Ashirin da tara
Rayuwata
Babi na biyu
Ranar Goggo ta zo duba ni, ita ma ba yanda ta ke dake tana fama da ciwon kafa sosai. "Hala na miki laifi ne tunda mahaifiyar ki ta tafi kika daina zuwa guna?" Goggon ta fada cikin harshen fulanci. "Ba haka bane Goggo" na amsa mata.
"To kullum na tmby sai ace min baki ce zaki zo ba"
"Goggo akwai abubuwan da nake yi ne" Harara na tayi tace "abubuwan da yafi zuwa wurina, to ko da wasa kar in kara ji" kallon Anty Yana tayi tace mata "in ma kece ke hana ta zuwa daga yau ya kare kina jina?"
"Ni ba ruwana" Anty Yana ta amsa tana kasa da kai.
"Yana kiji tsoron Allah dai" nan ta ke Anty Yana ta fara kame kame.
Tun daga lokacin aka fara barina zuwa wurin Goggo, INA son tsohuwan sosai, fata na Abbah ya barni In koma wurin ta sai dai ba daman tmby" Tun asali Goggo ta fito son Ummi na akan Anty Yana. A yanda lbr yazo mana, tun farkon aure Anty Yana da Abba, da kyar Goggo ta amince aka yi auren. Kuma daman ance halinka ke siyan maka mutunci. Tuni Goggo tayi watsi da Anty Yana da ta gano halin ta, don sai ta shekara in ba Abbah ya data ba ba taje gaida Goggo ba. Ko da Abbah ya tashi auren Ummi, sosai Goggo tayi na'am da zancen ganin Ummin bafulatana ce. Sai do Kowa ya shaida halin irin nasu da ya banban ta ne ya sa hakan.
Wani ranar juma'a munje wurin ta, tunda mu kaje na lura tana ta kallona, ko dan ganin yanda ban saki jikina cikin yan uwana bane, oho. Sai dai ta bari su Adda Falmata sun bar gun ta jawo ni har dakin ta. "Ke lafiyan kuwa? Ko da wani da ke damun ki ne?" Cikin inda inda nace mata "lfy kalau Goggo kin ga wani abu ne?" Hade rai tayi tace "ke dai Wlh kinji kunya shegen tsoro kaman ba Aeey bace ta haife ki, Allah en shamtata an kam"
Ni dai bance mata komai ba, sai fada ta ke yi a cewarta wai na rame sosai. Ko da mu ka tashi tfy gida cewa tayi ba inda zani. "Bari baban naku ya dawo dole in San abinda ake ciki" wani irin kallo na ga Adda Falmata na bina dashi, ni dai duk tsoron abinda zai biyo baya nake. Har rokon Goggon nayi ta bar ni na koma, maimakon hakan rankwashi na tayi ta maida ni cikin dakin ta.
Ranar ko nayi kwana dadi ba wani fargaba a ciki, ko da na tashi da sassafe na riga na saba da aiki don haka tuni na hau yi wa Goggo aikin gidan ta gabadaya. Ko da ta farka taji dadi sosai sai cewa ta ke "Ayyah ai da kin bari su ..
"Goggo me za a dafa miki?" Na tmby duk ba wai iya girkin nayi ba, banda su jajjage da nake yi sai gyaran kayan miya da su alayyahu. Harara na tayi tace "ke yanzu har wani aiki kika iya?" Marairai ce mata nayi nace "Goggo toh ba sai in koya ba" dariya tayi tace "to ai ni ba ma abun kari a gidan nan, daman dumame ne da shayi. Ke dai bara su Ajiddah su shigo su samo miki Kosai da fanke ko kuma Za kici danwake ko doyon da kowan fulawa" wai, na manta rabon da naji ana tmbyn me zanci, daman yawanci a garinmu siyan abin karayawa ake yi. Ko kuma a dinga hadawa, kuma ma sha Allahu ma su saidawan sun iya ga arha gashi kuma ba ha'inci.
