Arba'in da bakwai
A hanyar fita daga kotun, Suhaima suka hadu da Nainarh. Kallon kallo su ka tsaya yi ma juna kowa ya rasa abun fadi.
"Suhaima" Nainan ta fada cike da abubuwa dayawa daga sautin muryan ta.
Kafin ta hado abinda za tace mata back, taji Dr Fahad yana fadin tazo su wuce. Gabadaya su Engr murna suka dinga taya su. Abun mamakin kuwa wai harda Faroukh. Ikon rabbi kenan, ita dai Suhaima ba ta da wani bakin magana.
A hanya take fadawa Dr Fahad Anty Nainah ce ya gansu a tare. Shi kanshi Sai da ya jinjina abun.
Ranar wani irin kwanan farin ciki tayi duk da in ta tuna ita tayi sanadiyyan Amal Sai taji wani iri a ranta. Za taso taga zayd, tana bukatan ya mata bayani dayawa game da ciwon Amal in. Duk da dai ta riga ta tafi, yanzu Addu'a ne kawai mafita. Kuma tana yawan mata sosai, ta kanyi mafarki da ita tana mata murmushi. Duniya kenan, Allah ya sa mu dace.
Washegari Barr ce ma Suhaima yayi kawai tayi zaman ta a gida ba Sai taje ba Amma fir taki zancen. Da ita aka fara Kuma da ita za a gama shi a cewar ta. Hakanan dai suka isa kotun da ta cika makil, cikan ta har ya fi na jiya sosai. Kowa zuwa yayi ya gane ma idanun shi labarin da ya watsu ko ta ina cikin gari.
Kai tsaye Patricia aka nemi ta bada nata bayanin. Da farko fir taki bada hadin Kai, Sai da Alkali ya nemi da a mai da ta cell Sai ranar da ta shirya fadin dalilin da tasa Zayd Shan wannan abun bayan har ya manta ya tafi.
Da dai attack in yayi yawa dole ta bude Baki "Hafeez ya dade yana ce min yana so na, ban San ko wasa yake min ba Amma ni kam yayi min ba kadan ba. Don haka mun kasance yana yawan sani wasu aiki da bai kamata ba a cikin company in Kuma ina yi mishi. Ya kan ce zai min duk abinda nake so in nayi mishi, barin ma da ya gane zan iya yin komai saboda shi. Yace zai iya min komai in dai ya samu abinda ya ke so, I can even be his wife. Wannan dalilin yasa nayi tunanin sa ma shi Oga Zayd poison saboda ina ganin if he is no more, Hafeez zai iya samun duk wani abinda yake so tunda na San burin shi kenan. Am the one behind it but is not my fault. Even the fire, Nina kunna gas in Yana fita da kadan kadan sannan na sa igiyan yin leaking so that I will get what I want" nan take wurin ya dau hayaniya Sai da Alkali yayi magana tukun.
"Are you sure you are the only one behind it?" Nan take ta kara tabbatar. Shi kan shi Hafeez never expects this. Turn out Faree is even using Hafeez to gather Information akan Al-mansur. Abun dai duk kwamacala, Sai dai Alhmdlh da komai ya bayyana.
