Ashirin

Washegarin POP in Amal mu ka hada dukkan wani abu mai mahimmaci da niyan tattara zuwa Abuja, domin cewa tayi ita kam zaman Lagos in ya ishe ta. Zayd ne ya lallashe ta mu ka zauna a cewar shi he got a surprise for herda zai faru a daren, hakanan ta hakura ta zauna.

She is over the moon tana ta tunanin menene Zayd zai mata. Ni kam na riga da nasan menene saboda a wuri na ma ya nemi shawaran duk abinda ya ke bukata. Abinda kawai yace ma ta shine, ta shirya sosai in her best outfit. Nan naja ta mu ka tafi salon, tana da gashin ta baki mai sheki da tsawo sosai, so ma sha Allah. Don haka gyara kawai aka mata yayi wani irin mugun kyau, su kan su yan salon in sai dai su ka yi ta maganan yawan gaahin na ta. Nima ina da gashi na dai dai gwargwado kam, daganan aka tsantsara mana wani shegen unique make up da ban cika ganin irin shi, kudi ne yayi kuka a wurin. Duk yanda ake cewa make up yafi ma bakake kyau, sai dai na ga na Amal ya fita daban fiye da misali, wani mugun kyau ta min da duk yanda ake ta ce min nayi kyau kasa ganin nawa nayi. Da wannan na fara tunanin mai ma Zayd ya gani a wurina ne da ya ja ra'ayin shi har ya taka na Amal in? Maza dai sai a bar su kawai, ni dai nasan ba abinda zan nuna ma wannan baiwar Allahn duk da ko nasan na fita kugu da dan wasu abubuwa na jiki wanda na ke ganin su ba a bakin komai ba.

Sai wani irin murmushin farin ciki da jindadi ta ke, she couldn't even keep quiet, tana ce min kila fa Zayd proposing inta zai yi sabida the last time da yayi proposing aka hana ta auren shi kusan hakan ya mata. Amma wannan karon alwashi ta daukan ma kanta babu wanda ya isa hana ta auren zayd in ba haka ba ko har suicide ta na iya yi. Sai da na girgiza jin yanda ta ke maganan da dukkan iya gaskiyan ta. "Ke yanzu za ki iya attempting suicide?" Kai tsaye tace min "my life has no meaning without his Frnd" tausayi ta bani, amma sai na daure na ce mata "amma kinsan ba kyau ko?" Tsaki taja tace "abubuwa nawa ne kuma ma rasa kyau mu ke aikatawa" nan take jiki na yayi sanyi, ba shakka irin rayuwan da ta taso ta gani kenan, sabili da cudanya da musulman mu su ke da turawa, yau da gobe dole lifestyle in su ya shiga kan ka. She is so use to abinda ta fada da babu any doubt ma a cikin sa.

Da tunanin abinda na ke aikata wa mu ka tafi mashayan da Zayd ke jiran mu, kokarin yaki da zuciya ta na ke ta faman yi. Hadewa sosai Amal tayi ranar cikin wata arniyar long mermaid armless sequins gown, dark blue ne with glittering silver stripes mai split ta baya, sosai ya fidda shape in jikin ta. Takalmi da jewelries ma gabadaya silver in ne sai ta kama gashin ta in a bun, yanda kasan model haka ta zama a ranar har idanuna sun kasa daukewa daga kallon ta, she looks so ethereal and luscious. Ban yi mamaki ba da tace min throghout her secondary and University life ita take winning beauty contest, sai dai ko in ba tayi signinng ba amma ba ta samun wata a gaban ta. Ga ta fara sal, hakan ke kara sa sau dayawa mutane ba su iya resisting kallon ta. Kyau kam ta sha shi har ta gaji.

Ni kam Sequin palazzo pant na sa da turtle neck top all in silver, kai na kuma na daura mishi sparkling half turban, shi ma silver in ne sai na zubo da gashi na baya kawai. Amal na ganina tace "wow friend kinyi kyau" murmushi kawai nayi, because i wasn't in the mood balle ma na riga nasan duk kyan da zanyi ba zan kai rabin nata ba.

Ni nake driving motan nata, jefi jefi muna hira can tace min "Frnd wai ina zamu je ne? Bestie fa bai gaya min inda zamu ba"

"Kar ki damu kawai, mun kusa iso wa" na fada concentration ina na kan driving in da nake, dake nan cikin victorian island in ne ma nan da nan mu ka isa club in da a wajen shi aka rubuta Quilox.

"Me zamu yi a quilox? Amal ta bukata, ban ce mata komai ba sai da na bude kofan na juyo wurin, sauran kadan in ce mata “me kike zuwa yi da a wurin?” sai na fuske da kyar nace mata " let just go and see" ita kanta sai da ta fahimci something is wrong with my mood.

