Arba'in da biyar
Rayuwata
Babi na Sha takwas.
Dole Sai a kwana na ukun ne na iya Kai wani abu baki na, shi inma ruwan shayi ne. A bakin Adama nake jin irin raman da nayi, fada take yi wai ban yarda da kaddara bane da bazan fawwala wa Allah lamari na ba. Sai dai banga laifin ta ba a wannan lokacin saboda Adama bata taba fuskantan daya daga cikin matsalolin da na gani ba. Na dade da sanin rayuwa ta bata da wani mahimmanci, tunda na taso ma fuskanci mahaifiyar da ta haife ni ma ta tafi ta barni cikin gararin rayuwa hannun wadanda basu damu dani ba.
Bansan Ya akayi Umar Sanda yazo ba, Amma dai naga shigowar shi tare da maigidan Adama. Ban yi wani mamakin zuwan nashi ba, saboda a halin da nake ciki ba wani abun girgizan da zai shudar da mutuwar Goggo a raina ba. Gaisuwa suka min suka tmbyn ya jiki, duk dai a takaice na amsa musu.
Ina ga alluran cin abinci likita yasa aka min saboda shi kadai ne dalilin da zai sa naji ina jin mahaukacin yunwa. Duk da haka ban wani kula yunwan ba, banda uban fruit da abun ruwa dana dinga durawa ciki na. Shi inma a sanadiyyan nasihan da Umar Sanda ya zauna yayi min, Wanda ba shakka ba karamin ratsa ni yayi ba.
Ranar throughout yana asibitin, motsi kadan zaka ganshi ya shigo. Ina jin Adda Falmata na bala'in wai wani munafunci ne ya kawo shi wurina, daman an bata lbr. Kala ban ce mata ba, don na rasa dalilin zuwa wurina asibiti da take yi. Yaya Baba dai banda shi a maidugurin ma, naji dadin hakan saboda ba wanda naki jini a rayuwa irin shi, tabbas shi in wani irin dafi ne da ganin shi kadai zai ma mutum illa.
A daren ranar Umar Sanda yazo min Sallama, akan wani batu ya taso mishi a Abuja, dole gobe ya ke kafin ya koma Egypt. Nasihan dai ya kara min sannan ya wuce tare da sanar min zai turo min sako ta waya.
Hakanan aka sallame ni a asibiti, na koma gidan Baffah cikin da tunanin wani irin rayuwa zan afka a wannan karon. Ganin ni kadai ne a gidan yasa baffan yace in koma side in Uwargidan shi na zauna. Haka ko aka yi, ba wani abinda ke hada ni da ita banda gaisuwa. Daganan ba ta damu da mai naci ba ko ina na kwana. Ko bata ganni ba, ba abinda ya shafe ta. Har ma gwara dayar matan in bata ganni ba zaka ji tana wai Suhaima kwana biyu kaman bata gidan nan. To tun farko basu dauke ni wata tsiya ba balle in wani girmama su sosai. Duk da haka dai nayi Amanna zaman gidan yafi zama gidanmu dadi ta kowani sashe. Tunda su ba aiki suke sani ba ko aika ko wani wahalan ba. Kawai dai kowa na rayuwan shine.
Da aka koma makaranta Abbah ya turo min kudi na biya registration and all. Accommodation Kuma kudin hostel ya bani, Sai dai faree'a ta nemi da mu Kama wuri nan cikin makarantar kawai mu zauna. Tunda wajen ba security, saboda haka nan staff quarters muka samu wuri muna zaman tare. Zuwa yanzu halin ta ya lalace, ban mata wani wa'azi saboda ba dauka take ba. Takan ce kowa rayuwan da ya zaba ma kanshi zai yi, don haka ita nan ta fuskanta. Na dade da sanin tana bin maza, bi ma'ana runs take yi. Takan ce min ni naga ina da hanyan samun kudi ne Amma ita ba ta da wani da ya wuce wannan in. A lokacin kam Sam bata wasa da Sallah, abinda na jinjina mata kawai kenan. Akan ce ka guji aboki batacce, Sai dai ni a wannan lokacin ina ganin soyayyan da take min ya take komai sannan Kuma ban ganin za ta iya canja min ra'ayi. Babban kuskuren da nayi kenan.
Domin dai a hankali a hankali rashin gata na ke kara bayyana yayin da rayuwa take cigaba min. Abbah ba irin mutum bane wanda ya damu da yaran shi sosai, zai dai sauke muku hakkin makaran ta daganan Kuma sauran Sai anyi da kyar. Duk bayan kwanaki dai zai turo min kudi Sai Kuma in ni na Kira in gaishe shi.
