Arba'in da Hudu
Rayuwata,
Babi na Sha bakwai.
Bayan bikin da kwana daya ya zo wurin Googo a cewan shi Mustapha suka you dashi zai maida ni maiduguri. Da ke Goggon ta San shi ba tayi wani musu ba illa ma godiya da ta hau mishi. Hakanan ba Shirin na dauki jaka na, na bishi duk da na so zuwa Ajeyari yiwa Anty Amarya bankwana don a watan zasu kaura Bauchi.
Ko a hanya ba wani magana mu kayi ba illa Nasihan da ya dinga min akan in natsu in maida dukkan hankalin a kan karatu shine kadai zai zame min gata a rayuwa. Godiya kawai na mishi, ya min fatan alkhairi. Ko da muka isa a tsaitsai ya gaida Goggo saboda ya sanar min daga maidugurin straight Abuja zai nufa. Washegari flight in su zuwa Egypt zai tashi. "Me zan fada ma Wanda ya bani sako a Baki?" Hakan da ya fada ne ya kara tabbatar min namiji ne mutumin.
"Allah ya saka da alkhairi" na fada kawai yayi murmushi yace "To zan isar, Sai munyi magana" daga haka ya ja motan shi ya wuce abun shi. Sai lokacin ma na tuna ban bude ledojin nan ba at all. Kayattatun Gift ne irin namu na mata, na Kuma ji dadin su sosai. Tun daman Abban ba mutum bane mai siya ma yaro duk abinda ya ke bukata balle kuma yanzu da nake wurin Goggo. Ni Kuma ban cika son ina tmbyn ta abu ba. Har ma da kudi, Wanda yawan su har Sai da suka girgiza ni Sai dai ko da muka yi magana na tmbyn shi ba'asi. Sai ce min yayi wai Wanda ya bani, na cancanci fiye da hakan ma a wurin shi.
Har na fara gajiya da zaman gida ba abinda nake yi tukunna Admission in Unimaid ya fito. Kuma na samu medicine in da nake nema dake duk wani abinda ake bukata na samu. Abbah shi ya min komai na makarantan, registration da sauran su. Ya ma so ya sama min hostel Goggo ta hana. Baffah kam mutum ne sam da bai da kara ko kadan. In ba rashin kara ba, har na gama secondary ba abinda ke hada ni dashi. Ko kudin break da kudin transport Sai dai in ya ba Goggo da ya zame mishi dole tukunna ta bani. Mutum ne Wanda bayan yayan shi ba wadanda ya damu da su. Su kam duk abinda su ka bukata Sai dai in basu furta ba. Dan ma ni ba irin mai sa abu a rai bane, komai nawa simple ne hakn ya kara sa suke ganin matsayina da nasu ba daya ba. To wadanda ma muke Uba daya basu soni ba balle kuma cousins.
Da muka yi magana da Yaya Sanda ta waya, ya nuna farin cikin shi sosai tare da kara min fatan alkhairi. Sai dai bayan nan Goggo ya Kira, ashe acc no ya bukata a wurin ta ban sani ba har tasa aka tura masa. Nan wasu kudaden ne aka turo har sun fi wancan. Goggo dai ya sanar mata kyautan shine gare ni. Ta ko ta godiya har da ce mishi wai ya dawo Egypt in nan hakanan kawai ayi auren in yaso na karasa karatu na wai a dakina. Ni dai ba mu taba zancen soyayya dashi ba, Amma duk lokacin da Goggo ta mishi irin maganan nan Sai ya bata wani positive reply. Amma ni da muka yi magana dashi cemin yayi wannan da ya aiko min sakon ne ya kara turo min kudaden. Na so takura shi ya fada min waye wannan hakanan, Sai dai fir yaki zancen wannan karon ma.
Cikin ikon Allah na fara zuwa makaran ta. Sanadiyyan kara haduwa na da Faree'a kenan. Domin tun a ranar na farko na fito lectures karfe daya na nufin wurin alwala domin gabatar da sallan asuba. Na sunkuya ina cikin shafan Kai naji an riko baya na. "Suhaima" da sauri na juya muka hada ido da ita. Yanda naga ta sakan min fuska nasan ba muyi wannan sabon da ita ba. Na dai share mu ka gaisa faran faran. Daga wannan ranar kuwa har aka gama semester a masallaci muke hadu da ita. Tun muna dagawa juna hannu har muka zo muka fara hira sama sama. Har ina tmbyn ta Anty Nainah, tace min tana Abuja. Daganan dai ban bar zancen yayi nisa sosai ba.
