Arba'in da tara

"Why are you not eating? Ko ba kya son abincin ne?" Da kyar ta it's bude baki tayi magana "Aa, ina ci" bai ce komai duk da hakan ya maida attention in Jiddah da Abdallah kanta. Wanda zuwa yanzu ta gane cewa shima dan gidan ne, musamman saboda kamannin da taga suna yi da Hajja. Sai dai da tayi Dana sanin fitowa cin abincin duk da ma Hajja ba ta wurin. Don haka kawai taji tana jin wani mahaukacin kunyan ta.

"Adda Suhaima how is Nigeria? And everybody? Na dade ina son ganin ki, Ummi keeps promising to take me there Amma Allah bai yi ba" she is confuse ko da ta amsa jiddan. Dan ba ta ma gane me take nufi bane kwata kwata. Zuwa can aka danna ring bell in. Da sauri Jiddah ta nufi wurin kofan tana fadin "Ina jin Ya Baffah ne, he promise he will come tonight"

"Jidd jidd" taji Wanda ke bakin kofan ya fada. Da sauri ta jawo hannu shi tana fadin "Close your eyes i have a surprise for you Allah" ganin yanda ta matsa mishi ya sa ya rufe idon dole. Wurin Suhaima ta Kai shi dake zaune kan couch yanzu tana ganin drama in da ke unfolding. She didn't get wai za ayi surprising in Wanda ya zo da ganin ta. Don dai har suka karaso gaban ta bata gane waye ba.

"Now open" jidda ta fada da karfi tana dariya. Ko daya bude idon Sai da ya kifkifta tukunna suka dawo dai dai.

Four eyes su kayi da Suhaiman. Kowa na kokarin fahimtan Wanda yake gani a gaban shi. Da sauri ta mike tsaye tana fadin "Baffah?" Gyade mata Kai yayi, cikin rawan murya yace "Adda ke ce?" Sai Kuma yayi saurin hugging inta. "God i thought i will never see you again" wani irin hawaye taji ya fara cika mata idanu.

"Baffah Kai ne?" Da Kai ya iya amsa mata, shi inma hawayen ne ke fitowa hade da Kuma murmushin tsantsar murna.

"But wait why are you here? Ina Anty Jamila?"

"Tana can gidan ta. Wait baki gane Jiddah ba wai? Maijiddah ce fa, maijiddan Ummi" da sauri ta sake Baffah tana kallon jiddan. Maijiddah? Kanwar ta? Da Ummi ta tafi da ita tana baby, she can't even remember her face?" Wani iri hawaye ne ya fara silalo wa daga idanun ta lokacin da jiddan kw cewa "Haba i know she didn't recognize me, na fada ma Yaya Abdallah da brother sunce wai i talk to much"

Riko hannun ta Suhaima tayi tana kallon fuskan ta sosai. Da sauri ta rungumw ta wasu hawaye na kara silalowa. Dukkan su kukan suke, ita Jiddah ba tasan kukan me suke ba. Halin ta ne in wani na kuka ita ma yi take. "Why are crying? Please tell me" tana fada tana cigaba da kukan.

Umar Sanda ne ya kara so wurin su Yana fadin "it okay please"

Lokacin Kuma Hajja ta shigo falon. Kallon su tayi ta girgiza Kai. Zuwa tayi ta jawo Suhaima gefe, tana lallashin ta. Sai a sannan ta lura Baffah ma yazo. Sai da suka natsa bayan lallashin da Hajja ta Sha. Tukunna Suhaima ta dago da rinannun idon ta, tana kallon Maijiddah "Ina Ummi na?"

"She will back in a weeks, sunje Sudan da baban ku" bata son ta cika tmby shiyasa ba ta tsaya tmbyn waye baban ba. Amma she wonders mai ya kawo Mijiddah da Ummi Egypt, gwara Baffah tasan Yana wurin Anty jamilah ne. Sannan most importantly, miye hadin su da su Umar Sanda.

