Arba'in da biyu
Rayuwata
Babi na sha biyar
A motan shi mu ka tafi har garin Maiduguri. Ya kaini har cikin gidan Baffah. Hatta kafa na ma da kyar na ke taka ta, ga magunguna kala kala daya hada ni dasu. "Ki kulla da kanki Dam Allah Suhaima, da kuma dukkan abinda nurse in nan tace miki. Bakomai, Allah na nan sannan ina so ki cire damun da nake ganin kin sa kanki a ciki"
"Damuwa dole ne? Duka duka shekaru na nawa ne a duniya? Amma kasan abubuwan da na fuskanta wani tsohin ma har ya gama rayuwan shi ba zai taba ganin irin su ba" Hawaye shara shara ke zuba a idanuna yayin da na ke magana "Ballantana kuma yanzu da gabadaya rayuwan tawa ma bata da amfani?" Da rudu sosai a fuskan shi ya ke kallona "Ba zan ce kiyi hakuri ba suhaima saboda ina jin baki cancanci wannan kalma ba. Ba a wurina kadai ba, har a wurin kowa ma. Abinda zan ce miki kawai kuma shine, Allah na nan kuma ya san dake" yana fadin haka ya shiga mota yana kokarin tayarwa. Da kyar na iya tsaida shi "Ka gaida Goggo Dan Allah" Hakanan ya bini a baya har zuwa dakin da take zaune. Ina ganin ta na ruga da guda na duk da ciwon da kafafu na keyi, na shige jikin ta. Sai da kuma na shige jikin nata na ji alamun ba karamin ramewa tayi ba. Rudewa nayi in tmbyn ta ba'asi, ba ta amsa ni ba sai datijjuwan matan da ke dakin wacce na gane an kawo tane saboda ta kula da Goggon. "Au Goggona zo da bako bara ya shigo ya gaishe ki"
"Siriki kika kawo min?" Abinda ya fara fitowa bakin ta kenan. Sai da na danyi dariya sannan nace "Aa dan layin mu ne a sabon fegi" ba dai tace komai ba, har Ummar sanda ya shigo su ka gaisa. Har kyautan kudi kuwa ya mata sannan ya fita. Goggo ko taji dadi, dan ita ba dai son mutum mai kyuta ba saboda ita ma gwanace wurin kyautan. Tayi ta sa mishi albarka, sai ce min tayi "Ba zaki je ki raka shi ba?" Ban ce komai ba, haka kuma ban fitan ba har naji tashin motan shi ya wuce. Daganan kullum Goggo sai ta tmbyni gane dashi, ni kam share ta nake yi na kauda zancen. Dan nasan ba wani abinda zai iya taba shiga tsakaninmu dashi a wannan lokacin.
Ba laifi duk da ana yawan zuwa asibiti amma jikin nata yana dan sauki, Alhmdlh. nima naji sauki, saboda duk maganin da aka bani sai da na shanye haka na dinga gasa kaina ina kuka ina zuba Allah ya isa, don har duniya ta kare ban jin zan taba iya yafe ma wadanda suka min wannan abun. Musamman Yaya Baba dashi ne silan komai. In sha Allahu nasan sai sin ga karahen su tun a duniya ma.
Sanda aka koma makaranta ba karmin Dramamu kayi da Abbah ba. Duk dagewan shi, na nuna mishi da in koma Nana Aisha na gwammace in mutu banyi makaranta ba. Goggo ne ta tilasta shi, dole aka siyan min foam in El-kanemi Maiduguri. Haka kuma na fara rayuwa ta a garin Maiduguri, Borno wato birnin Yarwa. Ba laifi rayuwa gidan ya fi na gidan mn sau dubu duk da ko na san saboda Goggo ne abubuwan suka zo min da sauki, to gashi itama fama take. Rayuwa dai gatanan kawai ne, yau dadi gobe akasin ta. Ban wani samun matsala a makaranta saboda ina jin cewa banda matsalan ind dai ta fannin karatu ne. Ga kuwa dalibai masu kwazo ne sosai aka tattara a makarantan. Haka kuwa muke fafatawa son duk da abinda Mai Aliyu yayi sanadi na katse min dukkan wani mahimmancin rayuwa. Ban jin zan iya hakura da karatun likitanci, ko dan ceton mutane dayawa daga cututuka da kuma taimakon Al'umma musulmi.
