Babi na bakwai

Karfe Tara da rabi dai dai Suhaima ta gama duk wani abinda za tayi a dakin, ta share shi tayi mopping, ta wanke bayi, sai da ko Mai yayi tsaf sannan ta kunna burner ta fito falo.

A falo ta samu matar gidan da Kayan bacci a jikin ta tana zaune tana Kallo, Haidar ko na bacci akan kujeran da ta ke zaune "Ina kwana Maman Haidar"

"Lafiya kalau Suhaima an tashi lafiya? Ya kafan?"

"Alhamdulillah"

"Gashi kin tashi ko breakfast ba a dora ba, akwai ruwan zafi a flask ko Zaki Sha kafin Baban Haidar ya fita ya siyo mana breakfast"

"Ah bara na yi mana, ba akwai kayan abincin ba"

"Eh akwai kinsan Hadiza ba ta Nan so sai a slow"

"Ba matsala bara na yi in" Suhaima ta fada tana nufan hanyan kitchen, can kasan zuciyan ta ko tana mamakin hali irin na Maryam, gabadaya ta gama fahimtan ta a sati biyun da suka zauna tare. Kiwuya gare ta na bala'i ba ta iya komai na gidan in ba yi Mata za ayi ba to Bata damu ya zauna hakan ba.

Da tunanin hali irin na Maryam ta shiga kitchen in Wanda shima din kacha kacha ya ke kaman zai yi ihu. Saurin girgiza kanta tayi, a fili ko ta furta "No" ma'ajiyan tsintsiya ta nufa ta share kitchen ta tattare shi ta yi wanke wanke sannan ta goge ko Ina. In 20 minutes kitchen ya dawo hayyacin shi ita ma Kuma sai a Nan tayi feeling satisfied ta fara Shirin girkin.

Golden yam da sauce ta musu sannan ta daura ruwan shayi da ya Sha kayan kamshi kaman yanda ta ga anayi kullum a ajiye a dinning, may be maigidan ke sha. Nan ta gama ta je tayi setting dinning in, dai dai fitowan Mustapha daga bedroom yana daura cuplinks, cike da girmama wa Suhaima ta dan durkusa sannan ta gaishe shi. "Ah Malama Suhaima yau ke ki Mana girki kenan" murmushi kawai tayi ba tare da ta amsa ba. "Ai ko kin kyauta Kinga I don't have to waste my time and money" ita dai ba tace komai ba sai daukan nata share in da tayi ta nufi dakin ta. "Ah Suhaima ya za ki shiga ciki" Maryam tayi maganan tana Kallon ta.

  "No bar ta Kila za tafi sakewa a can in ne" Mustapha ya fada Yana zuba ruwan shayin a cup inshi.

Tun da ya Kai abincin bakin shi ya ke ta yabon girkin. Tun Maryam na mishi dariyan Santi har ta hade Rai ko yayi magana ba ta tankawa, lura da hakan yayi ya sa yayi magana "mimi dear ya dai, wa ya taba min ke?" Banza tayi dashi ganin haka yasa yayi saurin ajiye cup in shayin da ke hannun shi ya tattara hankalin shi gabadaya ya maida kanta, Sa'a Daya da Maryam ta ci a rayuwar ta kenan, soyayyar da Mustapha ya ke Mata kaman zai lashe ta ko kadan bai son yaga baccin ranta.

"Kinga Dan Allah fada min Mana ko ni na bata Miki rai"

Ganin yanda ya marairaice ya sa ta dan saki fuskan ta "Ji fa yanda kake ta yabon girkin ta as if ba Ka taba cin abincin da ya Kai shi ba"

"No ba Haka bane Mimi na, na kwana biyu ban ci abincin da yayi dadi like wannan bane kinsan ba wai Ina son abincin restaurant bane and Mai aikin am not enjoying her food but you insist a bar ta"

"Whatever am very sure Zan iya Wanda ya fi wannan ma"

"Ba kiyi karya ba mimi, you are a very good cook but ba ki son you so i have to manage since i love my queen" murmushi farinciki ne yayi appearing a fuskan ta har ta manta wa abinda ta ke wa fushi.

Roudah watch da ke hannun shi ya dubo "I've to go mimi, shari'an mu will Soon starts"

"Okay dear Allah ya bada Sa'a"

"Ameen, wait ba za ki rakani" ya fada Yana Kallon idon ta yanda tayi kicikicin da fuska kaman za ta yi kuka. Da kyar ta daure ta Mike ta bi bayan shi har gun motan.

