Ashirin da takwas
Kaduna
Yana fadawa Anisa, jiki na rawa ta gaggauta kawo mishi manuscript in kaman yanda ya bukata. Bai yi wata wata ba kuwa ya amsa sannan ya wuce gidan shi da duba iyalin shi. A falo ya iske maryam zaune tana danna waya, ga gidan duk yanayin shi sai a hankali. Abinda ya lura shine a kwana biyun nan ta fara maido halin ta na da. Tayi farin cikin ganin shi musamman da zuwan nashi ya kasance bazata, amma da ke shu'uma ce ta buga a jarida sai ta basar sannu da zuwan ma da kyar ya fito daga bakin ta. "Au baki ji dadin ganina ba in koma inda na fito?" Hararan ta yayi, dole ta ajiye wayan hannun ta, ta dan turo baki "Mu dai kawai an kwace mana kai wlh" daganan su ka dan sakewa juna, duk can kasan ranshi bai ji dadin irin tarban da ya tarar ba gun masoyiyar tashi kuma mallakin shi.
Sai da ya dan natsa tukunna ya fara bude manuscript in cike da son ganin abinda ya kunsa.
Rayuwata
Babi na daya
Damaturu, Yobe state
Ina tsalle tsalle na shiga layin gidanmu ina cilla jakan Islamiyya ta sama ina cafkewa cike da farin ciki a raina, buri na in isa gida in sanarwa Ummi tabbas yau na bada hadda ta dai dai malamin mu har kyauta ya min. Ina jin kawata Adama da muke dawowa islamiyya tare tana kwla min kira in zo in amshi pencil in da na bata aro nayi mata banza.
Tun a kofar gidanmu na cire hijabi na na ci dammara ina faman kwallawa mahaifiyata kira. "Ummi Ummi Ummi na dawo" da yayata Falmata na ci karo da sauri na matsa saboda saura kiris in buge ta, saurin matsawa nayi a tsorace Sanin halin ta, muddin kuskure ya Sani na buge ta kwana zanyi jiki na na ciwo. Kwafa tayi tana galla min harara "Allah ya rufa miki asiri kuma kar ki cika mu da ihu gantalalliyar uwar ta ki da kike kira tayi gaba tabi duniya" kallon ta kawai nayi domin shekaruna sunyi karanta in fahimci abinda ta ke nufi. ba don na damu da abinda tace ba na nufi wurin mu ina kokarin karasawa dakin Ummi ina cigaba da kwalla mata kira.
Sai dai wasa gaske ba Ummi ba alamun ta haka kuma ba kanwata maijidda. Gajiya nayi na fito na zauna kan baranda ina jiran ta inda za ta fito. Shin ina Ummi taje? Ni dai nasan in zata unguwa tana fada min amma yau ba ta fada ba. Cikin falon na sake komawa na ga komai na nan yanda ya ke. Don haka nayi saurin nufan dakin ta ina kallon shi. A hankali na duba akwatinan da ke wurin sun ragu ko da na duba wardrobe naga ba kayan ta haka ba na maijidda, ban San lokacin da na saki kara ba na fara birgima a kasa, duk a tunanina tafiya su kayi su ka barni. Ni ko babban bakin cikina shine zan koma wurin Anty Yana. Duk lokacin da Ummi tayi tafiya ta barni a wurin ta ba karamin wahala na ke sha ba wurin Adda Falmata, Anty Yana dai ba za ta buge ni haka kuma ba zata hana a bugen ba, ko kallo ban ishe ta ba, kai ko gaisuwana ba cika amsawa tayi ba.
Wani irin tsawa naji a kai na daya Sani saurin yin shiru ba shiri, jikina har karkarwa yake a sanadiyyan wanda na gani a gaba na yana bina da harara alamun ba wasa akan fuskanshi. Yaya baba ne tsaye a kaina da abokin shi Umar sanda.
"Kukan uban me kike wa mutane? Har da birgima don tsabagen iskanci da samun wuri ko"
Cikin rawan murya da duk ya dishe tsabagen kuka nace "Ummina ban ganta"
Wani irin dariya na ji an kyakyata min, har cikin raina naji bakin cikin dariyan nan mai kama da na mugunta, sai dai ba daga bakin Yaya baba ya fito ba, abokin shi ne Umar sanda da su ke tare.