Daga Masallaci next inda muka fara haduwa Kuma wurin cin abinci ne. Nan kam da kawaye kala kala na ke ganin ta. Da ke cafteria in hostel nake zuwa Kuma mata ne kadai a nan. Yawanci ni kadai nake zuwa saboda banyi kwashe kwashe wasu kawaye ba Sai dai course mate da muke magana daya biyu a Abuja. Watarana bayan na gama lectures naje wurin ni kadai. Sai ga ta nan ta shigo ita ma. Ban taba ganin ta ita kadai ba ma sai ranar. Tana ganina da fara'an ta ta karaso ta zauna inda nake bayan tayi ordern abincin ta.
"Ni kam wai wani course kike ne?" Nan na fada mata tace "kice manyan Unimaid ne kawai" cikin hiran take tmbyn ko a hostel nake zama. Dan wautana har address in gidan Baffah na bata, tace min zata zo ta gaida Goggo. Ai ko hakan ya faru, wani weekend kawai ina zaune Sai gata da wata kawar ta. Naji dadi har raina har waje na raka su, ban zatan a mota suka zo ba Sai da na ga motan. Hadadden mota ne sosai, ba wani abinda ya zo min rai banda na gidan su ne ko na kawar ta.
Sai da lokacin Exams ya zo, sannan na gane fa'idar zama a hostel. Domin duk yanda na so karatu a gida ba Kaman yanda nake a library ba duk Sanda na samu dama. A gari har yanzu ba lfy bare ince zan bari Sai dare ina dawowa. Yanzu haka zancen da ake ma an fara kawo hari cikin makarantar.
A wani zuwa library da nayi, wuraren karfe biyu na hadu da faree'a. Wanna karon ma ita kadai ne, tace min "Suhaima lfy kike karatu haka da tsakan rana" dariya nayi nace "kefa ba karatun kika zo ba?" Nan ta sanar min tazo amsan abu ne gun wata. Ni Kuma na shaida mata ban samun daman karatu in na koma gida ne. Kai tsaye tace min "To ki dawo hostel mana?"
"Ai banda accommodation" rike baki tayi can tace "Bani numbanki Suhaima" mu kayi exchanging contact ta wuce.
Har na manta munyi magana da ita, ta Kira ni tana shaida min in same ta cafterian da muka saba hadu in na gama lectures. Ban gane me take nufi ba, Sai da na isa na ta kara ce min inzo common room. Nan na iske su, su dayawa suna kallo. Tana ganina ta taso, can wani block mu kaje da ita. Kusa da dakin da take ta kaini, wai free space in friend inta ne Amma yanzu an samu matsala ta bar school in. Saboda haka in ba matsala in dawo in zauna man. Na mata godiya Amma na shaida ta mata dole Sai nayi magana da Goggo. Ta so ta hanani, Amma Abbah yayi kokarin fahimtar da ita dake shi ya amince. Da ke yanzu jikin ta da sauki sosai ta kyale ni. Ko da faree'a ta kirani, na sanar mata ina son yin siyayya ne. Sai tace in zo akwai nata Kuma waccan kawar ma bata kwashe komai ba, ta barshi a wurin ta. Hakanan na tafi ganin yanda ta matsa. Ko Umar Sanda da yaji komawa na hostel Sai da yace hakan na da kyau, Amma in dinga yawan addu'a saboda security reason. Dake yanzu zaman Borno ya fara gagaran mutane dayawa, shi inma kullum yana cikin kirana domin jin halin da muke ciki. Bafferh kuwa yanzu haka yaran shi gabadaya ya kwashe su daga garin ya Kai Kano. Sai matan shi kawai da Goggo, shi inma Yana nan. Abbah kuwa wannan karon aiki garin Jigawa ya Kai shi.
Haka muka fara rayuwan hostel tare da faree'a. Da ke kullum ina wurin karatu, Sai a hankali na fara fuskantan bata cika zama a hostel ba. Hatta kwana kam Amma in dai tana nan to tana wuri na har girki take yi ta kawo min. Hakan yasa na fara bata babban matsayi a wuri na. Tana so na sosai, duk wani matsala na tana kokarin share min. A lokacin ina 200 level kenan.
Ko a 3 inma ita ta neman min hostel, wannan karon ana su dakin ma na yan final year. Da ke room of 2 ne Kuma, daga ni Sai ita a daki. Lokacin Kuma na kara fuskan tan ta da kyau, domin yawancin ni kadai ke kwana a dakin. In na tmby ta ina take zuwa tace wurin friends ita. Tana dasu kala kala Kuma yawanci yan duniya. Lokacin nasan tayi canjin department yafi sau biyu Kuma har yanzu ba karatun bane a gaban ta. Sai dai Kuma akwai tsafta sosai ga sanin ya kamata sannan akwai karrama dan Adam.
Gabadaya shekarun nan Umar Sanda bai zo Nigeria ba. Sai dai Kuma yana nemana akai akai, duk ya San abinda nake ciki kuma. Kudi kuwa har bansan adadin da ya turo min ba, duk dai da sunan wani ke bashi sako. Ni kam na gama sa wa raina ba wani kawai shi inne kawai. Har Faree'a ma ta San shi sosai duk da ba su taba haduwa ba.
