Arba'in

Rayuwata

Babi na sha uku

Ina wurin har aka idar da sallah, na fara jiyo hayaniya an fito kenan. "Keh lafiya me kike yi a nan wurin a jike?" Rufe idon da nayi ya sa banga mai maganan ba, a hankali na bude su na sauke jajayen idanun nawa a kanshi. Nan take rai na ya baci na ji zuciya na suyi. Duk da na dade ban ganshi ba zan taba iya manta shi ba. Haka kuma ba zan iya taba cin fuskan da ya min ina karamar yarinya. A yanda na ke a lokacin duk mai imani in ya ganni ba zai zageni ba, inma bai ji tausayi na ba baya ci min fuska ba. Duk da halin da nake ciki bai hana na galla mishi harara ba, ina jin tsanan shi na ratsa ni har cikin gangar jiki na. "Me kika zo siyo?" Banza nayi dashi, ko bai ga kallon da na ke aika mishi bane? Ni kam har zuciya wlh na tsani ganin muguwar fuskan shi. saleh mai shago ne ya karaso wurin mu "Wai Suhaima ce a nan cikin ruwan nan kika fito? Me kike so?" Da sauri na fada mishi, kasancewar yawan zuwa shagon shi da nake yasa munyi mugun sabo dashi. In har zanzo shagon shi ko ya rufe sai ya bude ya bani abinda aka aiko ni. Bude shagon yayi ya dauko min abinda na zo siyo, shiko Umar Sanda ganin naki tanka shi yasa ya kama gaban shi ya shiga shagon domin ya siyo abinda ya kawo shi shima. Sai da Saleh ya kulle shagon shi sannan ya kawo min abinda na siyan, nan ya ke fada min shima kulle shagon zai yi saboda wani Sabon hadarin ne ke faman haduwa. Amsa nayi na mai godiya na kama hanya cikin sauri. Hadarin sosai ne, ina shiga layin gidan mu ruwa ya fara saukowa. Layukan garinmu manya layuka ne sosai, gidan farko layin da karshe ba karamin nisa ke tsakanin su, mu kuma tsakiya don haka akwai tafiya sosai. Garin akwai wadatattun filin da layuka su ke da matukar girma ga fadi sosai. Akwai land kam har ba a magana gashi kuma ba mutane dayawa a garin sosai. Ganin ruwan zai fara karfi ya sa na fara gudu in samu in isa, sai dai ina tuni ruwan ya sauko da karfin shi. Ina neman mafaka naga wani mota a gabana na faman min horn. Bazan nayi da motan saboda ban taba ganin ta balle in San mai ita. "Suhaima! Suhaima! Kizo in sauke ki gida" naji ana fada bayan an sauke glass in motan, sai a lokacin nagane Umar Sanda ne a ciki. Ban sa lokacin da na ja tsaki ba, ganin hakan ma na fasa fakewan na sa gudu sosai, har faduwa nayi tayi a hanya ina tashi, da kyar na samu na karasa gida. Ina ganin yazo ya wuce ni na kara yin tsakin. Ina Sallama zan shiga gidan Adda falmata ta zo fita barander mu ka ci karo. Harara ta bini dashi tana tunkude ni "kefa baki da hankali Allah, a haka za ki shiga gidan ki bata mana ko, duk kina diga" tsabagen takaici ban san Sanda na ce mata "to ai ni ke gyarawa ko na bata" kallo na tayi da mamaki kwance a fuskan ta. Ina ga ba ta taba kawo zan iya maids mata magana ba, amma daman ance yau da gobe sai Allah. Hakanan naji har raina banyi na daman abinda na fada ba. "Ke don uwarki ni kike maidawa magana? To ki shiga in gani, shegiya mai bakin hali irin ta uwar ta. Ki shiga mana Wlh sai dai Uwarki ta haifi wata" ban kula ta ba na nemi wuri na zauna abu na, ina ajiyan zuciya don ba karamin wahala na sha ba. Zagin da ta min bai isa ba sai shiga gidan da tayi tana mitan na maida mata magana. Anty Yana ne ta fito tana cewa "ke dallah ni bani aikin da na miki in kingama dama ki kwana a nan. Kuma wlh in battery in nan ya jike sai kin nemo wani wato ke wuyan ki ya isa yanka ko? Kin fara maida wa yayar ki magana ina ga watarana kaina zaki dawo" mika mata nayi ta tafi tana banbami. Ba ta sake dawo ba sai sadiya da ta zo ta kulle kofan da karfi a gabana tayi shigewar ta ciki. Na kai mintu talatin a wurin zaune har na fara gyangyadi sai ga Al-lawan da hijab da zani. Bai ce min komai ba yayi saurin mika min ya wuce side in Ummiy a da Wanda ya zamo nasu a yanzu kaman yanda Umar Sanda ya taba kawo shawara. Daurawa nayi na shanya kayan jiki na sannan na shiga gidan. Adda falmata na waya hakan ya sa ko kallo ban samu ba, da sauri na shiga wanka. Na samu nayi salloli na sannan na bi lafiyan gado. Na san dole zazzabi sai ya kama ni.

