Arba'in da daya
Rayuwata
Babi na sha hudu
A daddafe na daure na ke rubata jarrabawan da duk rubutawa kawai nake. A ranar papern mun na karshe ne muka hadu da mai Aliyu. Don har cikin school yazo ya same ni, yan makaranta na ta gulman su mu kayi kaman bamu ji su bama muka fita abin mu. Yanda muje yi duk ranar da yazo ya same ni a makaranta, direct wucewa muke ya taka min har zuwa kofan gidan Goggo. Yau in ma hakan ne ya kasance, mostly ma labarin School insu ya ke bani dake ya kwana biyu da fara karatu a garin bauchi.
"Bai in dan amso abu a wurin abokina pls" Ban kawo komai a raina ba na ce mishi "muje mana" Haka mu ka cigaba da tfy, yana ara jana da hira ina dan amsa mishi sama sama dake matsalolin da ke gabana sun fara fin karfin kaina.
A haka har mu ka karasa kofan wani gida mai dan girma. Wayan shi ya ciro ya kira abokin nashi ni dai ina tsaye a gefe ina jiran ya amshi abinda zai amsan mu wuce dake ma duk hanya ne sai dai kuma ba hanyan da muka saba bi ba. "Suhaima mu shiga please, yana so wai ku gaisa da matan shi" bude baki nayi idanuwa na kyar akan shi. "Matar shi? Kana da abokin da yayi aure ne daman?" Dariya ya min yace "lallai ma suhaima wlh kin raina ni. Kuma ma fa mu maza ba wai irin ku bane, saboda mu muna abokantaka har da wadanda suka girme mu, ba kaman ku da kuke ganin shi a matsayin ci baya ba." Ban ce mishi komai sabida nasan gsky ya ke fada. "To Amma ya akayi ya sanni da har zai hada ni da matar shi ku gaisa" murmushi yayi yace "Suhaima kenan an gaya miki akwai wanda yake tare dani da bai san ki bane?" Ina shirin magana sai ga abokin nashi ya leko. "Mai ku shigo mana ku tsaya nan, ko madam in taka ba ta son shigowa ne?" Saurin sadda kaina kasa nayi, ina mamakin sunan daya kira ni dashi. Nasan maganar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi balle har ma a kirani da madam in shi. Fara'an abokin nashi yasa na basar kawai muka gaisa. "Please shigo ku gaisa da madam sai ku tafi mana" wani nauyin shi naji a lokacin, hakan yasa ban iya musu ba na bi bayan su muka shiga har cikin gida.
Sai bayan mun shiga naga girman gidan sosai. Ashe ta waje nema bai nuna wani girma ba.ga kuma space sosai kafin a kara sa cikin main house in. Haka dai na ta bin su har zuwa falon gidan. Iya haduwa wurin nan nayi don har na fara tunanin baban yarinyar wani attajirin mai kudi ne a cikin Damaturu, in ba haka ba irin wannan kaya kan sai dan wane da wane. Muna zaune kusan mintu uku ya shude, sai ga abokin da tray dauke da drinks da cups. "Sorry Suhaima, ta fito wanka ne tana sa kaya bara tazo" ban ce komai ba, banda murmushin da nayi. Motsin da nake ta faman ji ya sa na aminta akwai mutum a cikin. Duk yanda abokin ya matsa ku sha ruwa, kokallon teray in banyi ba. Ina dai zaune a haka dan har na far kosawa. Abokin ya kara fito, wannan karon kala bai ce min ba yayi hanyan kofan waje. "Ni kam mu tfy kawai" na cewa mai Aliyu sai dai banda murmushi ba abinda yayi min. Ina shirin kara magana naji bude kofa, ban juya ba don nasan abokin ne. Sai dai jin karan mutum a kusa dani, ya sani daga kai. Dum! Naji gaba na ya fada a sanadiyan wanda na gani tsaye gabana, Yaya Baba. Har ga Allah ba abinda ya fara zuwa min a kai sai shi inma kila gidan abokin shi ne. Nan take na murtuke fuska saboda na tsanin ganin shi. Dariya yayi ganin reaction ina "an gaya miki zaki taba guje min ne? Lallai baki sanni ba yarinya" ko kafin hankali na ya gama fahimtan abinda ya ke nufi sai jin wani irin nauyi nayi a kaina. Ban san lokacin da na saki wani irin razanannen kara ba saboda bugun wani abu ds ban iya tantance menene ba ya sauka a kaina. Idanu nane su ka fara kokarin lumshewa, yayin da nake iya jiyo sautin muryan maza dayawa a take a kaina sai babbakewa da dariya suke "Yarinya yau kin shigo hannu, irin wannan nama haka?" Ban san wa yayi maganan ba saboda yanda nayi nisa da fara fita daga cikin hayyacina. Da kyar na iya saita idanuna kan Mai Aliyu da naga wanda ya shigo damu gidan yana mika mishi wasu irin makudsn kudi. "Jeka kuma kar in sake inji wani zance kan wannan abun" da kai ya amsa ya mike, sai da yazo fita mu kayi ido huddu dashi. Wani irin kallo naga yana jifa na dashi, ba zan ce kallon menene ba amma dai nasan bana mugubta bane. He looks so helpless a haka ya fita ya barni a wannan wurin daban san me ke shirin faruwa dani ba. Ga wani irin azaban zugi da kaina har ma gabadaya jiki na ya dauka. Kwakwaran motsi na kasa, haka sautin murya na ba abinda ke iya fitowa. Ban kuma fahimtan duk wani abinda suke fada gabadayan su. Kasa fada nayi dasu lokacin da daya ke kokarin yaga kayan jikina, tun ina bige shi da kafana, yana zuba min wata azababbiyar mari na rafke a wurin gashi dama can kaina bai iya motsi. Amma haka na ciga da kokarin hana shi da hannuna, yana jan kaya ina ja. Hauri na yayi a karahe da kafa, a kuma kan cikina dole yasa na kasa komai har ya cin ma burin sa.
