Ashirin da bakwai

Jigum Mustapha ya zama kafin farfadowan Anty, ko bayan ta farfado ma barin ta aka yi a asibiti ba abarin wani ya zauna gun ta. So Mustapha bai samu daman komawa Abuja ba duk yanda ya so hakan.

Yana nan garin kaduna har aka sallami Antyn sai ranar su ka hadu da Antyn, kallon shi kawai tayi ta dauke kai, to duk sanda ta mishi wannan ya san ba karamin fushi take dashi ba, barin ma yanzu da yake tunanin shine sila. Sai da ya bari a dan natsa washegarin dawowan ta yaje ya same ta its kadai a dakin ta. Ba ta mishi magana ba dai haka kuma bata daure fuska ba. A hankali ya taka har ya je gaban ta ya zauna, kwanciya kuma yayi ya daura kanshi akan cinyan ta. Yayi mamakin sa hannunta da tayi cikin suman shi tana shafawa. "Little drop that case bana ka bane na fada maka kaki ji,  kai ba ka tsoron ba wani abu ya faru da kai?"

 

Murmushi yayi sannan ya dago yana kallon ta ya dan dukar da kanshi "Anty na ke kike min wa'azi akan taimaka ma duk wanda ya ke cikin halin neman taimako, yarinyar nan looks so innocent i have to help her"

"Looks can be deceiving Little kuma ma in taimakon kake so ai ba dole sai kai za kayi case in nan ba"

"Na riga na fara Anty kuma wlh ba accusing Faroukh nake ba kawai dai ina tunanin akwai abinda ya sani wanda ya boye min" shiru tayi kaman mai wani lissafi "Ba zan ce Faroukh ba zai iya aika ta koma mai kake zargin yayi ba but little Faroukh is my son,  kai kawun shine da kuka matukar shakuwa shin ko ya yi abu kai ba mai iya kare shi bane?"

"Faroukh bai yi ma komai ba Anty, ai muna magana dashi kuma ko bayan zaman court in ba abinda ya dauka na fushi tsakaninmu, min samu kyakyawam fahimta saboda haka Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Anty na, i have nothing against my boy" jinjina kai tayi tace "ban son hana ka abinda kayi niyya saboda a ko da yaushe kai mai yin biyyayane a gare ni, ba case in ku bane ya sani a halin da nake ciki little kawai news in yazo min ne a lokacin da nake cikin wahala"

A tsorace yace "me ke damun ki Anty na?"

"Stress little kuma jini na hawa"

"Ya ilahi!" Ya furta sannan yace "please Anty ki ajiye lecturing in nan" da ido ta amsa shi.

...

Abuja, Nigeria.

Dr Fahad da Barr zaune, kokari su ke su saurari labarin suhaima da har ya jawo mata fadawa irin wannan mummunar rayuwan haka. Sai dai abin yana neman ya gagara domin dai Suhaima ta ki basu hadin kai. Ita a ganin ta ko ta rayiwan ma ba wani amfani don haka she want to end everything for good.

"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa,  ta gaji da kukan ne saboda Bai da  amfani a gareta domin bakin tabon da ke jikin ta ba zai taba gogewa ba.

"Karuwan ci? Tabbas nayi shi haka kuma na kasance maci amana ga wadanda su ka bani yarda, shin me kuma kuke so ku sani bayan wannan? Ku barni kawai ayi hukuncin da ya dacen ina ganin nayi deserving komai ma.

"Kin yi yunkurin kashe Zayd" kaman ta daga kai ko za su kyale ta sai dai kalman kisan ya mata mugun nauyin da take jin ba ta ma kanta adalci ba in har ta amince da abinda ba tayin ba.

"Then ki bar mu muyi abinda ya dace" ba wanda yace komai ba har bayan yan mintunan "Suhaima please tell us" Dr Fahad ya fada cikin marairaicewa. Ita kam mamakin yanda su ka dage suna rokon ta akan abinda tasan ita zai amfana. Sai dai tasan duk yanda ta so basu labarin rayuwan ta yana da tsawon da ba zata iya zayyana shi cikin lokaci kankani ba. Ba ma wannan ba tukun, ba taji bakin ta xai iya dauriyan furta wahalolin da su ka mata katsalanda a dukkan rayuwan ta.

