Babi na biyu

Hankalin Dr Fahad bai kwanta ba sai da ya amsa sakon Dr Usman,  babban Neurologist a jahar Lagos. Haka ma a cikin asibitin ya tsaya kai da kafa domin ganin komai ya zama ready ta yanda likitan na iso wa za a hau aikin. Response patient in nashi kam har yanzu ba a magana.

Dashi a ka shiga Surgery in yayi assisting. Daki daki haka Dr Usman ke aikin shi a tsanake har ya cima burin abinda ke gaban shi. Wani ajiyan zuciya Dr Fahad ya saki lokacin da Dr Usman ya mishi alaman they are done. He hate losing his patient,  a duk lokacin da abun ya zo da karar kwana ya kan tsinci kanshi cikin tashin hankali. Amma ya za ayi in lokaci yayi? Ba makawa tabbas sai an tafi. Kokarin kulle ta su ka fara. Engr da Mustapha ya ma bayanin yanda aikin ya kasance, Yanayin fuskokin su kadai ya isa tabbatar ma farin cikin da su ke ciki. Balle kuwa Maryam da ta ke ganin itace sillah, da Baban Haidar ya bata lbr har hawaye sai da tayi. Alhmdlh aiki yayi kyau sai kuma jiran farfadowan ta,  nan fa duk su ka dukufa wurin addu'a.

Dr Fahad Jin Suhaima ya ke tamkar wata jinin shi shiyasa bai kyashi Mata komai although su Mustapha na Mata komai but shi in dai ya tsaya akan ta tare da taimakon Nabeela da Rufaida of course.

                Some hours later

A hankali ta fara motsi da idanuwan ta tana kokarin bude su duk da matsanancin zafin da su ke mata haka ta daure tana ta kyaftawa har sai da ta yi nasarar bude idon kadan a haka tana bude tana kullewa har ta bude su gabadaya duk da hasken da ta ke jin ya ma idon yawa bai sa ta kulle ba. Wani irin ta ke Jin jikin ta kaman ba nata ba ga kanta ya mata wani irin nauyi da ba ma zata iya daga shi ba. Mata biyun da ta gani zaune a daki ta kafawa ido tana son tuno anya ta San su kuwa?

Dai dai lokacin Sister Rufaida da Nabeela zaune a dakin suna kallon wani Indian series mai suna Sehr Alasmar a tashar Bollywood da yake da yamma ne around 6:00 pm. Rufaida ce ta fara Jin alamun kaman ana kallon ta da sauri ta juya aiko four eyes su kayi da patient in ta zuba mata idanu ko kyaftawa ba tayi.

Tashi tayi ta nufi wurin ta tana Mata smiling "Sannu ko, are you alright?" Murmushin ta yi kokarin mai da mata ita ma a hankali can kason makoshin ta ta ke kokarin furta "ruwa ruwa" sai a sannan Nabeela ta juyo tana kallon su cike da mamaki. "Wow!! Yaushe ta farka? Let me call Doctor" da sauri ta fita dakin cike da zumudi. Rufaida ko matsawa tayi sosai domin ta ji abinda ta ke kokarin furtawa "Ruwa" ta ji tana furtawa a can kasan makoshi.

"Bara a samo miki" Rufaida ta amsa ba wai dan zata kawo ma ta in ba. Ta san cewa ba ruwa bane abinda ya kamata a fara ba ta bayan ta farka. Kokarin Mikewa patient in ta fara yi amma Kuma ta kasa sai ma wani azababben ciwon da taji bayan nayi.

Fahimtar hakan da Dr Fahad yayi ne ya sa yayi kokarin yi wa Rufaida magana "Faidah help her Mana" cije baki yayi cike da takaici, he can't believe he is the one messing things not her saurin basarwa yayi gudun ta fahimce takaicin da ya shiga "sa mata pillow ki daga ta she can't do it" ita Rufaida ba ta ma san ya shigo ba don haka obeying abinda ya ce tayi.