Washegari Sai wurin la'asar na samu aka bar ni tafiya ajeyari dubo su Anty Amarya da kuma Inna, itan ma dai gsky ba yanda take. Zazzabi na nan amma da ke nayi kazar kazar sai bai kwantar dani ba. Ina isa na gaida Inna,  gidan duk sai ya min wani iri dake Govgo bata nan. Dan ma Ajiida na na sai na shiga gidan su muka zanta,  a nan Mai Aliyu yazo ya same ni.

Sai bayan magriba na tafi wurin Anty Amarya, ita ta bani maganin zazzabin da nake jin yana damuna,  ban boye mata komai hakan yasa na fada mata duk abinda ya faru. Fada ta min sosai na shiga ruwan da nayi "ai da fakewa za kiyi har sai an gama ruwan, yanzu da kika kwanta ciwon asaran su ne?"

"Bakomai Anty in ban shigan ba ma wani matsalan ne za ace na Dade, watarana ai sai labari, zai wuce." Dole ta hakura ta bani magunguna har da na ido, da ke ma nursing school ta ke ta san abubuwa da dama. Sai da nayi bacci sannan na dan warware.

Da ke jarrabawa muke, dole na koma gida a ranar ko dan in wanke uniform ina ma. Washegari kuwa bayan na dawo exams da yamma na samu daman gama aiki da wuri, don haka na shiga na fadawa Anty Yana ina so in je gidan su Adama. Banza tayi dani sai zuwa can na kara mata magana "na hana kine?" Ta fada da dan tsawa, girgiza mata kai nayi nai saurin fita na wuce gidan nasu. Daman tsifa mu kayi da Adama za ta min, muna hira tana min tsifan tana bani lbrn samarin ta. "Ban fada miki yi nayi sabon kamu ba ko? Ke ince sai a dade ba a ganki, kullum ni kenan jelen zuwa gidan Ku"

"Adama kenan yanzu dai  ba nazo yau ba? Ni dai fada min sabon kamun"

"Kan layin nan mu ka hadu dashi naje shago, babba ne fa. Kuma ma har yazo ya gaida Goggo" zaro idanu nayi ina binta da kallo "Adama yanzu aure zakiyi?" Dariya ta kwashe dashi sannan ta girgiza kai "nace mishi sai na gama makaranta ai kuma yace ya amince domin shi ma karatun yake, ke zama fa ki san shi dan abokin su Ya baba ne kuma unguwan nan su ke"

"Ke ko Adama me za kiyi da abokin su Ya baba?"