Nan fa Alkali ya fara yan rubuce rubucen shi bayan wani lokaci ya dago ya fara bada verdict in shi kaman haka "Kotu ta yanke hukuncin danka Hafeez a hannun jami'an binciken tsaro na kasa domin su cigaba da gudanar da binciken su. Kafin nan Kotun na Umartar Kulle Company da ake zaton anyi ta'asan a ciki har zuwa lokacin da za a kammala binciken. Bayan haka kuma, za a kiyasta duk wani al-mundahana da Hafeez in yayi ya biya company kudin shi tare da tara da zama kurkuku na wata biyar da Kuma dama da kotun ta bawa Umaymah tana iya shigar da nata karar akan abinda Hafeez in ya mata. Sai Faree'a da aka ci tara dubu dari uku na mutanen da tayi amfani dasu domin cimma wani manufan ta. Batun Rasuwan Amal da lauyan gwamnati yaso ya daga Kuma, dukkan bincike ya tabbatar da ba hannun Suhaima a ciki don haka Kotu ya wanke ta daga dukkan wani zargi da ake mata. Bayan haka dai akwai taran da suma aka cisu ita da Umaymah na kudirin da su kayi akan Zayd Al-mansur. Shi Kuma Zayd in kotu ya bukaci da ya nemi gafarar duk wata yarinya da ya san ya cutar wa rayuwa, Sai duk Wanda bata hakura ba to tana da daman shigar da karar ta." Bayan ya gama fadin wannan ne ya dago ya kalli jama'an kotun da kyau kafin ya kara maida hankalin shi kan abinda ke gagan shi. "Kaman yanda dokar kasa ta tanada, kotu ta yanke ma Patricia zaman kurkuku na ... A sanadiyyan..." Da karfi ya buga guduman da ke kan table in "This is my verdict, kotuuu"
Ko ta ina Yan jarida kawai kake gani suna kokarin ta yanda za ayi su tattauna da wadanda aka yanke ma hukunci a wannan lokacin. Cike hadda Patricia da ke ta faman zabga kuka tana fadin ita fa taimako taso. Umaymah Kuma Sai faman tmby take ta amsa akan za ta shigar da Hafeez kara ko zata kyale? Murmushi kawai tayi ta shiga motan ta. Rayuwa ta riga da ta nuna mai darasi so ba ta ganin sai ta wani wahalar da kanta da dukiyan da take Shan fama kullum wurin tara su. Bayan haka, she have her own issues to face yanzu haka musamman a yanzu da duniya ta San me take ciki, ta Kuma San asalin ta. Sai dai kowa da irin nashi matsalan don haka bata ganin saboda wannan za ta iya durkushewa.
Faree'a dai Sai zaro idanu take yi, musamman inta tuna cewa ba ta da takamaiman inda zata je. Ko giyan wake ta Sha ta San gidan karuwai ba nata bane a yanzu. Daman Hafeez ne take gani a matsayin mafakan ta to shi Kuma ga yanda ya kasance dashi nan. Shawara daya ne, ta hada kayan ta tayi garin potiskum wurin yan uwan mahaifin ta da a da ta nuna musu su bakomai bane. To tasan duk abinda zasu mata in taje, hannun ka bai rubewa ka cire ka yar don haka tuni ta gama yanke shawaran mafitan ta. Duk bata da wani abun arziki a yanzu, Amma tasan akwai kudin da zai ishe ta biyan taran da ake bin ta sannan sauran taje ta Kama sana'a dashi, tun da shi kadai ne tasan zai zame mata rufin asiri a yanzu.
Hafeez kuwa tuni a ka wuce dashi. Umar ke gaba har Sai da ya tabbatar da an wuce dashi sannan yayi saurin karasawa wurin Barr da ke tsaye. Hannu ya bashi su ka gaisa ya mikawa Dr Fahad dake gefe. "Am Umar Faroukh Machina" kafin yayi wani magana Sai ga Faroukh ya bayyana a gare su. Wani sarawa yayi wa UF Machina sannan ya juya gun Uncle Musty da Dr da suka saki baki suna mishi kallon mamaki.
"Weldone Faroukh" Uf ya fada yana fadada murmushin shi. "Your nephew is my agent, ni ya ma aiki all these while na San you have been suspecting. Ni nasa shi aikin har akan Suhaiman ma" bashi uncle Musty ya kalla ba sai Faroukh da ke ta murmushi. Hararan Barr yayi "Amma Faroukh baka da hankali, you should have told me everything"
"Ai ya sabawa aikin mu In yayi hakan" in an understanding ya amsa Sai dai har lokacin yana mamaki. "Let me get your no, ina so mu hadu dole zamu yi magana" Suhaima da Zeenah ta riga taja ta sun wuce gida bata ma San me ke faruwa. Sai dai daga Barr har Dr sun riga sun gama gane waye UF Machina. Bayan haka suka rabu da zummar zasu yi waya kafin su tafi Kaduna.