Muna fara taka kafan mu bakin club in wurin ya dauki ihun "Gi-gi Gi-gi Gi-gi" in some very loud voices, lakabin da yawancin friends in Amal ke mata kenan “Gi-gi Amal" murmushi sosai ke kara deepining kan fuskan ta, tana shaking hand da mutanen da ke zuwa wurin ta suna congratulating inta on her NYSC completion, sai lokacin ta fahimci party in da Zayd ya shirya mata kenan, she couldn't avoid been a little bit disappointed. Mostly, da su gama magana da ita su ke juyowa wurina "Hey dear pulchritude" da fake smile in da ke kan fuskana na ke amsa musu muna shaking hand. As more people are approaching sai ya zama na akawai mutane dayawa a tsakanin mu.

Ban ankara ba sai ji nayi an fisgo hannu na ana kokarin ja na zuwa wani direction, koma wanene nasan dai dai na ke dashi hakan yasa ban wani ji tsoro ba. Da ke dim light ne sai daga baya na fahimci zayd ne ke jana, yana ta kokarin matso da ni jikin shi sosai. Da saurina fisge hannu na saboda wani irin haushin shi da naji yana ratsa ni a wannan lokacin, my first instinct shi ne in kifa mishi mari saboda tunanin  shi ya yaja min abinda na ke yi. "In ka kyale ni ai zan bika ko? You don't have to keep pulling me" cike da tsiwa nayi zancen sannan kuma na karashe da guntun tsaki na.

Bai yi fushi ba ko kadan sai ma dariyan da yayi "jewel yau rigiman ake ji kenan ko?" Ban tanka shi ba sai ma wani kare hada rai da nayi. Rike da hannu na, focus in shi kuwa gabadaya a kaina cikin wani irin raunaniyar murya a hankali yace "shine rigiman har da bawan Allah Zayd za a ma wa koh? Wato dai babe na lura ko tausayi na ma baki ji" duk da naji ba dadi yanda yayi maganan, sai da naji wani tausayin kaina.

"We are in public kuma Amal is here" shrugging shoulders in shi yayi yace "who care? I just want to appreciate and feel your beauty, you look so stunning my babe kin ganki kuwa?" Tabe baki nayi na dan dauke kai, wanda shi a tunanin shi yana ganin am just pretending ne unknown to him har a zuciyana am not feeling well with him very close to me.

"Naji kuma nagode, is better you start looking for ur girlfriend now."

Basar da zancen yayi da cewa "you are my girlfriend and am with you" kafin in samu daman magana yayi saurin hade jikin shi da nawa holding me so close to his chest "kin min kyau da yawa jewel, i can't resist ur sight gashi mun yi anko" sai lokacin na kai idanuwa na wurin kayan da ke jikin shi. Shi inma sequins blazer ne navy blue and silver gliters, buttons a bude su ke hakan ya sa ake ganin V neck silver t shirt in shi da ke ciki, sosai ya kame jikin shi har ana iya ganin shattin packs in da ke adane a cikin.

"ka dai yi anko da girl friend in ka Amal" bai tanka ni ba ma sai ma wani hot kiss da naji ya bani a wuya na yana tabo gashi na da ya zubo baya da hannu shi daya dayan kuma yana kara manna ni da jikin shi. "Ina sonki sosai Suhaima despite all your rigima da rikici" duk da wurin da mu ke ba mutane sai da nayi kokarin fisge jikina daga nashi, a bazata abun yazo mishi shiyasa har na ci nasara.

Dariya ya min yana dan sosa wuyan shi yace "ni ko? Lallai babe kin ci tuwo" kaman ance in daga kai naga Amal na approaching in da mu da dan damuwa kwance a fuskan ta "ai sai ka juya ga bestien ka nan tahowa" ya so basar da zancen nawa, sai kuma ya juya. Suna hada ido a tare su ka sakan wa junan su murmushi, bai jira ta karaso ba ya taka inda ta ke.

Kallon juna su ka yi na seconds kafin yace "you look hot as always" wani blushing tayi a hankali ta matsa wurin shi sosai, a kunne ta rada mishi "all for you" wani wawan runguma ta mishi sosai har tana ajiyan zuciya. Hada ido mu kayi dashi, na tabe baki na juya saboda na lura kokarin min magana ya ke son ta idanu, ni ko ban son fahimta.

"Sun burge ki ne?" Naji an fada daga bayana, da sauri na daga kai dan ganin wanene. Oga Hafeez ne, kaman yanda naji Zayd na fadi ke ta faman washe min hakora. Tun haduwan dashi sanda su kazo tare dasu Faroukh ban kara ganin shi.

"Miss delicate skin" yana maganan ne yana kokarin jan hannu na, saurin matsawa nayi saboda duk duniyanci na a wannan lokacin ba kowani sharan na ke bari ya sa hannun shi a jiki na ba.