Yanayin rashin natsuwan ta karara su ka fahimta, hakan yasa su ka yanke shawaran barin ta har sai lokacin da ta ke jin za ta iya. "Shknn Suhaima tunda kin zabi kin maganan,  ina so ki sani a kowani hali ni mai iya tsaya miki ne haka kuma yanzu ma ba gazawan zanyi ba. A dan kalilan labaran da kika bani tsakanin ki da Zayd in zanyi fatan samun hujjar da za ta kubutar da ke. Saidai ina so ki sani shi shari'ah yana da wani irin cakwakwiya da mu da ke cikin ta ne kawai mu ka fahimci hakan. Za ki iya ganin ke kina da iya gskyn ma fa in bamu da cikakkiyar hujjan da zai tabbatar da gskyn naki sai kiga kin kwana a ciki. Mutane ke ganin kotu wuri ne da ake fida mai gsky aka kama mai laifi,  sai dai mafi akasari abun ba haka yake bane. Ba kuma na gaya miki hakan bane da kin karaya,  Aa ina so dai ki sa a ranki komai na iya faruwa." Ba suhaima kadai ba hatta Dr Fahad jikin shi yayi sanyi, zai so kadaice wa da Suhaiman ko dan tausasa ta taba barristern abinda ya ke bukata sai dai shi ma he want to respect her decision.

"I don't know ko zaki ji dadin abinda nayi,  sorry ban fada miki ba munyi magana da Zeenah za tazo ku zauna tare har zuwa agama shari'an" da dan mamaki a fuskanta tace wa barristern "zeenah zata zo? Anya xa ta iya zama a wuri daya kuwa?"

"Ta dai Amince and we are talking with her tana fada min abubuwan da ta sani" da kai ta amsa shi wannan karon a zuciyan ta tana tunanin me zeenah za ta sani da har zata iya fadawa Barrister. Duk ta san akwai ta da dan banzan surutu amma kuma tasan ita ba ta taba fada mata komai ba balle kuma faree'ah da tasu bata taba zuwa daya ba.

Su Dr da Barr ba su dade da tafiya ba sai ga zeenah kuwa da katon trolley inta. Rungume juna su kayi da suhaima,  ba ta san lokacin da ta saki hawaye ba tana fadin "kawa da gaske dai kece" dariya kawai zeena ta dinga yi tana kallon reaction in suhaima. "Ya bayan rabu?" Zeenan ta tmby, dan tabe fuska suhaima tayi tace "gamu nan dai kawai kawa, atleast we are still alive"

"How is your case kuma?" Wannan karon suhaima ba ta amsa tmbyn ba sai ma tashi da tayi da niyyan kawo mata ruwa da abinci. Da dai zeena ta fahimci kawarta ta ba ta son ayi maganan sai ita ma kawao ta share, ta san komai akwai lokacin sa haka kuma ba ta shakkan za su gangaro wannan.

...

Barr kam yana barin apartment in numban El-yas ya kira. Har Company insu yaje ya same shi, sanin wurin is not safe suyi magana yasa ya ja shi zuwa wani restaurant.

"Uncle musty any news ne akan case in?" Girgoza kai barr yayi yace "Ina fatan dai samun news in daga gareka"

"Toh fah" El-yas ya fada, murmushi barr yayi yana dan taba gemun shi. "Ina son any information akan Hafeez, friend in oganka." Dan zaro idanu El-yas yayi kafin yace "Oga Hafeez, i don't really know much about him ai saboda ba wai yana aiki damu directly bane though shi ya ke fidda duk wani tsari da abinda za ayi a company in Al-mansur both telecom da drink shop, he is the director"

