Arba'in da takwas
Ba yabo ba fallasa, Ummin ta amsa gaisuwan Suhaima. Sai dai Kuma ta lura Sai kallon ta take, kaman mai son karanto abu a fuskan ta. Hakan yasa Suhaiman dukan da kanta. Ba su wani dade ba, Dr Fahad yace zasu wuce. "Ba zaku jira lunch ba?" Ummin ta bukata.
"Kai muna kan hanyan Ummi" ya amsa.
"Toh Shknn ba matsala" mikewa tayi ta nufi ciki. Can Sai gata ta fito, da Dan gift nylon a hannun ta. Lailah ta bama wai ta ba Suhaiman. Amsa tayi tai godiya. Abu daya Kuma Suhaima ta fahimta gun Ummin. Ba za ta wani iya tuna Ummin ta sosai ba Amma memories inta na nan cikin kanta. Don haka bata shakkan wasu abubuwan nasu na shige, kaman yanayin takama da rashin son magana duk. Ko dan ba ta manta cewa Dr ya gaya mata ita ma yar kollere bace. Maybe shiyasa abubuwan nasu ke shige.
Da suka zo fita ne Sai ga mota yayi parking a haraban gida. Surprisingly, Amma to Dr in banda Suhaima. Faroukh ne ya fito, Sai ga El-yas ma. Dukkan su sanye da manyan kaya, which is unusual domin dai ba shigar su bace. Yau Kuma Sai ya musu kyau fiye da tsammani. Kallon su kawai Dr yake ya kasa shiga mota, Suhaima Kuma didn't offer any explanation. El-yas ya fara ganin shi, dake shi in ba wani sanin shi yayi ba Sai ya tabo Faroukh. "Ahh Dr Fahad ne ai"
"Ga Suhaima a gefen shi ai" a tare suka karasa wurin Dr in. Ya basu hannu suka gaisa. Dr na Shirin tmbyn ko wurin wa su ka zo Sai ga Kiran Zahra ya shiga wayan Faroukh. "Hello zee mun shigo"
"Wurin Zahra kuka zo?" Dr in ya tmby, El-yas ne ya amsa shi. Kafin yayi demanding for more explanation ya shiga cikin big brother mood in shi. Zahra ce ta fito, hakan ya tabbatar mishi da abinda yake tunanin daga yanayin noke noken da Zahran ta fara tana ganin shi.
"Shine F in?" Dr ya bukata, kasa amsawa tayi Sai Laila da ke bayan su ta amsa mai, zo kuga harara gun Zahra.
Irin kallon attack in da Dr ya fara aika mishi yasa Faroukh in dukan da kan dole. "Bani numban ka" kawai yace, El-yas ne ya bashi sannan ya bude mota ya shiga. Suhaima already na shiga don haka kawai ya ja motan su ka bar gidan.
"What ur future plan" kaman daga sama taji tmbyn nashi. Kusan 30 minutes kenan su kayi da barin Abuja, duk lokacin ba Wanda yayi magana Sai yanzun da ya katse shiru da ke ta tashi a tsakanin su.
"Housemanship" ta fada ita ma kaman ba da shi take yi ba.
"Finally, then?"
"Service" ta sake fadi, tana kallon titi. Cikin yan kalilan kwanakin nan, ba tayi zaton cewa zata kara taka wannan hanya ba a rayuwa. Ashe tana da wani sauran farin ciki da sakewa a rayuwa. Ashe tana da sauran dama yin magana hankali kwance kaman ba ta tattare da wani matsala ko damuwa a rayuwa.
"Good, daga nan fa Kuma?"
Tl
Tunani dayawa ne ya fara mata yawo a ka. Zuwa can tace "Work?" Yanayin amsan nata ya sa shi gane kaman by ta ke.
"Nothing special?" Murmushi ta sake sosai, Sai dai yafi Kama da na ciwo akan farin ciki.
"Me kake expecting?"