Wataranar Asabar aka wayi gari da bakin ciki hade da jimamin babban rashin da aka yi na Inna, abokiyar zamn Goggo kuma mahaifiyar mijin Aunty Amarya. To lamarin Ubangiji kenan, duk da tana fama ita ma dajiki wanda tsufa ne ya jawao amma ko kusa ba za a hada ta da abinda Goggo ke ji. Amma da ke lokaci yayi, ko ba ciwon tafoya za ayi. Goggon kuwa ta ji mutuwan sosai. Musamman su mutanen da, duk da ba za ace ba a taba samun sabani ba, amma kuma anyi zaman mutunci. Duk da ciwon kafan ta hakanan ta sa su Abba da Baffah a gaba sai da suka hakura suka kaita Damaturun. Har aka yi zaman gaisuwan kwana uku, sai daida ka ganta kasn abun yana damun ta sosai, karshe dai ciwo ya tashi gadan gadan kuma shi yayi sanadiyyan komawan mu Borno ba shiri. Abinda ake gudu kam hakanan sai da ya faru. Wannan lokacin ma ba karamin jinya tayi a asibiti ba, da ka ganta kasan tan jin jiki. Ni kam duk lokacin da tayi irin wannan ciwonba karamin damuwa nake ba, kai hatta yanayi na bai boye hakan har wani irin rama na daban nake. Na riga na san ita ce gata na a duniyan nan, kuma raahin ta ba karamin girgiza ni zai yi ba. Sai dai alamu na yawan nuna ban da wani zabi a rayuwa kuwa.
Tun bayan tafiya Umar Sanda bai kara waiwayo ni ba sai bayan shekara daya. Lokacin already na riga na shiga SS3. Kawai sai dawowa makaranta nayi na iske shi suna ta hira da Goggo. Da ke jikin kwana biyu ya mata sauki. Ni da farko ma ban gane shi ba sai da na matso kusa sosai. Ya kara fari sosai sai kace wani balarabe ga kuma wani irin kasumba da duk ya cika mishi fuska.
"Baki gane shi ba halan?" Goggo ta fada. Murmushi kawai na mata, daga yanayun muryan shi ne ma ya sa na gane shi da kuma kamannin shi da bai gama bacewa ba. Gaishe shi nayi, ya amsa cikin fara'a. Daga nan na basu wuri da Goggo su ka cigaba da hiran. Sai da yazo tafiya ta sani raka shi. "Ko ki zauna muyi hira" ya fada bayan na taka mishi wurin motan shi. "Ai naga kuna yi da Goggo." Dariya ya dan yi sannan yace min "Da fatan kina lfy dai ko? Kwana dayawa"
"Alhamdulillah" kawai nace mishi, a raina kuwa ban daina mamakin har irin kiban da ya kara ba. Ni dai ganin nan a yar figigiya ta har yanzu.
"Sorry tun da muka rabu dake ban kasan ne shiyasa ban zo na duba ki ba" ya fada yana kokarin bude motan.
"Lah bakomai, karatu kaje hala" bai amsa ba sai ma ce min yayi "Ya makaranta Suhaima, hope dai komai yana tafiya lafiya ko? Baki da wata matsala?" Da kai na amsa mishi, a raina kuwa ina mamakin mai yasa ya damu da rayuwata. In fact ni tun bayan wancan abun ma ban taba tunanin wai zai kara dawowa wuri na ba. Kallo na ya juyo yana yi sosai kaman mai son fahimtan wani abu a fuskana. Ban san me ya gano ba naji dai yace "Dan Allah ki dinga fawwala wa Ubangiji dukkan lamarin ki Suhaima, Allah ya shige mana gaba. Bara naje kinsan garin naku is not zafe, mutum yayi dare sai kiga yaran can su tare hanyan azo a samu matsala" Yana nufi Boko haram, saboda zuwa lokacin ta'addancin da suka yi a garin Maiduguri har ya baci. Infact har ya ma shiga garin Yobe. Sai dai dake Unguwan su Baffah unguwa manya manya wadanda su ke ji dasu ne. A ta nan wurin gidan yake hakan yasa tarzoman bai ciki ketarowa ta wurin ba. Sai dai kuma zaman kullum ciki fargaba ake, ba daman fita ko makaranta a rufe a bude haka ake yi.