"Au ba ta fada miki za ta bar gidan nan bane? To tafi na har abada, ba za kuma ta kara dawo ba har abada. Kin San halina sarai ban son iskanci taso muje Abba na kiran ki" Yaya baba ya fada yana bina da harara.
Daskarewa nayi a wurin, tsabagen rudanin da na Shiga, shin wani irin abu me shirin samun rayuwata?
Ga mamakina abokin Ya baba na gani ya Shiga falon Ummi yana dube dube.
"Kai Faruk fito mu wuce mana, me kake yi a nan?" Yaya baba ya tmby.
Fitowa yayi still da dariya a fuskan shi "Adams wlh side in nan ya hadu, kawai kace wa Abbanku ya maido Ku nan harda Al-lawan tunda mai wurin ba dawowa za tayi ba wlh zai kawo light" wani irin tululin bakin ciki na ji ya sauko min, wai shin shi wannan ma ina ruwan shi da harkan gidanmu ne. Ban San lokacin da na juya ina kallon shi ba, ido hudu mu kayi dashi, cike da kallon tsana na zabga mishi harara.
Dariyan ya kara yi wannan karon harda rike ciki "calm down little girl, bani na kar zomon ba"
Magana na ke shirin mayar masa duk da nasan ba abinda xai hana Yaya Baba dukana, sai dai shigowan Abbah ya katse ni. Da sauri su ka fita su ka barmu ina cigaba da kukana.
"Keh lafiyan ki?" Naji an fada hankali na dago iddanuwana suka fada kan Abbah. Mahaifina mutum ne Wanda bai iya zama yayi wasa da yaro ba balle yaja shi a jiki hakan yasa dukkanmu tsoron shi mu ke jin har ma da su Anty Falmata. Sauri shiru nayi na kama baki na ina kallon shi jika na na kyarkyarwa. "Dum dume?" Me ya faru? Ya fada cikin kalman Fulatanci, kasancewar shi bafulatanin Ngelzarma. Karamin hukuma a nan Yobe state. Amma sun dade da dawowa jikin damaturu domin mahaifiyar shima a Unguwan Ajayeri ta ke zaune.
Saurin girgiza kai nayi, wani irin kallo naga yana bina dashi mai cike da alamun tausayi. "Ki hada kayan ki maza zaki koma dakin su Falmata" a rikice na dago ina kallon shi sai dai duk tsoron shi da nake ji bai sa na kasa mishi magana ba. "Abbah zanje wurin Goggo ni" kallo na yayi for the first time naji yana lallaban mutum. "Ba kuna zuwa ranar juma'a b?" Gyada kai na nayi. "To ki bari in anyi hutu da kaina zan kai ki dinga mata Hutu"
Ganin ya amsa ni ya bani karfin guiwan tmbyn shi "Abbah ina Ummiy da Maijidda" kallo na ya sake yi nan ta ke kuma naga ya koma bata rai kaman kullum. Don haka ban iya kara magana ba na sa kayana a akwati na bi bayan shi.
Tun daga kallon da yaran Anty Yana ke min na San tabbas ina cikin matsala. Kaf cikin su Al-lawan ne kadai mai dan sauki da shekara biyu ya girme ni. Shi ne ka dai mai zuwa wurin Ummiy na ya gaishe ta at times ma har yaje mata aike. Adda Falmata tsanan duniya ta dauka ta daura ma Ummiy na to nima ko kadan ba ta raga min, sannan komai za ta min Ummiy ba ta taba daga kai tace mata kala. Ummi na bafulatanar kauyen kollere ne, shima Yoben ya ke. Baffah sunan kani naga da ke bi min, mai sunan baffan Maiduguri ne, hakan yasa yana gama nursey baffan ya bukaci ya koma wurin sa da zama. Maijidda ita ke bi mishi.
A dakin Anty Yana ko Ya baba (mai sunan Abbah) shine babba sai Adda Falmata, Al-lawan sai Sadiya da autan ta Zainab.
