Arba'in da Shidda
Burj khalifa, Dubai.
United Arab Emirates.
Wani irin murmushi ne ya sauka kan fuskan shi dai dai lokacin da hannayen shi ke typing Mission accomplished a Email address in ogan shi. Wani iri annashuwa da farin ciki hade da kwanciyar hankali ya ke jin yana mamaye duk ilahirin shi. Ba yau ne na farko da ya fara samun saa akan case in da ya ke dauka ba. Wannan in dai ya kasance daban ne, saboda mahimmanci da ke tattare dashi. Bai ko shakkan komai ya zo karshe. Nan da nan yayi dialling wani numba, visa ya sa a mishi processing. He can't wait to be finally back in Nigeria. Har ya kwanta, tuno tan da yayi ta sa shi saurin mikewa yana mai lalubo wayan shi. Nan da nan yayi dialling numban ta, kaman Wacce ke jira yana shiga ta dau wayan. Saukan sautin sallaman shi a kunnen ta kadai taji ta gane shi ke magana.
"Faroukh" tayi sauri fada. Sai da yayi murmushin da ya tsaya iya bakin lebba. Sautin muryan ta kadai ya tabbatar mishi she have been longing for the call. Dama ya San dole hakan zai faru, Sai dai Kuma wannan na daya daga cikin punishment inta ne.
"Zan sa a miki processing Visa zuwa jibi you are good to go In Sha Allah, Sai ki zauna cikin shiri" Godiya ta fara yi, Sai dai duk yanda ta so ya tsaya su gaisa da kyau hakan bai faru ba. Duk da haka taji dadin call in nashi, a da tayi tunanin ba zai cika alkawarin ba ya manta da ita. But now it good to feel like Nigeria is safe for her. How she miss her job, Kai Allah ya kiyaye ta a abinda zai sa ta kara shiga dana sani. The good thing, kyautan da ta samu daga wurin su Rawan da ku sunan da bikin ya jawo mata. Ba taji akwai wani Event planner da ke tashe a kasan yanzu kaman ta. One good thing about her, ba ta Nigeria amma hakan bai sa ta samu gargada akan sana'an taba. Saboda hakan ya sa take making sure she work with professional. Mutanen da ke da principle, in kaga harka yayi kasa to tabbas kaddara ce kawai irin ta Ubangiji.
...
Kotu ta cika makil wannan karon fiye da tunani ma. Abun mamaki hadda fuakokin da ba ayi tsammani. Domin dai Hajiya Binta ce zaune a gefe daya, wato uwar gidan Al-mansur, Wacce ake kyautata zaton ita ce ta shigar da karar. Sai cika take tana batsewa, fuskan nan a tamke ko alamun fara'a ba za ka hango. Gefen ta kuwa, Amina ko ince Nainarh ce a zaune. Kana ganin yanayin fuskan ta zaka san ranta a bace yake. Da dukkan alamu ba da son ranta ta halarci wannan wurin ba. Can gefe guda kuma, Umaymah Ameen da mukaraben ta. Kowa dai jira yake yaga ta yanda shari'an zai kasance.
Bayan Alkali ya samu shigowa ne, a ka karanto karar da za a gabatar a wurin kafin Kuma a gurfanar da Wacce ake kara wato Suhaima Adam Bello a gaban kotu.
Suhaima dai kaman yanda kowa ya sani, she plead not guilty akan abinda ake zargin ta dashi. Saboda haka Alkalin ya bama lauyoyin daman su fara gabatar da shari'an.
Barr mustapha ne ya fara magana cikin natsuwa da addu'an neman nasara a bakin shi ya Mike kan kafafun shi. Bayan ya gaida Alkali, ya kara neman a bashi daman tabbatar wa kotu ba Wacce ake zargi bane ta aikata laifin da ake zargin ta dashi.
Kai tsaye Faroukh ya fara Kira, abun mamaki Sai da ya Kira Faroukh inne idanun shi ya fada kan Engr Usman, mijin Antyn shi Kuma yayar matar shi. Bai San yazo ko alama bai sanar mishi da zai shigo Abujan ba ma. Kusa dashi Faroukh in ya miko rashin a hade har ya karaso wurin da ake bukatan ya tsaya.