"Marriage?" Ta gane tmby ne ya mata. Amma Kuma sai ta dan fuske.
"Let me just hope for the best" ta fadi, tana dukan da kanta saboda juyowan da yayi yana kallon ta.
"To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi"
Suna isa Kaduna ya wuce da ita gidan shi. Faran faran su ka gaisa da Rufaida ta mata tarba mai kyau da mutunci. Ta Kuma yaba sosai. Duk da yanayin Rufaidan ta San fuskewa kawai take tana dannewa. Amma dole akwai kishi. Sai dai ta rika tasan cewa ba wani abinda zai shiga tsakanin ta da Dr banda mutunci, bayan nan ita ma ba ta fatan wani Abu. Ba wai Dan ya mata wani abu ba. Aa kawai saboda tana ganin mutum kamili kaman shi bai dace da irin ta ta gurbataciyyar rayuwan ba.
Bayan sun natsa ne Dr in yazo ya same ta da alamun magana ya ke so suyi "Barr ya Kira ni, yace a kaiki gidan Anty, mum insu Faroukh, so yakike gani?" Dan shiru tayi dan bata ma San abun fada ba. Tunanin ta daya bata San wani irin tarba zasu mata ba, musamman ma Antyn. Tun dai yanzu ta San everything is open, kowa ya San komai. An San halin ta na boye da Kuma na zahiri.
"Ba matsala muje" tace saboda sanin banda wani mafita bayan wannan.
Suna shigo Sai ga Anisa dasu Muhibba da gudun su. What she never expect to happen har zuciya ta. "Sis I miss you" Anisa ta fada bayan tayi hugging inta. Da farin cikita duk ta Kama su. Gaskiya yaran nan, Sai dai godiyan Allah Amma akwai zuciya mai kyau.
"Ina mum?" Ta tmby jiki a sanyaye
"Tana ciki, wow sis I thought I will never see you again ma" murmushi tayi, Wanda ta dade ba tana yin shi kawai ba wai ya Kai har kasan zuciya ta bane. Sai dai dan yin is more like an obligation ne kawai.
Mum seems nice and welcoming. Har congratulating ina tayi akan yanda case in yayi turning out. More like she is so over the moon about her son achievement. Ba wanda ya San Faroukh is involved Sai yanzu kawai. Dakin su na da suka tafi da Anisa, the house is still comfortable but God! Ji take kaman she no longer belong there. Haka dai na daure.
Da yamma Faroukh su ka zo da Maryam. Ita ma ba yabo ba fallasa suka gaisa da ita. Sai dai yanayin ta kaman na Rufaida, nasan akwai abinda take dannewa. More especially inta ji Barr na mata tambayoyi.
"Ina so inyi registration for license Exams ina. Amma kafin time in ina son zuwa gida." Ta amsa mishi tmbyn plans inta da yayi. He seems glad, ganin am finally moving on with my life. He still cares duk ta lura interest in nashi ba Kaman da bane. She likes that he is moving on, dan har ga Allah ba ta shirya wani tashin tashina a gaba ba Kuma.
"Sai dai zan dan katse miki hanzari Suhaima" haka kurum taji gaban ta ya fadi more like tana jin kaman he is about to tell her something huge and demanding.
"Umar yazo ya same ni, ya naso ku tafi tare dashi zuwa can kasan da yake zaune. He tell me his reasons Kuma mun gamsu dasu. Sai dai zan so kije ki ganewa idon ki da kanki zai fi akan in na gaya miki" Confusion ya mamaye ta Baki daya. Na farko tunani ta fari waye Umar? Sannan taya za ta bishi zuwa wani kSa can da ba ta sani ba Kuma su yarda da hakan? Anya ba suna neman hanyan da zasu yi getting rid of her bane?
Ya karanci abinda ke fuskan ta. Dai dai lokacin Kuma Anty ta shigo. Maryam da ke falon Kuma ta fita ganin maganan ba nata bane ba.