Sai da ya shiga motan ta Mika mishi briefcase inshi da ta amsa. Murmushi Mai kayatarwa ya sakan Mata kafin ya tada motan. Waving ya Mata kafin ya ja motan ya fita ya bar Mimi na blushing.

Da ga Window dakin Suhaima ta  ke Kallon su, wani irin sha'awa su ka bata, she didn't missed  affectionate looks in da Mustapha ya ke bin Maryam dashi, it's so obvious how he loves and care for his wife. Wani irin hawaye Mai hade da murmushi ya saukowa Suhaima. She can't believe smiling and crying at the same time reminiscing her passed moment, she wonders how he is doing now, the love of her life, the man behind her mystery. Saurin goge hawayen ta tayi kafin ta yi answering call in Dr Fahad da ya shigo phone in da ya Bata.

Just like everyday tambayan ta yayi ya ta ke? Hope ba abinda ke damun ta da Kuma zaman shirun da take. Murmushi ta yi kawai ta amsa da she is enjoying every bit of her life now and she meant it. She has always been lonely... Tambayan shi tayi Amarya and gladly they are really trying to makes it work as they plan, sai da ya tuna Mata da ranar da za a fara events in bikin nashi kafin su kayi sallama.

Musamman Dr Fahad yasa kanwar shi Shahida ta siyo Kaya ya sa aka Dinka ma Suhaima. Duk a zaton ta Karin kayan Amarya ne shiyasa ba ta ce komai ba. Ummi dai ta yi shirun tana ganin ikon Allah don ko an Fi karfin ta ta ko Ina, sai dai ta dau aniyar Hana Rufaida Jin dadin zaman aure da danta. Su Shaheeda da Zahra sun Sha fahimtar da ita Amma Ina Ummi ta you nisa a kiyayyar Dada da Ya'ya'n ta.

Maryam da Yan uwanta ma ba baya sun yi Suhaima abubuwan alkhairi iri iri har rasa bakin gode musu ta ke. Kaya Kam wata Yar gatan da take wurin iyayen ta ba sa nuna Mata ba.

Yanzu Kam Suhaima kusan ita ke komai na gidan Hadiza ta fi rainon haydar shi ma ta Kan rike shi. Maryam ta so Hana ta Amma Sam ta ki ta nuna Mata bakomai. Ita Kam na ta jam Gidan ta kullum tsatsaf ba ta da matsala dama wurin gyaran jiki ba ta da matsala, tsaf za ka ganta kullum tana kamshi sai da ba ta iya Zama ta gyara muhallinta Kam Amma danta ma tsaf yake. Kusan kullum ko sai ta samu inda zata ba su hada hanya da yawan zaman gida, da kullum tana wurin Anty. Tsawata Mata da Anty ta ke Mata ne akan hakan yasa ta daina yawan zuwa gidan gabadaya, don ko ita mace ce da ta tsani fada ko Kuma a Sata Abu. Aa abinda ta ga dama shi ta ke yi ba Mai Hana ta shiyasa ma Antyn ta zuba Mata ido said ya Kama za kaji tana mata fada shima ko Mustapha Bai son laifin matar shi.

Hadiza Mai aikin su irin yan matan Nan ne na kauye masu fama da rawan Kai. Shiyasa Maryam na fita ita ma za ta Sabi hijab ta Sabi haydar sai makota.

Yau ma hakan ne ya kasance Maryam na fita ita ma ta dauki hijab za ta fita. Dakatar da ita Suhaima ta yi "Ina Kuma Zaki Hadiza da Yaron da yamma Nan ana sanyi"

"Makota Zan leka Kuma tunda Mahaifiyar shi ba ta damu dashi ba ta ke fita ta bar shi Nima dole na fita dashi" girgiza Kai kawai Suhaima tayi, ko kadan ta San hadizan ba ta iya magana ba "kawo shi to sai ki tafi" ba musu ta Mika Mata shi, Daman abinda ta ke so kenan ta yi waje da wuri.

  Har  ta gama abincin dare haydar na zaune abin shi Yana wasan shi, yaro ne Mai hakuri har tausayi ya ke Bata. Sai da tayi Sallan magreeb ya fara gyangyadi kawai ta goya shi. Wani English novel da ta gani a Falon Mai suna may be someday na Colleen Hoover da ta gani a book shelf in da ke falon ta dauka tana karan ta wa ita daman ta fi preparing karanta novels akan Kallon film.