Yanzu ma shigana wurin su Al-lawan ne kadai ya min kallon arziki sauran ko duk harara su ke bina dashi sai dai ba daman magana saboda Abbah na wurin, kusan ma sunfi ni tsoron shi don su fini sanin halin shi. Hatta Anty Yana in yana wuri zaka ga tana dar dar duk mulki irin nata sabanin Ummi na da ko kadan ba ta dauka, a wurin Ummi ne kadai za kaga yana raha da dariya har ma yana tsokanan ta. Duk iskanci Anty Yana da Adda Falmata ba su iya taran Ummi su mata, akwai wannan shakkan tsakanin su sai dai ko su sauke a kaina ko suyi habaici shi ma tana kallon mutum zai sha jinin jikin shi. Akwai ta da wasa amma Sam ba ta daukan raini, abinda na ke tunanin ya raba su da Abbah kenan domin har yau ba Wanda ya dube ni ya fada min dalili.
Dakin Adda Falmata na kai akwati na, ita da sadiya ne a dakin. Lungu daya na nemi kayana nasa, a dakin na takure na zauna domin Allah ya gani ina tsoron fita falo.
Nayi mintuna kusan Goma a wurin sai ga sadiya ta shiga tana banka min harara. Na kan yi mamaki domin ita din sa'an Baffah CE ba nawa ba "kizo Anty Yana na kira" abinda ta fada kawai kenan ta fita. Jiki na rawa na nufin hanyan Falon dukkan su suna zaune suna kallo. A hankali na durkasa gaban Anty Yana na ce mata "gani" harara ta bini dashi kafin in ankara ta cakwumo wuya na kaman wata sa'anta sannan ta sake in ta kama kunnuwana duka biyu ta murde da karfi har sai da na saki karan azaba "Warning zan miki domin ba a sona zan zauna da ke, tun can kin sanni ba shiga harkan ki nake ba don haka ban son shishigi ki yi harkan ki inyi nawa, ba zan hana ki hulda da yan uwanki ba amma kar ki sake ko da wasa kice zaki taba min sadiyya da zainab, ba zan dauka ba. Ba zan miki fadan tsabta domin naga uwarki ba laifi akwai shi don haka ki kiyaye ni kina jina?" Da karfi na amsa mata da "in sha Allah" siririyan tsaki taja a hankali tace "in banda ma abun Aeey wa ke tafiya ya bar dan shi a wuri, ni wlh ta bani kunya don da nice maza ne kawai zan kyale" shiru nayi, a raina ina gasgata Anty Yana, ko bakomai tana ma yaranta son da baza ta barsu su wulakanta ba sabanin nawa Uwar da ban San dalilin da yasa ta ke haka ba. Munafunci irin na Anty Yana kasa kasa ta ke yin amma in kana so kaga bala'in ta kama taba mata da. Amma Anty na a gaban ta Adda Falmata da Yaya baba za su min dukan tsiya amma ko dagowa ta kalle su ba tayi. Iyaka in na gama kuka na tace in wuce daki, daganan zancen ya wuce.
"Tashi ki bani wuri ni!" A firgice na tashi saboda yanda ihun nata ya sauka a kaina. Sum sum na koma daki, ina shiga naji an jawo ni an hada ni da gini, kafin in ankara naji saukan mari ta ko ina, ba shiri na zube kasa.
"Taso ko in kara mini" Adda Falmata ta fada tana bina da harara, da sauri na dago a tsora ce. "Kar kiga laifi na kiga laifin Uwarki, kin San mai ta fada min da zata wuce?" Ta fada tana bina da kallon tsana.
Saurin girgiza kaina nayi nace "Aa" nasan rashin amsawan ma wani matsalan ce, ga hawayen da ke ambaliya a idona ba hanyan yin kuka.
" ce min tayi Falmata ga Suhaima nan zan barta a nan gidan. ke da sauran yan uwan naki in kuga dama Ku kashe ta Ku bar min gawan ta, in zo in dauka." A firgice na ke kallon ina kokarin gasgata zancen ta, ni kam na shigo meyesa Ummi zata min haka? Nasan halin zafin ta tsab za ta iya fadan hakan.