Cike da kwarewa, Barr mustapha ya kalle shi "Sannu Faroukh, wata yar guntuwan tmby ce nake da bukatan yi maka." Bai amsa kawun nashi ya cigaba dacewa "Zan so ka sanarwa kotu ina kuka je kai da ranar da staffs in company inku su kayi meeting a guest house in Al-mansur"
Kai tsaye ya bashi amsan inda suka je in da Kuma dalilin da ya Kai su.
"Wa ya fara barin wurin a tsakanin ku?"
"Shine, saboda Kiran shi da aka yi a waya. Sai dai yana fita nima na fita" Sosai Barr ke samun karfin guiwan amsoshin da yake samu gun Dan Yayar tashi. Ba shakka they are going somewhere.
"Ba ka San wa ya Kira shi ba?" Girgiza Kai kayi hade da cije dan lebe.
"Kun ci wani ko shi kadai akwai abinda yaci bayan fitan ku har zuwa rabuwan ku dashi?" Wannan karon ma Aa ya amsa.
"To nagode Faroukh" juyawa wurin Alkali yayi ya sanar mishi iya tmbyn da ya zai mishi kenan. Daga nan aka Sallame shi.
Next hujjar da Barr ya gabatar Kuma, short video clip ne da aka yi connecting aka sa a laptop. Hoton Zayd Al-mansur ne ya bayyan baro baro akan screen in a cikin wani bar, gefen shi Kuma Hafeez wato ogan shine yana faman mishi bayanin cigaban da aka samu game da wani software da suke kokarin creating. Wani magana Zayd yayi akan Faroukh, nan da nan aka hango fuskan Hafeez in ya baci sosai "beware of that guy i don't like him" murmushi Zayd yayi, har ya dan mike yana fadin "bara naje jewel na jira na" har zai tafi Sai ga daya daga ciki ma'aikaciyyar su pat wato Patricia tayi appearing tana ta faman murmushi. "Oga har zaka tafi, baka sha abinda na maka ordering ba?" Dariya yayi sannan ya dauka ya kurba sau biyu Sai ya ajiye sannan Kuma yayi saurin kara dauka. "This is the best, I need it. Have fun with my oga pat" Yana fadin haka da saurin shi ya bar wurin. A nan clip in ya kare.
Tsit wurin ya dauka kafin Barr mustapha ya tashi ya fara gabatar da bayani kaman haka. "Binciken mu bai tsaya a iya Al-mansur ba kawai, Aa ya Kai har kan duk wani ma'aikacin shi Wanda su ka hadu a ranar dama Wanda bayanan da Kuma duk na kusa dashi. Interestingly, bincike ya nuna mana cewa baya rabuwan zayd da Faroukh, bar ya tafi wurin hafeez a sanadiyyan wayan daya mishi zasu tattauna. A Kuma wannan bar in ne muka samu duk wani rahoto da muke bukata, nagode ya mai shari'a" bayan yan wasu lokutta ne, Alkalin ya bukaci ko akwai magana da lauyan Wanda ke kara zai yi kan batun.
Kai tsaye ya tashi ya fara bayanan shi "Tabbas kwana wata da ya shaidu ya tabbatar da bayanin inda Zayd yake bayan rabuwan su da Faroukh Amma Kuma ba wani kwakwaran hujja da ta bayyana cewa wannan wine in da ya Sha ke dauke da poison in da aka saka mishi ciki. Sannan Kuma har mintuna nawa ya dauka bayanan kafin poison in ya fara attacking in shi? Wannan ba ta isa hujja ba a ganina rakan shi dade, ina fatan kotu tayi duba akan hakan."