Su uku suka tafi Apartment in da Suhaima take. Da taji labarin Faroukh aiki yake ma CID sai da ta girgiza. "El-yas fa?" Tayi saurin tmby saboda ya ma fi mata Kama da jami'in bincike akan Faroukh. "Tare dashi mu ka samu aiki. Secret Investigator ne shi inma. Ta kasa muke aikin mu, har mu ci nasara Kuma ba a gano mu. Sai dai mutum yaga an Kama shi. But aikin ki is personal, shiyasa har kika San ina bibiyan ki." Rasa abun cewa dai tayi kawai, sai dole shirun ne ta dauka.
Abun da yafi damun ta bai wuce tasan cewa a yanzu zaman Abuja ba zai mata ba, kaman yanda zama gidan wasu ma ba nata bane a yanzu. Don haka take ganin duk yanda ba taso dole ta nemi mahaifanta, da kuma mahaifinta don a yanzu shi kadai ya rage mata. Rokon ta daya Allah yasa wani Abu bai same shi, tana bukatan neman gafaran shi ko ta samu albarka a rayuwan ta.
Washegari, Zeenah ta dau akwatin ta it's ma ta nufi hanyan nasu garin. Komai dai ji suke ya kare musu, yazo karshe Sai dai duk da haka suna mai gode ma Allah da irin kyautan daman da ya musu. Da sun mutu cikin wannan hali basu San mai zasu sanar ba. Godiya mai yawa Suhaima ta mata tare da dimbin kyauta daga kudin mutum da ya dinga bata kudi a zaman ta gidan yanci a Lagos. Wanda har yau bata sake gani ba, ba Kuma tasan dalilin shi ba. Sauran kudin ko daga wurin Zayd da Amal suka fito. Ko bakomai they owe her, dole ta nemi gafarar su su inma.
Ko da kudin Faree'a ya iso ta. Kiran Faree'an tayi ta maida mata daga ita har Umaymah. A gidan Umayman suka hadu. Suhaima dai daman bata rike ta da komai ba, domin har yanzu tana ganin Umayman kaman wata babban jigo a rayuwan ta. All thanks to her yanzu za ta iya cigaba da karatun ta a inda ta tsaya. Farko dai license Exams za tayi Sai Kuma housemanship Sai tayi service shikenan Kuma Sai abinda Allah yayi. Duk da haka dai Umayman ta nemi gafaran ta. Faree kuwa Sai da ta basu tausayi. A nan take gaya musu gsky ta San Zayd mijin Naina ne tun asali. Sai a lokacin Suhaiman ta tuna ta hanyan ta zata iya ganin Zayd. Don haka ta nemi address inta. Haka suka rabuwa kowa zuciya ba dadi, wannan kadai ya ishe su hukunci saboda duk cikin su ba wanda zai ce Yana jin dadin rayuwan da yake Shirin fuskan ta a yanzu. Karshe dai, duk an hadu an gane duniyan ba komai bane. Allah kenan, mai yanda ya so.
UF Machina, musamman ya nemi su Mustapha da Fahad suka hadu over Dinner. Sun tattauna abubuwa dayawa daga cikin har da yanda ya nuna musu Yana son tafiya da Suhaiman kasar Egypt. Duba da hujjoji da dalilan shi, nan take su ka amince. Amma fa sun shaida mishi Sai taje Kaduna, yazo ya tafi da ita a can. Passport inta ya nema domin yasa a fara mata processing VISA, da duk wani abinda ya dace kafin zuwan lokacin.
Ana gobe zasu tafi Kadunan ta ziyarci Nainah. Duk mamakin ganin ta da Nainah tayi, sosai taji dadin zuwan ta. "Suhaima" kawai take Kira tana rike Baki Amma a hakan Sai da kwalla ya fito mata fuska. Bayan sun dan natsa ne, take ce mata "Kema ashe yanda rayuwa tayi dake kenan? Faree'a ba ta kyauta ba domin nasan da Baki hadu da ita ba da komai bai Kai da hakan ba. Nayi Dana sanin harka da Faree da har hakan ya zama sanadiyyan sanin ki da tayi" tana fadan hakan ne cikin matukar jin zafi. Hakika Suhaima har gobe ba karamin matsayi take dashi a wurin ta ba.
