Ashirin da shidda
Washegarin Dinner in ma ba karamin kayatuwa event in yayi ba. Da farko dai Amaryan wani hadadden lace ta sa su kayi anko da angon ta da ya sha many an Maya, sai daga baya su ka canja I zuwa outfit insu na larabawa. Events yayi dadi sai sam barka, Yanuwa su ka koma in da su ka fito aka bar Amarya da Ango da za suyi honeymoon a kasan.
Kwana biyu su ka jera ita da Faroukh Machina su na kewaya birnin mahe island, ba dai wani magana tsakanin su but it like that are all witnessing the attraction between them. It become intense lokacin da su ka fara fita shopping, suna different games a tare sai kace wasu couples. Sai dai dare nayi kowa ke kama hanyan masaukin shi. Ba ma mahe island kawai ba, ya dauke ts sun je different islands da ke cikin seychelles wanda ta taba zuwa da wanda ma ba ta san su ba, they explore the country sosai a tare, it suvh a bliss for her.
Har hotel in da take Rawan da mijin ta suka kawo mata ziyara, rungume ta Rawan in tayi tana ta faman mata godiya. "I can't believe you make this happen Umayamah you are the best" sun taba hira kafin Rawan In tayi requiring account details inta. Sai bayan ta tafi ta ke ganin alert, she is so shock da irin kudin da ta turo mata, ta kira mata complain ma ce mata tayi its a gift from her dad da kuma Adam.
Da ta sanar ma Faroukh machina kam bai wani yi mamaki, domin shi yasan dukiyan nasu. Ranar da yamma suna zaune a apartment in Faroukh in suna kallon wani movie da ya matukar jan hankalin su ta sanar mishi tana son ta wuce because its getting late.
"But you can sleep here ai" dan zaro idanu tayi tace "No i have to go" dan bata rai yayi, ya cire glasses in da ke idanuwan shi "Kina tsoron am going to do something ne?"
Shaking head inta tayi tace "Aa am avoiding issues ne kawai" ba ta jira cewan shi ba ta mike, dan yanda ta ke ji minti daya ta kara tare dashi, anything can happen and she is done with everything related to boys.
"We shall talk tomorrow" ta fada tana kokarin karasa wa wurin kofan, da azama ya is a gare ta ya jawo hannayen ta duka biyu. Hakan yasa tayi saurin sakin bag inta dake hannun ta, kokarin yake yaga sun hada ido sai dai hakan ya faskara, karshe ma runtse idanuwan ta tayi gam tana ji wani irin abu na mata yawa. Ba ta kwace hannun ta daga nashi ba ba sai dan ba zata iya ba sai dai dan wani irin fadin da ta ke ji yana ratsa ta, it a moment she wouldn't like to end. Jan ta yayi har zuwa kan couch ya made kafafuwan shi kaman wani yaro karami yayi tagumi yana kallon ta. Ba ta dai ce komai ba haka kuma ta kasa yin wani motsi. Sao da ya gaji dan kanshi yace "Umaymah why are you trying to avoid what is between us?"
Mamaki ne ya bayyana a fuskan ta, sai dai kana ganin shi zama san pretense ne kawai "Ni fa ban iya kwana kwana ba Umaymah, when I like something i go for it immediately i get the message and you know we like each other why are you voiding us the right to?" Tsit tayi, tabbas tayi expecting fiye da haka kuma sai dai yanzu da yake faruwan sai ta ke jin rashin jin dadin faruwan shi. He surely have so much effect on her sai dai duk yanda ta ke ji, duk yanda zuciyan ta ke azalzalan ta she is willing to resist everything, willing to resist the urge to fall for him. Runtse idanun ta tayi saboda zafin abinda ta ke niyyan furtawa a gare shi "Am sorry Faroukh if i make you feel that way, ban ce nima ban jin abinda make jin ba sai dai wlh ba zan iya, i just can't do it" hawaye ne su ka fara fita sharara a idanuwan ta.
"But why?" Ya fada da kauraran murya, ba ta amsa shi saboda haka yace "Dan Allah ki daina kuka muyi magana" da kyar ya iya lallashin ta ta dawo hayyacin ta, ita kanta mamakin kukan nata take, she don't know she can still be weak like this, she have been strong for years ba ta tuna sanda tayi hawaye, kai duk nacin Namiji ma ba ta bari wani abu ya shiga tsakanin su.