Bayan Kotu ta bawa Barr Mustapha dama ne ya kara tashi yana fadin "Saboda sanin hakan ne yasa binciken mu ya Kai har asibitin da aka Kai Al-mansur da ita Wanda ake zargi bayan gobaran. Shaidan dai da lauyan gwamnati ya bayar kan tabbatar da poison aka sa mishi a abinci ko abin Sha. Sai dai Kuma ina ganin anyi omitting fadin wani irin guba ce wannan. Bayan samun sunan ta da yanayin ta a asibitin, mu ka Kai bincike akan guban research center." Mikewa Barr mustapha yayi ya amso wani paper ya Mika aka ba wa alkali sannan ya cigaba da cewa "Wannan gubar an tabbatar mana da cewa guba ce Wacce ta ke aiki a hankali a cikin jikin dan Adam a hankali tana mishi illa. Sannan ba ta fara bayyana kan ta har Sai ta Kai kaman wasu awanni a jikin Dan adam. Duba da irin lokuttan da duk abubuwan nan suka faru, za a gane cewa lokacin da guban ya diba bayan cin abincin da Wanda ake kara ta bashi yayi kadan ace a wannna abincin ya samu. Baya da haka daya daga cikin ilolin wannan guba ya kunshe sa yunwa da gaggawa kafin fara aikin ta. Wanda anyi hakan ne saboda an San zai koma wurin ta Kuma wurin ta zai nemi abinci in yunwan ya taso mishi. Nagode ya mai shari'a" gani kake kawai fuskokin dayawa daga cikin kotu ya dau fara'a, musamman wandanda su ke tausayin Suhaiman. Har ko da Nainah, duk da alakan da ta fahimci cewa akawai tsakanin ta da mijin ta, hakan bai sa taji cewa tana jin haushin Suhaiman ba.
Nan da nan kotu ta bukaci ganin Hafeez da Kuma Patricia. Shiru ne ya dau kotu, bayan wani dan lokaci wani force ya shigo, wurin aka samu sanarwar Hafeez na hanyan karaso daga airport saukan su kenan daga UAE Sai Kuma pat da aka tafi dauka ta a ma'aikata.
Lauyan gwamnati ne ya mike domin gabatar da shaidun shi, shi Kuma. Duk biyun magana su ke akan halin girman Kai irin na Suhaima da Kuma yanda aka santa da Amal. Hujjar shi dai daya ce, Wanda tayi haka it so clear she is after something don ta kashe shi bakomai bane. Har ga Allah, bai San haka shari'an zai kasance ba, ya dauka cewa ba ta wani hanya da za a cire ta daga wannan zargin. Musamman ya raina Barr Mustaphan, Yana ganin bai wani kware sosai ba.
Next Wacce aka nemi gani a gaban kotun kafin isowan su Hafeez, Zeenah. Cike da dagawan ta, ta tashi ta karasa wurin. Kotu ta bukaci jin sunan ta da alakan ta da Wacce ake zargi. " Sunana Zinaru Amma an fi kirana da Zeenah. Suhaima Kuma kawata ce mun hadu a gidan yanci" Hankali kwance ta ke amsa tmbyn da ake mata har aka zo kan shaidan da za ta bada.
