Ashirin da ukku

Ina nan cikin zulumi washegari har wurin azahar ba ta farka ba. Ko da naje gaishe da mum ta tmby ni Amal in, nace mata tana baccin har yanzu.

"Ta fadi abinda ya same ta a jiya?"  Sai lokacin na gane Amal ba ta fadawa mahaifiyar ta abinda ya faru ba a jiyan. Dan haka na dan sake. Amal fa har bayan Magreeb ba labarin ta, duk addu'an da na taba sani ba wanda ban jarraba ba amma ko motsin ba ta yi. Ko dana fadawa zayd ce min yayi "she overdose herself ki kwantar da hankalin za ta tashi"

"Kwanciyar hankali fa kace zayd ina na gan shi? Why are you so selfish ne Wai?" Bala'i na fara mishi a wayan da har sai da ya firgita. "Kai wani irin mutum ne ina fada maka halin da mutum ke ciki kana irin... You know what, I just realize you are not the best person to talk to" ina fading haka na kashe wayan, tsoron kar yar mutane ta mutu da alhakina yasa na gudu cikin gidan na fadawa mum abinda ke faruwa. Ina jin yan matan da ke gidan na ta kananan maganganu akan menene nake damuwa? Ai ba sabon abu bane da Amal ta sha drugs. Ban bi ta Kansu na isa ga mum. Da gudun ta ta nufi side in namu, ganin Amal ya ruda mata tunanin. Da ihu ta fara kiran driver ya fito, ni da wasu daga cikin cousins in Amal in ne mika dauke ta izuwa mota.

Ihun da mum ke yi yasa driver ke ta speeding har zuwa the closest hospital daga gidan. Direct su ma A&E su ka wuce da ita. Ba dadewa likitocin su ka sanr zuciyan ta na neman buguwa za a shiga da ita operation zuciyan ta za iya buguwa anytime soon. Kai wannan ranar na ga tashin hankali, ya guilt da ke ta faman bibiyata. Zayd ma yazo asibitin a rude, sai dai ba wanda ke ta tashi. Mum ta tana ganin zayd tq cakume wuayn rigan shi tana fadin "Duk abinda ya fara da diyata you will be hold responsible zayd, kai koya mata duk wani abinda take in ba haka ba ina Amal ina irin wannan drugs in? In ba kai ke kawo mata ba" da kyar ake raba mum da zayd saboda Marin da tayi ta zuba mishi sai da yayan Amal in Salim ya shiga tsakanin su. It was a terrible day saboda haka mika kwana ni da mum bamu runtsa.

Ko da aka fito da ita daga operation bata farka ba dai amma likitocin sunce it successful. Da kyar aka twankwashi mum mu ka tafi gida. Sai dai da gidan da asibitin kaman abu data ne, don ni a ganina ma asibitin har yafi sauki, at least a nan za ka leka ta ka ganta.

Har safiya Amal kam ba ta farka ba, a takaice dai kwana biyu ba a San tana rayuwa ko mutuwa ba. Gata nan kawai a Raye numfashi ma sai da taimako ta ke shaka, it hurt to see someone in comatose barin ma shakuwa irin namu da Amal, a girl with such a pure heart. A ranar na fizgi mota da kaina na tafi wurin Anty Umaymah, a vows na same ta. Ban tsaya mun gaisa ba ma nace mata "Am done Anty Umaymah"

Da sauri ta zare glasses in da ke idanun ta. Girgiza kai tayi tace "no you can't baby"

Siririn tsaki naja nace "shin kin san irin halin da na ke shiga a duk lokacin da nake abinda zuciya ta bata so, ko kinsan zafin pretending to be nice with people when all you are doing is breaking them? Kin san zafin ganin wanda ya so ka a rayuwa ya baka dukkan yarda da amana a kwance cikin mawuyacin halin da kai kasa shi a ciki. Baki san zafin butulcewa ba" da kuka na karasa zancen nawa. Da sauri ta tashi daga seat in ta ta dan jawo ni jikin ta tana comforting ina, she is so caring in every situation.