"Kije daki ki huta Suhaima, we will talk tomorrow kinj. Jiddah raka ta" mikewa tayi jiki na rawa, da kyar ta it's musu sai da safe sannan ta lallaba dakin tare da jiddah. A dki jiddan ta sata a gaba tana ta mata tambayoyi, short short amsa take bata. Sai dai ita duk tana bukatan hakan Amma ta kasa tamabayan jiddan abu daya kan Ummin.

"Na kosa Ummi ta dawo, nayi missing Su Aseem. They couldn't wait to meet you also" dan shiru Suhaima tayi kaman ba zata tanka ba. Sai Kuma tace "who is Aseem?" Rolling eyes Jiddah tayi "Kah Baki sani ba?" Triplets in Ummi ne. Aseem, Areef da Afrah. They are 10 years old, year in nan in sun dawo za su shiga high school"

"Ke fa wani Class kike?"

"University, am in my Second year" murmushi Suhaima tayi a ranta tana tunanin how time flies.

"Baffah fa?"

"About to finish his second degree" Wani irin dai Suhaima ke ji a ranta. Abun yafi karfin farin ciki ma. Dan wani irin feeling na daban take jin Yana shiga jikin ta. Ba ta taba zaton Rana zata zo irin wannan ba in her life. All thanks to Sanda, she owe him.

Ranar kam, ba ta iya bacci ma Sai ma juye juye da ta dinga yi da kyar baccin gajiya ya tafi da ita.

Yau, kusan kwanan ta uku a gidan su Sanda dake kasar Egypt. Tana cikin kwanciyar hankali sannan kwata kwata bata da matsala da daya daga cikin su. Musamman Hajja, matan na da shiga rai haka Kuma akwai sanin muhimmancin dan Adam. Duk yanda Suhaima taso ta dinga zaman daki, hajja ta toshe kofan hakan. Sa wa take a Kira ta, ta fito falo suyi ta hira ko kallon film. Haka lokacin girki, duk da mai aikin su Amma haka Hajjan za ta sata a gaba ita da jidda su shiga kitchen, tare suke aiki Kuma duk da kwarewan ta a girki a dan zaman ta da Hajja ta koyi abubuwa dayawa. Ba abinda yake burge ta kaman yanda matan kwata kwata ba ta wasa da Sallah. Inta fara karatun qur'ani Kuma ko azkar Sai ka dauka bacci take a dakin saboda yanda take daukan lokaci. Musamman ta sasu Jiddah, Abdallah da Baffah su ka Kai ta mall, taje tayi siyayyan abubuwa da dama. Ko taki daukan abu Jiddah dauko mata take yi. Haka su ka dawo da kaya niki niki, tama dauka Hajjan za tayi fada Sai taji yaba ma jiddan ma take akan kokarin da ta mata. Ashe ita ta sata yin hakan. Ai ko ba abinda ta nema ta rasa. Babban abinda ya kayatar da ita, yanda ya zama al'adan gidan, da an idan da sallan Asuba za a zauna karatun qur'ani duk a babban falon gidan kowa na bitan nashi. Ta gode ma Allah, ta Kuma kara gode ma Sanda sannan Dr. Dan da ba don su ba da taji kunya a wurin. Duk da haka Sai da Abdallah ya dinga dan mata ya gyara, don da alama duk cikin su yafi su ilimin addinin sosai. Abincin gidan kuwa ba a taba girki ba olive oil wato Zaitun da Kuma Habbatu sauda a ciki. Domin neman tsari daga cututtuka da dama.

Sai dai tun daga ranar da Sanda ya kawo ta, bata Kara ganin shi ba Kuma. Tana jin nauyin tambaya duk da damuwan da tayi. Ranar tana cikin kallon pictures da Jidda ta kawo mata, tana nuna mata su Aseem da Ummin da baban su. Ummin ta, ta zama babban mace. "Hotunan sunyi kyau sosai"

"Ai brother ne ke daukanmu yawanci. He got a great skill in photography. Kinga wallpaper in da ke courtyard In gidan nan, duk shi ya dauka, yayi enlarging insu suka bada nice view in nan. Shine aka yi printing ya zama wallpapers.

She almost ask waye brother, Sai Kuma ta tuna ashe abinda duk suke fada mishi kenan. Abdallah step brother in shine ashe, two years ke tsakanin su shiyasa they are more like friends.