Da farko mafitan da na fara gani shine yakama ta in bi aure ne. Sai dai duk yanda mutane ke fada min Umar Sanda na so na, har yau bai taba furta hakan ba. Ban da maganan karatu Sai Kuma makudan kudin da ya kam turo min da sunan wani ke sa shi. A hankali na fara jan hiran mu a waya kaman yanda ya kanyi ko zan samo mafitan a nan Sai dai bai wani nuna komai ba. Zai dai bani lbrn abinda yayi ranar da Kuma irin rayuwan da yake fatan gina wa kanshi a gaba. Kullum dai kara daure min Kai yake. Ban fadawa Faree'ah ba saboda bata nan, Adama Kuma she is not an option to me don haka direct na Kira Ajiddah.
"Suhaima share shi kinji, maza yan iska ne wlh kema yanda kike da kyan nan ki saki jiki nasan maza dayawa na son ki, ki saurare su kila akwai Wanda za a dace" In har an bi lbr na da kyau tun farko, za ku gane cewa ni mutum ce mai saurin daukan shawara ba tare da yin wani dogon tunani ba don haka a yanzun ma hakan ya faru. Lokacin mun riga mun fara zuwa practical asibiti. Saboda haka duk wani Wanda da yake nuna min ra'ayi ina share shi Sai na fara sakan mai fuska. Kaman ko mazan jira su ke, nan da nan na fara tara samari kala kala. Yau wannan ya zo wuri gobe to wancan zai zo. Ban gane ina da kyaun da takama da zan ita jan ra'ayin da namiji ba Sai da na afka wannan rayuwan. Duk da haka ban wasa da karatuna saboda nasan shine zai zame min gata a rayuwa, Kaman dai yanda Ajiddah ke fada min mazan ma yan iska ne.
Lokacin da faree'a ta fuskanci ba Suhaiman da ta sani da bane Sai ta fara hada ni da wasu daga cikin mutanen ta. Tunda bazan ce ina da matsalan kudi ba Sai dai ba ko shakka akwai matsalan yanda zan sarrafa su. Da nakan rasa me zanyi da kudi Amma yanzu har kadan suke min. Rayuwa dai ta fara gargada Sai dai Kuma ba wanda zai daura ni a hanya in dawo hanyar dai dai.
Tuni na dawo bana ko dar dar dan in shiga motan namiji ya Kama min hannu yana wasa dashi da sunan yazo hira wuri na. Kai har da masu sa hannu a wuya na ma yana matso dani kusa dashi ko kugu. Nan da nan na fara fice, suna na ya fara yawo cikin Unimaid. Har yazo da an Kira sunana kowa ya sanni. Duk wani gasan kyau nice a gaba, dake na fahimci ina da kyan duk dani ba fara bace kuwa. Awards kala kala duk na amsa.
Umar Sanda kuwa wayan mu yaja baya sosai dashi tun da ya fahimci interest ina ya fara raguwa. Sai ya koma wani lokacin kawai Sai dai ya turo min text yana tmbyn lfyna da karatu. Text inma ba ko yaushe nake amsa mishi ba dake duniyan ga min dadi. Na dada gogewa, duk nayi realizing dayawa daga cikin mazan ba da aure suke so na ba. Sai dai ba wanda na sakan ma jiki na. Barni dai ta harkan romance ya Kare a nan, don duk duniyancin namiji dai dai na dawo dashi. Kusan daman ance Wanda bai iya abu ba in ya koya, yafi kowa gogewa. Gidan baffa kuwa Sai na shafe watanni banje ba, ba Kuma Wanda ya damu.
A hankali faree'a ta fara gane a yanzu na fita wayewa da sanin duniya abu daya ta fini zuwa lokacin, shine Kuma wayau. Duk saurayin da ke zuwa wurin ta, guna suke dawowa. Lokacin ta gane lamarin ta ya fara ja baya, barin ma da ta gama Unimaid da result da ba wani Wanda zai kalle ta. Ai Sai ta cilla Lagos, daman tun tuni ashe tana da daki a can gidan yancin, don haka taga gwara kawai ta tsunduma karuwancin gadan gadan, don zata fi kasuwa yanzu a nan. Barin ma a garin Lagos.
Mun dade bama tare, har ta na kusa gama karatuna. Kwatsam Sai ga Faree'a tazo nemana. Nayi mamakin ganin ta domin ma dauka Wanda yayi gaba ai bai waiwaye. Ce min tayi wai ta dawo maiduguri, ban wani tsaya dogon magana ba nace mata "sannun ki to Sai ki dawo mu cigaba da zaman mu" Hakan ko akayi. Duk da kullum tana cikin attending to customers, har nemo min take yi, nace mata ni ban kwana da maza Amma ba ta yarda, Sai dai yardan ta bai dame ni ba. Kuma lokacin na maida hankalina kan karatuna, na fara rage samarin duk da ba kowa ya yarda ya tafi ba. Ni inma ma bazan so duk su tafi ba, domin yanda nasan kudi nasan amfani su to dole Sai da mazan a harkan. Lokacin ne Kuma gadan gadan boko haram suka girgiza borno, kuna lectures Sai a ce muku bom ya tashi daga wani bari a cikin makarantar. Kowa dai a tsorace yake, daga karshe tilas aka rufe makaranta. Gamu muna gab da karasawa Amma ba daman hakan. Maiduguri ya fara gagaran zama kowa ta kanshi yake, ba nan inba ba damturun ba, hankalin jama'a kowa ka gani a tashe.