Ko a gida yawancin siya ake yi sai dai sai abinda sadiya su ka rage ne ake dan bani shima ba kullum ba. In ko anyi a gida, ba wanda ya damu naci ko kar naci, sannan in ana yi ba zan iya zuwa ince a bani ba na jawo wa kaina magana, sai dai in an gama in lallaba inci a kitchen in.
Gidan Goggo gida ne irin na zamani, sashe kusan uku ke ciki daya nata dayan kuma kishiyan ta ke ciki sai dayan autan Aidah (kishiyar Goggo" da yayi aure nan ya kawo matar shi. Dukkan su biyun da yan uwan su su ke zaune, barin ma Goggo da musamman ta ke sawa a kawo mata yaran Yan uwan ta su zauna tare. Yanzu haka mata biyu ne a gidan sai dai dukkan su sunyi aure sun fito.
Sallaman yaran da naji ya katse min tunanin da nake. Yara na mata su ka shigo, ina kallon su su ka gaida Goggo. Dayan ta girme ni amma dayan za tayi Sa'a ta. "Goggo akwai abinda za a siyo miki ne?" Babban ta tmby.
"Ku dai je da shuaima ko akwai abinda ta ke so, maza dauko hijabin ki " da sauri ko na dauka, ta miko naira Dari ina ta murna muka fita dasu Goggo na fadin "a dai kula da titi Mairama" ta nan na gane babban ce mairama.
Muna fita karaman ta matso kusa dani "sannu, ke jikan Goggo ce ko?"
Murmushi na mata nace "eh"
"Ai ina ganin ki kina zuwa da yan gidanku, ina unguwan Ku?"
"Sabon fegi" na amsa
"Lah layin PS" dariya nayi sanin kowa layin PS ya Sani a Sabon fegi ko gidan 530.
"Aa mu layin Ladabi mu ke"
"Oh inda ake saida naman nan ko? Layin Gidan Khadija Bukar matan gwamna" dariya na mata ganin ta gane layin. "Ai muna da Yan'uwa layin ko Yah Mairaman" yayar dai ba ta maida hankalin ta wurin mu ba.
"Ni sunana Ajjidah, ina primary 5 a central, kin ganta can" ta fada ta na nuna min makarantan da ke gaban gidan su Goggo kadan.
"Suhaima, Islamic center mu ke zuwa. Ni primary 4 na ke"
Dariya tayi tace "Ashe ma na girme ki"
A haka mu ka karasa wurin saida abubuwan muka siya, a bakin Ajiddah na ke jin su makotan su Goggo ne, kuma Dadan su yan garin su. Da ke Goggo bafulatanan Kauyen biriri ce.
Su Ajiddah shuwan cikin Maiduguri ne su, in ka gan su Farare, kyawawa ga kuma gashi tubarakallah, kaman labarawa. Mamarsu ce bafulatana na biriri garin su Goggo.
A kwana biyu mugun sabo mu kayi da Ajiddah, ko shago aka aike ta sai tazo na raka ta. Sai da ta kaini gidan su na gaida Dadan su, sannan muka wuni muna wasa. Zan iya cewa Ajiddah ce kawata ta biyu domin duk yaran da ke islamiyya da boko suna shiri dani ne saboda malam yace ina da kokari, ni ko ban iya magana ba balle in shishige musu. Yan unguwan mu ko a shago mu ke haduwa, in kika cire Adama da har gidan tana zuwa tun Ummi na nan. Maman ta kawar Ummi ce sai dai itan wurin kakanta ta ke zaune. Musamman Ummi ke dauka na mu je mu gaida kakan, har yanzu ma ina zuwa amma a sace.