"Kar ka ga laifina dan Allah ina so kaji dalilina a yanzu" bai tmby ta ta fara bashi labarin. "A Maiduguri na taso, baba na ba laifi yana da kudi na rufin asiri dai dai gwargwada, matan shi uku, mahaifiyata ce ta farko. Nice ta biyu a gidan sannan kuma a gabadaya gidan ma, kanne ko kadan ya rage su cika Ashirin saboda duk mata banana Allah ya basu yara dayawa. Gsky Alhmdlh gidan mu ba wani rashin hankali sosai, sai dan yan kanana nan maganganu da za kaji ana yi kasa kasa. Bsrin ma akan yan dakinmu ko dan saboda soyayyan da mahaifiyar ta ke mana, ita mace mai wa yaran ta wani irin makahon so da a ko ina bata iya boyen shi. Zaka ji ta na Umaymah na, Aisha na, Aliyu na da sauran. Kullum dai kaji ta maganan yaran ta ne a bakin ta. Mahaifin mu kam bai wani nuna banbanci tsakanin mu kuma gidan mu gidan Mutunci ne sai Sam barka. Matsala ta ta fara ne ranar da na dauki kafa na tafi garin Kaduna wurin kanwar mama na. Sauka ne garin Kaduna kenan na jawo trolley na ina Neman taran abun hawa sai ga mota ta tsaya a gabana, loakcin duka duka SS1 nake hakan yasa ko kallon motan ban yi ba. Amma bawan Allahn nan sai da ya san yanda yayi yayi convincing ina na shiga motan shi. A hanya sai dadin baki ya ke min ta hanya gaya min kalamai dada da har mu ka isa gidan da zani. Wayata ya amsa ya samin numban shi, tun daga ranar ya fara kira na a wayan tun ban sakewa dashi har na sake, Barin ma in ina tuno labaran da kawayen na ke bani kan samarin su ni kuma bani da su, tuni na saki jiki na dashi ko bakomai in na koma maid na samu labarin da zan ba kawayena. Zayd maye ne a fagen soyayya, cikin kwanaki kadan sai da ya tabbatar ya kama ni a hannu, sau daya na sha Satan jiki mu fita tare ya kaini shopping, da yake ma a Abuja yake sai da kullum yana hanyan Kaduna saboda ni har na gama hutun. Lokacin kuwa ba abinda na sani bayan shi, komai ma in dai daga gare shi ne to fa ban ganin bakin shi, soyayyan shi kawai na sani, na so zayd fiye da dukkan wani iyawata, na mishi soyayyan da banji zan kara ma wani da Namiji a duniya kuma. Babban dana Sanin da nayi kuwa shine lokacin da zan koma maid, har moto park aka sani a mota sai da na bari ya fara tafiya nayi wayan karya, nan da nan na saki kuwa ina fadin a ajiye ni an mana rashi yanzun nan dole in koma. Ko tsayawa sauraran driver in da yake cewa ya za ayi da kudin ban yi ba. Ina fita na kira Zayd ya zo ya dauke ni sai Abuja. Suka duka lokacin shekaruna sha biyar ne amma haka na sabi jiki na bi zayd hotel saboda ba abinda na sani banda shi. Ba irin soyayyan duniya da zayd bai nuna min, ni kuwa na shgalta gabadaya da irin duniyan da na fada. Abu daya da ya kara dulmiyar dani shine yanda yayi ta kashe min kudi, ba Wai akwai abinda na nema na rasa bane Aa, abin kawa na duniya Wanda na san a gidan ba za ataba siyan min shi ba Zayd ya dinga siya min, ya canja min waya na wullar da waccan saboda kar ma a same ni daga gida. Sai dai dare nayi ya dauki hanyan da ya ke bukata, bai taba sa hannun shi a jiki na ba hakan yasa ko kuma rashin wayau ne ya sani tunanin ba abinda zai min. A daren ya karbi budurcina ya gurza ni son ranshi kuwa, daga baya kuwa ya dinga tarairayata har asibit ya kai ni da ke bakarami wuya na sha ba. Dare nayi ya kara komawa, har yau what am guilty of kuwa shine I enjoy everything he did to me. Kwana na biyu a wurin shi yana nuna min tsantsar kulawa da soyayyar shi da ta matukar shagaltar dani. Ticket in jirgi ya siya min ya raka ni har airport na tafi maiduguri. Sai bayan mun rabu dashi na fara tunanin mai zan fada a gida, lokacin gabana ya fara faduwa, shiyasa ina isa garin Maiduguri na nufi gidan su kawata, nan na ajiye duk wani abu da nasan zayd ya siyan min banda waya, ita ta bani tsohon kayan ta nasa duk na firgice sannan na tafi gifa. Ashe wai hankalin su gabadaua a tashe yake, har Anty na da naje wurin ta a kaduna na same su sunyi cirko cirko su ka dinga kallo na, mamana kawai ta iya min magana. "Sannu" ita ma kawai tace ta fisgi hannu na zuwa daki, abinda ba ta taba min ba iya rayuwar ta tamu, mari kake ji ko ta ina sai da ta gaji sannan ta fashe da kuka ta bar dakin, to nima dai kukan nake yi. Ba kuma wanda ya kara bina sai da baba ya dawo gida, salin alin ya kira ni yana tmby na ina yaje, labarin da na shiryo na motan mu tayi hatsari nima da kyar na sha kwana na uku a wani kauye. Dariya ya fara yi sai yace "Au