Ashirin da biyar

Yau ma kotun a cike ta ke taf, dan har ya kusan ninka zaman da aka yi na farko. Bayan Alkalin ba ya buga a fara sauraron kara, Barr Mustapha ya tashi kaman yanda aka bukata. Da takardu guda biyu a hannun shi ya fito kai tsaye ya mika wa magatakarda.

"Ya mai mai girma mai shari'ah ina bukatan kotu ta bani daman gabatar ds wannan takarda a matsayin shaida na cewa wacce ake kara ba guduwa tayi kaman yanda lauyan gwamnati yayi ikirari" bayan alkali ya bashi dama ne ya cigaba da cewa "Ya mai girma mai shari'ah gobarar ta faru da ya ritsa da Zayd Almansur ya faru ne a ranar 31st watan july kaman yanda binciken mu ya nuna mana. Wannan takardan da ke hannu na kuma takarda shaidan rike Suhaima da aka yi a asibiti ne 1st August a sanadiyyan hadarin mota da ya gifta da ita a kaduna. A maganan da nayi da client ina, gigicewa ne ya sa ta barin asibitin da aka kai su bayan goboran nan har ta shigo motan Kaduna saboda rashin madafa bayan yan uwan Zayd sun tafi da nasu sun barta ita daya a wurin. Watan Kusan uku tana jinya a asibitin a sanadiyyan karaya da ta samu" nuna takarda yayi a matsayin shaidan record na asibiti "Ya mai girman mai shari'ah bayan ta warke ne ta zabi ta cigaba da zama a wurin wadanda su kayi jinyan ta a asibiti saboda rashin wani na ta a kusa, don haka malama Suhaima ba guduwa tayi ba illa ma nata jinyan tayi a asibiti." Amsan takardan Alkali yayi ya duba sannan ya jinjina kan shi alaman gamsuwa."

"Lauyan gwamnati kana da abince wa?" Girgiza kai yayi nan alkali ya sanar za a fara sauraron karan.

Lauyan gwamnati ne ya tashi sannan ya fara jawabi kaman haka "Ya mai girma mai shari'a in za a bani dama ina da gamsassun hujojin da zasu tabbatar da cewa wanda ake zarhi na da hannu dumu dumu a zargin da ake mata"

"Go ahead and present your witness" alkaline ya fadi hankalin shi na kan court in gabadaya.

"Da farko dai zan so in yi ma wacce ake zargi wasu yan tambayoyi" bayan kutun ta bashi dama ne ta koma sa Suhaiman fitowa gaban witness box, karasa wurin ta yayi yana kallon ta da murmushi dauke akan fuskan shi yace "Malama Suhaima right?" A hankali ta amsa shi. Yace "ko kinsan Zayd Al-mansur? Kuma waye a gare ki?"

"Saurayi nane" ta fada kai tsaye idon ta a kasan domin ba ta iya fuskantan mutanen da ke cikin court in ba.

Dariya prosecutor in yayi yace "Da kyau, Amal idriss Hayatudden fa?"

"Kawata ce" ta amsa a sanyaye, murmushin ya kara yi ganin yanda yarinyar ke bashi hadin kai cikin sauki.

"Da yawan mutanen da su ka san zayd su ka kuma san Amal sun san su a tare, ma'ana a matsayin saurayi da budurwan da su ka debi shekaru da dama suna tare, shin ko zaki iya fada ma kotu ya akayi kika dawo budurwan zayd in? Bayan kuma su in masoyan juna ne?"

Shiru kotun ya dauke, Suhaima kuwa idanun ta na kasa ta rasa ta inda za ta fara amsa wannan tmbyn. Kana ganin yanayin ta kuma kasan jikin ta yayi sanyi ta rasa bakin magana.

"Tou shknn tunda ba ki da amsan wannan amma za ki iya fada min mai ya faru ranar da gobara ta tashi a gidan zayd in" nan kaman tiryan tiryan ta bada labarin duk abinda ya faru.

