Ashirin da daya

A gajiye likis mu ka koma gida ranar, ko kallo na Zayd bai kara yi ba har nayi parking, daukan Amal yayi da ba ta san inda kanta ya ke ba yayi cikin dakin ta. Ni baccin ma ji nayi ba abinda zan iya yi, haka nan na zauna a falo na kunna film duk da hankali na bai wani kai, mutane kawai na ke gani suna ta displaying action. Sautin da ya ke fito daga dakin Amal yasa ni sanin abinda ke faruwa, daman ganin abinda a club in nasan dole hakan zai faru. Its been long sex yashiga tsakanin su as far as i know, they are all louders hakan yasa na ke ganewa.

Na dade a falon ni kadai ina kallon TV ko kuma ince film yana kallo na dan gabadaya ban sa abinda ake ba. Tunanin kunci rayuwa da tausayin rayuwa irin tawa ya sa naji gabadaya duniyan na neman fice min a kai. Kwallan da na dade ban zubda bane naji suna zuba a idanu na, na dauki lokaci a haka ina jin kaina na juyawa yayin da hawayen ke cigabda da tsiyaya. Ban ji fitowan Zayd ba ko takun shi sai tafun hannun shi da naji kan fuskana, hawayen ya laso da dan yatsan shi manuniya. Yatsan ya koma bi da kallo ya tsaya a kaina kaman mai son gano wani abu, can ya girgiza kanshi sannan ya saman ma kanshi matsugun ni a daf da inda nake. Hannuwan shi ya ratayo ta kan wuya na, sai lokacin na iya daga kai na kalle shi, idanuwan nan sun yi jajur kaman wanda ya sha kuka ya koshi.

Bai dai ce min komai ba har na fauke idanuwa na daga kan shi, kara jawo ni jikin shi yayi ya juya yana fuskan ta na da kyau. "Why are you here?" Na tmby, magana na farko kenan tun bayan fitowan shi.

"Suhaiima please" sauri dakatar dashi nayi da hannu na, a hankali nace "tmbyn ka kawai nayi nd you can only give me an answer" kan shi ya sadda kasa, focus in shi gabadaya na kan yatsun kafana. Ban san mai yake nema a wurin ba. "I want to check on you" more like a whisper maganan ta fito daga can kasan makoshin shi. Siririn tsaki na ja, na janye jikina daga nashi "You can pretend all you want, na riga da na gane komai" saurin girgiza kai yayi yace "pls babe kar muyi haka, ki saurare ni kafin ki yanke min hukunci"

"Wani saurara kuma Zayd? Bayan abinda idanuwa na da kuma idon duniya su ka gani. Ba ma wannan ba, me kuke son in fada wa Mum bayan yarda dani yasa ta amince ma zamana da yar ta, tun dazu na ke ganin miss calls inta" zaro idanu yayi, yace min"dont tell me abun nan yayi yawo?"

"You can check the media ai nd ka kwantar da hankalin ka am not talking about the kiss" ba wani reaction in da yayi sai can yace "am not happy seeing you with Hafeez, kinsan wanene Hafeez? Ta ya zaki biye mai har ki bari ya taba jikin ki bayan kinsan hakan bai dac..." Kaman ya karasa nayi saurin mikewa ina kallon shi cike da mamaki ina jan baya "kai har ka san abinda ya dace da wanda bai dace ba Zayd? Ko kuma kai da kake tabanin muharrami na ne? Fada min yaushe ka fara kokarin kiyaye dokokin Allah" jin yanda na ke magana a fusace ne ya sa yayi saurin mikewa.

"Yi hakuri jewel zo ki zauna Dan Allah muyi magana" tsaki na ja kaman ba zan zaunan ba sai kuma na koma inda nake kafin in mike. Ina jin wani irin tafasan da zuciya na ke fama da, i so much hate my life to the extend na ke jin gwara ayi komai kawai a kare ta cikin kankanin lokaci ko na samu in gina wa kaina sabon rayuwa dai dai da tsari na.

Girgiza kafa nake in hararan shi, hakan ya sa shi yin murmushi. Kwantar da murya yayi ya fara magana "nasan ban kyauta miki ba Jewel but kinsan Amal, kinsan yanda ta sani cikin rayuwar ta abu ne mai wahala kwatsam ace ba ma tare da ita, shi..."