banda iskancin hadda karya kuma kika koyo?" Da farko nayi mamaki sai da naji Antyn kaduna na fadin "Umaymah in kika je? Ba kiyi tunanin zamu je muyi bincike a tashan motan bane? Baki na da driver in mu kayi magana ya sanar min kin sauka bayan kin sanar an muku rashi" Tab! Gabadaya ma ni tunanin bai zo min ba, daganan kuma banda wani bakin magana duk zagi da fadan da aka dinga min. Ga gori daga abokan zaman mama, suna fadin soyayyan da ta ke nuna mana ne ya jawo komai. zayd ko soyyaya mu ka ci dayi, in takaice ma har zuwa yayi takanas daga Abuja zuwa maid kawai dan ya ganni, haka na kara bin shi hotel mu ka aikata masha'anmu. Kwanan shi uku a maiduguri, shi da wani abokin shi wai Hafeez, kullum sai mun hadu dashi. Tashin hankalina ya fara ne bayan two weeks da zuwan shi maiduguri, gabadaya sai zayd ya dauke min wuta, ko na kira shi bai cika dauka ba wani lokaci ma abokin shin nan Hafeez ke dauka ya na min wasu maganganun banza, na tura text sau da dama, a cikin har da wanda nake fada mishi ko da ya same ni ne ya ke min hakan. Daga karashe kirana yayi ya wanke ni akan kar in sake kiran shi. Ka tuna nace maka lokacin SS1 nake, gabadaya shekaruna 15 ban sa mai ke min ciwo ba, cigaba da kiran nasa nayi karshe ma sai yayi blocking. I felt so heartbroken to an extend da harna fara fita hayyacina, gida kullum cikin ciwo, tun dawa na daga kaduna iyaye na su ka fita sabga ta hakan yasa ni kadai na ke nukurkusa ko kanne na ba kowa ke tanka ni ba. Duk abinda zayd ya min bai hana na cigaba da kiran shi da duk numban da na samu ba, sai dai kowani kira da irin nashi wulakancin.
Da ciwo ya cini sosai, dole Mamana ta sani a gaba mu kaje asibitisaboda baba kamya zare hannun shi akaina, barin ma da ya samu labarin naje hotel wurin saurayi. Sai dai duk wani test na typhoid da malaria, sugar da sauran su anyi amma ba a ganin komai sai kuwa jinina da yayi kasa. Sosai na yi wani mahaukacin jinya duk maganin da ake bani ba sa min aiki, har makaranta dole tasa na ajiye agefe banda karewa ba abinda nake. Nan fa dr yayi shawaran yi min scanning, gwajin farko na Hiv ya nuna positive, shi kan shi wanda yayi test dan rudewan ganin karantar shekaru na sai da ya dinga yin test in da different kits amma it showing the same thing. Gashi lokaci ne da ake mugun kyaman cutan, hmm Faroukh naga rayuwa, takai ta kawo a gidan mu Mamana ne kawai ke iya min magana har ta bani abinci da magani shi ma cup, spoon da plate ina daban a gidan kullum karewa nake. A cikin wannan rayuwan na ziyarci kawata Siyama, da tun farko ita na kai wa ajiyan kayan da Zayd ya bani. Yanda kasan karya haka siyama ta min, sai banyi wani mamaki ba ganin yan uwana ma sun ki ni balle ita. Rayuwa fa gabadaya ta juya min, bayan na fito gidan su ina kuka ne na hadu da wata mata neighbors in su siyaman, a kullum duniya in na ganta ni da siyama mun di ga tsine tsine kenan saboda sanin da kowa ya mata a harkar mata gashi duk na ganta ta dinga bina da wani mugun kallo. Yanzun ma zuwa wuri na tayi tana tmby na lfy? Banda wani mafita sai na tanka ta barin ma da na fahimci ita kadai ke burin min magana ahalin da nake ciki. Jana tayi gidan ta, sai da na natsa ta tmbyn abinda ke faruwa, na ko fada mata komai. Murmushi naga tayi tace "Ai su daman mutane haka su ke, kar ki wani damu domin kin zo inda za a tarairaye ki" Wani irin kulawa ta bani na musamman, gidan mu kuwa ba wanda ya wani damu ban dawo ba sai mamana ita ma da taji labarin inda nake tazo ta sameni fir na ki binta nace mata zan zauna inda ba a kayamata. Wani irin soyyaya Hajiya safiyya ta nuna min sannan a hankali tana sa min ra'ayin harkan ta tun ina ja da baya amma tarairayan da takebani na yaudarata harna bada kai bori ya hau. Duniya ta dawo min sabuwa, zayd ko tuni na share shi sai dai na dauki alkawarin rama abinda ya min ko da kuwa ta wani hanya ne, kullum duniya kara goge na ke cikin sabuwan duniyata, ga kudi da su ke zaman min duk lokacin da nake so. Da maganaya fra yawa, ga mamana ta na zuwagidan Hajiya yasa Hajiyan ta kwashinimu kayi kano inda na cigaba da cin kare na babu babbaka sai bayan rasuwan tana koma maiduguri na fara zaman kai na ta duk hanyan da yazo min. Toh Faroukh kaji labarina a takaice, nasan ba za kaso had a zuri'a da mai fama da lalura irin tawa ba da kuma rikakkiyar yar lesbian" Gumin da ya fara keto mishi ya share, still idanuwan shi na kanta.