With a very cool voice tace "now tell me meke faruwa?" Cikin sheshekar kuka na sanar mata halin da Amal ke ciki a halin yanzu.

"Suhaima kenan to ai butulcewa shine ki kyale ta da zayd yana cigaba da zurmata cikin rayuwan da ba zai taba bata ba."

"He loves her" na fada ina kallon sju'umin murmushin da ke kwance kan fuskan ta.

"He claim so sai dai ke ma yana sonki right? Ga kuma matar shi Aminatu. To ki fada min waye ke so a ciki, kar ki manta fa yana tare da Amal in tuntuni ya gani kuma yace yana so. Ko an gaya miki in yaga wata macen ma bazai so ta bane?"

"He is not bad as you say Anty Umaymah, ni fahimta da zayd mai kyau ce"

"Saboda bai shayar da ke guban da ya shayar dani ba? Da daya wa iri na? Suhaima we need to make a change, and you promise helping in it. So please kar ki rushe abinda muka dade da ginawa, it wasn't easy kema kin sani. Mema ya rage? Abun da ya riga da yazo karshe ma?"

"Amma dai kinsan in ta tashi we are over ko?"

"Ba ita mu ke bukata ba ai, target inmu na hannun ki" tana fadin haka murmushin da ke fuskan ta ya kau. "Alkawari na daukan wa kaina suhaima, sai naga karshen mutum irin zayd. Kinsan irin masifan da ya sani a ciki kuwa?" Kwafa tayi sannan tace "ke dai kawai ki cigaba da alkawarin da kika daukan min. One thing da zaki rike shine you are helping your friend, dole ko ba yanzu ba ta gane zayd bai da wani buri a kanta wanda ya wuce dakawar shi da ta dagawa, she need her for benefit purpose" sauraron ta kawai na ke, sai dai na riga da nasan ba tayi rayuwan da nayi da su ba da har take judgement in nan. He may needs her for benefit but definitely he feels sometimes for her. Akwai mutunci da sanin girman juna kari ma he always try hiding his dirty world from him.

A safiyan mu kayi magana da zayd, he look so pale and worried "za ta warke In sha Allah" a hankali nayi maganan, saboda kawai in dan saman masa da kwanciyar hankalin da na san yana bukata.

"Nasan zata farka Suhaima, matsalan sai shine is she ready to accept my reality? Ina son ki suhaima and I can't risk anything for that" hakanan na ke jin daukan maganan shi na min wani iri a kaina.

"Wai Zayd me ye sa kake sona? Is there something special that I don't know? Na dauka ma damuwan ka akan tuhuma da mum tamaka ne" cije lebe yayi ya fiddo idanun shi waje sosai "Batun mum komai zata ce ba zanga laifin ta na wlh Suhaima, na cancanci haka. Da bani a rayuwan Amal da rayuwan ta bai kai da irin wannan ba. Nasan da haka saboda ita in mutum ce wanda Sam na taji bata gani akan soyayya. Na shayar da ita soyayya ta kuma ta afka cikin shi tsundum ta yanda na ta ganin kowa sai ni. Nasan Amal tana sona but we are better of without each other. Iyayen mu basu taba supporting in mu ba"

Siririn dariya nayi wacce ba ta da kara, tunanin da ya fara zuwa min shine tunda bai san iyayen su ba san son tarayyan su ba sai yanzu? Abu daya dana fara fahimta wurin Zaid Al-mansur shine he is so selfish to an extreme.

"Baka ban amsa ta to ai ni"

"Suhaima, it just happen wlh ina sonki soyayyan da ya fita daban dana kowace mace dana taba tarayya da. Ina ganin ki nasan kece irin maccen da na dade ina burin samu, kinga yanzu da dama ta billo min ba na iya bari ya kwace min ba ai ko?" Daga haka mika var zancen.