A cikin irin wannan halin mutanen ba tausayi ko wani digon imani su ka fara far min, bansan su nawa bane haka kuma ban san ko har da yaya baban a ciki ba. Tun na farko da ya fara shiga na, na saki wani irin ihun da nasan ba zan kara yin irin shi a rayuwa ta ba. Ba ko alaman tausayi ya cigaba da abinda yake yi, yayyin da nake jin wani irin dimauta, zafi, azaba da tashin hankali na kewaye dukkan ilahirin jiki na. Karan da nake yi yasa su ka kure sautin waka suna cigaba da kwasan dariyan su, daga baya yana sauka wani ya sake hawa kaina. A ranar na san cewa duniyata tazo karshe, amfani na ya gana karewa haka kuma banda sauran utunci a cikin ta. Na sha azaba irin azaban da nake ganin ba wanda ya san ta, a lokacin duniya ta tsaya min. Tun ina kuka da ihu har sautin murya na ya fara gushewa. Sai ya zaman to gani nan ne dai kawai a raye, ba ehmm ba ehk ehm banda hawayen bala'i da ke ta faman bambali daga cikin idanuna. Rounds suka maida abun, sai da suka gama yin yanda za suyi dani sannan su ka kyale ni a jefe a gefe kaman wata tsumma, dai dai lokacin kuma na fara jin kaman abu na shirin gushewa daga jiki na. Don wlh na dauka mutuwa ce tazo min gadan gadan. Tun ina kokarin tsaida numfashi har na gagara, nimfashin kuwa ya tsaye tak.
Ban san tsawon lokacin da na kai a hakan ba Wai dai saukan ruwan sanyin da naji a jiki na ya sani farkawa a gigice ina kallon mutumin da ya shigo da mu cikin gidan a tsaye a kaina. "Malama kina iya fita? Ina bukatan kulle gidan" sama sama ba ke jin sai dai ko yunkurin mikewa nasan bazan iya ba. Bala'i ya hau yana ta masifa har yana kokarin harbi na da kafa. Dai dai lokacin kuma naji an turo kofan falon da karfin tsiya. Ina iya jin saukan idanuwan mutum a tsaye a kaina. "Meya faru?" Shine abinda na fara jin ya fito saga bakin shi. Dai dai ban iya tantancewa dani yake yi ba koda Wanda ya iske a tsaye a falon yana kokarin harbi na. Haka kuma tsakanin mu ba Wanda ya iya amsa shi.
"Nace me ya faru" cikin tsawa yayi maganan dan ko ni da nake cikin rai ko rashin shi sai da na girgiza. "Wai ka duba mana" dayan ya amsa shi hade da Jan siririn tsaki "Mu za aka ustazancin karya? Da ba a San ungulu ba..." Bai karasa yayi tafiyan shi ya shige hanyan dakin da ya fito.
Rike kai yayi,ya cire glasses in shi ya ajiye gefe. Sai na ga ya sunkuyo ya tsugunna a gabana yana kokarin juyo da fuskana. Ido hudu mu kayi, said lokacin na gane wanene a gabana. "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Adams ya shiga uku, ya tabe kuma ba zai taba gamawa da duniya lafiya ba wlh" nan da nan naga ya rike da, yayin da idanuwan shi kuma suka sauya kala. Jijiyoyin kanshi kam duk sun taso.