Ranar lahadi har aka yi magriba Goggo ba tayi maganan komawa na ba, ni in banyi ba saboda ban son komawa In har ga Allah. Sai bayan an idar da Sallan isha'i mun tafi wurin Anty Amarya da Anty bilki (bakuwan Goggo) muna kallo sai ga Anty Zulai ta shigo tana Sanar min kiran Goggo. Ban kawo komai a raina ba na fita domin kwata kwata ban kawo maganan tafiyana ba tunda na ga had dare yayi shiru.
Ina Sallama dakin Goggo na ga Abbah a zaune, nan ta ke gaba na ya fadi, da kyar na daure na gaishe shi. "Dauko hijabin ki Ku tafi gida Suhaima. Amma Adamu Dan Allah ka bincika yarinya duk ta rame, sannan kuma duk juma'a a dinga kawo in ta in yaso ran lahadi da Yamma sai kawunta Bukar ya maida ta"
"To Goggo islamiyya fa?"
"Akwai islamiyyan safe da yamma da su Ajiddah ke zuwa sai a sata, yanzu ma dan suna Hutu ne ba su je ba"
"In sha Allahu Goggo" ya amsa sannan ya mata Sallama na bishi a baya har motan shi.
Sai da muka fara tfy yace "akwai abinda ake miki a gidan ne ba ki fada min ba kika fadawa Goggo?" Da sauri na girgiza kai na daman yanzu ma ina tsoro abinda zan tarar wurin Adda Falmata.
"To Goggo tace kina ramewa"
Da sauri nace mishi "daman daman ina so inga Ummi ne" kallona yayi sai na ga ya hade rai dole na ja baki na nayi shiru. Ban San meyesa Kowa bai son maganan Ummiy na ba, ko Goggo da na tmby ta ce min tayi "ban Sani ba ki tmby Ubanki shi da suka samu matsalan"
A haka na shiga gidan cikin wasi wasi. Sai dai sanin tare da Abbah mu ka taho ba Wanda ya tanka ni sai Al-lawan da yace min "Yar Goggo ashe zaki dawo? Na dauka goggon ta kwace mana ke ne ai" murmushi yake kawai na mai na gaida Anty Yana, domin na kasa tantance habaici ya ke min ko wasa, Anty Yana na shan kamshi ta amsa gaisuwa na ban wani damuwa saboda na riga na saba. Ban zauna sanin dare yayi, ko ba ma hakan ba daman ba son zaman falon na ke yi ba sai ya zama dole. Daki na wuce kaman kullum Adda Falmata na ciki tana waya, duk da karancin shekaruna na kan rasa wani irin wayana ta ke yi haka da saurayin ta rai da rai. Duka duka ma a lokacin ita kanta SS1, Ya baba ne ke SS3 shi kuma boarding School ya ke yi so bai cika zaman gida ba. Adda Amina ne naji ana fadin shekaran nan ta gama makaranta.
"Nyalli jam Adda?" (An wuni lfy Adda?) Na gaishe ta kaina a kasa na ka sa shigowa dakin. Ba ta amsa gaisuwan nawa ba sai tsakin da ta ja "ni fa ban son munafunci in zaki ki shigo" ta amsa sannan ta cigaba da wayan ta. Duk da yawan wayan da take yi nasan bai kamata. Sau dayawa na kan godewa saurayin nata domin duk sanda ta ke wayan kwakwaran motsi bai so ya katse ta. Na rasa zuciya irin na Adda Falmata, tun tana yar kankanuwan ta ta ke da shegen bakin hali da mugun zuciya da sau dama da na ke jin mutane su na cewa ita da ta tashi gadon nikkanwa tayi. Saboda Abbah rashin fara'a kawai gare shi amma bai da mugunta kuma Yana da kirki, Anty Yana ko bakin halin ta da mugun ta na ciki ne sai Wanda ya zauna da ita ke gane hakan.