"Oh sorry" ya fada amma ina iya jiyo tsantsan duniyanci a muryan nashi.

"Ashe kana nan" kawai dai nayi maganan ne saboda ban bukatar wani tunani ya darsu a zuciya nashi.

"Nayi tfy ne shiyasa bamu hadu ba, ya drinks shop komai dai lfy ko?" Assuring in shi lfy nayi  sannan ya cigaba da kokarin ja na da hira.

Daga wurin ina hango kallon da Zayd ke ta jifa na dashi, yanxu kam a zaune su ke a gefe kadan, Amal in tayi luf a jikin shi kaman hira su ke dan naga tana ta dariya.

Zayd ganin naki tanka shi, a zuciye ya dago Amal kaman jaririya ya sunkuce ta su ka nufi wurin bar. Hankali na gabadaya ya kama, hakan ya sa rabin abinda Hafeez ke fada ba jin shi nake ba sai ma na fara tafiya zuwa inda na ga sun nufa. Bina yayi yana fadin "can i have the special dance please?" Kaman in ce mishi Aa, sai kuma nayi saurin tunani "Yeah" na amsa ina daga gira.

Muna isa wurin ya dau tsit kaman ba mashayan nan da ke ta faman tashi to the sound of the music ba, a hankali wani cool music ya fara tashi sai ga waiters na kokarin table da ya sha varieties of flowers sai sparkling ya ke ta faman yi. Attention in mutanen wurin gabadaya wurin ya koma har a ka tsaida abun gaban su Amal da Zayd. Wani rantsatsen Huge cake ne a kai mai steps bakwai, cake in ya hadu iya hadu da bazan iya describing in shi cikin sauki ba. Green and white ne dai, da ya sha poundant da mini pictures inta a jiki sai stickers in make up product, ita kam akwai kaunar make up duk da ba wai ta cika zana wa fuskan ta bane. Happy successful NYSC completion, a ka rubuta a jikin cake in. Gafen cake in kuwa wata katuwar bottle in wine ne, girman shi har ya baci, gashi guda daya tak amma kana ganin shi kasan it worth a lot money.

Kallo abubuwan da ke gaban ta tayi sosai kafin ta juya tana kallon Zayd, da sauri ta bashi side hug tana blushing tayi pecking in shi a cheeks. "You are the truly the best one ever my bestie love"

"I love love" naji Hafeez ya fada, juyawa nayi ina kallon shi da tarin kwallan da ya fara cika min idanu, love is just wow if you are lucky to meet the one. "Are you crying" ban ce mishi komai ba na goge kwallan da ke shirin zuban min. Baki Hafeez ya fara bani unknow to him tunanin yanda zan katse wannan alaka ne ya min tsaye a zuci, ba shakka na san dole in sa aya a walwalan su dukkan su biyu kuwa kafin na bar rayuwan su. A lokacin na fara tunanin dalili na na jinkirta manufa ta kawai don ina jin tausayin su ne ba wai don abi komai a sannu kaman yanda na ke fadawa Aminiya ba. Sai dai bature ya ce the earlier the better, dole in ture duk wani emotions in da ke min yawa in fuskanci abinda ke gabana.

A tare su ka yanke cake in, sai da su kayi wasan shafen shafen cream icing in a fuskokin su, they look so happy together. Har inda na ke Amal ta jawo ni ta tura min cake in a baki, wanda da kyar na iya ci saboda yawan shi, tana ta min dariya. Lokacin mu ka hada ido da Zayd, na so karantar shi sai dai na kasa yin hakan saboda gani na ke kaman zai gano manufa ta in dai na cigaba da yarda muna hada idanu. Barin ma kallon da yake min a lokacin was so intense.

A lokacin aka fara rawa, da sauri Amal ta ja hannu Zayd su ka nufi filin rawan tana ta giggling abin ta cikin wani irin farin ciki na daban da ya bayyana a fuskan ta, har tsalle ta ke abin ta tana jin wani daban. Mugun sanyi jikina yayi ganin mood inta, rawa sosai su ke yi da Zayd, ba irin juyin da ba tayi a jikin shi ba. Alkawarin da nayi wa Hafeez ya sa nayi rawan dashi, mutane wurin sun yi mamaki sanin banda Zayd ban taba attempting rawa da wani ba. Ganin yanda su ke tafi suna faman mana kirari ni da Amal ya sa nasa jiki mu ka kwashi rawa da Hafeez, irin special rawan da na saba biyu. Daga ni da Hafeez in sai su Amal a tsakiyan wurin.