Shi ga motan yayi, Babban leda ya ciro ya miko min "Ga tsaraban Cairo, zan kira ki na wuce" amsa kawai nayi ina kallon ledan ina kallon shi. Sai dai tun kan na samu daman mishi godiya. Yayi saurin jan motan shi ya bar wurin, Allah kenan, abun godiya.
Ko da na shiga gida kuwa banyi wata wata ba na bude ledan. Kayan da na gani a ciki ya sani daukowa da mamaki ina dubawa. Abaya na har guda biyu da veils insu peach da black. Nayi mintuna ina mamakin wannan irin kaya haka, tunda dai ba wannan sabin a tsakaninmu da zai kawo min irin wannan abu. Bayan kayan kuwa, sai wani perfume na larabawa mai dan banzan kamshi sai kuwa yar karaman waya. Na dade a raina ina tunanin dalilin da zai sa ya kawo min irin wannan kyautan. Rudewa nayi, dile na dauke su naje na nuna ma Goggo.
Dariya ma tayi ita kam. Tace "wannan ba dan gidan Umaru Machina bane?" Da kai na amsa ta, tace "to ina ce makocin ku ne daman, dan ya miki kyauta kuma sai ki dinga wani mamaki?" Shiru nayi, dan dai a raina ban yadda da wannan dalilin zai sa ya kawo min kayan nan ba. Musamman da nasan ba wani jituwa mu keyi dashi ba, duk da yanzu ya min abinda bazan taba iya mantawa a rayuwa ta ba. Hakika shi din ya kasance mai tausayi, ban shakkan wannan.
Bayan kusan sati biyu, Hakanan na hada wayan daya kawo min duk da dai nasan ba wanda zan kira ko kuma wani ya kira ni. Banda yan danne danne da rage ma kai kewa ba abinda nake yi a wayan sai ko game amma ko app daya na social media ban sauke ba. Ranar da naji wayan yana ringing, banbarakwai naji abun don ni ko ringing tune in wayan ban san shi ba. Kallon wayan kawai nake ina mamakin numban da ya fito baro baro. "Ki dauki waya mana ana kiran ki" Tsohuwar da ke zama da goggo ta fada. Hakanan dai na daure na dau wayan ganin tana kallo na. Hae na amsa sallaman da akayi ban gane waye bane. Sai da naji yace "Sai yau aka kunna wayan kenan?" A daburce na gaishe shi sannan nace "Ban zauna bane saboda school, kuma ma ni banda wanda zan kira ko a kira ni."
"Baki da kawaye ne?" Girgiza kai nayi kaman yana kallo na "Ina dasu kawai dai bama magana a waya ne"
"Yakamata ko a dinga gaisawa, Kinga yanzu sai ki amshi numban su. amma dai kar ki kashe wayan, ko su basu kira ki ba ni zan kira ki mu gaisa ai ko?" Shiru nayi, ina neman inda zan ajiye maganar shi.
"Ko baki son in dinga kiran ki?" Ya sake tambaya.
