ko su kayi drama da Rufaida saboda da kyar ta yadda ta ba ta shi for some minutes.

"Watan shi nawa?" Nabeela ke tambayan.

"Four months" Maryam ta amsa

"Ma Sha Allah ya na da sauri girma Amma dai gsky"

Da wasa da wasa Hira ya kaure tsakanin Matan ukun, Nurses in na kokarin kwantar mata da hankali suna tabbatar Mata patient za ta tashi domin ko sun Sha samun case in da ya fi haka Kuma su farka sai dai in kwana ya kare. ganin haka ya sa Mustapha ya Mike "Mimi na ga kin samu abokan Hira ba ra na dan leka gidan Anty, jiya da na Kira ta Anisa ta dauka Wai ta kwanta kanta na ciwo"

"To shikenan, ka gaishe ta Pls Zan ma Kira ta"

"Ehmmm sai na dawo"

"Allah ya kiyaye hanya"

"Ameen" ya fadi kafin ya rufo musu kofan dakin.


A kofan gidan yayi parking motan shi sanin ba dadewa zai yi ba sannan ya kutsa Kai cikin gida. Su na Jin Sallaman shi su ka taso da gudu gudu suna "oyoyo ga Uncle" daya bayan daya ya daga su sama, su uku ne Amma kallo Daya xa ka yi wa mazan guda biyu ka gane twins ne sai karamar kanwar su da su ke kama, gabadayan su suna cikin uniform in makarantar Bosede prestige da ke kagoro "Good morning uncle" muhibba ta fada hankalin ta na Kan littafin ta, tabe baki yayi Yana fadin "na ki gaisuwan muhibba ko kallo na ba ayi" da sauri ta Mike tana fadin "sorry uncle, Assignment gare ni in ban yi ba Uncle Victor xai Zane ni"

"Me ya hana ki yi tun jiya? By the way ya baku tafi school ba its already late"

"Uncle its raining Kuma Anty Anisa ma tace teachers inmu ma duk ba su Zo ba" Kulsoom yar 5 years ke bayanin Nan.

Ai ko lokacin Anisa ta fito jiyo muryan Kulsoom na kokarin yi Mata sharri "Kulsoom ke na fada wa haka? Ba momy na ke fadawa ba?" Hararan ta Mustapha yayi "ke Kika ja misu latti ko?"

"No Uncle musty Allah bahaka bane, tun safe ake ruwa Kuma ba su fito ba Ka ga driver ma Bai zo ba. Ina kwana, ya baby haidar? Ya hanya Kuma?"

"Lafiya, Ina Yayanku ne shi ba sai ya Kai ku ba"

"Bacci ya ke yi"

"I will wake him up Ina momy?"

"Typing ta ke a system

"Tell her na zo bara in tada Faroukh ya Kai ku school"

Dakin Faroukh in ya nufa ya ko same shi Yana ta faman minshari "Faroukh! Faroukh!" Ya Kira sunan shi Amma shiru bai farka, bayi ya shigo ya debo ruwa no second thought direct ya watsa mishi Kan fuska, a firgice ya tashi "Anisa wasa da ke ne?"

"Ba Anisa bace bude ido ka ga waye" ba ma sai ya bude idon ba muryar kawai ya ji ya gane Uncle in nasu ke magana.

"Kai Uncle musty" ya fada Yana turo baki can Kuma ya gaishe shi.

"Tashi ka Kai kannen ka schl"

"Uncle mustyyy driver in su bai Zo bane?"

Harara ya bishi dashi "da ya Zo ya na nufin zan tashe ka kena.." Bai jira ya ida zance ba ya tashi da azama, jallabiyan shi da yayi hanging kawai ya dauko ya zira sannan su ka fita dakin.

Ashraf da Arif ne su ka fara rugawa motan sannan sauran su ka bisu bayan an yi ma Mommy da Uncle bye bye.

"Ina kwana Anty" Mustapha ke gaida Antyn ta shi bayan tafiyan yaran.

"Lfy lil"

"Kai Anty da Dana da Mata na Amma ba za ki daina ce min lil ba?"

"You will always be my little brother Musty"

"Ya Kan naki Anisa ta ce min ba ki Jin Dadi Yesterday"

"Wlh Stress, ka San sha'anin business sai a slow"

"Ki dai dinga hutawa Anty, Daman na Kira in fada Miki ne, Mimi got involved in an accident"

Da sauri ta zaro idanu "shine ba ku fada min ba? Tun yaushe? Yanzu Ina ita mimin?"

"Calm down Anty, Ba abinda ya same ta, wata dai ta kade she is still unconscious, ta samu karaye dai abin ma duk ba dadin Jin"

"Oh my God, Ba ga irin ta ba, Fisabillahi Yaushe Mimi za ta daina rough driving...