Dariya tayi tace "Nasan abinda Suhaima ba ta sani ba. Kuma akan kawarta da tayi sanadiyyan zuwan ta Lagos wato Faree'a. Abinda yasa Faree'a kawo Suhaima Lagos ba dan komai bane Sai don son cimma burin ta akan Zayd Al-mansur da Kuma budurwar shi Amal. Tunda nasan Faree'a nasan ta mutum ce mai buri, Kuma in tayi buri ko ta wani hali Sai ta cika ma kanta. Nasan ta tun farkon da ta fara shiga harka. Haka Kuma nasan tsakanin ta da Hafeez wato abokin aiki Al-mansur, saurayin tane tun kafin Suhaiman ta zo Lagos. Amma tun zuwan ta bai kara zuwa. Burin Faree'a kuwa shine, Al-mansur. A Instagram ta San shi, farko a handle Amal kafin ta fara following in shi. Ta dade tana bibiyar shi saboda yanda ya ke burge ta, hakan Kuma tana tunanin shine dai dai target inta na irin matsayin da take son takawa a rayuwa. A cikin sambatun samun shine, ta hadu da Feedo, yarinyar Umaymah Ameen. A wurin ta, ta samu labarin alakan da ke tsakanin Umaymah da zayd da Kuma irin yanda take neman fansa. To taba ba Feedo aikin Sai dai maimakon ta rama ma ta, ita ma fadawa tayi tsundum a soyyayn zayd, kafin ta ankara ya gama da zamanin ta ya watsar. Faree naji hakan ta tafi nemo Umaymah Ameen, bayan sun saba ta nuna mata cewa tana da wacce zata dau mata fansa wato Suhaima. Tayi Using Inta ne saboda tasan Suhaima na da daman da zata iya daukan attention in Zayd, musamman ma dake sun gane irin macen da ake nema. Da gaske ne akwai plan akan da Suhaima da Umaymah su kayi akan Zayd, sai dai sun fasa Amma abinda basu sani ba dukkansu Faree using insu tayi. Nasan hakan ta hanyan Feedo, Wanda yanzu haka tana cikin kotun nan" To shari'a ya fara juyewa inda ba ayi zato ba. Har ma ga Barr Mustaphan, don ko da Zeenah tace mishi zata gabatar da shaida bai zaton irin wannan kwakwaran shaida gare ta ba. Lauyan gwamnati kam Sai dai zuba ido.
Aka Kira Feedo, duk ta kara maimaita abinda Zeenah ta fada. Kai har pic insu da Zayd sai da ta nuna a matsayin shaida. Mum in Zayd fa ido ya raina fata, Sai dai Nainerh kam jin ikon Allah kawai take. Abunda basu sani ba kuwa shine, Faree'a ba a gun Amal tasan Zayd ba. A gunta tasan shi domin dai da Faree'a aka yi bikin ta. Kuma tayi ta kururuta Zayd, ita Kuma Nainerh tasan halin Faree'a shiyasa ta yanke alakarta da ita. Nan Kuma ta fahimci ta bibiyi Suhaima ne don ta nuna mata bata isa ba tun da tace a kyale ta. Dadi da karawa, Faree ba Zayd kawai ta hango ba harda Amal, don tasan halin a barta musamman da ya kasance ita ma yar kungiyar ce. Sai dai a yanzu ido ne nata.
Tana ji kotu ta nemi Umaymah Ameen, duk tsoron reputation ranar ajiye shi a gefe tayi saboda kwarin guiwar da Umar Faroukh ya bata. Nan ta gabatar da abinda ya faru tsakanin ta da Suhaima da ma Faree'an tiryan tiryan. Mutane sun jinjina abun sannan Kuma dayawa sunyi tur da halin zayd. Ballantana Kuma da kowa ya San mutuwar Amal, Wacce har yanzu ba wanda zai ce ga exact abinda ya faru da ita. Mahaifiyar shi a wurin sosai tayi Dana sanin karar da ta shigar musamman da ta gane ta zubarwa danta mutunci warwas. Nan Kuma tayi godiya ga Allah da yasa ba ta sa an wahalan da yar mutane ba. Domin dai duk ita ta hana.
Da manya jami'an tsaro Faree'a da Hafeez suka iso wurin shari'ar. Zo kaga idanu, duk sun kade. Ga Allah wadai da ke ta faman tashi a cikin kotun kafin a saisaita komai Sai ga Patricia ma an daddago ta.
To zance fa ya Sha kwana. Domin dai asalin dalilin kamo su Faree'a da Hafeez ba wai akan case in Suhaima bane. Aa akan wani bincike ne da aka kungiyan CID na Nigeria bincikawa. Wanda ke hannun dan Nigerian da ke aiki a Egypt as a military intelligence. Sai dai CID inma sun bashi aiki yana musu wato Umar Faroukh Machina. Binciken kuwa akan Al-mansur industry ne Wanda ke hannun Zayd wato na computer. Abu ne kuwa da ta shafi intellectual theft.