Satin ta daya, Kuma gabadaya ta saba dasu musamman Jiddah. Hakanan zata zo ta zauna kusa da ita, ta kwantar da cinyan ta kan Suhaima tana fadin "Adda I've been dreaming of this moment ashe zai zo" irin maganaganun yana sa ta jin hawaye na Shirin zubo mata. Sai dai ta kan yi kokarin boyewa gudun kar Jidda ta fahimta. Sai dai duk da haka akwai kadaici, saboda duk suna zuwa school. Shi daman Baffah, ashe ba garin ya ke karatu ba, so a campus yake zama, Sai dai weekend ya shigo. Jiddah na zuwa Al-azhar. Abdallah Kuma na zuwa aiki Sai Hajja da ke zuwa wani Islamic College da take lecturing a can. Ganin yanda take zuba larabci, hakan yasa Suhaima ba tayi mamaki ba.

Don haka Hajja tayi deciding ayi enrolling inta a wani school ta dinga zuwa. Da ke tana da interest sosai akan catering, kawai sai ta zabe shi. Itama Sai ta zama occupied, da ta dawo Kuma ta tafi Islamiyya, da it's da kanta tace ma hajjan tana son shiga. Akwai ranar da suka je gidan Anty Jamila, cousin in su Abbah da ta dauko Baffah. Turn out taga halin da baffan ke ciki ne a maiduguri yasa ta dauko shi da niyyan zata rike shi,  itan kawar Ummi ce Kuma ta San abinda  ke faruwa. Bayan ta dauko shi Sai ta Kai ma Ummin danta, Ummi tayi farin ciki sosai Amma Sai tayi ma Anty Jamilan kara tace ta rike shi kawai. Haka akayi, a gaban ta ya taso Sai dai Yana yawan zuwa wurin su, ta yanda har suka you sabon ban mamaki.

Taji dadin ganin Suhaiman sosai, harda hawayen ta. Sun dan tattauna da ita Anty Jamilan kafin suka dawo gida. Sai da Suhaima ta shafe wata biyu da kwanaki a gidan Amma ba Sanda. Tana jin dai ana waya dashi Amma ta kasa tmbyn kowa ina yake. Baban Abdallah ma da ya dawo, ashe yaje wani aiki ne Canada. Musamman yasa aka Kira mishi ita suka gaisa, shi inma dai Yana da kirki sosai.

A wani Weekend, taga an tashi gidan gadan gadan da aiki. Abinda ta lura shine aikin yafi focusing akan dayan side in dake gefen wurin da suke zama. Shi inma babban wuri ne sosai, don girman duk kusan daya ne. Bayan gyaran, Sai Kuma Hajja tasa su suka hau girke girke, musamman ita dake catering school ita aka sa a gaba tana ta abubuwa. Duk dai a wancan side in aka shirya su a kayataccen dinning table. Haka kurum Kuma take jin bata jin dadi ranar. Bayan ta gama aiki, ta gaji likis ne ta nufi dakin ta, ta dan watsa ruwa. Sai Kuma ta hau bacci mai nauyi.

Ba ta San iya lokacin da ta dauka tana baccin ba sai dai kawai taji muryoyi sama sama a kanta ana magana. "Ga Addan nan, Ina baku yarda dani ba" da kyar ta iya dagawa, tana bude idanun ta ta hadu da wasu kyawawan yaran guda uku duk suna smiling. Kaman da taga dukkansu suna yi yasa ta gane ba shakka triplets in da jiddah ke basu labari ne.

"Hey dear sis Adda my name is Aseem, this are my siblings Arif and Afra" ya fada yana nuna yan uwan nashi. Murmushi ta masu sosai sannan duk ta Mika musu hannu "nice to meet you little ones"

"Ba nace muku Kar ki tashe ta ba?" Jidda ta shigo tana fada, duk Sai suka juya wannan ya kalli wannan suna murmushin rashin gaskiya. They look so cute to her, nan da nan taji yaran sun shiga ranta. Duk suna Kama da Abdallah hakan yasa take tunanin ko iyayen su na da alaka.