"To uwar ki ma ba son ki ta ke ba ta ajiye ki ta shiga yawon duniya don haka duk wani aiki na gidan nan ke zaki dinga yi kama da shara, wanke wanke, gyaran daki ke har ma da mopping." Ni dai ban tanka ba, illa hawayen da ke zubo min. A lokacin na samu kaina da tmbyn shin meyesa Ummi na ba ta jira na dawo daga Islamiyya ba mu ka tafi tare?
Tun daga lokacin kuwa na fara bautan. Kullum na tashi da safe sai nayi wanke wanke, na gyara dakin mu da na Anty Yana. da har dakin su Ya Baba, Al-lawan yace zai dinga yi. Na share tsakar gida da parlor Bayan na gama sannan a bani abincin da aka ga dama In tafi School. Islamic center da ke Yobe mosque a GRA dukkanmu mu ke zuwa, da ke ba nisa a kafa mu ke zuwa, babban titi kawai ake tsallakar damu mu karasa. Hakanan in mun dawo da islamiyya da yamma sai nayi wanki uniform ina da na sadiya sannan ake bari na cin abinci. Aike ko komin dare duk nisan wurin sai naje, Al-lawan ke satan hanya ya raka ni.
Abbah bai cika zama a gari ba, aikin shi tafiye tafiye su ke hakan yasa bai San abinda ke faruwa ba.
Duk ma ni abubuwan ba wanda yafi daga min hankali kaman debo ruwa. Muddin ruwa ya kare to dole ne naje na debo a gidan su Umar Sanda, da ke suna da dam. Haka zan ta kaiwa da kawowa, in ya hadu dani ya dinga dariya kenan yana "ah su kuka kuka miye na zunburo baki in zaki debi ruwa ki debi ruwa kawai" na rasa me ke mai dariya a jikina. Watarana in naje haka zai sa sai zubawa duk wanda ya zo deban ruwan nan kafin na debi nawa. Maman shi ba ta gida sai Hajja kishiyarta, wanda ta ke aminiyar Anty yana, ita kam daman yar zugawa ayi ce.
Yau juma'a tunda na tashi ina cikin farin ciki saboda nasan yau za a gidan Goggo. Da murna na dawo daga makaranta kasancewar an bamu script in test in maths da muka yi. L.C.M da H.C.F sai Long division, topics ne da su ke matukar bani wuya amma tunda Ummina ta zauna ta warware min na iya su sosai. Gabadaya test in na cinye, Ummina mutum ce mai hazaka sosai don gabadaya gidan su ita kadai tayi karatun boko har zuwa secondary. Ganin haka Yayan maman ta ya dauke ta zuwa Maiduguri inda ta jona F.C.E. Tana karatun su ka hadu da Abbah har su kayi aure. Bayan ta gama karatun ta samu aikin koyarwa a injiwaju, nan Adda Falmata ta fara yi kuma a nan kiyayyar ta da Ummi na ya samo asali. A cewarta kwata kwata Ummina ba ta raga mata a makaranta, failing inta ta keyi kuma ta dake ta. Ni ko sanin halin Ummi nasan ba tayi dai dai bane, Adda Falmata kuma akwai taurin kai ba za ta yarda ta koya ba. Ni dai nasan ko ni ce ba zai hana ta dake ni ba. Kusan ince akan hakane aka fara jinsu da Anty Yana duk da Ummi na ba ta tanka ta kuma ita Anty Yanan tana shakkan Ummin.
"Kenan ni za tayi farin ciki da abinda naci?" Wani kololon bakin ciki ne ya tsaya tunawan da nayi yanzu Anty bata nan. Kuma har yau ba Wanda yace min ga inda taje. Haka na karasa gida jiki a sanyaye. Ko abinci ban ci ba na kama aiki na kafin lokacin zuwa gidan Goggo yayi. Tsab na shirya bayan na gama ina zaman jiran su, har mun fito zamu tafi muna ma Anty Yana Sallama naji tana fadin "keh zo ki min wankin su Sadiya, me ake yi a gidan Goggon" wani hawayen bakin ciki na ji ya zubo min nayi saurin gogewa. Ina ji ina gani su ka tafi, ni kuma aka jibga min wankin su sadiya.