"Umar Faroukh Machina or should I say Sanda?" Da sauri ta mike tsaye dai dai lokacin da Antyn ta karaso tana fadin "Lafiya?"
"A ina ka ganshi Barr?"
"Relax ki zauna muyi magana"
Da kyar ta iya zama sai dai kana ganin zaman kasan tana cikin tension "Ya sanda?" Ta ambata, Sai dai still tana cikin doubt. Musamman in ta tuna Barr ya karanta labarin ta Sai da kawai ka man zolaya ne ma kawai ya ke mata.
"Shi Faroukh ya ke ma a aiki" a hankali ya warware mata komai. Sai dai still komai na zuwa mata kaman almara. Still Sai tace "Ni kam bazan bishi ba, Zan koma gidan Mahaifina duk kuwa kalubalan da zan fuskanta yanzu a can in" Abun mamaki, tana fada zuciyan ta na kara mata wani zafi. Neman yaki da zuciyan kawai take, domin ambaton gidan ma kadai na sa mata wani irin kuna na zuciya. Tana jin kaman ba ta yanda za ta iya abinda ta ke fada. Musamman inta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaya Baba da abokanan su, yanda suka keta mata mutunci. Duk da haka she is willing to overcome duk wani kalubalan da ke Shirin kunno mata.
Cikin hikima da dabara Anty ta fara lallashin ta. Musamman da yake Mustaphan ya gama sanar da ita duk yanda su kayi da Sanda. Itan ne kawai ba ta sani ba, ba Kuma sa so taji a bakin su. "Kije in kin ka sa zama nami alkawari zan sa a dawo dake. Kawai ke neme ni in kinji wani Abu" Abinda Antyn ta fada mata kenan. She is not convinced though, har lokacin ba ta jin za ta iya bin Sandan. Mutum da ta watsar Baki daya a baya. Ba ma haka ba "Amma miye fa'idan hakan? Ba wani abu tsakanin mu dashi fa"
Shiru Antyn tayi ta rasa ta yanda zata bullo mata. "Ba wurin shi Zaki zauna ba, Mahaifiyar shi na can. Ita tace ya Kai mata ke, tasan duk abinda ke faruwa" shiru kawai tayi tana tunani, yanzu abun ya Dan fara mata making sense. Tasan a labarin da take iya tunawa Ummin ta na bata, Maman Sanda mutuniyar tane. Sunyi zaman mutunci da amana kafin ta bar gidan su Sanda. Maybe saboda hakan ta ke son taimaka mata. Shirun da tayi, ya tabbatar musu da sun shawo kan matsalan. Sai dai ita tunani daya ya makale mata. Yanda zata fuskanci shi Sandan.
Is not like she got a solution, don kuwa washegari bayan Anisa ta taya ta shirya kayan ta Baki daya. Cike da jimamin kara rabuwan da zasu yi a karo na biyu. Ita kanta Suhaiman duk da ta girmi Anisan sosai Amma tana jin dadin zama da ita. Yan biyu ne suka shigo da gudu suna fadin "Anty Suhaima wai kizo ya isa"
Dam! Haka taji gaban ta ya buga. Hatta Anisan da ke kusa da ita Sai da ta fahimci hakan. Amma Sai ta hau tausasa ta. Tun daga corridor take jiyo hiran su da Barr. Ga muryan zar Yana tashi, ba ta tunanin zata taba mantawa da wannan muryan kuwa. Jiki na rawa, sanye da hijab inta ta karasa falon tana kallon kasa. Idon nun da ke ji a kanta ne dai, ta kasa tantance na waye. Wuri ta samu a kasa ta fara musu gaisuwan jam'i. "Ina kwananku?" Ta fada tana jin maganan na Shirin makalewa a bakin ta. An dai amsa ba Kuma za tace waye be daga cikin su ya amsan ba saboda hankalin ta da ya fara gushewa.