Hannun ta Kan shi nauyi ya ke Mata da kyar ta yi kokarin daga shi sai rawa ya ke ganin haka ya sa Rufaida kwantar mata da hannu duka biyu. Dayan ma kam ta kasa dagawa saboda karayan da ke hannun. Ita dai Nabeela tana baya tana Kallon su, a zuciyan ta tana ayyana yau za ta tmby Rufaida ina ta San Dr Fahad Banda Asibiti coz she can't take it anymore.

"Sannu Koh" Dr Fahad ke maganan Yana Kallon patient, daga kanta kawai tayi "me kike ji Yana Miki ciwo" ya bukata. Jikinta ta bi da kallo sai a Lokacin ta ankare da bandages in da ke kafan ta da Kuma hannun ta, hannun da ba bandage in ta daga da kyar ta shafa goshin ta nan ma ta Kara Jin wani bandage. Kan nata kaman ba nata ba haka ya mata,  kara shafawa tayi ta tabbatar da da gasken dai ba komai akan. To ina gshin ta ya tafi? Life is full of wonders. Jikin ta nuna mishi gabadaya "sannu ko bara in baki pain reliever, Nabeela samo Mata Tea please, she needs to put something in her stomach" Fita Nabeela tayi ta hado tea in. Waya yayi aka kawo mishi maganin sannan ya Kira Mustapha ya sanar mishi farkawan patient in tasu.

Tea in ma dole Rufaida ce ta yi kokarin bata sannan ta Sha maganin. Sai bayan Magreeb su Mustapha su ka iso, Maryam har kukan murna tayi tana mai godewa Allah da ba ta zamo sanadiyar ajalin ta ba. Sannu su ka dinga Mata tana amsawa da Kai coz maganan nata da kyar ya ke fitowa.

Suna nan a kazo gyara mata karayan da ke jikin ta. Wahala kam ta sha shi har ba a magana sai faman hada zufa ta ke tayi har aka gama.

A Daren Anty na Jin farfadowan ta tazo asibitin tare da Faroukh. Ita dai Suhaima kallo kawai ta ke bin su dashi tana mamakin Ina ta San wadannan mutanen da su ke nan nan da ita haka.

Rufaida ce ta yi suggesting ya kama ta ta yi wanka ko za ta ji dadin jikin. Wheel chair Dr Fahad ya sa aka kawo su sister Nabeela su ka daura ta akai, Wankan ma su dinne su ka taimaka Mata.

Aikin kwanan da Rufaida ta yi kwana biyu yasa ta taho da kayan shafan ta asibitin. Su ta kawo wa patient in ta yi amfani da wani silk material gown inta. Daman all these while uniform insu na asibitin da patient ke using ke jikin ta, aiko cib cib ya mata kaman tun can daman na ta ne. Ko da yake yanayin jikin su daya da Rufaidan. Rayuwa kenan mai abubuwan ban mamaki mutum da ranshi amma sai dai a daga a tayar.

Rufaidan ce ta kwana da ita tana taimaka Mata duk da ba aikin dare gare ta ba ranar. Ta tsaya ne bi sa ga Umurnin Dr Fahad, Nabeela ma dole ya sa ta tafi gida .

8:00 am dai dai Dr Fahad yayi Knocking a dakin Rufaida ta tashi ta bude. "Ina kwana" ta fadi tana yamutsa fuska kaman an sata dole, hararan ta yayi ba tare da ya tanka ba ya nufi gun patient in tashi da ke kwance tana Kallon sama da alamun ta yi zurfi a tunani. "Good morning" ya ce Mata.

A hankali ta juya ta sauke idanun ta cikin nashi "Ina kwana" ta fadi da hausan ta da bai fita sosai "Kin tashi lfy" ya fadi Yana nazarin shin wani yare ce ita don yana da tabbacin ba bahaushiya bace.

Tambayan ta yayi ko da inda ke Mata ciwo sosai, girgiza kanta kawai tayi ta tabbatar mishi da bbu sai dai abinda ba a rasa ba wanda a hankali zai warke.

"Dr what happen to me?" A hankali tayi maganan muryan ta na rawa tana Kallon bandage in da ke hannun ta.

"Sorry, you got involved in an accident" ya bata amsa

Shiru tayi tana nazari tana son tuno abinda ya faru, ganin haka ya sa ya jawo kujeran da ke gaban ta ya zauna, idanu ya zuba Mata yana Mai wani nazari akan shi.