Lokacin da Amal ta farka, ni kadai ce a asibitin don haka aka kira ni in ganta. Duk yanayin da ya sa ta sunan shi ta fara kira "Besty Besty" samun wurin zama nayi gefen ta har ta gama farfadowa sannan nace mata "Sannu frnd" kallon da ta min kaman na wacce ba ta taba gani ba, sai kuma na ga ta daga min kai.

"Ina mum take?" Cikin muryan ta da bai gama dawo wa dai dai ba tayi maganan.

"She will be on her way, nace mata kin farka" daganan zaman shiru muka yi sai likitocin da suka kara duba ta. Kwanan kusan uku a asibitin, wani hira dai bai shiga tsakanin mu kaman da amma kuma har yanzu ba wanda yayi ma wani magana akan zayd. Sau uku yana zuwa duba ta in ya daidai ci wanda mum bata nan ko kuma ya biyo Saleem su zo tare. Su inma dai ba wani magana su ke tsakanin su ba.

Ranar da aka sallame muka koma gida, kusan wurin mum muka wuni ni da ita said daga baya mu ka koma daki. Duk ta zama wani irin, na farko saboda tunanin zayd na biyun kuwa dalilin hana ta shan duk wani abu da ta ke sha a baya. Wanda ta ke dashi duk an zubar sannan kuma ba ta daman fita siyan wani. Ta sha roko na in nemo ta, har kusan kuka take min gabadaya duk sai ta zama kaman ba Amal in da na sani mai dakakkiyar zuciya ba.

"Suhaima, can you tell me what is happening?" Cikin sanyayar murya tayi maganan, naga kokarin ta matukar amma duk da sai na fuske nace "akan me kenan"

Tsaki taja sannan tace "Ba maganan wasa bane. Zayd tell me something about you, duk da na yarda da ke ba zaki ci amana ta na so tell me what exactly is happening?" Sai da na danyi Jim, domin duk zama na dasu komai sai nayi lissafi nake yin sa. "Yace min yana sona..."

"Ke kuma mai kika ce masa?" Katse min maganan tayi niko nayi murmushi kawai. Ina ganin anzo kaban da yakamata in mata taimakon da ta min komin kankantan shi. "Ba zan fada miki sai ki min alkawari za ki dauki shawaran da zan baki a yanzu"

Kaman ba ta fahimce ni ba ta Bini da kallon zai can tace "Ehmm hmm"

"Tun muna yaran a islamiyya ana koya mana tauhid. Kuma yarda da kaddara mai kyau da mar kyau yana days daga cikin shishikan Imani. A matsayin ka na musulmi mai addini ya kama ta a San ka da imani. Zan so kin san cewa ba fa komai mutum yake so yake samu a rayuwa ba. Me zai hana ki samawa zuciyan ki hutu ta hanyar kyautatawa Ubangiji da fawwala masa dukkan lamuranki"

Murmushi mai ciwo tayi, kana ganin shi kasan tana cin radadi "Suhaima kin san so kuwa? Kinsan illan shi kin kuma san ciwon rasa wanda kake so kuwa? I can't take it gsky" ni kam har ga Allah a lokacin ma dariya ta so bani, na dai fukse nace "Amal na san fiye da tunanin ki, kuma so ya shayar da ni guban da ko da wasa ba ki dandana ta ba kuma ban miki fatan kin dandanan har abada." Kallo na kawai take amma daga yanayin ta na gama gane ba ta gamsu da abinda na fada mata ba. Sharewa nayi dai na cigaba da cewa "Zan so ki gwada ko da kuwa na kwana biyu zuwa uku ne. Cikin kwanakin kiyi kokarin yin sallah a duk kan lokacin sa, a cikin duk sallan da kikayi ki roki Allah yaye miki musibun da kike ciki. Ki yawan ta abinda kika iya na daga cikin Qur'ani, sannan ki kwatanta yin azkar. In kiyi na kwana ukun nan sai guda hada rayuwar ki ta baya wanda kike daukan barasa da sauran su abun dauke ciwo da kuma sabon rayuwan da nake so ki gwada. Kar kiyi focusing akan jin dadin, ki duba dai yanayin natsuwa da za ki sama wa zuciyan ki"

"Ni ma fa ba son shan wannan abubuwan nake ba, I think na fada miki to amma tsaya tukkunna I thought you also drink" girgiza kai na nayi nace "No, it all fake am just pretending to keep off to your standard amma gsky ni ba abinda nake sha" ta danyi mamaki kafin aka bar zancen ya kau.