Zaman shiru ne ya gudana na tsawon minutes. Can Sandan yace "Yakamata mu tafi, banson muyi missing flight duk da dai na dare ne" Yanayin maganan shi kwata kwata bai canja mata ba, Sai dai ta kasa kallon shi taga ya yanayin shi ya koma. Duk da yanda zuciyan ta ke azalzalan ta tayi hakan.
"Aa na dauka za ku tsaya lunch ai. Abujan naga 2 hours drive ne" girgiza Kai Sanda yayi "ban son a samu matsala ne dai kawai"
"No ka bari Dan Allah" Baban su Anisa zai zo ba Sai ku gaisa ba. Kuma Anty ma ba ka gaishe ta ba, let me talk to her. Tashi yayi ya bar su, su biyun a falon. Duk cikin su ba Wanda yayi ma wani magana a haka kowa na harkan gabanshi har Antyn ta fito. Suna cikin gaisawa Sai Engr tare da Faroukh, gaisuwan mutunci su kayi, har da karawa da musu godiya. Su ka nuna mishi bakomai. Duk yanda ya so su wuce, Anty kin yarda tayi. Tilas su ka tsaya aka yi lunch sannan su Anisa su ka fidda ma Suhaima kayan ta. Gabadaya ma ba ta hada wani abun kirki ba, ta dai debi abubuwan da take bukata Sai kaya da basu wuce five set ba duk a trolley saboda Kar tayi kaya dayawa.
Gabadaya su ka fito raka su, ita dai jikin ta a sanyaye ta shiga front seat in. Tana musu Sallama har Umar Sanda ya ja mato su ka bar gidan ba ta it's dago idanu ta kalle shi ba. Abun ma har da wani irin nauyi da kunya da take ji ya mamaye ta duk a kanshi. Shi inma kala bai ce mata ba ya cigaba da tukin shi cikin kwanciyar hankali. Ba ta San dalili ba taji yayi parking a wani gida.
Sai da ta dago kanta, ta gane gidan Dr ya kawo su. A tsaitsaye su ka shiga, su ka gaisa. Shi inma Sanda godiyan ya mishi. Da suka ki cin abinci, Rufaida ta hado su day snacks da drinks dole Suhaima ta amsa. Dr in dai shima jikin shi duk a sanyaye haka suka bar shi suka Kama hanyan Abuja. Da Shirin yayi yawa a motan, kawai sai yasa wa'azin Sheikh Aminu Daurawa na Kundin tarihi. Shi yake ta tashi a cikin motan. Sai dai zuciyoyin su na dauke da abubuwa dayawa, musamman Suhaima da har yanzu ba ta San the best way da Yakamata tayi reacting wa zaman ta kusa da Sandan ba. Ga tarin tambayoyi a bakin ta, Amma ba ta ita ya kallon shi balle ta ga yanayin fuskan shi, ko ta hasaso yanayin yanda zai amshi tambayan nata. Sai dai Kuma shi inma ba magana ya mata, balle ta gane wani irin yanayi yake ciki game da ita. Fushi yake da ita ko kuwa?
Haka suka isa Abujan ba abinda ya shiga tsakanin su. Wani wuri ya fara zuwa, aka kawo mishi wasu takardu yayi godiya suka tafi. Sai a sannan taji yace "Akwai abinda kike bukata, ko abinci ko dai wani abun?" Sanin bai kallon ta yasa dole ta bude Baki tace "Aa" daganan bai kara cewa komai ba ya dau hanya. Wannan karon wani estate taga sun nufa. A bki wani apartment yayi parking yana fadin "ina zuwa" ya dan dau mintuna a ciki. Sai can Kuma ya fito dauke da jakan baya babba Sai Kuma jaka guda biyu, daya dai tasan na system ne Amma dayan she can't say. Daganan kam hanyan airport ya dauka, Sai da ya fara tsayawa Immigration office ya amshi abu sannan suka karasa airport in.