Sai da karatu ya fara zafi sosai sannan kwatsam Sai ciwon Goggo ya tashi gadan gadan. Wannan karon ciwon yaui zafi sosai, mun kwana a asibiti har ba adadi. Gabadaya a tsorace nake, ga wani irin banzayen mafarke mafarken da na fara. Sai ni inma na rame, na zamo sukuku karatun ma Sai Wanda naji kawai a lectures. Lectures inma ba kowanne na ke zuwa ba. Ba wanda ke tausa ta Sai Faree'a Sai Kuma Sanda idan mun yi magana. Ya kan cemin in maida lamurana wurin Allah ina addu'a ba wata mafita bayan hakan. Da tausasawan nan nake samu ina karatu, a shekaran dai da kyar na tsallake ajin lafiya kalau. Dan nikam har na cire Sai na kara maimai ta wani jarrabawan.
Daga hostel asibiti na wuce, Goggo kam jiki Sam ba dadi har dialysis ake mata na kidney. Magana ma da kyar take yi, abinci kam Sai anyi da gaske shi inma ba kowanne ba. Baccin kirki dani da mai kula da ita ba wanda yake yi. Ina kanta kawai ina kallon ta. Sai addu'a kawai da godiyan Ubangiji. Daganan Kuma ba Sai kafa daya baki daya ya daina aiki ba. Nan fa hankali likitocin baki daya ya tashi aiki ba, dole suka hada da kiran wani babban likita yazo mata surgery.
Ranar Faree'a tazo da ke ana hutu ba ta garin. Hankalina a tashe, don haka tana tare dani ta rike hannu na tana bani Baki. She was there for me in my difficult times. Ranar dai idanuwa na sun yi luhu luhu, maganan ma yaki zuwa haka kuka ba uhm ba uhmm uhmm. Barin ma tunda aka fito da ita awa daya, biyu, uku Kai baki daya wunin ranar ba ta farka ba. A ranar kam da baccin yana Dan zuwa , Amma lokacin gara rau idanuwa na na karaci daren. Sai wurin asuba ta farka, Sai dai kana ganin ta kasan bata cikin wani lafiya ko kadan. Ga oxygen amma numfashin fita kawai yake ba wani alamun shiga duk da nurses In sunyi denying hakan ni dai abinda idanuwa na suke gane min kenan. Barin ma yanzu da karatun mu ya fara nesa, nasan abubuwa dayawa daga cikin medicine in. Ko da na gaya ma Sanda, ce min yayi inyi hakuri ai sun san aikin su. Don haka na kyale zancen. Amma jiki kam baki daya ya rikice, motsin kirki ba tayi. Abinci kam ba ma ama maganan.
Wani ikon Allah, wurin magreeb abun ya dan yi sauki. Har ta sa na mata alwala na kawo mata hijab, duk ta gabatar da sallolin da ake bin ta. Tana ta min murmushi kawai abin ta, tana tasbihi har Sallan isha tayi. Tana idar kuwa bacci ya dauke ta. Ni kam har na fara murna jiki ya fara kyau, Sai dai su Abbah da Baffah duk ban ga alamun farin cikin tattare dasu ba. Anty Yana ma na nan, gaisuwa kawai ya hada ni da ita. Har yanzu dai ban gaban ta domin ko kallon inda na ke ba tai ba.
Goggo ba ta farka daga wannan baccin ba sai wurin goma da rabi. Nan ma dai murmushin kawai take, Sai dai kana ganin ta kasan tana jin jiki. Abun da na lura Kaman ciwon ya kara tasowa ne. Haka dai Kuma aka dinga fama, motsin kirki ba wanda ya ke iya. Ana zaune Sai ta juya ta kalli wannan Sai ta juya taga wancan duk tana ta murmushi kawai. Zuwa can ta yafi to ni ta ido. Ina gane hakan na kara matsowa daf da ita. Hannu na ta fara kokarin kamowa nata na karkarwa. Da sauri na hade hannayen namu, gam ta rike ni tana kallona. Naji wani irin hawaye sun fara zubo min, girgiza min Kai tayi sannan ta lumshe idanun ta ta bude. Na gane tana nufin inyi hakuri ne, saboda ta taba min haka a wancan ciwon nata. Murmushi ta kara min sosai daga nan kuma ta dade idanun ta na kaina. Abbah ne ya zo wurin ta yana kokarin mata magana, dan haka na saki hannun nata da gudu na fita daga dakin ina jin kaman wani sabon tashin hankali na shirin taso min. Ina fita saura yan dakin suka biyo ni, wai ashe jikin ne ya kara tashi gadan gadan. Daga Abbah Sai Baffah aka bari a dakin da likitan da ke kanta.