"To mai zai hana ku kasancewan a tare? Kai ma fa na gane kana bukatar hakan. Dan haka please ka kyale min rayuwa tun wuri Zayd"

"Ba zan iya" yayi saurin fada "Zuciyan Amal ni ta ke so sai dai kuma ni nawa zuciyan ke ta hange, ke ce a cikin ta. Ban zan miki karyan ban son kasancewa da Amal ba saboda ita in wata jigone babba a rayuwata, i like her sai dai  i have many reasons da yasa ni kasancewa a tare da ita. Nasan kin san me ya shiga tsakani mu a daki, she wanted to and i can just resist her. Amal mace ce Suhaima sai dai ban mata irin son da ta ke min. Ko da inma tausayin ta yafi son yawa, i befriended because of her eloquence amma sai mu ka tsinci kaman a cimin rayuwan da kika same mu."

Ban ce mishi kala ba har ya gama koro min bayanin shi. "Baki ce komai jewel" kallon shi sannan na juya kai gefe "banda abin cewan ne . kaga it better kawai kaje ku dai dai ta da budurwa ka, i can't stay in this kind of relationship ni dai da daraja ta, i just can't be a second option to someone" tagumi yayi, sosai na ke hango tashin hankali akan fuskan shi "Yanzu me kike so? Suhaiima" kaman zai yi kuka tsabagen yanda muryan shi ke rawa. In ba wai dan na san raggonci namiji akan soyayya ba, da sai ince nayi mamaki yanda mutum hadadde, mai ji da takama kaman Zayd zai tsaye a gabana yana marairai ce min ba. Wlh da farko na dauka yanayin jiki na ne kadai ya jawo min soyayyan Zayd a gare ni, a hankali na ke fuskanta iya gskyn zayd soyayyan gsky ya ke min. Zayd in nan ne dai, da ya san sirrin soyayya, ya afka mata da dama a cikin ta ya kuma juya su son ransa. Har a jiki na ji nake hakkin matan da zayd ya yaudara a baya ne ya kawo shi gare ni har ya kai da afkawa gabadaya, in ba haka ina ni? Ina Zayd? Duk da matsayi da na siyan wa kaina. Dan ko Club mu kaje sai kafi jin tashi na akan na Amal, ita kam kullum da kyar mu ke lallaba wa mu koma.

"Zayd Almansur" na kira sunan shi, bai amsa sai kallon da ya bini dashi da tagumi manne akan fuskan nashi. "If you truly love me ina son ka bayyana wa duniya kowa ya sani, ko nasan matsayi na. Am tired of the hidden game" girgixa kan shi yayi kaman wani yaro karami yace "nikam ai daman ke kika hana ni fada, bara in tashi Amal in in fada" da gaske tashin yayi, sai da na jawo hannun sa sannan ya juyo yana kallo na "a Abuja kaman yanda mu kayi" gyade kai yayi sannan ya koma ya zauna, yana cigaba da nuna min iya gskyn shi sona yake. "Jewel kin san yanda na ke ji akan ki kuwa? I wanted to punch Hafeez so much dana gan shi yana rike min ke. Ina son ki sosai babe ina" yana maganan yana riko tafi hannu na, kallon su ya ke sosai yana maganan. "I've always want to have kid" ba tare da na dago na kalle shi ba nace "you have a wife" tabe baki yayi yace "I don't want her children" idanuwa na akan shi ina shirin yin magana yace "she don't want to have my children either, ko tayi cikin ma aborting ta ke, she is always taking pills ni kuma na gaji na kyale ta. Now she badly wanted the kids ni kuma ban bukata a gareta kuma" suya naji zuciya ta nayi, wasu na neman yaran amma ita wannan gudun su ta ke ma, yanda na ke son ganin jini na ina jin ko dan shege ne, duniya ba wanda ya isa hana ni rainin abu na.


"Ina son yara kyawawa daga tsotson ki Suhaiima, ai zaki bani ko?" Gyade mishi kai kawai nayi saboda banda interest akan zancen. "Masu kama da ke" ya kara fada, dan zaro idanu nayi nace "masu kama da kai dai, you are more beautiful among the two of us."

"Liar" tsakulan hanci na yayi "i love dark ladies, Suhaiima you are just a dream come true, tun ina saurayi na ke son bakar mace, i love the melanin sai dai am not so much lucky. I like your eyes sosai" hannun shi ya sa ya shafo idanun, a dole na na lumshe su. "Da dan karamin bakin na, i couldn't wait to devour one day" murmushi kawai nayi, ya cigaba da tsaro min kalaman shi masu dadin sauraro amma fa ni kam a kunne kawai ya ke tsaya min. Zayd ya iya soyayya wacce za ta tafiyar da hankalin yan mata, ni kam dai wani ya riga da ya ma tawa illan da bai bar ma wani wurin shiga ba.