"Au wai dan bakin hali shine kike kuka don za kiyi wa kannen ki wankin? Shegiya mai bakin hali irin na uwarta aiko hakanan zakiyi wankin nan" kala bance mata na dauko wankin na fara yi tun ina kuka har na gaji na daina. Abin takaici sai da nayi tsakiyan wanki ta zo ta sa na sake da ga farko, wai basu fita. Hakana libgi wanki jikina duk ciwo har su ka dawo ina wanki, ba Wanda yace min sannu sai Al-lawan da yace "Suhaima har yanzun ba ki gama ba?" Ganin ban tanka shi ba shima yayi wucewar sa.
Wasa wasa har na kusan shafa wata biyu cikin bakar rayuwannan, wahalan yau daban na gobe daban kullum da irin nashi salon. Cikin wata biyun nan kwata kwata ban taba zuwa gidan Goggo ba, tun ana Sani aiki ko kuma Anty Yana ta fita tace ni zan kula da gida, har yazo kiri kiri ko za a tafi nasan bani a ciki.
Ranar tun da yamma bayan na gama wanki na ke jin zazzabi zazzabi, don haka ban tsaya bitan karatu ba kaman yanda na saba sai na kwanta. Da rawan dari na tashi a firgice jin zazzabi ya zuba min sosai, wani irin amai naji ya taso min ko kafin in tashi na zuba shi a kasan tiles in dakin. Na dauka baKowa a daki sai jin muryan Adda Falmata nayi tana fadin "bala'i ke wannan wani irin iskanci ne?" Kafin in bata amsa ta kwashe ni da mari Wanda yayi matukar girgiza ni na zuba kara a wurin. Ban San Abbah ya dawo ba sai jin muryan shi nayi yana fadin "lafiya wa ke kuka?" A firgice Adda Falmata ta kalle ni tana min warning. Da alamun ita ma ta manta yana gida. A tsorace ta fara fadin "Abbah daman Suhaima ce bata da lfy shine ta ke kuka" kallon mamaki na bita dashi, kenan daman ta San bani da lfy in ashe?
Har Dakin Abbah ya shigo, idanuwana sunyi jawur ina kallon kasa ya jawo hannuna. "Falmata gyara wurin nan" ya fada yana jan hannuna muka fita. Sauran kiris ince mai "Abbah zan gyara da kaina" sai dai shima ba zan iya mai musu ba amma tabbas nasan sai na tsani kaina wurin Adda Falmata muddin ta gyara wurin nan.
Zaunan dani yayi a kujera ya taba wuya na. "Tun yaushe ne baki da lfyn?"
"Tunda yamma na fara ji" na amsa mishi.
"To shine zaki zauna kina kuka? Ba ki San ciwon kai zai kara miki ba?"
"Kayi hakuri Abbah" girgiza kai yayi yace "Daga yau in baki da lfy fada zaki dinga yi ba kuka, dauko hijab inki mu je asibiti"
Jiki na rawa na shiga dakin, Adda Falmata ta zuba wa inda nayi Amai ruwa, ta toshe hanci ta. Ban ce mata kala ba na dauki Hijab INA, ina jinta tana kwafa a raina nace, sai dai kin goge in. Ajiko hospital mu ka nufa da Abbah, suna ganina su ka ce banda karfi sai na kwana an sa min ruwa dole. Bayan an min allurori aka sa drip in yace wa nurses in bara yaje gida ya dawo, zai zo da Wanda zamu kwana, a raina na dinga rokon Allah yasa ba Adda Falmata bace domin ni gwara min Anty Yana akan ta sau dubu, ita komin abinta ba duka sai sa aiki da rashin kula da al'amura na. Amma Adda Falmata kaman ta samu jaka, a cewarta tana rama abinda Ummi na ta mata, ni dai na San 90% sharri ne kawai. Kafin Abbahn ya dawo har nayi bacci, sai dai na farka da safe naga Anty Yana ta hada rai sai hura hanci ta ke. Kiri kiri matan nan ba ta taimaka min yin komai ba, a cewarta ita ba ta sa kanta abinda ba hakkin ta bane. sai da Al-lawan ya zo ne ya taimaka min da ke ya riga Abbah zuwa. Shi kanshi Al-lawan in na kan kasa gane kanshi domin wataran kirki watarana kuma ko a jikinshi.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top