"Nagode amma ko malama Suhaima za ta iya fada mana me ya zaunar da ita a gidan Al-mansur bayan kuma ba aure a tsakanin su kaman yanda addinin musulunci ya wajab ta"

Da sauri barrister mustapha ya tashi "objection my lord, lauyan gwamnati na kokarin sako addini a inda bai kamata"

"Sustain, Ka kiye lauyan gwamnati, this is not a shari'ah court" amsawa yayi cike da ladabi sannan ya juya gun Suhaima yace "ki cigaba da bamu labarin abinda ya faru a wannan rana har zuwa barin ki Abuja" labarin ta fada kaman yanda aka bukata.

"Wani dalili yasa ki barin asibitin bayan saurayin ki da kike ta kokarin ceto yana kwance baki san halin da yake ciki ba?"

"Ai na fada maka hiran da naji yan uwan shi nayi akan farkawan shi hakan yasa nima na kama gabana"

"In zan dubi labarin nan naki, kina so kice ke kika bawa Zayd abinci yaci kuma ya fara aman jini amma kuma kina so in yarda ba ke kika zuba mishi wani abu ba?"

"Wlh ban zuba mishi komai" ta yi saurin amsawa muryan ta na rawa, yanayin fuskan ta kuwa na cikin rikicewa. Kallon ta Barr Mustapha ya ke ta kokarin yi yana son aika mata tayi calming kanta coz her action is witness by the judge sai dai attention in Suhaiman gabadaya ya karkata gun lauyan gwamnati.

"To waya zuba" ba ta amsa shi ba sai girgiza kanta da tayi tana son tabbatar mishi ba ita tayi. "Am done questioning her my lord" rubutu alkalin yayi sannan ya dago ya kalli Mustapha. "Barr kana da abun cewa?"

"Ban dashi ya mai girma mai shari'a" Daganan lauyan gwamnati ya kara presenting next witness, Faroukh ne hankalin shi kwance ya karasa wurin witness box yana amsa tambayoyin lauyan. Gabadaya zargin da yake a kanta sai da ya fada da kuma abubuwan da ya gani da wanda kuma yaji da kunne shi.

Bayan lauyan gwamnati ya gama tambayoyin shi, kotun ta bukaci ko Barr Mustapha na da nashi tambayoyin. Amsawa yayi da Eh sannan ya mike a hankali ya taka zuwa witness box in da Faroukh ya ke a tsaye. Idanuwa su ka hada na da sakwanni sannan bare Mustapha ya juya kaman wanda bai ma taba ganin Faroukh in na yace "Faroukh, ka mana bayanin abin da ke tsakanin Suhaima da ogan ka Al-mansur gar ka ma kayi ikirarin cewa Cin amanar kawar ta tayi ko miye dalilin ka na fadin hakan?"

Dan tabe baki Faroukh yayi, ya juya kan shi daga kallon Uncle in nashi kafin yace "Ai a fili yake, they were even living together kuma ina jin da bakin ta ta fada cewa saurayin ta ne"

"Haka ne" Barr ya cigaba da magana "Amma ban tunanin hakan zai haka right cewa raba su da kawar ta tayi, in kawar ce tace ba ta son shi fa?" A nan Faroukh bai ce komai ba, sai tunanin da ya dan fara darsu a ranshi, is Uncle Musty going against him? Tabbas Suhaima evil ce.