"Ehmm Ina so in tafi gida" Rufaida ke mishi maganan. Banza yayi da ita, ita ma shiru tayi ba tare da ta Kara maimaitawa. "Allah ya kiyaye hanya" ya fada after kusan 3 minutes.

Sai da ta hada koman ta sannan ta yiwa patient in sallama tare da Mata fatan samun sauki.

"Zaki dawo?" Patient in ta tambaya.

Murmushi Rufaida ta Mata sannan ta yi nodding kanta "okay later" patient in ta Kara fadi.

mamakin Sabon da su kayi just in a day Dr Fahad yake. Yasan Rufaidan ba mutum bace mai saurin sabo.

"She is nice" ya ji Suhaiman ta fada bayan fitan Rufaida. Ko ba a fada mishi ba ya San ta fada mai hakan ne Saboda kin amsa gaisuwa Rufaida da yayi instead ma sai ya bita da harara.

Murmushi ya mata har sai da hakoran shi su ka bayyana sannan ya ce "I Know"

"How long have i been here?"

"Three days" ya bata amsa.

Wani ajiyan zuciya ta saki tana wasa da yatsun hannun ta.

"Sorry I have to go, Ina son duba patient in da nayi bedridden. Hope you won't mind been alone for some time"

"No problem" ta fada da alamun hankalin ta ma ba kan shi ya ke ba.

"Zan sa a kawo Miki breakfast, may I know the name please"

"Suhaima" ta fadi tana lumshe ido cike da tunanin wani yanayi da ya shude a rayuwarta.

Bude kofan da aka yi ne ya katsewa Dr Fahad abinda ya ke Shirin fadi.

Anty da Faroukh ne sai Mustapha rike da basket a hannun su da Kuma Flask sai carton in faro. Sai da su ka gaisa da Dr Fahad sannan ya bar dakin. Kai tsaye Anty ta gabatar mata da abincin, ba musu ta amsa ta fara kokarin ci bayan ta kuskure bakin ta. Faten acca ne da ya Sha kayan lambu da nama da ya dafu lugub, taji dadin abincin sosai saboda ya matukar Kara ma ta appetite saboda haka ta ci abincin da dan dama, da alamun Antyn ta San Kan abincin mara lfy.

Tea ne dai Sha kawai tayi ba dan tana marmari ba, Aa su din ne ba ta so su ga taki sha su ji wani iri ganin yanda su ke kokarin kyautata Mata.

Daga baya Maryam ta zo tare da Anisa da alamun daga kasuwa su ke saboda ledojin da ke hannun su harda trolley. Fruit, brush, Soap, sponge da Kuma cosmetic da dai kayan bukata gabadaya Maryam sai da ta tabbatar ta siyowa patient inta sannan ta baro kasuwan nan. Ita dai Suhaima mamaki ne ya cika ta, shin wannan wasu irin mutane ne haka masu zuciyar taimako? Har rasa bakin gode musu tayi, dama tayi attempting hade rai Maryam tayi ta nuna mata ba ta son hakan. A Nan su ka tambaye ta sunan ta ta sanar musu, ita Kam ba sai ta tambayi nasu ba Saboda gabadaya ta ji an fada.

Suna Shirin tafiya Rufaida ta shigo da Flask in kunu a hannun ta. Daman ita za ta kawo breakfast in da Dr Fahad ya ce za a aiko da Kuma ya ga sun zo dashi ya sa a bari. sanin za ta so kunun ya sa Rufaida taho mata dashi. Aiko sosai ta Sha kunun, ko da Anty ta aiko su Anisa da abincin rana ma ba wani na kirki ta ci ba sai da yamma. Abincin dare ma cewa tayi su barshi kawai za ta Sha fruit.

Hakan ya kasance yawanci Rufaida ke jinyan ta duk wani Abu ita ke taimaka mata ko da ko bata da aiki time in hakan ya sa sabo ya shiga tsakanin su sosai though dai ba wani hira su ke ba saboda gabadayan su mara sa son magana ne. Maryam da su Anisa su kan zauna da ita at times sai kuma Dr Fahad in bai da aiki. Haka kurum ta fi sakewa dashi kodan shi Likita ne? Nabeela ko ta Kan dan shigo in Rufaida na nan Amma mostly ta fi zuwa in Dr Fahad zai shiga dakin in ko tazo ta Dade baya nan to fa tabbas a bisa umurnin shi ne.