Har ta gama chapter one ta ji takun mutum a Falon. Maigidan ne ya shigo "sannu da zuwa" ta fadi kanta a kasa. "Yauwa karatu kike Ina ta sallama baki ji ba" shiru tayi tana mamaki ya akayi ba ta ji ba "Mimi fa?" Ya katse Mata tunanin nata. "Ta fita" ta bashi amsa, "har yanzu ba ta dawo ba" ya tambaya kanshi hade da girgiza Kai. Sai a sannan Hadiza ta shigo ta na Yan noke noke sanin ya Hana ta yawo. Ko Kallon ta Bai yi ba ya nufi daki, he never like the girl, ta cika surutu ga rawan Kan tsiya, shirmen abincin ta kuwa bai da case tunda Suhaima ta fara girki.

Sai da ya fita Sallan isha'i ya dawo sannan ya nufi dinning ya fara cin abinci. meanwhile Suhaima da Hadiza na small parlour in da ke farko and they can all see him ta transparent glass in da ya raba tsakanin parlours in. He is completely enjoying the food sai dai during the process Yana ta trying numban Amma ya ki shiga, tsaki ya ja mai karfi kafin ya tashi ya dauko car key in shi.

Haydar zai fita ya sa ihu Yana Mika mishi hannu, cike da tausayin Yaron ya karasa gare shi. "Sorry son ba dadewa Zan yi ba kaji" sai ka rantse da Allah Yaron naji abinda ke fada sai dai Yana matsawa zai wuce haydar ya saki wani Kara da ya gigita su gabadaya, an tabo mai hakuri. Still dai kuka ya ke yi. Juyowa Barr yayi Yana Kallon Suhaima "gidan Anty zani ko za muje ki gaishe ta ba Zan Dade ba" shiru tayi tana tunanin ganin har yanzu haydar bai daina kukan ba ya sa tayi saurin daukan hijab in da ke kusa da ita ta amshi haydar a wurin Hadiza. "Ki kula da gidan saura Kuma ki fita" Barr ya fadawa hadiza kafin su ka nufi mota.

Sun yi two minutes da fita daga gidan Amma ba Wanda yayi magana a motan sai haydar da ke ta wasan shi. "Dan naki dai da alamu yawo ke so" ya fadi Yana Kallon kwanan da zai yi. Ita ko a zuciyan ta fadi ta ke Dan Maryam Kuma ai dole ya so yawo. Kaman daga sama ta ji ya na fadin "so you are a bookworm?" Nodding Kan ta tayi in affirmative looking interesting "wow! I love books too"

"They are interesting" ta fada ba ta so ta bar shi kadai Yana surutu.

"How many novels have you read so far?"

"Countless" ta bashi amsa.

"That's great, hope kina enjoying wannan in"

"Sosai ma, na karanta may be now online time in ta riga ta cire may be someday so am happy to finds it finally"

"Haba no wonder, na yi mamakin me yasa out  of all the books Kika dauke shi. You have been wondering how ridge ya fara son Sydney har yayi breaking up da Maggie right?"

"Exactly, Naga storm and silence ai. I will love to read that book again its awesome" she can't believe ta sake tana lbr dashi but he is talking books, for crying out loud he can't ignore him.

A haka su ka Isa gidan Anty. Cike da farin ciki su Anisa su ka tare su haydar sai washi baki ya ke yaga yan'uwan shi.  Anisa ko sai faman Jan Suhaima da hira ta ke, ita dai Allah ya hada jinin su tana matukar son Suhaima though ta San ta girme Mata, Ringing in wayan tane ya katse musu hiran nasu da su ke tayi. Da murna Anisa ta dauki wayan tana ihun "waw! Ya Faroukh i can't believe ka Kira ni. Ya ya zayd ya ke? Hope he is fine?" Daram dam Suhaima ta ji gaban ta ya buga a sanadiyan jin sunayen mutanen da Anisa ta ambata. Ba ta ma ji Mai su ke cewa bayan Nan illa ta ji Anisan na fadin "sun ma sallame ta since yanzu ma su ka Zo da Uncle musty, ayt" ta ce kafin ta Mika wa Suhaima wayan.

She wants to reject but Anisa ta zuba mata pleading eyes, ba yanda ta iya haka Nan ta amsan jikin ta na rawa ta Kai kunnen. "Hello" ta fadi a hankali.

"Wato ba kiji warning in da na Miki ba ko?" Abinda ya fada ke ne ba tare da ya amsa ta ba.

"Suhaima is better ki fita daga rayuwar Yan uwana kafin na dawo na same ki, in ba Haka ba za kiyi Dana sani, wannan ne warning na karshe da Zan Miki and mind you I will be returning in 3 weeks" dif ya kashe wayan.