Washegari, bayan mun dawo daga islamiyyan yamma ina cikin wanke wanke na tsinkayi Sallaman Adama, dariya nayi saboda na San ta ji shiru ne kwana biyu ta biyo ni. Tana ji ina kiran ta tayi banza dani ina ji ta shiga ciki tana gaida Anty Yana. "Anty Yana daman Goggona ne ta aiko ni in kira mata Suhaima amma tace in fara fada miki tukun" shiru Anty Yana tayi kaman ba za ta tanka ba sai can tace "gata can tana wanke wanke in ta gama sai Ku je amma... Ko dan ma barshi kuje in" wani murmushi ne ya subuce min domin tabbas nasan da Anty Yana cewa za tayi kar inyi dare amma tunawan da tayi Goggon Adama ce ke kiran ya sa ta fasa, tasan halin ta tass za ta zo ta sile har inda ta ke. Ita ma kam ko kadan ba ta daukan raini, ko don garin su daya da Ummi na.
Nan Adama ta zo ta same ni ba tace min kala ba sai daurayan da tasa hannu ta taya ni sai har muka gama na canjo kaya sannan mu ka fita da ita. Sai da muka fita na jawo hannun ta naje haba "Aminiyar ke ma kin San ban Unguwan ne shiyasa ban zuwa, na fa je wurin Goggon Ajeyari ne" tabe baki tayi tace "bawani nan Suhaima ko kina nan ba zuwa kike ba sai dai ni nayi ta zuwa"
Hade hannuwana nayi nace "yi hakuri kin fa San ban samun dama ne in dai ina gidan to aiki nake" Ina fadan haka na ga duk tayi wani iri, da alamun tausayi na ba ta, cewa tayi "wai Suhaima ina Ummin ta je?"
Nan da nan idanu na su ka ciko da hawaye "Adama ban Sani ba kuma ba Wanda ya sanar dani"
"Mu je mu tmby Goggo"
Ko da mu kaje wurin Goggo, na samu tayi shinkafa da miya, kaji ne a ciki sannan an yanka salad, hade da ferfesun kayan ciki da kunun aya a gefe. Allah sarki Goggon Adama musamman in ta dafa abin dadi ta ke aikawa a kirani, ban taba fada mata halin da na ke ciki amma ta fuskanci hakan. "Joda nyamu mana Suhaima" (zauna kici mana Suhaima) ta fada bayan mun gaisa. Ban yi musu ba na zauna naci sosai saboda Allah ya gani ina jin yunwa, ranar gabadaya ban ciki abin kirki ba.
Bayan na gama Goggon na ja na da hira Adama sai tabo ni ta ke da kafa da alamun tana so inyi tmbyn ne. Cikin inda inda nace "Goggo daman ina son in tmby ki"
"Me fa?" Ta tsare ni da ido. Nan da nan idanu na su ka cika da ruwa "Goggo daman Ummiy ce ban San inda ta je ba" shiru tayi tsayi lokacin tana ajiyar zuciya kafin tace "Gsky Suhaima ba zan miki karya ba ban San Inda Aeey taje ba, sanin kanta ne ba zan barta ta shiga uwa duniya ba shiyasa ko Sallama ba ta zo min ba. Amma tabbas ba ta can kollere kwata kwata ma ba take ba. Ko don ta ga iyayen ta ba sa raye ne? Hatta Maiduguri duk ba bincika ba taje ba" shiru nayi duk jiki na yayi sanyi. Shin ina Anty ta tafi ta barmin cikin kangi wahala? Cikin rayuwan da ko babba ba kowane bane ya ke iya jurewa, anya Anty ba naso na kuwa kaman yanda Anty Yana ke ji dana ta yaran?
Haka na cigaba da wannan bakan rayuwa, kullum da irin ibtila'in da ya ke fada min, saukin ta ma duk juma'a zuwa lahadi gidan Goggon Ajayeri na ke yin shi. Sai kuma na kanje wurin Goggon Adama, watarana in saci hanya In an aike ni, duk da nasan hukunci da zan fuskan ta in na dade.