Cewa Jiddah tayi ta daina musu bala'i. Sai bayan sun fita sannan fargaba ya fara kewaye ta. Sai lokacin abun ya sinking in, she is about to meet her mother. Bayan dimbin shekaru masu yawa. Rudu da rashin sanin abun yi ne ya cika mata kwakwalwa. Ba ta San farin ciki ya kamata tayi ba ko akasin shi. Hakan yasa ta kasa ko da mikewa daga kan gadon, baki daya jikin ta rawa yake ga Kuma zufan rikicewa da goshin ta ya fara fiddawa. Ta dade da cire rai da samun wani abu daga mahaifiyar ta, shiyasa ko yanzu bata wani tsammani wani abu mai mahimmanci, illa iyaka ta San idanun ta na matukar bukatan ganin fuskan da ya kawo mata duniya. Kaman yanda zuciyan ta ya dade yana suya akan hakan. Shin mahaifiyar ta, ta mata adalci kuwa a rayuwa? Shine har yanzu abinda ta kasa tantancewa. Shiyasa ta zabi zama a dakin saboda ba ta da ra'ayi akan me yaka mata tayi yayin da idanun ta suka sauka kanta. Ta dai samu wani sauki a ranta, ko don sanin da tayi zuwa Ummin nata ba yawon duniya ta shiga ba Kaman yanda aka dade ana ikirari, ko Kuma tace kaman yanda ita in tayi.

Ta naji aka bude kofa, Sai da gaban ta ya girgiza domin tsoron wanene zata gani. Wani sanyi ta dan ji ganin Baffah ne, jira yake ta bashi izinin karasowa. Da Kai ta amsa mishi, ya tako har zuwa inda take ya zauna daf da ita. Hannuwan ta ya kamo duka biyu, yasa cikin nashi Yana kallon yanayin ta.

"Adda nasan cewa is not easy abinda kike Shirin fuskan ta a yanzu. Ban San me ke zuciyan ki Amma Ina sin sanar dake Ummi ba ta bar ki wurin Abbah don bata sonki, Sai don hakan ne kadai mafita a gare ta a wancan lokacin. Ina so ki mata kyakyawan zato, domin rashin ki a rayuwan ta Abu ne Wanda bai taba gushewa ba. Kana ganin ta, tana cikin wadata da kwanciyar hankali Amma Kuma kallo daya ake mata a San akwai babban abinda ya gushe a rayuwan ta. Ba ta cika ma kowa maganar ki don bata so abun ya dame ta Amma Kuma ya dame ta in, I can assure you daga ni Sai Kuma brother kadai ta iya sanarwa abinda ke damunta. Ki zo muje ku gaisa, Sai ina so in akwai wani kullatan da kika yi don Allah ki min alfarman goge hakan a zuciyan ki" ba ta amsa shi, Sai dai Yana tashi ta Mika mishi hannuwan ta, ya dago ta. Hannun su a hade suka tafi har zuwa sashen Ummin. Su Aseem da Jiddah duk suna side in Hajja, hakan yasa wurin daukan shiru.

Da baban su Aseem suka fara cin karo zai fito falon. Cikin ladabi, Suhaima ta gaishe shi. Yana ganin ta ya gane itace, domin labari ya iske su. Albarka ya sa mata sosai, sannan ya sanar da ita zai fita Amma in ya dawo zai zo suyi zama na musamman.

Baffah ne yayi Sallama a side in, yana jin amsawan Ummi daga cikin dakin ta. Don haka suka cigaba da tafiya har wurin dakin.

"Ki shiga, duk munje mun mata Sannu da zuwa saura ke. Itan tace in shigo da ke" da Kai Suhaima ta amsa me shi. Ya mata wani kallo mai cike da nuna karfin guiwan sannan Sai ya juya.

Tayi seconds a wurin tana contemplating bude kofan. A hankali ta Kai hannun ta kan handle in kofan, ta fara murdawa. Sai dai duk yanda taso jarumtan, kafafun ta sun gaza bata hadin kai. Sam Sam ta kasa matsar dasu gaba, Sai ma ja da baya da ta fara yi a hankali, ita kanta ba zata iya cewa ga direct abinda kanta ke processing ba.