Hannun shi ya dora akan goshi na yana sake min kallo, sosai na ke hango tausayi na kwance cikin idanun shi. Tabbas, ba dan waccan karon shi ya kwace ni saga sharrin Yaya baba da wannan karon ma da in amshi taimakon shi gwara in dawwama a cikin halin da nake ciki har mutuwan tazo ta riske ni a wurin. Tun da na Riga na gama Sanin rayuwata ba ta da wani amfani kuma. Bai kara cewa ya mike. Shiga daya data cikin dakunann yayi sai gashi ya fito da dogon Riga da hijabi. Daman kayan da ke jiki na Uniform ne kuma duk sun yayyage ta inda har ana iya hango wani sashi na jiki na. Ni ko duk hakan ma ban jin ya damene. Tun dai mai afkuwa ya afku ai shikenan komai ya zo karshe kuma,don nasan rayuwata ta tsaya cak. Ganin ba yanda zai yi ya sa Mon rigan ya sa ya ajiye kawai ya dauke dogon hijab in nan ya sa ka min. Kaman jaririya haka ya cincibe ni, yayi waje dani. Saukan nan da ya min ya famo min azaban da nake ji ya mamaye a gabadaya ilahirina. Tun ina sakin wahaltaciyyar kara har ban san lokacin da na kara wani suman ba.
Ban kara Sanin komai ba kuma sai tashin da nayi na tsinci kaina kwance a gadon asibiti. Ga drip nan a hannu na, haka kuma azaban da na keji har ya zu bai gama gushewa ba. Gani ma ban yi da kyau, ga dan banzan nauyin da nake ji kaina ya min. Kokarin daga shi kadan, sai inji kaman dutse aka dauko a ka dasa min a kan.
"Sannu me ke miki ciwo?" Sai lokacin na gane akwai mutum a dakin, taso yayi dagabinda yake zaune, idanuwan shi sunyi ja jawur har yanzu. "Dan Allah ka fidda ni da garin nan" shine abinda ya fara fitowa baki na.
Da tausayi fall idanun shi ya ke kallona, ban san abinda yake ji ba amma nasan abun ba karamin zafi ya ke mishi ba.
"Kiyi hakuri Dan Allah Suhaima, let me follow the appropriate way in kwata miki duk wani yancin da kike bukata. It won't go free, wannan alkawari na miki. Dukkan tsanani da rashin hankali sai na kwato miki yancin ki"
Runtse idanuna nayi yayin da hawaye yayi saurin fitowa ta cikin idon. Tabbas na Riga da nasan na shiga tashinnhankalin da nasan bai da karshe. An riga an cuceni iyakan rayuwata na duniya.
"Daga yanayin ki kadai Suhaima nasan kina jin dacin da rayuwa ta yi miki. Nasan kina jin da man baki zo duniya ba. Tabbas, abun nan da ciwo irin Wanda ba zan iya misalta shi ba saboda ban san ya hakan yake ba. Amma let us do the right thing" a hankali na bude idanuna ina kallon shi, yayin da zuciya ta ta fara kitso min shin me ye sa Umae sanda ke taimako na a halin yanzun bayan nasan yana daya daga cikin manyan makiyana a da.
"A yayin da kunci, bakin ciki da kuna suka kasance abokan zaman ka.
A lokacin da jigo majigina ya bace ma.
A sanda mahimmanci, natsuwa da annashuwa ya kau
Rayuwa ta zama tamkar guba a gare ka.
komai ya zama tamkar dafi da daci a wurin ka.
Sanadiyyar gushewar Uwa, Mahaifiya a rayuwar ka." Magana nake ina jin zafin na Dada karuwa a raina haka kuma ina kara jin a raina komai ke faruwana dani mahaifiyar tace ta na min, domin ita ta bada lasisin abinda ke faruwa. "Tun bayan gushwan ta, banda komai kuma mai ma'ana illa mini da ke ratsa rayuwata a ko wani irin hali. Ni kam na gaji, ina ma haka CeCe ni ba, ka barni da team tsan wahala na, kila da na rasa rayuwan gabadaya, ni na huta wadanda su ke burin ganin gushewa ta su huta suma"
"Subhanallah!" Saurin taron numfashi na yayi, yanzu kam ba shakka kwalla ne ke tsiyaya daga idanuwan sa. "Kar ki fadi haka Dan Allah, ki duba rahaman da Ubangiji ya miki Wanda wasu ma basu samu irin shi ba. Suhaima, nima na rasa mahaifiya ta tun ina dan kankani, na taso cikin rashin gata sai dai ba kaman irin naki ba saboda ba Wanda ya tsunguma min amma kuma bani Wanda ya damj da tawa rayuwan. Hakan ya sani kwace hanya, har na fara rashin ji kala kala duk unguwa ya dauke da irin mugun hali na. Nina fara koya ma Adams shaye shaye, wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa ni din ban iya barin shi ba bayan ya zama abinda kike gani a yanzun. Sai dai ance dalibi ya kan koya ma yafi malamin, hakan kuwa ya kasance tsakanina da Adams. I used to have a messed up life, a lokacin kowa ya guje ni hatta Anty Yana kyarata take yi sai mahaifiyar ki kawai ke kokarin kira na tana min nasiha at the same time tana kyautata min. Rashin hankali na a lokacin sai ya bani cewa dan aiken da taga tana min yasa take kira na da sunan nasiha, sai na dauke ta a matsayin wanda ya takura min shi yasa lokacin da aka ce ta tafi nake farin ciki, ko bakomai ba wanda zai dinga min fada. Recently, da na koma gun mahaifiyata da zama, da addu'a da daura ni kan hanya na gano hanya mai kyau. Hakan yasa na gane kaina sannan na kuma gane na miki babban laifi a wancan lokacin, ina fatan zaki yafe min?" Kasa amsa shi nayi, ina mamakin lbrn da ya bani wanda ba ko shakka nasan hakan ne.