"How possible kuma ba za kuyi tare ba? Taya yake sanin duk abubuwan da ke faruwa to?" Kyabe baki El-yas yayi yace "mu ma mun jima muna mamaki, both he always makes it work yana kokari sosai gsky. I think dan uwan oga ne fa ma ko kuma neighbors because tjey have always been together tunda nasan su" da kai Barr ya amsa sannan ya kara tmbyn shi "akwai wani abu da ka taba fahimta tsakanin su da Suhaima?" Shiru El-yas yayi yana tuanin kafin ya tafa hannun shi da karfi "He seems to like her first day in da muka fara haduwa da ita a lagos"

"Daga nan kuma ba wani abu da ka kara gani?"

"Babu gsky" jinjina kai Barr yayi sannan yace "ina son tmbyn ka wasu abubuwa game da abokin ka faroukh, ina ganin kaman akwai wanda ya sa shi aiki akan suhaima, i mean not in a bad way fa amma" dan shiru El-yas yayi dan yatsan shi a bakin shi. Can kuma yayi saurin girgiza kai "Faroukh got the job through me kuma bayan haka ma i was the one that convince him akan aikin. Bayan haka kuma ban tunanin akwai wani wanda Faroukh zai iya ma aiki ya sa mishi ido, bai son shiga harkar da ba nashi ba" da kai Barr ya amsa, sannan ya mai godiya su ka gaisa.

Ya riga ya san next target shi shine nemo waye Hafeez, me kuma yasa Zayd ya bashi ragaman kula da hidimomin shi. He can't do it alone, kuma yana ganin Dr Fahad ya fishi connections a Abuja don haka ya kira shi a waya su kayi magana.

The next target shine ya nemo Faree'ah sannan kuma yana bukatar sanin ina Amal ta ke da Umaymah Amin. Zuwan shi Vows Uku amma an tabbatar mishi ba ta garin Abuja kaman yanda Faree'ah bata nan ita ma. Hakan yasa shi tunanin ba shakka tabbas akwai wani abu a kasa dole kuma ya nemo koma menene sai dai kuma ta ina zai fara? Suhaima, shine kawai amsa da zuciyan shi ta bashi. Bai tsaya wata wata ba ya fisgi motan nashi zuwa apartment in. Ko da yayi Sallama Zeena kawai ya samu a falo, bayan sun gaisa ya mata sannu da zuwa. Bai tmby ina Suhaiman ba instead sai ya nemi magana da ita zeenan.

"Wai shin ina Faree'ah take ne?" Zaro idanu tayi kafin tace "Ai in zaka je gidan yancinmu, ina ni kadai ce ba za a iya tmbyn wani abu akan Faree'ah ba"

"To amma ko meyesa hakan?"

Kai tsaye tace "saboda kiyayya ke tsakanin mu" folding lips in shi yayi,  shi dai yanzu wannan ba shine damuwan shi don haka yace "Amma ya akayi su ke shiri da Faree'ah bayan abindake tsakanin su." Ko dabai fadi sunan ba zeenah ta gane suhaima ya ke nufi "To ai ita ta kawo ta gidan, tare su ke suna shiri sosai ko a gidan ma dakin faree'ah Suhaima ta zauna" jinjina kai yayi yace "Amma na tuna a kaduna da na sanar miki an kama Suhaima kin ce shegiya Faree. Zeenah in akwai abinda kika sani Dan Allah ki fada min kinji?"

Kyabe baki tayi tace "Da gaske Faree'a bata nan sai dai naji ana fadin tabi wani sabon Saurayin ta Dubai" shiru yayi yana wani nazarin da ya ke fatan ya kasance gsky. "Kin san saurayin?"

"Bansan ko zan iya gane shi ba amma na ganshi da ita a mashaya sau daya" da sauri Barr ya ciro mata hoton Hafeez yana nuna mata. Ta dade tana kallon hoton can tace "ni kam ban gane amma kaman suna yanayi, i wasn't lokacin da na gansu" daga nan pics in Hafeez dayawa ya dingagwada mata sai dai ba wanda ta iya tabbatar wa ko shi dinne.