"Anty ba fa haka bane, na dawo ita Kuma ta je schl sai ta biya wurin kawarta so ba ta dawo da wuri ba har na iso shiyasa ta ke sauri ta dawo gida da wuri, she don't want to leave me stranded"

Tabe baki Anty tayi "ai daman Kai ba ka taba ganin laifin Mimi shiyasa ta ke komai ta ga dama, wannan wani irin soyayya ne komai mutum yayi daidai ne ba a gyara, Da baban Faroukh Zan hada ku duka biyun, bara na dauko Hijab mu tafi asibitin"

Shiru yayi kawai ba wai Dan ya yarda da abubuwan da Antyn ke fada Kan Matan shi ba, For God sake shi ko kadan bai ganin aibun Maryam.

Sai da ta Kira mijin nata ta sanar dashi sannan su ka tafi bayan ya sanar Mata zasu hadu a asibitin.

Ko da su ka isa har Baban faruk in ya iso Yana jiran su a harabar a asibitin.

Su na shiga dakin da gudu Mimi ta fada jikin baban Faroukh in ta wani irin kuka mai taba zuciya "Subhanallah haba Maryama kaman ba ki San kaddara ba calm down mana" da kyar ya lallashe ta ta fara sakin ajiyan zuciya sai a sannan ta gaida Anty da gabadaya ita ma hankalin ta ya tashi ganin situation in patient in.

Shiru ne ya ratsa dakin kowa da abinda ya ka ayyanawa a zuciyan sa, ajiyan zuciyan Maryam kawai ke tashi kafin Fahad ya shigo dakin.

Sai da su ka gaisa da mutanen dakin kafin ya nufi gun patient in ya na duba yanda ta ke numfashi zuwa yanzu. Drip in hannun ta ya kalla ya ga ya kare.

"Faidah Zo ki cire Mata" sai da ya fada sannan ya yi realizing abinda yayi, me ye sa ya Mata magana? Gashi Kuma sunan da ya Kira ta yayi showing ya Santa personally, cije baki yayi alamun bai so hakan ba.

Ita ma Rufaidan banza ta yi dashi, hakan ba karamin tunzura shi yayi ba "Ku Zo ku cire mata Mana!" A tsawace yayi magana jikin Rufaida na rawa ta yi saurin zuwa ta zare ma ta drip in, ita dai Nabeela har yanzu mamaki ta ke don't sanin da ta yiwa kawar ta Rufaida ta san a gidan su ne kawai ake ce Mata Faidah.

"Ina ganin za mu kaita scanning room yanzu a duba brain in,  Ya ka mata ace ta farafado gsky"

"Any news about her family?" Engr Usman alkali yayi maganan ya na Kallon dactan.

Girgiza kai Dr Fahad yayi "ba abinda mu ka samu ba komai a hannu ta lokacin da incident in ya faru"

"Then dole ayi contacting police station ayi cigaye a gidajen TV da Radio."

Hakan ko ya faru Dr Fahad da su Nabeela su ka tafi da ita daki Scanning. Engr da Mustapha Kuma su ka wuce police station yin report, Maryam Kam da kyar ta hakura ta bi Anty gidan ta ba dan ta so ba, a cewarta a barta ta jira in ita ma dole sai da Engr ya sa baki daman in ta murde in ba shi ya sa baki ba to fa baza ta yi ba har gwara ma Anty tana shakkan ta Mustapha ko Daman duk abinda ta ke so to fa shima shi ne farin cikin shi.


Kaman yanda likitan ke zata kan nata ya tabu sosai,  dole sai an mata surgery a gun. Nan da nan aka yi contacting Neurosurgeon. Kan ta ko dole sai da aka Mata aski gabadaya ga gashin ta Mai yawa cika da tsawo duka Allah ya wadata ta dasu, Anyway ta lafiyan ta ake for now.

An shigar da Report, Jaridai, Gidan TV da Radio ba inda ba a dauki hoton an sanar ba Amma shiru kake ji ba Wanda ya fito ya nuna ya Santa, hakan ya sa suka fara doubting Anya Cikin Kaduna ma ta ke kuwa?

Kwana biyu gabadaya ba ta Kara ko motsi tun bayan Wanda tayi daren ranar da aka kawo ta a asibitin, ta ko wani bangare kokarin kulawa da ita ta ke duk da tana cikin halin da ita ba duniya ba ba Kuma lahira ba.

Maryam ko ba karamin rama tayi ba a kwana biyun nan duk ta bi ta susuce ba ta da kuzari, Islamiyyan da ta ke zuwa ma dainawa tayi kullum cikin zulumi da tunani hakan ko ba karamin shafan Haidar yayi ba shi ma in har wani raman yayi saboda rashin kula kullum Yana hannu Mai aikin su. Har Gida Anty ta same ta ta musu tas daga ita har Mustaphan da ya ke biye mata sannan fa aka dan samu sauki, shi Kan shi Mustaphan yaji dadin zuwan Anty yasa ta rage abubuwa da dama.

A/N:

TGIF, Juma'at Mubarak.

And here is our first chapter...









Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top