"Faroukh kama kotu bayanin sau kusan hudu kana haduwa da Suhaima a lokacin da take kokarin aika ta rashin gskyn kaman yanda kake ikirari to amma ta ya kake tunanin hankali zai dauki cewa a dukkan lokuttan nan ba daya ba ba kuma biyu ba duka coincidence ne?" Sai da Faroukh ya daga kanshi sama sannan ya mai da attention in shi kan Barr "Ni dai kawai nafi yarda Allah ne ya zabe ni saboda ya tona mugun nufin ta"

"Kai dan baiwa ne kenan?" Yanayin da yayi maganan sai da ya girgiza Faroukh Baron ma da furucin ya sauka akan shi, lallai uncle musty is so serious akan case in nan. "Ni bance ba" dan dariya Barr in yayi yace "okay, to ko dai kai waliyyi ne in ba haka ba taya za ayi ce sau kusan hudu kana kama mutum yana aika ta sirrin da ya boye ma kowa? Ba fa kuma a wuraren aiki ka ke ganin ta ba, yawanci ma a waje ne." Nan ma dai Faroukh nai ce komai ba sai takaici da ta mamaye zuciyan shi yana mamakin duk yanda su ke da Uncle musty, duk yanda take girmama shi sai shine yake mishi haka a cikin jama'a kuma akan wata can bare.

"Ka fada min gsky laifin ka kafin binciken mu ya nemo min, You are stalking her ko?"

"Objection my lord" lauyan gwamnati ne ya fada. "Overruled" judge in ya amsa. Idanun Bare Mustapha akan abokin karawan shi, yayi murmushin kana ya juya wurin Faroukh. "Kana iya amsa tmbyn"

Da kyar Faroukh ya hado abinda zai ce "I have a life so i don't think ina da lokacin da zan ta bibiyan ta ta rayuwan bayan bani da wani gami da ita. Haduwan mu a vows El-yas na raka, sai next zasu fita da oga ni kuma naje bashi abu sai sanda naje daukan ta zan kai ta airport naji waya sai kuma randa mu ka hadu a blucabana, restaurant in kusa da apartment ina yake so I usually go there for my meals" jinjina kai Barr yayi. Sai lokacin ya maida idanuwan shi kan Suhaima da kanta ke duke a kasa. Mai da hankalin shi yayi kan Faroukh yace "Amma ya za ayi yarinyar da kake tsammanin tana da mugun nufi ka ganta a cikin gidan Ku tana zauna ba ka dau wani mataki ba? Bayan haka ma meya dauke ka tsawon lokaci kafin kayi reporting zuwa wurin yan sanda."

Kan Faroukh a kasa yace "I try talking to many of my family members, sai dai ba Wanda ya saurare ni saboda wannan yarinya mutum ce da matukar kwarewa wurin Nuna wata fuskan ta daban saboda Munafunci dake cike a ranta da kuma kudirinta"

"Ka gyara kalaman malam Faroukh, kotu za ta iya kama ka akan hakan" dago kai faroukh yayi ya dan juya gefe bai dai ce komai. "Nagode ranka shi dade iya tambayoyin da zan mishi kenan" bayan yan sakwanni Alkali ya bukaci ko lauyan gwamnati na da abince wa.

Mikewa yayi ya tako zuwa gaban alkalin. "Ya mai girma mai shari'a duba da irin bayanin da muka samu daga bakin Faroukh dama ita kanta wacce ake kara nake rokon kotu da ta kama mai laifi domin amsan hukunci da ya dace da ita as we do not need to waste time akan abinda ita kanta ta fada da bakin ta, ita ta bashi abincin sannan kuma ita kadai ne a gidan sai kuwa shi Al-mansur in, kuma a gaban ta yaci abincin ballantana ace wani ya shigo har ya sa mishi wani abun a ciki. Ina fatan kotu ta yi duba mai kyau wa jawabin da nayi"

Komawa yayi ya zauna kafin Barr Mustapha ya taso ya fara nashi jawabin kaman haka "Ya mai girma mai shari'a, kotu na bukatan tayi duba da idon fahimta akan wannan shaidan da aka bayar. Ba ta inda Faroukh ya fito yace yaji wacce ake zargi tayi wani magana akan kashe zayd Al-mansur illa ma sai wasu maganganu da yayi ikirarin yaji tana fada akan wani shiri wanda shi kanshi bai san na menene ba. Zan so kotu tayi watsi da wannan shaidan ba saboda ba ta is a gamsarwa  cewa wacce ake zargi ta aika ta laifin da ake zargi ta na. Da wannan na ke rokon wannan kotun ta daga wannan karam domin mu samu daman gabatar da kyawawan shaidun da za su tabbatar cewa wacce ake zargi ba ta aika ta abinda ale zarhin ta dashi ba, Nagode" komawa yayi ya zaune, bayan mintuna kadan alkali ya sanar cewa ya daga karan zuwa nan da wata biyu masu zuwa.