Ko da Suhaima ta fito ta same su basu wani yi magana sosai ba har Dr Fahad ya kira Barr akan shima gashinan zuwa gidan.

"Hafeez Bature sunan shi, dan uwan makotan Al-mansur in ne tun yaran na kanana lokacin suna unguwan kubwa. Sun yi zumunci sosai da makotan nasu, shi kuma Hafeez lokacin yazo hutu gidan Neighbors in,  a hankali ya fara shiga gidan Al-mansur har ya zama dan gida. Ta haka su ka saba da Zayd tun yana karami, daga haka ma bayan su xayd sun tashi daga kubwa sai ya zamto ko yazo Abujan ba gidan yan uwan nashi ya ke zuwa ba. Yana family house in Al-mansur" Dr Fahad ke bayanin da Barr ke ta mamakin ina ya samo labarin nan cikin kankanin lokaci haka.

Kaman ko ya shiga zuciyan shi yace "Kaman ansan ina neman news in, wlh ina zuwa Restaurant cin abinci naji wani mata na lbrn Hafeez bature dan uwan Al-mansur ya taba cewa yana son ta. Nan fa rigima ya kaure musu akan daya tace sam taji lbrn ko kadan basu da dangan ta nan ne fa ta bada lbrn,  ni kuwa ina ji na ja mota na sai kubwa. Da ma akwai friend ina da mu kayi karatu tare a india,  har layin muka je wurin wani cousin in shi nan fa ya tabbatar mana da labarin"

"Ikon Allah,  yanzu kuma sai sanin yana da alaka da case in nan ko bai da ita"

"Bai kasan yana Dubai" Dr Fahad ya bada amsa, da sauri Barr yace "Dubai?" Sai kuma yayi shiru, he needs someone da zai mai bincike a can Dubai in. Faree'ah da Hafeez na Dubai,  to saura kuma Umyamha sai kuma Amal.

"Dr ko akwai binciken da zaka mana akan Amal Idriss Hayatuddeen nd her suicide issue?" Dan jim Dr yayi kafin yace "Kanwar Saleem ko?" Da kai ya amsa mishi. "Childhood friend in Yusuf ne, da ke kubwan i will try to get something"

Shiru ne ya dau falon kowa da irin tunanin da yake sakawa a zuciyan shi. "Suhaima ina zan iya samun Umaymah ne?" Kallon barr Suhaiman tayi, ko bai fada ba tasan cewa ya dai yi maganan ne kawai. "I don't know"

Dr Fahad yace "Suhaima are you still not willing to say something?" Ba ta kai da amsawa ba zeena tace "Kawa you have to give them the book tunda ba za ki iya basu lbrn ba nasan kin rubuta komai" saurin juyawa Suhaima tayi tana kallon Zeenah kafin tace "Wani littafi kuma kawa?"

Dariya zeena ta danyi kafin tace "Ai nasan kin rubuta littafi about your life, ki basu shi mana may be zai taimaka ma binciken nasu" Da mamaki sosai a fuskan Suhaima tace "to how do you know amma?"

Sosai tayi dariya tace "kawa kenan an gaya miki a banza faree'ah ke ce min magulmaciya?" Kafin suhaima tayi magana Dr Fahad yace "ki bamu littafin to" gabadaya zuba mata idanu su kayi hakan yasa dole ta bude baki tayi magana "Yana kaduna in kuka ma Anisa magana za ta baku"

"Anisa?" Barr yayi saurin fada.

"She knows nothing fa, kawai dai na bata ajiyen littafin ne ba copy bane, manuscript ne"

"Amma ina kika same shi?"

"Nayi saving a wani platform ne, so nayi loghing ne sai na bata ta min printing nace mata ina rubuta novel and she promise me not to read sai na gama gabadaya." Ajiyan zuciya su sake, ba shakka sun san kaduna tayi kira kenan. Sai dai daga karshe sun yanke shawaran Barr ya je ya amso manuscript in Dr kuma ya tsaya domin cigaba da bincike musamman akan Amal.