A wannan lokacin Faree'a ta hadu da Umaymah. Ban san taya suka hadu ba Sai dai kawai naji tana yawan maganan ta. Hutun makarantar da aka yi yasa ni zuwa gidan baffa saboda nasan inda nake is not safe Amma can in da guarantee. Sai dai me? Tun daga kofan gidan naci karo da gundumemen kwado ko alamun mai gadi bbu. Da na tmby wasu makota dasu ke Shirin barin garin suma, ce min su kayi ai sun kusa wata uku da barin garin. Ina suka je, ba wani labari. Tilas na Kira Abbah, ya ce min suma ba kowa a Damaturu Amma na hau mota na same su a Jigawa. In akwai abinda na tsana a duniya shine zama tare da yan gidanmu, Adda Falmata ma na nan har yanzu ba tayi aure ba duk da nasan a yanzu ba uban da ta isa ta min Sai dai banji zan iya hada inuwa da ita. Ban tsaya neman su Adama ba saboda nasan suma basa garin don haka nayi dialling Ajiddah, duka duka ba ta dade da aure ba Kuma nan maidugurin aka kawo ta. Wani attajirin mai kudi ta aura bayan ta gama ruwan idon ta, Sai dai babban mutum ne Kuma ana hudu ta shiga. Saboda yaran duk guduwa su kayi ta nemi na aure ta rasa. Sai da na Kira numbanta bai shiga ba ma sannan na tuna tace min zasu honeymoon Dubai yanzu haka nasan suna can.
To duniya fa tayi zafi ga ba wurin nufa. Duk inda na bari sai inji ance bomb ya tashi a wurin ko Kuma an tare mutane an musu yankan rago. Lokacin Umar Sanda ya fado min, Sai dai na dade da wullar da sim in da ya sanni dashi. Tun Yana nemo inda nake kyautata zaton wurin mijin Adama ya ke samu. Don haka last sim ina Adaman ma ba ta sani ba, ina jin fushi tayi ta share ni tunda ni numban ta na kaina. Shi ko har ga Allah ba wai na haddace numban nashi bane Sai dai in na gani zan gane. Duk yanda na so hada numban in same shi bai yiwu ba Kuma.
Daga karshe Jigawan na yanke shawaran zuwa, don har na gama hada kayana faree'a ke tmbyna inda na nufa. Bayan na fada mata ne tace min "yanzu gidan su Falmatan Zaki?" Faree ma taki jinin Adda Falmata, kullum Sai ta zage ta in dai aka yi maganan ta. "To ai banda wani mafita"
"Ni ina dashi" yanda ta fadi zancen ta karfi Sai da naji saukan shi cikin kwanyar kaina. Kalman da ya canja duk wani sauran farin cikin rayuwata.
"Shirya muje " kawai tace. Na ko shiryan na bita muka tafi Sai hausari, gidan Umaymah. Tana ganina ta saki murmushi tana fadin "Faree wannan ce ko? What a perfect lady, gsky kin kyauta min" Anty Umaymah kaman yanda naji suna fada mata nima na dauka. A ranar mu biyar ta siyan mana ticket muka sauka garin Kano a unguwan sharada. Lokacin ba a wani tare sosai a unguwan ba. Wani narkeken gida muka je Wanda bai rasa komai a cikin shi ba. Mun dade ana nan muna zaune lfy kalau, sim ina kam Kai banma da waya a lokacin bare Abbah ya same ni. Karen mu kawai muke ci ba babbaka, ga Anty Umaymah akwai kashe kudi. Mutunci da take min na daban ne, ban gane manufar hakan ba Sai da nasan mata take nema. Yanda take taba ni, tana wasa da gashin kaina sai dai ko kadan ban hana taba duk da ban sakar mata jiki baki daya. Saukin abun ma tana zama a Abuja ne sosai yawanci. Akwai lokuttan da ni kadai take sa wa inzo muje Abujan. A haka muka saba da ita, nan ma Faree kishi take. Saboda haka nema ta hada kayan ta tayi Lagos duk da ba wanda ta fada ma dalilin yin hakan.