Tun daga lokacin kuwa in har zan tashi sallah ina tada ta tayi haka kuma duk lokacin da naga ta fara shiga yanayin damuwa musamman lokuttan da tsumin shaye shayen na ta ke tasowa, sai inyi saurin mika mata Qur'ani. Sau da dama tana kokarin sharewa amma sai in tunatar da ita abinda muka yi.

A ranar na ukun ne tace min "Wa'adin fa ya aika now can you tell me yanda kuka yi da Zayd?"

"Zan fada miki mana amma yanzu tell me yaya kike ji, akwai wani progress?"

"Tsakiya tsakiya, I like it saboda shi bai dauke min hankali ya hana ni sanin abinda duniya ke ciki even though am living with the pain"

"Kar ki damu a sannu za ki ji daidai. Shaye shayen nan fa Kar ki manta yanzu ma ance ya taba yayan ciki please try avoiding it komai zai faru"

"Nagode now tell me" dariya nayi sosai sannan nace "Kaman yanda na gaya miki Zayd yace yana sona, I try to make see reasons but he keeps insisting ta yanda har sai da ya samu wurin zama a zuciya ta" ido na kyar akan ta, seriously ban damu da duk wani abun da za ta min ba. Wani irin bala'i ne kuma ban gani ba? Ni da naga fadan boko haram ma.

Kallo na take tayi ba kakkauta wa ta ma NASA magana jikin ta ko har rawa yake "You are betraying suhaima ke dashi? My closest people" ban ce mata komai ba, har ta gama kallo na sai kuma ta dafe kai ta fada kan gado weakly tace "nikam na shiga uku"

Na San zaki yi Dana sanin shigowa rayuwanki da nayi Amal, but you will always matters to me. Zan bar gidan Ku tun kafin ki fada min in tafi kuma a yau ba sai goba ba sai dai kuma ba zan iya yiwa Mum sallama ba saboda ban tanaji amsoshin da zan bata ba. Kar ki dauki Sallah da karatun Qur'an in Dana daura ki a kai shima wani daga cikin yaudara na bane, ko daya, ba hanya mafi gsky da yafi wannan Amal. Kina zaune cikin gidan iyayen ki ta ko ina kina samun kulawa da gata sabanin bi hakan yasa na ke ganin nafi bukatan Zayd a tare dani, ina ji a jiki na watarana sai kin gods min na raba ki da nayi da Zayd. Na barki lfy, sai watarana" daga haka na jawo bags Ina Dana hada tun ranar da zayd ya fada mata muna tare dashi. Ba dai tace min komai kuma ba ta hana ni ba har na fita daga cikin gidan daman na Riga da na nemi uber.

Direct guest house in zayd in na nufa. Nawa kaina masauki a days daga cikin dakunan gidan. Kwana na biyu a gidan bamu hadu ba kuma ina zuwa aiki muna haduwa sai dai ban fada mishi ba. Sai ranar kwatsam tashi, da farko yayi mamakin gani ba daga baya kuma yayi replacing mamakin da farin cikin.

"Kin dawo nan ne?"