Wani Software Industry a can kasan ake ma zagon kasa. Sai sun gama designing abun su kafin su Kai da sakewa Kuma Sai su Al-mansur su saki nasu, banbancin abu daya biyu ne. Anyi hakan kusan sau uku, gashi nasu company in Sai bunkasa yake da abin su. Hakan ya sa su ka shigar da karar a can kasan su, nan Kuma karar ta shigo har cikin Nigeria. Abun da Machina ya fara yi shine samun wani mutum daban ya shiga cikin company in Al-mansur in Yana kawo mishi rahoto. A nan suka gane cewa Hafeez ne mai designing duk wani abu anan wurin. Don haka ake son tafiya dashi domin bincike Amma he have to be cleared here.
Hafeez bayan yaji baki daya zargi da ake mishi, ba wanda ya karyata a ciki Sai na attempting kashe Zayd. "Nasan ina mishi zagon kasa, ina Kuma amfanuwa dashi ta hanyan cuwa cuwa Amma kuma Shirin kashe Zayd ba ya daga cikin tsari na gsky." Kallon kotun yake cike da nadama a idanun shi, bai zaton duk abinda ya aikata zai bi shi har Dubai ya dawo dashi ba Sai da hakan ya faru. Ya San ba za a yarda akan zancen da ya fada kan Zayd ba, Amma Kuma shi ya San bai aikata hakan ba.
A hankali ya karkata kallon shi kan Umaymah Ameen. "Kiyi Hakuri Umaymah, ba Zayd ya sa miki ciwon da kike dauke dashi ba. Nine" wani irin kallo Umayman ta Kai mishi, idanuwan ta sun yi jajur ba ta Sanda ta silale kasa ba.
"Ba a sanin ki ba nayi amfani dake lokacin Zayd ya shiga wanka, shi inma Kuma bai sani" rasa bakin magana tayi, shi can't believe all these years da ta dauka tana zargin Zayd tana tsine mishi wai ashe bashi ya sa mata cutan nan ba. Duk da kuwa hakan bai goge cutan son da ya shayar da ita ba. Amma Kuma taji wani Abu daga cikin kullatan shi da tayi ya kau. Sunan Allah ta koma kira kafin aka bukaci Faree'a.
Duk abinda Zeenah ta fada gsky ne Kuma ita ma ta tabbatar da hakan. Yau dai rana ne na fadin gsky da gsky. "Ba a Instagram na san shi ba, mijin kawata be Kuma tun a bikin ta naji ya kwanta min" Abinda ta fada kenan, da ya tabbatar da zargin Nainah. Duk da hankalin ta ya kwanta jin cewan Zayd bai da HIV amma Kuma har zuciyan ta tana jin ba ta cancanci yi ma wani hukunci ba saboda tarin nata irin laifukan ga mahaliccin ta. Musamman ma da likitoci suka kara tabbatar mata ba zata taba haihuwa ba a rayuwan ta domin mahaifan ta ya lalace, karshe ma Baki daya cire shi a kayi. Bayanan wani irin wari take jin Yana fita daga kasan ta, duk da yanzu dai an fara samun sauki saboda ta saduda ta fara komawa ga Ubangiji.
Faree'a ma kiri kiri tayi denying sanin wani abu game da zargin kashe Zayd. "Son shi fa nace nake, domin me zan kashe shi? Haka ma Suhaima ina da tabbacin ba zata taba iya yin kisan Kai ba" Nan fa kotu ta dauka, kowa da irin abinda ke fitowa daga bakin shi. Ba wanda yayi tsammanin shari'an za ta zo da sauki haka. Sai dai Suhaima kam ta riga ta gama yarda ranar addu'a ce kawai ta gani. Ta Kuma kara yarda cewa ba wanda zai rike Allah a rayuwan nan ya taggayara. Sabuwan nadama ne ke shigan ta musamman inta tuna cewa wai yau Amal ba ta duniya. Tana da bukatar haduwa da Zayd, domin sanin asalin abinda ya faru da kawarta.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top