Tunda Did da Barr Mustapha su ka dauki Suhaima a cikin mota ba Wanda ya samu daman furta wani abu, tsit kawai kake ji sai ajiyan zuciyan da Suhaiman keyi lokaci zuwa lokaci. Ita kadai ce a baya a zaune yayin da ta daura kanta kan cinyoyin ta, gabadaya ta rasa gane wani tunanin ma ya kamata tayi.

"Where are we going?" Dr Fahad da ke tukin ya  tmby Barr Wanda bai amsa shi sai can kuma yace "are you planning on taking her somewhere ne?" Gabadaya sai yanzu su ke tunanin inda yakama ta su wuce da ita, abun ya sha musu kai ne ya kuma hade da basu samu ishashen lokacin sun zauna ba balls sun tattauna.

"Akwai gidan mu a nan, iyaye na na cikin garin ko mu kaita can?"

Nazari Barr ya danyi kafin yace "Ina ganin hakan fa ba mafita bane gsky, akwai apartment in da nake zama in na shigo aiki garin nan, ina ga mu kaita can"

"Its not risky kuwa? Ita kadai fa"

"No zan kira zeenah sai ta zo su zauna" daga haka ba Wanda ya kara magana har su ka is a apartment in da Barr in yake. Sannan su ka fita suka siyo mata dan abubuwan da za ta bukata har da kayan sawa ma. Sai daga baya Barr ya kira zeenah su kayi magana, ta amince zata zo but they needs to compensate her with something.


Seychelles

Din dirin din din din, ga  Amarya ga Ango. Abinda kawai kake jin yana tashi kenan a cikin da ake gabatar da kamun Adam da Amarya sa Rawan. Rashin samun masu busan algaita da kidan kwaryan ne yasa su ka nemi dai dai irin kidan aka sa shi a speaker. Wurin ko ya sha ado da kwarya kala kala manya da kanana da kuma ludayi su ma daban daban sai kilisai da kumbo da aka zuba zuba su ka matukar bada ma'ana. Kujerun wurin ko duk abin an musu kwalliya da tsintsiya na laushi da na kwakwa akai wadan su kuma turmi da tabarya aka sa saboda ya bada tambarin arewa. Akan kowani table akwai side plates da aka sa sa aya mai suga, tuwon madara, iloka, gullisuwa sai kwakumeti. Abun ba zai kara kayatar da kai ba sai kaga ana wuce da cups in zobo, ginger da kunun aya, duk anyi infusing insu da haddadun natural flavours sai kuma goruna fura da nono. Shigowan Amarya kuwa kida saurata na musamman aka sa mata, tana sanye da simple fitted gown na atamfa, plain alkyabba ke kanshi Wanda aka mishi kwalliya silver stones sai ta kasa aka sa patterns in jikin atamfan. Kanta a rufe da hulan alkyabban tana kallon kasa aka haka ta shiga filin zuwa seat inta, kawayen ta da su ma su kayi ankon wani atamfa da yayi matching da outfit in amaryan su na take mata baya har ta zauna su ma suka nemi seat insu. Abun ya kayatar da larabawan sosai, su dai ba so taba ganin irin haka ba balle ma wadanda su ka sa atamfan da basu taba sawa ba. Mc in dai da harshen turanci ya gabatar saboda sanin ba kowa zai fahimci shi ba in yayi Hausa. Kaman a garin sokoto haka yan uwan ango mata su ka feshe Amarya da sanyayyan turare sannan su ka bude mata fuska. Ji kake buda na tashi, ayiriririri ayiririri, banbancin dai kawai wannan speaker ne keyi maimakon mutane. Hotuna aka dinga yi, banda murmushi ba abinda Amaryan nan keyi ganin yawan dagaske ga burin ta na cika, sai rungume kawayen ta take da yan uwan tana farin ciki. Barin ma da aka bide wurin da wakar Hausa na ado gwanja da Naziru sarkin waka. Har kwalla farin ciki ta dinga yi, ana haka aka fara raba abinci lokacin kuma aka samu daman dauke Amarya domin samun daman canja yanayin shigan ta. Abincin da aka dinga rabawa kuwa Waina ne da snacks su samosa, meat pie, spring rolls da sauran su dai aka hada da gashashen naman shanu da na kaza.