Sun kusa awa daya a ciki. Tun daga yanayin fuskan shi na riga na sadakar. Sai dai duk da hakan kafafuwa na sun gaza taka zuwa cikin dakin kaman yanda sauran suka shiga. Zama nayi dabas kawai a kasa na zabga tagumi yayin da kunnuwa na ke jiyo min sautin kuka na tashi daga cikin daki. Hakan ya kara tabbatar min da Goggo dai babu ita. Nan take na fara jin kaina na juya da sauri da sauri Kuma Sai jiki na ya dau rawa. Kaina ya min wani irin nauyi Sai Kuma na fara ganin zallan duhu nan take na kasa fahimtan dukkan wani abinda ke faruwa. Daga nan ban kara sanin ina kaina ya ke ba har na kusan awanni sannan na farfado. Drip in da na fara cin karo dashi ya tabbatar min da kilan faduwa nayi a wannan lokacin. Ashe wai har gari ya waye. Faree'a na gani a kaina sai Kuma Adda Falmata da bansan zuwan ta garin ba ma. Faree'a ce ta min sannu, da kyar na amsa. A firgice na tuno abinda ya faru, jiki na rawa nayi kokarin fisge drip in faree'an ta rike min hannu tana bani Baki. "Goggo Goggo" kawai baki na ke fadi. Yanayin fuskan su kawai yasa ni gane ba mafarki nake ba.
"Da gaske Goggo ta rasu kenan?" Ba wanda ya bani amsa Sai dai nan take na fara jin zuciya ta na bugun fat fat fat. Tabbas yau manya sun kwanta kasa, Allah ya sa karshen wahalan kenan. Addu'a na tsinci kaina dayi da sauri na Mike nace "ina son in ganta, ko an tafi da ita?"
"Bara drip in nan ya Kare mu tafi gidan" Faree'a ta amsa. Adda Falmata kam bansan makasudin zuwan ta wurin nawa ba ma. Da alamun Abbah ne ya sata. Ai kuwa Abban ne ya zo ya dauke mu, muka tafi gida. Tun daga taron nagane mai afkuwa dai ya riga da ya afku. Karfi addu'a ne ya karasar dani cikin gidan nan. Dai dai shiganmu, ana fito da ita filin gidan inda za a mata sallah. Da sauri na karasa wurin makaran, zaman dirshan nayi a gaban makaran ina Kare mata kallo. Kaman in na mata magana zata amsa haka nake ji. Tayi haske abun ta, ta kara wani kyau. Tabbas nata kam yayi kyau, Sai dai muyi fatan namu ma ya kasance hakan.
Da karfin hali baki na ya hau mata addu'a, ina kallon ta ina wani irin murmushin karfin hali komai nawa Kuma a cinkushe yake. Ina jin idanuna ya min wani nauyi Sai dai Kuma ko alamun kukan ma ban ji. Na dade ina addu'an, jiki na kam duk ya kasa dagawa. Ban San waya zo ya janye ni ba.
Mu ma a baya muka tsaya aka mata salla tare damu. Dai dai lokacin da aka daga makaran za a fita da ita. Naji wani hawaye mai zafi ya biyo kunci na. Yanzu shikenan ba zan kara ganin Goggo ba? Ban ko shakka tabbas gata na ya kare.
Ina ji ina gani aka tafi da Goggo gidan ta na gsky. Bbu abinda na iya haka Kuma ba abinda na isa in canja. Sai dai jin komai nake tamkar a mugun mafarki da nake bukatan farkawa cikin gwaggwa. Har mintsilin Kai na, na dinga yi ko zan farka amma ina abun yaci tura. Ban tunanin ina gane mutanen da ke ta Kai komo a cikin gidan nan. Ko su Adama da su kazo blurry na gansu ballantana Kuma wayata da bansan inda yake ba kar ma Kuma a zo kan batun abinci. Har mamaki nake yanda mutane su ka saki jiki suna ta faman diban abinci sai Kuma hayaniya kawai ke tashi don ba wai na wani fahimtar abinda su ke fadi bane. Bansan adadin mutanen da su ka sani a gaba inci abinci ba Sai dai hakan bai sa na cin ba. Gabadaya ma da suka gane ba wai na San inda kaina yake bane, a karshe Abbah aka kira, dole aka kara maida ni asibiti.
Kwana ukun da suka shude min a asibiti baki daya bazan iya cewa ga ta yanda nayi su ba. In za a barni cikin bacci yawuce, baccin gaske da Kuma baccin zaune, domin dai duk abinda ke faruwa kusa dani dai bawani fahimta nake sosai ba. Hana rantsuwa dai nasan Ajiddah, Adama da Faree'a suna tare dani. Sai dai bazan ce ga tsawon lokacin da su kayi a tare dani ba.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top