"Bakomai Anty Nainah. Kaddara tace kawai, Kuma ko bata sanadiyyan Faree ba it will happen ba wanda ya Kuma isa ya canja hakan." Shiru Nainah tayi, kalaman Suhaima na shigan ta. "Hakane Kuma, Allah ya shirye mu baki daya" daganan shiru su kayi. Zuwa can hiran ya karkata kan rayuwan da har tana tmbyn ta Halima. Abun mamaki a wurin Nainahn ta ke jin kawar ta Ajiddah dai zama bai yi dadi a gidan Alhajin da ta aura ba, don haka dole ta fito daga karshe. Yanzu kam wani take aure mai dan rufin asirin shi kawai, matar shi daya da yara biyu. "Rayuwa kenan, in kinga Ajiddah kaman ba ita ba Suhaima. Ba wannan gayun da kwalisa. Baki daya duniya ta gama nuna mata hankali. To gwara ita ma. Ni nawa mijin dani da bbu ai duk daya. Nayi aure ne Amma kaman ban ma taba yi ba" ta fadi hakan tana jin wani kuna na fita daga ranta.
Suhaiman ce ta dan tausar da ita. Ta nuna mata kasa sittin laifin tane ko a baya. Amma yanzu ta zake damtse ta Kama mijin ta hannu bi biyu. Ba ta kara tabbatar wa da gaske laifin nata bane Sai da taji yanda Suhaima ke faman fada mata abinda Zayd ke so, yanda yake so ayi shi da Kuma abinda ya ki jini. Dayawa daga ciki duk zaman ta dashi na shekaru bata sani ba.
"Amma Sai ina gani kaman ko mai zan mishi a yanzu bashi da wani amfani" sanar mata da dukkan abinda ya faru game da marar ta da gaban ta tayi. Nan dai Suhaima ta lallashe ta sannan ta cigaba da nuna mata duk wannan ba zai hana ta kula da shi ba. Amma farko ta fara sanin waye shi tukunna da duk wani takun sa. Tasan tana lacking abubuwa dayawa daga ciki kuwa har da karatun addini. Sai dai ita ma Suhaiman ba ta jin tana da isashen da zata iya ba wani. Ko akwai ma yanzu ba ta da wannan lokacin. Recommending mata inda zata samu Islamic book tayi sannan tasa ta shiga wani group na addini da Dr Fahad yasa aka sata ciki. "Ubangiji ya miki gatan samun miji, gatan aure" tana fadin haka ne tana jin wani zafi a nata ran. Sai lokacin ta gane aure Rahma ne. Gashi dai duk sun gama tsiyan su basu da mafaka. Amma ita Nainah a ba dadi, gata gida auren ta cikin rufin asiri. "Kar kiyi wasa da auren ki yar uwa. Domin baiwa na irin naki. Kar ki damu da duk wani hali na mijin ki. Kiyi ta mishi addu'a kina bin dabarun da Zaki koya. In Sha Komai mai karewa ne da izinin Ubangiji. Sannan Kuma ki rike kaddarar ki hannu biyu, ki yarda dashi sannan ibada Kar ki sake ki taba wasa dashi" Ranar dai Nainah Sai da taji dadin zuwan Suhaima sosai. Sai dai itama Suhaiman tana jin cewa ba ko shakka, Nainah ta mata abubuwa da dama a rayuwa Wanda ba ta iya mantawa. Ta so ta a lokacin da ba Wanda ya maida abun arziki. Allah sarki, Allah ya ji kan Goggon ta. Ita ce ta tsaya mata. Nainah ma Kuma ta bada nata gudunmu wan babba.