Washegari, dole mu kayi postponing flight inmu zuwa next day, ni da Amal ne kawai saboda zayd yace akawai meeting in da za suyi a wani gu tare da ogan shi Hafeez. A daddafe mu ka farka bayan mugun baccin da mu ka sha, cook in Amal ta riga da ta mana abinci. Muna ci Zayd ya zo fita damu wai zai kaimu shopping. Amal tayi tayi ya bar shi amma yana ta insisting. Hakanan mu ka tafi, duk ma kayan ciye ciye ne mu ka dauka daganan ya ja mu beach.

I so much like it in the beach, mu uku mu ka zauna wuri daya muna sharing the best moment, lokaci zuwa lokaci yana satan kallo na duk da Amal da ke like a jikin shi kaman wata mage. Kaman wacce aka tsikala ta mike tsaye har da dan tsallen ta, the girl can be fun and childish. "I have a plan" ta fada tana wani rolling idanun ta "let do a game call Tell us ten things we don't know about you." Duk dariya mu kayi, mu ka hada idanu ni da Zayd, kashe min gira yayi ya juya wurin ta "okay bestie go first, we are all ears"

"Yeah" ta fada da dan saurin ta ta koma jikin shi ta fara magana "No judgement fa" duk amincewa mu kayi sannan ta fara lissafo wa

"1. Nasan ba ku sani but i so much like the name gigi Amal.

2. I prefer Lagos club to Abuja's

3. I like making friends sai dai i always fail in making the relationship work

4. I feel like my relationship has an underneath problem that will unfold

5. I hate taking wines and alcohols

6. I don't really like dark chocolate as i claim to

7. Lagos life isn't as bad as am exaggerating

8. The idea of getting married scared me

9. I don't really like it at my fathers house

10. I don't like been independent on my own“

Ba wanda ya katse ta har ta gama, sai lokacin na yadda ko ya kake da mutum akwai abinda ya boye ma kanshi sanin shi kadai. Imagine, wai Amal hate alcohol and wine, duk yanda ba ta iya dauke idanuwan ta daga kan su, sai dai in bata gani ba kuwa. "Besty ba fa kya son dark chocolate kika ce?" Zayd ya tmby cike da mamaki, like she is always taking them a ko da yaushe. Gyade mi shi kai tayi tana dariya kasa kasa "it just some sort of addiction, at first i pretend loving them and then it turns that way, Love you can go next, asking question isn't part of the rules.

Dariya yayi sannan yace " ni kam ta ina ma zan fara?"

"Ko ina ma" a tare mu ka bashi amsa ni da Amal.

”Okay:

1. I like kids, as in my own kids.

2. My wife Amina was my first love and i still feel something for her

3. I admire my Mom even though we were never on good times

4. I hate going to work

5. Am eager to have a second wife of my dream

6. I hate publicity, though am always getting them.

7. I like employing people and making friends out of them

8. I wanted to be a Police man

9. I really don't have any friend whom i share my problems to

10. I enjoy having people who raise my status around me" yana gama wa ya saki murmushi, all through maganan da yake focus in shi na wurin ruwa, hakan za ka gane he is saying things directly from his mind.

"You like kids? I never know" Amal ta fada tana kallon fuskan shi, shrugging shoulder yayi yace "i just say things i couldn't avoid ne, no matter how i want to" tafa hannu tayi "It okay, Frnd your turn" annurin fuskana ne ya dauke dan ni ban ma san me zan ce musu ba. They may be saying the right things ni kam ban son in musu karya, domin zamana da su kawai gabadaya karya ne.

"Am feeling hungry" nayi saurin fada "Eyyah sorry" Amal being Amal tayi saurin fada, a cikin ledan shopping bags in da muka zo dasu beach ta dauko wani ledan tana mika min "pepperoni pizza, you gonna like it" amsan nayi ina murmushi na.

"You can still tell us while you eat" Zayd da curiousity ke cin shi ya fada, dan ita Amal har ta manta ma. "Yeah besty please tell us" ajiye pizzan nayi nace "okay kun san is not good to talk while eating"

"Yau kika san rules in kenan?" Zayd ya fada, dariya nayi na fara cin pizza in. To mai ma zan fada musu? They don't know almost everything about me, i don't know the ten to choose.

"Oya tell us" Zayd ne yayi maganan.

"Yayana ba zaka bar wannan maganan ba ko? I have no idea mai zan fada muku"

"Then we can ask you?" Amal tayi saurin fada, duk da tsoron da naji amincewan nayi.