Da sauri nace mishi "Aa"
"To ya jikin Goggo" Brief gaisawa mu kayi kafin ya ajiye wayan. Tun daga nan ya kan kira ni amma dai ba kullum, wani lokaci har wurin bayan kwana uku ma. Sai dai yana yawan tmbyna ko akwai wani abu da nake bukata. Akwai ranar da yayi min irin wannan tmbyn sai kawai nace mishi "Ina son Dan Allah a samo min numban Adama kawata ta layin mu"
"Amma gsky baki da kirki Suhaima, ashe ba kwa ko waya?" Kokarin fara kare kaina nayi yace "Aa fa baki da gsky, ko ince dukkan mu baku kyauta ba. Amma shikenan tunda yanzu kin nema, In Sha Allahu za a samo miki"
Ranar da dare kuwa sai ga text in numban ta ya shigo. Da azama na, na dana mata kira. Aikuwa sai ta dauka.
"Suhaiiima" abinda ta fara fada kenan da dan ihun ta.
"Ya akayi kika san nine?" Tsaki taja tace "Dazu Fa Ya Sanda yazo da kanshi wai yana nema na. Ni abun mamaki ya bani sosai wlh, kin fa san shi ba cika shiga harkan mutane yayi ba tunda ya bar zama a garin nan sosai. Gaizuwan mutanema ba lallai ya ke amsawa ba. Sai da na fita yake ce min, wai ke kike son numbana. Ke Allah baki na kasa rufuwa yayi Suhaima, me ke tsakanin ku wai?"
Dariya nayi jin yanda ra dage tana ta min bayani "Kawai dai mutunci mu ke, kinsan kwanaki shi ya kaini Maid shknn tun daga nan mu ke dan mutunci dashi amma fa ba ma wani sosai bane." Siririn dariya tayi, tace min "Dadi na dake rainin wayau, dan mutunci ne har zai zo ya amsan miki numbana. Shikenan kar ki fada, in yayi tsami maji ai" Kyale ta nayi, dan nasan halin ta sarai komai na fada mata ba yarda za tayi ba daman.
"Ya labarin Saurayin mu? Ko ansa ranar ne?"
"Ke shirya dai kizo, ana gama makaranta da wata daya aka sa." Tab, wayaga Adama da miji. Lallai zai sha zuciya.
"Zan zo mana ai dole na ma, Kince mun kusa shiga daga ciki muma" dariya tayi sosai tace "ke dai kika sani Allah. Kuma ranar da aka yi graduation inku, washegari ki tabbatar kin kamo hanyan Damaturu daman" Da eh kawai na amsa mata, dan nasan in naki yarda ma yanzu sai muyi fada. Mun dade muna hira da ita, wanda duka duk maganan aurwn nata ne.
To bayan ta kuna sai Ajiddah da ita kam daman tun a wayan Goggo tana kira na, amma da yake tana makarantan kwana sai ta samo waya sannan take iya kira na. Akwai dai amana sosai, saboda har yanzu muna nan da ita yanda mu ka saba.
Rayuwa ta cigaba da tagoya ba tare da wani canji sosai ba. Kullum dai da irin yanda za tq zo ma dan adam. Umar Sanda ya dade da komawa Egypt, tun da ya tafi ko ya kan dade bai kira ni ba. Amma ranar da na fara ganin international number nasan shi ke kira. Har yanzu dai gaisawa kawai muke yi, sai labarai da ya kan kawo min daya biyu.
"Ya Cairo?" Dan jim yayi kafin yace "Gamu nan dai a cikin ta, Ya kamata watarana kizo ki dana kema ai"
"Ni kuma me zai kawo ni Cairo? Ya Sanda" zaro idanu nayi alamun ba zai yiwu ba, duk da ko ba gajina yake yi ba.
"Kika san ikon Allah? Ai ba yanda Allah bai lamarin shi. Ni ba gani nazo ba yanzun. Sannan kuma ki daina kira na da Sanda, shebi na sha gaya miki ban so"
Kiris ya rage ince mishi, ai kai dan gata ne. Duk da baban shi ba wani mugun attajiri bane amma akwai rufin asiri sosai gsky. Amma maman shi na sha jin labarin wanda ta aura a kanon bayan ta fita daga gidan baban shi, ba karamin mai kudi bane domin a garin kano ma duk girman shi sai da aka san dashi. Daman gata shuwa, kyakyawa don har tafi su Ajiddah kyau, sosai. Da yawan mutane sun ce ya dauko tane musamman a fata da kuma yanayin su baki daya.