Can aka umurci dukkan mutanen wurin su tashi domin shigowan Amarya wannan karon tare da angon ta. Kayatan kuwa A shape gown na saki in navy blue and silver, an mata dauri da silver headtie sai kuwa mayafin kayan da ta ya fa akai to shi ma dai angon ba a barshi a baya ba domin kuwa manya kaya ya sa navy blue ya kuwa sha banban rigan da ya dau aiki. "Wow! Wow! Culture is everything" abinda kawai kake ji yana tashi a wurin kenan wakan aljita na tashi na duba rana da wata suna da haske, har dai su kaje suka zauan. Daganan yan uwan ango su ka zo kaman yanda al'adar su take su wanke mata kafa da hannu da fresh madaran shanu, ba su gama mamaki ba su kaji wakan hausan da ya karade da sunayen su ana ta faman musu kirari. All through the event Umaymah ba ta zauna ba ita da Wanda su ka taya ta aiki said zagaya su ke don tabbatar da komai ya tafi yanda su ka shirya. Murmushi kuwa kin barin fuskan ta yayi ganin abun na tafiya yanda ta ke buri. A haka su ka hadu da Faroukh machina da ya sha jamfan shi fari sal, shima sai washe hakora yake yi da camera kuwa a hannun shi yana duba hotunan da yayi capturing so far.

"You look stressful" ita ta fara magana, yayi dan dariya hakora shi su ka fito kafin yace "it wort ai, it working and see you talking about me when you look exhausted" ita ma dariyan ta yi tace "to ni ai na saba, this my job" da annashuwa ta ke magana, sai ya debi mintuna yana kallon ta sosai har sai da ta gaji tayi gyaran murya, yayi saurin Sosa gefen "God! You are just awesome!" Muryan da yayi maganan dashi ne ya samu effect akan ta, dan sai da ta danyi still kafin tace "And you are superb!" Share zancen yayi "Kinyi kokari fa sosai ko a Nigeria ba a cika yin events yayi kyan haka ba, you are so wonderful, I like people who know their job"

"Thanks" ta amsa da farin ciki sosai ta kalli camera in "can i be a spoiler? I wanna see some pictures"

"You are so welcome then" camera in ya kara kunnawa, bai mika mata said maza da yayi daf da ita sosai ya fara scrolling pictures in. She likes them, irin sosai in nan, talking about people that know their job, he is also an epitome. Ba fuskokin mutane kawai ya daukan ba, Aa har da feelings in da ke kwance kan fuskan da kuma nature in gari. "I love the pictures, hope da su za a musu album in bikin ko?"

"Sosai ma kuwa" ya amsa, har yanzu dai GAF su ke da juna, sai ya zamo ba hotunan kawai su ke kallo ba, Aa har da suakan numfashin junan su da su ke ji. Ita kam ji ta ke kan ta na nema kuncewa, it been long ta bar kanta jin hakan akan wani da Namiji but now zuciyan ta har wani bugawa yake da sauri da sauri.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top