Sai can tukunna Suhaima ta bukaci ganin Zayd. "Ba ya kasar, ban Kuma San ranar dawowan shi. Domin Sai muyi wata ba muyi magana ba. Abinda nake fatan canjawa saboda nasihan ki gare ni. Amman in ya dawo zan neme ki. Sai dai zan neme ki wani alfarma"
"Fada inji, I can do a lot for you Anty na" murmushi tayi sannan tace "Why not ki auri Zayd, tunda ya na son ki kuma kema kin fahimce shi fiye dani da nake matan sa ma." Dariya Suhaima ta dan yi.
"Kiyi Hakuri Anty na, banda wannan. Bazan iya auran zayd ba"
"Why not? Kinga ni ba haihu zan yi ba. Kuma nasan a kwana a tashi dole Zayd zai bukaci yaran shi na kanshi" wani tausayin ta taji ya ratsa ta, kaman ta gaya mata yanzu hakan ma Zayd na bukatan yara. Shi in mai boye wasu abubuwan da yake so ne, in dai ba mace bane. Shiyasa ba ta San da hakan duk da matsayin ta na matan shi.
"Kar ki damu Allah zai kawo muku mafita" Suhaima ta fadi haka, har ranta dai tana tausaya ma ta. Domin da ko yar Zayd sai dai tsarin Ubangiji. Ya riga ya fadi cewa, duk Wanda yayi da matan wani za ayi da nashi haka duk wand aya lalata yar mutane to ya jira yi ganin hakan akan nashi. To Zayd hakin mata nawa ya dauka? Sai dai neman rufin asiri kawai.
Cike da jimami da kewan juna suka rabu. Sai dare Suhaiman ta bar gidan. Tana komawa Kuma ta hau Shirin saboda Barr ya riga ya sanar da ita tafiyan su Kaduna a washegarin ranar.
Washegari tun da safe Dr Fahad ya zo ya dauke ta domin tafiya Kaduna. Kafin su wuce ne ya bukaci tazo su je ta gaida mahaifiyar shi. She wasn't totally in for the idea Amma Kuma ba ta so ta nuna mishi ba ta son ko dan irin muruncin sa ke tsakanin su. Hakanan dai suka nufi gidan, a ranta tana tunanin wani irin tarba za ayi mata, duba da irin halin Ummin nashi da ya bata labari. Har suka isa ba ta wani tanka shi kan magana da ya ke ta faman mata ba. Already a ranta tana ta fama hada yanda za ta tafi Damaturu, irin tarban da za a mata. Ko Kuma za suki zama da ita ta kara shigowa duniya ne. Musamman jiya bayan ta dawo daga gida Nainarh, Umaymah ta Kira ta wai in ba damuwa tazo su zauna tare mana kawai. She can help in Vows. Ba tayi declining offer in ba, saboda tasan she may need it. Sai dai Kuma ba ta bata amsan ba. Alaman hesitation in da Umayman tayi recognizing in her silence ne yasa tace mata, she should go and think about it.
Har Sai da yayi parking da kyau cikin gidan sannan ta fahimci sun iso. "Bismillah" yace mata. Nan da nan ta fito, tana faman fargaba. Duk da ba wani abu ke tsakanin su da Dr ba a yanzu. Da suka shiga cikin gidan, Yan matan su ka fara iske wa a falon suna hidimomin su. Suna ganin shi, da fara'an ko waccen su suka taso suna gaishe shi. Sannan suka gaida Suhaima.
"Ummi fa?"
Wacce taji an Kira da Laila ne tace "Tana study" hanyan cikin gidan ya kutsa bayan yasa Suhaiman ta zauna. Lailan ce ta kawo mata refreshment. Tana niyyan tmbyn ta Zahra Sai ga ta nan ta shigo. Tana ganin ta, ta fadada fara'an ta. Zahran ma kuwa fara'an take. A mutunce suka gaisa, har suna dan labari kadan kadan.
"Ya Faroukh in ya fasa zuwa ne?" Girgiza Kai tayi tana blushing.
"To shine kika zauna a nan? Aje a shirya tarban shi ko" Suhaima ta fada, cike da kunya zahran ta sadda kan ta a kasa. Sai can Kuma ta tashi da saurin ta, ta koma inda da alamun can ta sauke shi.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top