Karfe shidda dai dai suka yi checking out sannan Kuma aka fara boarding. Duk abubuwan nan ba wani magana tsakanin su har suka samu wuri cikin jirgin. Sai da jirgin ya tashi tukunna ya fara hidiman gaban shi. Can ya bude side bag in ya dauko wani English novel ya Mika mata.
"Thanks" tace bayan ta amsa. Daman dai ta gaji da zaman shirun. Ai kuwa nan da nan littafin yayi nasarar dauke hankalin ta. Kaman ya sani, she definitely need it ko ba wai don kore zaman shiru ba. Ko Dan saboda current situation in da take ciki. Na rashin sanin mafita a rayuwa.
Karfe bakwai na dare jirgin su yayi landing a babban birnin Egypt wato Cairo. Bayan sun yi getting luggage insu su ka fita haraban airport in. Wani mutum taga Yana faman dagawa Umar in hannu. Suna karasawa wurin shi, suka rungume juna kowanne na fadin "I miss you" a bakin shi. Sai da suka tafa sannan wancan in ya dago kanshi.
"Suhaima?" Ya bukata, da Kai ya amsa mishi. Ai ko Sai washe baki Yana mata fara'a. Da English ya soma mata magana, Yana gaishe ta, ta amsa. She didn't miss the Arabic accent in his voice.
"Wow! I finally meet you after so many years" bata ce komai ba, Umar in bai fada ba.
"Am Abdallah, I know he never talk to you about me though" murmushi kawai tayi. Suka shiga mota, suka bar Airport in. Tana baya tana jiyo hiran da ke gudana a tsakanin su. Don ma Arabic suke yi, ita Kuma ba ji take ba ma balle hiran ya dau hankalin ta.
Sun dan yi tafiya mai nisa sannan su ka shiga wani babban gidan. Architectural building in baki daya ya tafi da ita.
"Bismillah" wannan karon Umar in ne yayi magana ganin ta tsaya bata motsi. Yana danna ring in aka zo aka bude musu. Wata budurwar yarinya ce, fara sal kyakyawa da ita. Tana ganin shi ta hau murmushi tana fadin "Marhaban brother, where is she?" Dan hararan ta yayi, yace "Who?" Ba ta amsa shi saboda hango Suhaiman da tayi a bayan shi. Da sauri ta karasa wurin ta, hugging inta tayi tana fadin "Oyoyo Adda kun Sha hanya" hook Suhaima tayi, har ga Allah ba ta taba tunanin yarinyar ta iya Hausa ba ma kwata kwata. Ita taja ta suka shiga ciki dukkan su harda Abdallah dake ta tsokanan yarinyar da har yanzu ba ta San sunan ta ba.
Tana ganin matashiyar matar da ta fito tasan cewa mahaifiyar Sanda ne. Da sauri ta tsugunna tana gaishe ta. Dago ta tayi ta rungume ta. "Oyoyo my daughter, welcome home" da kunya Suhaima ta amsa.
"Jidda nuna mata dakin ta mana, can't you see she looks exhausted. Ki kaita ta huta ko"
"To Hajja" ta amsa. Bin ta Suhaima tayi har zuwa dakin. Bai da wani hayaniya Amma ya dau hankalin ta. Bayin na ciki don haka nan da nan ta shiga ciki. Sai da ta watsa ruwa sannan tayi alwala ta fito. Tana tunanin ta ina ne gabas Sai ga jiddah ta turo kofa. "Wai Hajja tace a kawo miki abinci nan ko Zaki fita falo"
Da dan kunya tace "Bara nayi Sallah, ina ne gabas" nuna mata tayi sannan ta fita ta barta. Da kanta ta fita falon dake ta gane hanyan. Duk suna kan dinning saboda haka ta lallaba kusa da jiddah ta zauna. Ita tayi serving inta, a hankali ta fara tsakuran abincin. Abun mamaki Sai Kuma ta ji kaman ana kallon ta. Tana daga idanun ta, for the first time suka hada ido da Sanda. Kyar ya ke kallon ta ba ko kiftawa, tilas ita ta sauke nata idanun.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top