"Su waye ne?" Abinda na fada kawai kenan ya gane me nake nufi. "Kungiya gare su, da nima ina ciki saboda a lokacin ma ba wanda ya kai ni kaurin suna cikin su. Duk wadanda kika gani yaran masu kudi na a garin nan sosai hakan yasa Duke da daman yin iskancin su son ransu. Sun sha kawo mata suna raping, sai dai kuwa in ba a kyallo ki ba. Ke ma ai tunda suka ga kin fara mutunci da Mai Aliyu su ka fara bibiyan shi. Iyayen shi ba wasu masu shi bane, duk kokarin shi bai da hanyan zuwa jami'a ga kuma mahaifiyar shi kwance rai hannun Allah ba kudin asibiti. Da wannan su kayi amfani da, gabadaya ma su su kayi sponsoring karatun shi haka kuma suka biyawa mahaifiyar shi kudin aiki ta warke. All because daya daga cikin su ya ganki da yake wurin Adams kuma kin biya mishi rai. Ba dan nan garin bane ma, shi ma baban shi babban kusa ne a garin kano."
Wani irin rudu na kuma shiga jin labarin da yake bani kama shirin film ko tatsuniya. "Amma me yasa shi da kanshi yayi attempting far min?"
"Its all a plan Suhaima, shi wancan in yana daki yana jiran bayan komai ya kan kama yazo. Baki ban daman da zan iya miki magana ba ni kuma ban san in ta bibiyan ki. And don't think am so innocent, kaman yanda na gaya miki dani aka fara abun nan. I was the first guy da na fara raping daya daga cikin yan matan ba a nan garin ba a kano. Suna hude kungiya ne garin gari suna rabawa matasa kudi dominsu yada manufar su. Sai dai tun abinda ya faru tsakanina da yarinyar nan, naji rayuwata ta dimauce, na natsuwa duk wani tunanin na ya kau. A kullum duniya in na kwanta sai nayi mafarkin yarinyar nan tana min ihu in kyale ta. A haka abun ya fara yawo har ya dawo banda wani tunanin kirki kuma. Dole naje na nemo ta bayan dimbin wahalan da na sha da kyar na same ta. Sam taki ta yafe min duk yanda na nuna mata Dana Sanin sai dai ta sanar min yanzu haka an FASA auren ta saboda abinda na mata. Ta hadani da yan unguwan su, su ka min wani irin duka da zai da na kwana asibiti. Bayan nan aka wuce dani cell, ba karamin wuya na sha duk da haka ji make nayi deserving komai. Ban san ya akayi ba, daga baya yarinyar tazo tace ta yafe min. Ko da na nuna zan aure ta, sai ta sanar min an sa mata rana da cousin inta. It a life changing experience tunda daga lokacin na dawo turban gsky. Sai suka watsar dani duk da haka ban damu ba, haka kuma yanzun ma sun kira ni ne saboda in ga sun ci manufar dana hana su da farko. " wani irin zufa naji yana keto min a lokacin, da kyar na iya tashi daga kan gadon ko kafin ya ankara ma fisge drip in dake hannu na. "Dan Allah ka fidda ni garin nan. Wlh na tsani in bude ido in mini ina shakan numfashi a cikin ta. Duk da gari nane kuwa"
"Ina zamu je Suhaima? Dole mu tsaya ma a nemo miki yancin ki" girgiza kai nayi na dan cike baki "Baban ka na wani bane a garin nan haka kuma kaima nasan haka da abinda za ka iya jayayya da yayan attajirai irin su. Allah ya isa, Allah ya isa, Allah ya isa." Ina gama fadin hakan nace "Kai ni Maiduguri, Goggo na can ba lafiya" bai kara cewa komai ba sai wani irin sanyi da jikin shi yayi.
SLM, am sorry ban samu daman update ba kwana biyu. Ban dan jin dadi ne shiyasa.
Nagode.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top