A tsorace ta juya ta Mika wa Anisa wayanta sai dai hankalin ta ma gabadaya bai wurin tana can suna musu da Yan uwanta. Tana Mika Mata wayan Uncle musty ya Kira ta don su wuce gida.

Tana zaune a falo ta daura kafa Daya Kan daya su ka yi sallama, fuskan Nan nata murtuk kaman ita aka yi wa laifi. Da kyar ta amsa Sallaman tana binsu da wani mugun kallo.

Haydar na ganin ta ya fara mutsu mutsun Yana so ya je wurin ta sai dai ko Kallon shi ba ta yi balle ta tanka. Suhaima ce ta fara magana "Maman haydar kin dawo?"

"Ehmm Ina kuka je ne?" She is calm kodan ba mijin ke Mata magana ba.

"Munje gidan Anty ne ta ce a gaishe ki"

"Emhmmm" kawai ta ce ta tashi ta tafi daki ko haydar in bata tsaya ta amsa sai Barr ne ya amshe shi ya wuce dashi.

Baiwar Allah Suhaima ji tayi gabadaya jikin ta yayi sanyi kodai maryam ta fara gajiya da zaman ta a gidan ne? Tambayan da ta ke ta wa kanta kenan but littafin da ke hannun ta ya taimaka wurin Kore Mata damuwa.

Washegari ko da ta tashi har ta shiga kitchen ta fara hada musu breakfast basu fito ba, Dan wake tayi tana cikin yanka cabbage Hadiza ta shigo kitchen in tana Hamma. Wani tsaki ta ja ganin Suhaima tsaye tana faman aiki "Ayi dai mu gani" ta fada tana nufan sink. Kala ba ta ce Mata ba domin ko Hadiza ba sa'ar yinta baccin instead juyawa tayi tace "an tashi lfy"

"Lfy garas ni ke" ta fada hade da rike kugu, ita kam dariya ma ta bata ganin yanda ta ke son tsiran fada da ita.

Ba ta Kara tanka ta ba kawai ta cigaba da abinda take ita Kuma ta fara wanke wanken ta tana ta sakin habaici cin Waka "Komin bakin cikin tanda sai na ci Wa'ina ahhayye ni dije hadizatu Yar gidan malam abdu, a ganni a kyale Ni"

Allah ya tsare mu da jahilci, shine abinda Suhaima ta fada cikin ranta daga baya ma istigfari ta fara yi a zuciyan ta. She is far more than responding to that village girl, ko bakin cikin Mai zata Mata oho.

Tana gamawa ta shirya warmers in a dinning table sannan ta nufi daki. After Forty minutes taji Barr na kwala Mata Kira don haka kawai ta Sabi dogon hijab inta ta fita. Suna zaune Kan dinning in suna magana da matar tashi, haydar ko bai riga da ya tashi ba. "Ina kwana"

"Lfy kalau" su ka amsa a tare both of them are smiling at her.

"Sorry Suhaima na taso ki ko" Barr ya fada his gaze directly on her face, shaking kanta tayi ba tare da tayi magana ba "Ehmm Dan Allah Zan Zo da friends Ina anjima, Zan samu dambu kin iya ko?" Yana dariya ya fadi maganan sai dai ita hankalin ta na Kan Maryam da smile in da ke fuskan ta ya fara fading.

"Na iya" ta amsa

"Irin fa mai gyada da zogalen Nan, they love traditional things"

"Zan yi" ta amsa in short realizing yanda Maryam ke faman zabga mishi harara. "So i can't even know now if your friends are coming?" Bata jira amsan shi ba ta taci a zuciye ta wuce daki ba tare da ta Kara Kallon daya daga cikin su ba leaving them dumbstruck. Dariyan da Hadiza ta kwashe dashi ne ya dawo da hankalin su jikin su, Kallo Daya Barr ya juya ya Mata ta bar gun. Siririn tsaki ya ja hade da dafe kanshi. "Suhaima bara na tafi am getting late" briefcase inshi ya dauka ya nufi motan shi. Ita Kam Suhaima ta yi mamakin tafiyan da yayi ba tare da ya lallashi Maryam ba, it so unlike him ko kadan bai so ya ga abu ya taba ta but its like she enjoys giving him headache and it like he is getting feeds up with her attitude.

Ba ta dade da shiga daki ba Dr Fahad ya Kira ta akan ya tuna Mata shopping inda ya ce za ta raka shi,  ita kam har ranta ba ta son zuwan amma bata son yaga kaman ba ta son hulda dashi ne.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top