Zuciyan ta da tunanin ta sunyi cunkushewan da bata iya jin Karan bude kofan ba. Sai dai Kawai Mutum ta gani a tsaye a gaban ta. Kallon kallo suka tsaya yima juna, for some seconds, it all feel surreal and too good to be truth.

"Au taso ki yayi daga baccin? Me yake sauri ai Zaki tashi ko" Ummin ce ta fadi haka, kaman ba wani abu da ke damun ta. Suhaima kam ba ta ma amsa, Sai dai wani sanyi da take ji na zagaye dukkanin ilahirin jikin ta. "Shigo mana to" Ummin ta kara fada, ganin Suhaiman ba ta ko motsawa ya sa Ummin jawo hannun ta suka karasa cikin dakin.

A gefen ta, ta zaunar da ita tana kallon ta. She can't believe Suhaiman tane ta zama haka. Wani irin kwalla take ji sun cika mata idanu, Wanda ta rasa ba dadi ne ko Kuma na bakin cikin rayuwan da yar tata ta tsinci kanta a haka. Kamo hannayen ta, tayi duka biyu tana kallon ta, Sai ta bude bakin ta za tayi magana Sai taji kalaman duk sun bace mata. Ba ta San mai zata ce mata ba, ba ta San abinda ya dace ta fada wa yar tata ba. Taba ta kadai da take yi, ji take wani irin annashuwa hade da fargici na zagaye da ita. Lallashin ta zata yi? Hakuri zata bata ko kuwa? She all deserves them Sai dai Kuma ba ta San taya ba.

Da sauri Kuma ta jata a jikin ta, tana wadata ta da dimin Uwa Wanda tayi rashi a rayuwan ta. A hankali Suhaiman ta zare jikin ta. She can't resist this, it so good and beautiful. Sai dai duk seconds daya yana tuna mata abinda tayi missing kenan a dukkan rayuwan ta. Kallon Mahaifiyar tata, tayi Ido a raunane tace "Ummina meye sa baki jira ni ba? Islamiyya kawai Zan dawo, shine ya maki tsauri?" Tmbyn da ya dade yana cin ranta kenan, a kullum duniya Sai ta tuna wannan shiyasa a yanzun ma shi inne ya fara zuwa mata.

Girgiza Kai Ummin tayi, tana kallon yar tata "Saboda ban son kika tafiyana da idanun ki, a tunanina hakan zai fi Miki ciwo Kuma Zaki fi rike shi. Ko da na tsayan ma, Mahaifin ki ba zai bari in tafi dake ba, ya riga ya Gina katanga a tsakanin mu" Zuwa yanzu duk hawaye ne ke fita daga idanun su.

"Amma meye sa baki Kara nema na ba? Shin ki manta ina da bukatan hakan a rayuwa ta" Shiru Ummin tayi, a ranta tana mamakin yanda ta dinga jiran wannan ranar da Suhaima za ta sata a gaba tana tuhuman ta. Ashe zai zo? Ta dade da fara fidda rai.

"Nayi tafiyan da ba juyawa a cikin shine Suhaima, ko na dawo ba wani amfani tunda an riga da an min iyaka da ke. Ciwon nake gudu hakan yasa ban waiwaye ki ba, Sai ma hanyan da nake nema inga kin dawo gare ni baki daya. Ashe Allah bai nufa hakan ba"

da sauri sauri Suhaima ta fara girgiza kai "Ki dai nemi wani hujjan Ummi Amma wannan bai isa hujjan da Zaki bani akan bari na da kika yi cikin kunci, wahala da azaban rayuwa. Ashe daman uwa na gudun dan data Haifa? Meye sa kika zabi ki so kanki dayawa? Ki fada min gsky Ummi, dan na kasa daina zargin cewa ba ke kika haife ni ba, a duk yawan da nayi rayuwata, ban taba cin karo da Uwa irin ki ba don ..."

"Keh!" Ihun da taji daga bayan tane yasa ta juyawa. Ido hudu su kayi dashi sai huci yake "ashe daman har yanzu da sauran rashin hankali tattare dake?" Umar Sanda ne, wani irin kallon banza yake bin ta dashi kaman Wanda ke Shirin shake ta.








Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top