"Wa nake dashi a garin Abuja bayan Amal?" Da sauri yace "ni mana amma wait ya kuka yi da ita? Ko na kira ta ma bata dagawa" hararan shi nayi nace "Dan Allah ka kyale ta kar rainin hankalin yayi yawa" dariya kawai yayi yace "bakin sani bane dole in shirya da Amal, I need her"

Tabe bani nayi nace "then marry her" rufe baki yayi yana fadin "lallai yarinya ba ruwa na wato kishiya kike wa kanki tun kafin ki shiga ko?" Kai namiji bai da Kunya wlh, hankalin Zayd a kwance mu ka cigaba da zama a wannan gidan. Bai taba nema na kuma da wani abu ba, kaman yanda ya saba hugging ina sai kuma randa tazo mishi he likes kissing me. Ban yarda zayd na so na da gaske ba sai da ya fara min maganan zuwa Maiduguri ina Jan janyewa ba. A lokacin naje wurin faree'ah da ta zo garin na labarta mata, Jana tayi gidan Anty Umayamah mu ka labarta abinda ke faruwa.

"Baki da matsala ai, zan tura Faree ta min aiki akai then you can go" da full confidence inta ta fadi hakan. Ban yi mamaki ba sai bayan kwana biyu da ta kira ni inje in same ta. Daga Office na wuce, kuma duk lokacin nan ina lura da yanad Faroukh ke yawan sa min ido, hakanan zai drink shop ya zauna in bai da ai kin yi. Ni akwai sands kiri kiri na ganshi yana bin bayana a mota daga baya kuma ya bace min. There is more da faroukh bai fada maka ba" jin Barr bai fada mata komai ba yasa ta cigaba.

Tare mukaje Maiduguri, unguwan da ban taba zuwa ba duk zamana a Maiduguri Anty Umaymah ta sa naje. Da tmby muka karasa domin nace mishi unguwan ya canja saboda anyi kone kone dayawa. Da muka karasa gidan da zamu ko, kurmus yake ba kowa a ciki ginin har ya taba fadowa. Ina mishi bayanin karya na yanda aka kona gidan namu be sai ga wani babban mutum yazo da sunan shi makocin mu ne a da. Nima ko nace na gane shi, aka yi ta koke kike sannan na tmby shi yan gidanmu yace har yanzu ba wanda ya samu labari akai. Na ko ci kuka na wanda duk na rayuwa ta nake ma wa da gasken. Da zamu tafi Zayd ya ma mutumin nan alkhairi sosai sannan ya amshi numban shi da sunan ko an samu wani lbr.

"Ba Ku da wasu yan uwane da zaki iya kaini gidan su Suhaima?" Girgiza kai kawai nayi shi ko ganin halin da nake ciki na kuka ya sa ya kyale ni.

"Na so mu tsaya Damaturu wurin kanwar mum inta sai dai ita ce mahaifiyar Mata kar a samu matsala" daga mishi kai kawai nayi amma a batun gsky naji gaba na na faduwa. I mean Damaturun da na sani ada dai kowa yasan kowa.

"Ni ko ba ka cika min maganar ta ba" dariya yayi yace "her story isn't so nice" dai taga banji dadi bane yace min "Okay, but don't judge me. We were so young, mun yi soyayyan da bamu san wani abu mai kirki ba bayan shi a lokacin. Muna ma tare da Amal time in but as my best friend. Lokacin da muka fara dating da Amal kuma da na so barin ta sai aka ki zancen, she is the reason aka hana ni auren Amal da farko. And the worst happen, we were so tempted to each other lokacin, I mean temptation as in sexual ways. To cut the story short, Dad ya ganni da ita a dakina and we are in a very intimate way. Shi ya yanke hukunci duk da mum bata so hakan ba, saboda tasan at young age but Amina is into girls, ta taba kama su da kannen  na mata suna kanana ana tunanin canja kaman sisters in nawa. She is still lnto girls though, kuma ta san nasani amma na yi alkawarin bazan rabu da ita saboda tasan affairs ina and she didn't care"

What a mess! Na fada a raina sai dai kuma a dan labarin da ya bani na gane wacece Amina. Nainah ce, my school mother kuma ita ce ta farko da ta fara bude min idanu a rayuwa. Now, the game will be more interesting.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top