"In sha Allah ba zan kara ba, kayi hakuri" na fada cikin saukakan murya, ba tun yau ba ya sha sanar min bai son sunan. Daman baban shi ke kiran shi saboda sunan asalin mai sunan shi kenan. Umaru Sanda, kawai sai kowa ya dauka amma tun da can bai cika yarda ya masa ba, musamman ma abokanan shi bai bari su kira shi da hakan. Sai dai kaji ana Umar Faroukh, ko kuma ma UF, using the initials kawai. Da ke baban nashi ma Umar in sunan shi.
"Ai ke ba kya laifi a guri na, you don't have to apologise ma, kawai ban sin sunan ne" Ba abinda ya fadan bane yayi saurin daure min kai sai irin tune in da yayi amfani dashi wurin fadin. Ba wai yau ya fara ba, amma duk randa yayin sai abun ya zo min wani banbarakwai. Ni fa, ko wayan da muke yi da kyar na saba na dan saki jiki don har yanzu ban gama zama comfortable ba ma.
A haka mu kayi Sallama, sai dai abinda na fara lura dashi kwanan nan hiran namu ya fara yawa. Don wataran hakanan zai kirani ya fara ban labarin abinda ya faru dashi a ranar. Ni dai mamaki na nan dan kare a raina.
Ko da muka gama jarrabawan mu na SS3 baki daya, ban yi wani farin ciki ba kaman sauran yan ajin mu. Savodani kam banga miye na murnar ba, ni dai har yanzun rayuwata jiya i zuwa yau ne, ba wani dadin ta na ke ji. Kai rabo na da dandana wani dadi ma, ina ga tun ranar da Ummi na ta tsallake jiki ta barni cikin kangin Wahala. Duk da na rabu dasu amma ban taba iya manta azaban da na sha hanun bayin Allahn nan. Yaya baba kam, har abada ban jin zan iya yafe mai. Ya riga da ya cuce ni, cuta irin wanda zai bini har karahen rayuwata. Sai dai kuma ina tunanin tun yanzu a duniya ya fara ganin sakayyan Ubangiji. Domin dai karatyn da yake yi ma, tuntuni yaki gamu wa. Ya bar Buk tuntuni yayi Bauchi amma duk bai dade ba ya kara dawo wa gida anyi withdrawing in shi. Sai Yayi Yobe state uni shi inma dai hakan ce ta sake faruwa. Yanzu dai yana poly, amma batun natsuwa babu shi. Yana nan yana ta watingiri, sai arziki shaye shaye fa bin gindin yaran masu kudi yana musu fadanci. Sakayyan duniya dai, ita kan ta Anty Yana ta na gurban shukan ta yanzu. Adda Falmata kuwa, Nursing ta jona bayan secondary. Sai da tazo jarabawan karahe sannan aka zubar harda su a ciki. Taga takaici kam, yanzu dole ta koma State University nan cikin Damaturu ta fara daga farko. Batun aure kam shiru kawai kake ji, ban san jo ta na da samarin a yanzu ba hsky. Amma tub da nake gidan kam nasan suna nan buhu buhu, ina mamakin dalilin rashin auren nata kuwa. Al-lawan ne dai yake Karatu lafiya kalau a Gombe, state university. Ya kan dan kira Goggo shi kam, kuma muna gaisawa dashi ba laifi, lafiya kalau zamu yi ta hira in dai ya kira tan kenan.
Ba a dade da gama jarrabawan ba Adama ta fara min maganar zuwa Damaturu bayan bikin sauran kusan wata da kwanaki. Fir naki zancen, duk da fushin da tayi tayi. Daga karahe dai, sai gata a maidugurin ita da Goggon ta. Na ko ji dadin ganin su, ballantana goggo da na dade ban gani ba. Ganin su yasa Goggo cewa ai ko dole na in tafi, sai dai Adama tayi hakuri sai ana sauran two weeks bikin tukunna.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top