  5:30 pm ya gama aikin shi gabadaya, Kai tsaye ya fara Shirin tafiya gida saboda wani irin sarawa da kanshi ya ke yi. He needs to rest. Har ya Zo fita daga asibitin ya tuno da ita, kaman zai wuce sai Kuma yaji ya kasa. He needs to check on her, Yarinyar na matukar bashi tausayi.

Sallama yayi a kofan daki amma shiru bata amsa ba don haka Kai tsaye ya karasa cikin dakin. Zaune ta ke akan gadon a bisa taimakon pillows in da aka jera mata a bayanta ta sunkuyar da Kai sai ko hawaye da ke gangarowa da ga cikin idanun nata.

"Barka da warhaka" ya fada amma still kwata kwata hankalin ta ya tafi wani gun.

Karfen gadon ya buga da karfi, da sauri ta dago kanta a firgice tana Kallon shi. Murmushi ya sakar mata, idanuwan ta da ta zaro ya bi da kallo wani irin kyau ya gama ta mishi fiye da misali. "Astagfrillah" yayi saurin fada a zuciyan shi.

"An barki ke kadi ko?"

"Yanzu maman haidar ta fita" ta amsa kanta a sunkuye.

"Suhaima!" Wani yar taji sakamakon yanayin da ya Kira sunan kaman yanda mahaifin ta ya Kan Kira tane.

"Me ke damun ki?" Girgiza mishi Kai tayi.

"Ehm ehm talk to me an Miki wani Abu ne?"

"Aa" ta fada a hankali Amma dai dai yanda shi in zai iya juyo ta.

"To ki daina kukan nan kinji, ko da irin ta sa kaddarar in muka karbe ta hannu biyu sai Allah ya saka mana da abu mafi alkhairi" shiru tayi tana sauraron shi, da zai san cewa tafi appreciating rayuwar ta a yanzu kan wanda ta baro da bai mata wannan wa'azin ba sam.

"Me kike so in kawo Miki?"

"Bbu" ta fada a takaice

"Ehm ehm Suhaima be free with me fa, duk abinda kike so ki sanar dani kinji" nodding kanta kawai tayi don haka shima yayi shirun ya sa mu wurin ya zauna yana Satan Kallon ta. Mutum ce ita wacce ba ta cika son hayaniya ba coz magana ba ko yaushe ta ke son yi ba. Ganin hakan yasa ya ke yawan barin ta da Rufaida domin ko duk halin daya ne. Kuma ya lura tafi son zaman kuramen da Rufaidan akan kowa. Daga farko ya dauka Rashin sabo da boredom ke sata yawan tunani sai daga baya ya gane akwai abun da ke damun tane which he thought ciwon ta ne ke affecting inta. Saboda hakan ya sa yake mugun tausayin gashi tun da aka rike ta ba Wanda ya fito a matsayin Dan uwanta Yana neman duk da Report in da suka shigar a police station dama gidan jaridu gabadaya.

Da sallama Rufaida ta shigo dakin bayan gama round inta, four eyes su ka yi da Dr Fahad ta yi saurin dauke idon ta. "Sannu ku" kawai tace ta nemi wuri ta zauna.

"Allah ya kara sauki" ya fada sannan ya tashi ya bar dakin sakamakon kanshi da ya ke ji kaman zai fashe.

Ko da ya koma gida tunanin ta kawai ya ke ta fado mai. conversation insu da Mustapha ya tuno inda Mustaphan ke sanar mishi ya kamata a tambaye ta dangin ta domin su nemo su. Ko da ya gwada mata maganan ce mishi tayi kawai in ta warke zata tafi ba sai an nemi kowa ba.