...

Coocoon apartment

Seychelles

Umaymah Amin ba tayi wani baccin kirki ba taji ana tada ta. Da sauri ta mike ta ganshi tsaye akan ta idanuwan shi gabadaya a kanta.

"Ki fito parlor" kawai yace sannan ya fita dole ta mike ta biyo shi. Tayi mamakin ganin travelling bag ajiye a gefe amma sai ta fuske ta nemi wuri ta zaune. Kallon ta ya ke sosai sai dai wannan ba irin kallon da ya saba bin ta dashi bane mai cike da dimbin so da burgewa wannan kallo ne na tsan tsan tausayi da yake jifan ta dashi.

"I will be living now" a firgive ta dago tana kallon shi,  da kyar ta iya furta "but why?" Folding lips in shi yayi, a ranshi yana tunanin yanda zancen zai zo mata "Na gama aiki na a nan so yau zan wuce Dubai, i got another work there"

Da mamaki sosai tace "aiki? Nasan an gama bikin su Rawan but still you never mention you are leaving today ai,  is it because of what i told you yesterday?" Tayi mamakin yanda ba ko alamun tantama ya daga kanshi alaman Eh. Zaro idanuwanta tayi tana kallon shi, what is happening again? Abinda ta dinga ambata a ranta kenan.

"Sai dai kuma ba kaman yanda kike xata, am leaving becauee na riga na samu abinda nake bukatar samun" still confuse kallon shi kawai ta ke tana tunanin ina ya dosa?

"Bara dai in miki yanda zaki Fahimta. Like i told you Rawan da Adam duka Friends ina ne tare mu kayi karatu dasu." ID card ya dauko ya mika mata, ba dan ta san menene ba ta amsa tana dubawa. Kaman yabda ya fada mata sunan shi hakan ta gani rubuce a jikin card in,  Umar Farukh machina. Shaidan shi na Detective wanda ke aiki a karkashin Crime investigations department (CID) ta gani, a tsorace ta bishi da kallo. Kai ya daga mata alamun tabbatar mata da zargin nata. "I was hired for an investigation a company in Al-mansur, da kuma shi kanshi Al-mansur in. A nan kuma naci karo da lamarin case inku. Sorry to say Umaymah but you act so selfish gsky. I mean ta yanda zaki bar mutum a cikin case bayan kisan ke ce silan shigan ta duk halin da take ciki. Kar ki manta itan ma fa mutum ce mace kamar ke. I had no intention of coming to seychelles da baki zo bama da bazan zo ba, a safoyyar da zaki taho aka sanar dani in shirya, ina da visa da komai don haka aka dauke ni a private jet zuwa lagos inda na hadu dake a airport. Lokacin ds Adama ya ke sanar min burin Rawan, lokacin nasan na samu perfect solution na yanda zan bullomiki saboda nasan ke Event planner ce mai maida dukkan hankali akan aikin ta, nasan you will make everything work shiyasa na bashi shawaran ayi haka. Am sorry if you may think i used you, this is my job and i have to protect wannan yarinyar da kika bari behind bars" tsabagen shock in da ya kamata maganamai kyau ma kasa hada shi tayi. Key ya ciro da card ya ajiye a gaban ta. "You are so nice to me so taimakon da zan iya miki shine ga key in apartment in nan ki zauna har lokacin da zan neme ki when i think Nigeria will be safe for you" nuna mata katin yayi kuma yace "You can contact duk lokacin da bukatan hakan ya taso,  ko dan nima zan nemeki dole but now i have to go ina da mission a Dubai kuma" a firgice ta dago tana kallon shi, murmushi ya mata yace "Dole in ga yarinyar ki Faree'ah, so ina baran addu'a a wurin ki sannan kuma ki yafe ni kinsan lamarin tafiya" da shu'umin murmushi akan fuskan shi ya fada, daganan kuma bai kara cewa komai ba ya dau luggage inshi ya nufi kofa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top