"Do you love somebody?" Ta tmby, sai da mu ka hada ido a sace ni da Zayd sannan na juya nace mata "Yes"

"Who is he?"

"This is the second question and i will answer,   wani ne kuma soon za ki ganshi"

"Frnd wai ke wayau ko? Naji and the next question why are you hiding him?"

"Saboda ina so ya zame miki surprise lokacin da kika ganshi" tabe baki tayi tace "ba dai kyau, next question ur favourite food, you never tell me one" kallon pizzan da ke gabana nayi nace "Pizza" dariya tayi sosai sannan ta kara cewa "Novel or movie"

"Novel" na amsa mata, daga haka tace she is done with her five questions, Zayd yayi sauran. Sai da gabana ya fadi saboda ma irin kallon da ya min tun farkon.

"Kanwata what is your level of Education?" Folding lips ina nayi sannan a hankali nace "Just first degree"

"Degree is not just, a bangaren wani course" kaman ba zan bashi amsa ma sai can kuma nace "Medicine" dukkan su biyun a tare su ka juyo suna bina da kallo "Medicine Friend?" Amal ta fada, da alaman mamakin ma yafi yawa a bangaren ta. "Wow! Housemanship?" Zayd ya tmby. Girgiza mishi kai nayi nace "tukunna dai but soon"

"But why do you choose to focus on something else?" Zayd in ne ya kara tmbyn "I want to enjoy the pleasure of something else, i will get back to it ai" duk mamakina su kayi nit knowing the real truth behind everything.

"Ina ne state of origin inki?" Zayd ya bukata

"Borno" na amsa mishi.

"Ya aka yi kika zo Abuja to?"

"Boko haram crisis" na amsa, yanda nayi sounding so real ya sa ya yarda, it truth though amma partially.

"But Bestie me ya sa kika boye min? Kika ce you are family" kallon shi tayi looking apologetic tace "Dad ina ma fa Dan Borno ne and ina jin Suhaima kaman yar uwa, we are even family now" side hug ta bani, na rungema ta tare da share dukkan wani guntun kwallan da ya taru min, wadan na tuna asalin sirrin rayuwata ne.

"Suhaima is a nice girl, i like her" Zayd ya fada yana kallon Amal, murmushi ta mishi tana kara fadin "sorry for not telling you love" daganan zancen ya wuce bayan Zayd yayi ta insisting inyi Housemanship in mu koma Abuja, duk yanda ya so kin amincewa nayi nace ya barni sai zuwa next year kafin nan am done. "She get a mission here love let her" Amal ta fada.

Sai kusan magreeb mu ka koma gida, a nan ma wani hiran ne ya barke. Daga baya na ja jiki na nayi daki. Ina zaune text in Zayd ya shigo wayana. “babe why didn't you tell me about you before? I want to know every single thing concerning you”  Daman nasan za ayi haka, don haka na tanaji dukkan abinda zan fada mishi in ya tmby. “it wasn't a nice story dear, i lost them both during the crisis due to bomb blast in our house at night, rashin sanin ina zan nufa ne ya sa na biyo makociyan mu wacce ta ke bazawara garin lagos,  unknown to me gidan karuwai ta kawo ni so i have to left” Emojis in kuka ya turo min. Daga baya ko bayan Amal tayi bacci ya zo dakin, da ke shaye shayen ya zame mata addiction duk in bata sha ba ta iya bacci sai taji kaman za ta shide, ya riga da ya shige ta sosai don ko Zayd bai shan abinda ta ke iya kwankwada.

Da ke dan guntun labarin da na bashi ya taso min da tunanin rayuwata, nan da nan na rikide  na zama wata aban tausayi idanuna na sun zama jajawur dau. Ko da ya shigo ya riske ni a haka, he was so touched. Lallashi na ya dinga yi, nan na bashi labarin duk abinda ya fatu dani, yawanci zallan karyane duk da akwai gaskiyan sosai a ciki sai dai ban bada shi a yanda ya kamata ba. Rungumeni yayi har da dan kwallan shi yana min alkawaruruka, akan in na aure shi zai zame min gata a duniya, he will always be there for me, zai zame min duk wani abunda na ke bukata. In short, ba abinda zayd bai fada min ba, ni in ina kallon yanayin shi ma wani irin tausayin shi da ban san dashi ba ke tafiya dani. Nan ya ke sanar min maman shi yar yobe ce, i appear shock saboda ban san wannan in ba. A cewar shi za a nemo yan uwana a bornon sai a je in an tashi neman auren nawa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top