Hakan ya kasance a gun Dr Fahad kusan kullum yana Mai matukar tausaya mata ganin yanda a karancin shekarun ta wannan kaddarar ya afka mata. kuma tabbas akwai wani abu a kasa tsakanin ta yan'uwan ta, yanda ma ba ta so a mata maganan da ya dangance su kwata kwata. In zai shiga dakin sau goma to tabbas ko wani shiga da abinda zai kai mata kullum yana cikin mata hidima. Har magani ma shi yake lallaba ta ta sha in ba haka ba, ta dinga tabe baki kenan koma ta amayo shi in har ba wani abu mai kauri ta Kora ba bayan maganin. Da ya gane kullum cikin siyo mata yoghurt ya ke ko Kuma ya sa Rufaida ta hado Mata kunu. Ita ma Kuma duk ta fi sabawa dashi haka Kuma tafi sakewa dashi don yanzu har magana ta ke maida mishi sosai sabanin sauran da sai dai tayi ta bin su da murmushi har gara Rufaida ita ana mata sama sama.

Ta ji sauki sosai, duk wani ciwo da ke jikin ta ya fara warkewa sai dai karayen da saura sai ko kirjin ta da ke yawan ciwo kaman zai fita daga jikin nata.

"Please Ina son Qur'ani da husnul Muslim" Dr Fahad yaji Patient in tashi na fadi bayan ya gama duba ta zai bar dakin.

"Okay, I will send Nabeela. Ki tabbatar dai kin ci Abinci kin Sha magungunan ki please in time yayi Kinga Ina da Surgery in da zan shiga in 10 minutes"

Turo bakin tayi kaman wata karamar yarinya "Wai yaushe drugs in nan za su kare?"

"Soon" ya bata amsa yana dariya ganin yanda ta turo bakin kaman za ta yi kuka "Don't cry kinji wata Rana sai lbr za ma kiga kaman baki taba zaman asibitin nan ba" ya karasa zance can kasan ran shi ya na jin wani tausayin ta har cikin jikin shi. Suhaima ko shiru tayi tana wasa da yan yatsun ta. Har ga Allah ba ta burin zuwan wannan ranar da Dr ke fada mata zai zo. Bata ma ki ta kare rayuwar ta a asibitin ba gabadaya.

"Promise me za ki Sha"

"Okay for you"

"For me?" Ya fada with a shock expression all over his face.

"Why?"

"Because kana so in Sha and you are nice" shiru ta danyi kafin ta karasa "just like your sister"

"She told you?"

Girgiza Kai tayi sannan tace "I've noticed"

"Zan turo Nabeela In Sha Allah" kawai ya fada kafin ya fita daga dakin.

  Wani tsaki Nabeela ta ja Wanda ya jawo hankalin patient in da ta ke dubawa gabadaya har ko da Rufaida da ke kusa da ita.

"Lafiya sister Nabeela" cike da kulawa Rufaida ke maganan.

"Wannan Dr in Mana, Dr Fahad Wai in Kai wa wannan yarinyar Qur'ani da husnul muslim sai kace wata tubabbiya. Yayi ta samu aiki sai kace wasu bayin shi"

Sakin baki Rufaidan tayi tana Kallon ta, she is very sure da Nabeela ta nuna bata so ba abinda zai sa Dr in ya sa ta, infact ma ita ke zakewa ko bai sa ta ba tayi.

"Kice mishi ba ki so mana I think ba zai sa ki dole ba"

"Don't tell me ba ki gaji da ganin yarinyar nan ba" Murmushi Rufaida ta yi don ko ta fahimci kwanan zancen.

"Aa wlh, she is innocent" cike da manufofi Rufaida ta fada sai dai Nabeelan ba ta dago ba.

"Ni sai in ga kaman da wani abu tsakanin su. Ko ke baki fuskanci hakan ba? Nasan Dr na damuwa da patient insa amman wannan is daban ne" murmushi Rufaida ta yi ganin zargin ta ya zama dai dai.

Shiru tayi bata Kara magana ba ganin haka yasa Nabeelan ma yin shiru cike da zargi kala kala a ranta. Daga karshe dai dole Sister Nabeela ta je ta dauko qur'anin a office in shi ta Kai wa Suhaiman, fuska a daure tana hararan ta mika mata. Baiwar Allah ba ta ma San me ake ciki ba har godiya ta Mata tana murmushi.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top