A haka muka samun hutun shiga ajin gaba. Adama ke fada min za su je kollere da goggon ta. Don haka ni ma na je na samu Goggo nata ina kuka nace mata zan bita nasan in ta ma Abbah magana zai barta. Ban don ta so ba ta je ta samu Abbah ta sanar mishi, domin a cewar ta Abbah sirrikin ta ne.
Adda Falmata na zagi na tana kirana mara zuciya tunda har uwar da ta haife ni za ta iya tafiya yawon duniya ta barni amma in kwashi jikin in ce zan je in ga yan uwan ta. Ban ce kala ba na cigaba da hada kayana na bi su Adama kollere. Muna zuwa ta kaini gidan Yayan Ummin da ke wazirin garin.
Muna Sallama a gidan naga duk sun jiyo suna kallona kaman ba su taba ganina ba. Ganina tare da Goggo ya sa su ka gaisa da ita faran faran tace musu "ga yar gidan Aeey nan ta zo Hutu"
Duk cikin su mama Rakiya ne tace "ma sha Allahu sannun ki da zuwa" nan fa Goggo ta tafi ta barni, abin mamaki ba Wanda ya kara daga ido ya kalle ni bayan tafiyan Goggo, sai dai na ji suna ta kus kus. "Eh ai yar Aeey Wanda ta tafi yawon duniyan ta barta" wata tace "to daman mai kuke tsammani da wacce ta yi boko? Ai daman yan duniya ne" wata ta kara cewa "kai amma dai anyi abin kunya"
Mama Rakiyya ce ta sa Altine yar ta ta shigo dani dakin su har ta bani abinci, daman naji Ummi tana fadin ita in kawar tace tare su ka taso kuma ta auri yayan ta. Abinda ya bani mamaki shine duk sanda mu ka tako kollere da Ummi na sai kunga yanda ake nan da ita kaman za a hadiye "ai ga Aeeyn Maiduguri ta zo" abinci ko kala kala har sai mun ture. Amma yau dan batanan ko kallon arziki ban ishe su sai mama Rakiyya da naci albarkacin Ummi na ta sa aka dauke ni. Kawaye nane dai su Fandau, Hajiya, Aeeshatu da mami su ka zo mu kayi ta labari, sauran kam ce min aka yi iyayen su sun hana su zuwa wai kar na bi halin Ummi na zo na koyawa yaran su. Su wadannan in duk yan uwane shiyasa.
Kawu na da ya dawo da dare musamman ya sa aka kirani, muka ci abinci tare, yayi ta min nasiha game da rayuwa. Tabbas na so gasgata Adda Falmata da tace dangin Ummin ma ba so na su ke sai dai duk da haka gwara zama a gunsu akan bakin gidan mu.
Kwanan mu biyar mu ka koma, ba ko tsaraban nan da aka saba cika mu dashi in munzo da Ummi babu. Sai kawu na da ya bani naira dari.
A yan kwanakin nan tabbas na ga rayuwa kuma rayuwa ta koya min darussa kala kala masu wuyan mantawa.
Wannan karon ko da muka koma makaranta, sabon aji ne amma ko kadan ban murnar da na ke yi a irin lokaci kaman hakan na canjan aji. Ba sabbin Uniform kaman yanda Anty ke siya min. Na socks, jaka na na makaranta ko saukin har yanzu da kyan shi da takalmina. Sauki na kenan Ummi ba ta siya min abu mara quality sai mai kyau kuma maji gaba. Batun basket daman ba a maganan shi, to in samu inci a gidan ma mana.
Ban kara marmarin zuwa kollere ba amma mu kanje Ngelzarma da Goggon Ajayeri in sha'ani ya taso, ba laifi garin akwai su da son shagulgula. Biriri kam sosai mu ke zuwa da Goggo, gidan dan uwan ta sarkin garin. Fura da nono har sai na ture. In bi yan matan gidan muyi ta yawo gidan yan uwa, kusan duk sa'anin Adda Falmata ne, har babban gida mu ke zuwa da su.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top