"Abinda ya wuce ya wuce, but everything is wrong in the way you solve your problem"
Amincewa tayi "Da na koma Kano na koma schl, i study psychology in university kuma nayi realizing duk wani mistakes ina, i just can't clear them but can you believe yanda yan uwana ke sona a yanzu? Kowa alfahari ua ke da cigaba na wanda da kudin abinda su ke zagi na akai nayi su."
"Ai yanzu an dauki kudi sune mutum Umaymah, but tell me kin dau fansan?"
"Shi ya kawo ni kasan nan" da sauri ya daga kai yana kallon ta"Zayd in na garin nan ne?"
"Aa, there is this girl, daya daga cikin yaran da nake mu'amala dasu ta hada ni da, ina ganin ta nasan cewa she is the one i've been looking. Ta amince da bukata ta, muna gab da cin nasara nayi realizing it can't be good sai aka ci saa ita ma yarinyar ta janye and i don't know what happen but currently tana hannun hukuma ana zargin ta da yunkure kisan shi zayd in" rike kai Farokh machina yayi domin shi wannan kwamacalan ya mishi yawa.
"Amma kina ganin yarinyar za ta aikata?" A hankali ta girgiza kai "Nasan Suhaimaba za tayi ba"
"Amma meye sa ba kije kin kareta ba?" Kallon shi tayi kaman wacce ke shirin dago wani abu tace "Faroukh i have a reputation to save, am a public figure people looks of to me" In understanding ya juya kanshi. Ba su wani kara magana ba ya lallabe ta ta kwana gidan, ta riga da ta san cewa yanzi tunda ya san me ke faruwa da ita ba abinda zai yi yunkurin mata domin a yanda take ji ko ya neme ta bazata iya hana shi but now da ta fada mishi labarinta she feels ease knowing ba ta da matsalan rashin yafe wa kanta da zata yi muddin ta sa mishi cutan nan.
...
Bayan sun rabu da Dr Fahad, Barr daukan hanya kaduna yayi. Gidan Anty ya fara zuwa sai dai yana shiga gidan ya hadu da Anisa banda kuka ba abinda take. Yana cikin tmbyn ta abinda ya same ta sai ga maryam ma ta fito daga dakin, da alamun muryan shine ya fiddo da ita. Sake baki yayi yana kallon ta ita ma kukan ta ke "mimi wha.." Katse shi tayi da cewa "Why why?" Still dai bai fahimce taba, isa gare ta yayi ya riko kafadun ta "Tell me what is happening Mimi"
A hankaki ta furta "Anty Anty" kwalalo idanu yayi yana fadin "meya samu Antyn mimi, Anisa tell me what is hapening mana"
"Uncle Musty why not ba za ka ba wani case in nan bane wai? Ba kayi tunanin yin shi zai sa Mom cikin matsala ba?" Anisa ce ke magana yayi da kwalla ke zuba a idanun ta. Juyawa yayi ya kalli maryam tace "She almost had a stroke fa, you are accusing her own child akan wata karuwa Abban Haydar" bai damu da kiran suhaima da tayi karuwa ba yace "My God! Mimi ina Antyn yanzu?"
"Tana asibiti Dad ke kanta, an hana kowa zuwa wurin ta" zaman dirshan yayi ya zuba tagumi cikin rashin sanin abun yi.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top