Ba zanyi karyan cewa ban taba ba ma Anty Umaymah jiki na ba, duk da ban taba ra'ayin hakan ba. Ta dai karaci kidan ta da rawan ta ita kadai ta kyale ni. Muna Abuja tare da ita aka koma School. Da na fada mata, da kanta muka dauki jiki muka je maiduguri muka binciki komai na karatun. Ba karamin kudi ta kashe min cikin kankanin lokaci ta samar min inda zan zauna in gama makaranta gidan wata friend ita. Wanda kudi yaji kudi, Kai girman gidan ma har ya baci. Akwai securities sosai ta yanda boko haram ba zasu tunkari wurin ba Sai da babban shiri. In kun ga da securities in da ake kaini makaranta, Sai kun dauka yar wani shegen ne. A haka dai da darr darr in har na samu na kammala da kyar da niyyan zan zo Kano inyi housemanship ina.
Bayan na dawo, nayi mamakin ganin Faree a Kano tare da Anty Umaymah. Har yau ina iya tuna yanda suka zauna suna min bayanin abinda ya ke faruwa da abinda su ke son in aikata musu. Naji labarin Anty Umaymah, Kuma ya ratsa ni. Naji ba wanda na tsana kaman zayd domin gani nake tafiyan su day ta Yaya Baba duk daya ne. Nan take na dau alwashin komai zai faru Sai na cika mata burin ta, ko ta halin kaka kuwa. Saboda ta min alkhairin da ba batun mantawa. Ta so in cigaba da housemanship ina nace mata na gaji Sai na gama aikin ta. Abinda yasa nayi saurin amincewa Kuma shine in duba irin hadarin da ke tattare da karasa makaranta na, burina tun ban gama sanin kaina ba. Amma kuma sai gashi tabi hanyoyin ta, ta cika min shi. Don haka komai zan mata ban jin zan fadi.
Da da farko zayd muka yi niyan targeting direct Sai dai sanin Amal budurwar shi na Lagos sannan Kuma Yana yawan zuwa can Sai muka samu perfect opportunity kawai muka hau aiki. Lokacin na bi Faree zuwa gidan yanci, Sai dai ba wai da niyyan zama ba. Aa kawai saboda in samu daman observing komai da kyau. Don har taso ta Kama min apartment naki.
Zuwa na gidan ma wasu irin mahaukatan samari nayi, Sai ya zamto duk Wanda yazo in dai ya hadu, maganar aljihu kenan to dani magajiya le hadawa. Daganan na samo yar baiwa, dayawa suka fara jin haushi na duk ba shiga harkan su nake yi ba.
A club muka fara haduwa da Amal, duk da komai is delibrate. Na ganta a ranar ba inda kanta yake, ta Sha har ta bugu ba ta gane komai tana gab da zubewa kasa na taro ta. Wayan ta ya fado hannuna. Dai dai lokacin Kiran zayd ya shigo na dauka, nan na sanar mishi yanda na same ta. Sai gashi kuwa cikin yan mintuna ya iso. Shi ya tafi da ita gida, ashe ya bata labarina. Ta dinga nemana a club in nan kusan two weeks basu same ni ba. Sai ranar a wani club in daban, Yana gani na ya nuna mata ni Sai kawai naji an zo an rungume ni. So friendly, a ranar ta amshi numbana. Sai yazo tana Kira na in tasan club in da zani ranar Sai mu hadu a can. A haka har muka saba, har gidan ta mun Sha tafoya da ita in Zayd baya nan.
Nan take tmbyn inda nake zaune, na sanar mata wani single room apartment ne. Na bata lbrn na karya akan zancen boko haram sun kona gidanmu and am stranded a garin. Saboda haka taji tausayi na sosai ta tsaya convincing ina in dawo gidan ta da zama. Sanadiyyan fara zaman mu tare kenan, har kowa ya sanni har cikin gidan su."
Barr mustapha na Kai nan ya San ya gama kaiwa wurin inda yake bukatan jin komai da yake bukata, don haka ya rufe manuscript in yana runtse idanun shi da ya tabbatar su gama gajiya. Kan shi ne ke wani irin sarawa daya San duk na gajiya ne
Amma duk da haka ji yake lokacin hutu bai riga da ya zo mai ba har Sai ya ga karshen wannan shari'a tasu. Duk da dai yasan zuwa lokacin tunanin shi ya riga ya a gama cire mishi Suhaima a rai Sai dai Kuma yana jin zuciyan shi na mishi kwadayin kasancewa da ita.
Matsalolin ne kala kala kawai da suka dinga zuwa mata daya bayan daya Wanda in ana shi hukunci ne yana ganin yanda hanya da tabi wurin magance matsalolin nata ne ke da gargada mai dimbin yawa a tattare dashi.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top