"Time for something special" aka fada a mike, attention in wurin gabadaya ya koma gun. Zayd ne ya amsa mike in ya fara magana "sorry everyone i am going yo distract you a little, i have something special for my bestie" yana gama fada ya amshi wani karamin gift box hannun Hafeez, Kallo na yayi sannan ya juya ya wurin Amal. Ni ya miko ma box in "please open it" ba tare da na kalle shi ba na amsa na fara kokarin bude yayin da yasa ta kulle idanu, ihun da wurin ya dauka ne ya sa ta saurin bude idanu tana fuskan tan abinda ke gabanta. Mouawad 1001 Nights Diamond Purse worth 3.8 million dollars ta gani a gaban ta. She was so shocked har ji tayi kaman ba a duniya ta ke ba na yan sakwanni ko motsi kasawa tayi,  tafi wurin ya dauka rau rau rau.

Suman tsaye tayi a wurin tana kallon gift in, tasan cewa duk da kudin mahaifin ta ba zai saya mata wannan bag in ba, she watched the show ita da Zayd ranar da aka yi launching pursue, she was over the moon tana ta cewa ba ta san ya zata ji ba in ta wayi gari tana da wannan pursue in, she can do anything ma duk wanda ya bata wannan kyautan. Rasa abinda za ta mishi tayi, da ke kuma kwakwal war ta ya fara tafiya saboda wine in da tayi ta faman kwankwada. Kallon shi ta ke yana zama ma ta blurry blurry kaman zai bace ma ta, ba abinda ya fado kanta sai wani lokaci da yaso kissing inta in public taki. “i will love to take you in front of everyone ya san you are mine Amal" ba ta kara wani tunani ba tayi saurin crashing lips in su together so fiercly ta yanda ba zai iya resisting ba ko yaso haka. Hot french kiss su ke sharing a tsakiyan club in nan. Duk wani guntun doubt na Amal sai da tayi kissing in shi away a wannan moment in, kaman za su hadiye bakin juna, it was so intense da ya sa har su ka fara gogan jikin juna suna sakin numfashi a tare. Sound music aka saki a wurin nan da nan aka kara cuduwa ba irin kalan rawan da ba ayi ba a wurin ba tare da wani damuwa ba a fuskokin su, kowa abinda ke faranta mishi zuci kawai ya ke kallo.

"Can i get another dance?" Hafeez ne ke maganan yana bin dukkan jiki na da kallo. Murmushi dole na ara na daura wa fuskata. Slowly kuma na girgiza mishi kai. Da narkakkun idanun shi wanda su ka kankace saboda influence abinda ya kwankwada yace min "please mana miss gorgeous" folding hannu na kawai nayi ina kallon shi sanin da nayi ba nacin duniyan da zai yi ya sani bin shi a yanzu tunda banyi niya ba. Da karfi ya ke kokarin jan hannu na nima ina janyewa "Kar ki min haka mana? Kin san yan mata nawa ke aon ganin kansa a matsayin da kike" an zo wurin kenan, ban kaunar mutum mai girman kai, immediately nasan ba zamu taba shiryawa dashi ba. Nasan shi in mai kudi ne and he definitely not need to remind me of that.

"Na gaji, am feeling the weight of the world please allow me" duk magiyan da ke fitowa daga sautin murya na bai sa ya fasa sa hannun shi a jikina ba, wani bakin ciki nake ji yanda ya ke taba ni ba tare da wani tantama ba. Nasan cewa yau da a wuri mai mutunci ya ganni da shigan mutunci ba abinda zai bashi lasisin daura hannun shi a jiki na haka kawai.

Da dukkan karfin shi ya jawo ni jikin shi gabadaya yana fadin "it okay girl let us just cuddle to" fisge jiki na nake kokarin yi naji an ja shi gefe instead. "Oga don't you see bata so? Please allow her mana, you can't pressurize her ai" murmushin fatan baki yayi hade da cije leben shi na kasa, siririn tsaki yaja sannan yace "na dauka she is wise, exposed and civilized, why is she doing this kind of thing kuma"

A dan fusace zayd da ya fara harzuka yace "Whatever, you don't have the right ka sa ta abu in bata so, interest always matters" in annoyance Hafeez ya balla mana harara dukkan mu biyun sannan ya wuce yana cewa zayd "we have to attend the meeting kayi postponing tafiyan ka Abuja" zayd bai amsa mishi ba, sai key da ya wullo min ya nufi hanyan waje.


A/N: How are you all? Anya kuwa ba zan canja sheka ba? 🤔 Gsky ban samun karfin guiwan da na ke bukata a wurin ku. Are you not reading the story? Or you are not enjoying it? Ina bukatan jin ra'ayoyin ku. Maganar gsky in ban samu abinda na ke bukata daga wurin ku ba i will stop posting ne kawai gabadaya, like i can't even keep updating regularly saboda ban ganin comments inku.

Nagode.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top