"To ke ance duka aka taru aka zama daya ne? Mustapha ne fa, massan gidan Bukar mala" ban san lokacin da na mike tsaye ba nace "Massah dai? Ke ko da Adama ya aka yi kika lallashi Goggo ta yarda ki auri kanuri" tabe baki tayi tace "ai har yanzu case in muke, kinsan halin Goggo da yazo gaishe ta faran faran su ka gaisa amma yana tfy ta fara min fadan na kawo mata kanuri, ni kuma ganina nayi ai Yana so na nima kuma ya kwanta min kuma ma maman shi shuwa ce ai. Anty Fanne ai kin san ta"

  Ba ta fuska nayi "Ke ko waye bai san yan gidan bukar mala ba a unguwan nan? Kuma kar ki manta Anty Yana ma shuwa ne su ai duk da cikin kanurai ta taso amma Allah ya gani ban kaunar yarukannan"

"Ehm ehm Suhaima" tayi saurin katse ne "ba fa duka aka taru aka zama daya ba, ita ma Anty Yana saboda wani dalilin ta ne kawai da kuma matsalan da su ke dashi da Ummi amma Allah ya ganar da su gabadaya" bance komai ba sai sallaman sadiya da naji. Kallon sama da kasa ta mun sannan tace "Ya baba na kira" tana fada ta kwasa waje da gudu ba ta kara cewa komai ba.

Tare da Adama mu ka je gidan, Yana falo ran nan a hade kaman na mishi wani mummunan laifi. "Uban waya ce kiyi miyan kubewa bayan kin san banci"

"Yi yi hakuri ban san za ka ka dawo bane" na fada cikin inda inda. Tsaki ya ja sannan yace "na baki 20 minutes ki dafa min wani abu in ya wuce haka zaki Sani" jiki na rawa na nufi kitchen in Adama ta biyo ni tana jan tsaki "Allah Suhaima it high time ki fara karban wa kanki yanci, matsala na da ke tsoro wlh da naci da anga abu. Ke ni fa yanzu ban son ace ina zuba ki ne?" Murmushi nayi mai ciwo "bakomai Adama komai ma mai wucewa ne, ni kuma wani irin wahala, zagi da cin mutunci ne ban gani ba a gidan nan? Duniya ne fa Wanda bai zo ba ma tana jiran shi balle Wanda ke cikin ta" tabe baki tayi tana fadin "kullum zancen ki kenan" haka ta taya ni mu ka dafa jollof in taliya da dankalin turawa. Ba mu gama ba sai da aka kira Magreeb, don haka muna gamawa ta wuce gida. Daman duk nayi abinci dole sai na kai mishi har dakin, yau in ma direct can ta na nufa. Ni a tunani na ma ya tafi sallah ganin an kira magreeba. Amma ina sallama naji yace min shigo. Zaune ya ke abinda shi hankali kwance a falo yana kallon TV. Ban cika son zuwa side in ba saboda yanda ya ke tuna min memories in Ummiy na. Daurewa nayi na karasa na ajiye mai abincin a gaban shi. Wani kallo na ga yana bina dashi, gabadaya kwakwalwa ta taka sa tantance wani irin kallo ne wannan? Koma dai na menene ni kam ya firgita ni. "Iskanci me yasa zaki dafa min taliya?" Wannan karon kam idanunwan shi dukkan jiki na ya ke bi da kallo ko kunya. ajiyewa nayi da sauri na nufi bakin kofa zan fita, naji ya buga min tsawa "Uban wa yace ki tafi?" Jiki na rawa na dawo, a tsaye na tsaya jikina na faman rawa. "Kizo nan" hade rai yayi ganin hakan ya sa na kara matsawa inda ya ke. Ban ankara ba naji ya jawo hijabin da ke jiki na. Abin ya zo min bazata, gabadaya kwakwalwa ta ta cinku she na kasa fahimtar me hakan ke nufi. Ganin ya kusan nasaran raba ni da hijabi na yasa na fara kokarin hana hakan faruwa. Kokawa mu ka fara yi dashi, ban ankara ba naji lafiyayyun mari ta ko ina a fuska na, da karfi ya yaga hijabin ya wulla gefe, gabadaya ya rikide min kaman ba Yaya na dana sani ba? Kai ba ma shi ba kwakwalwa ta ma ta rikide, ta kasa fahimtar menene hakan. Da sauri nayi bakin kofa zan fita ya jawo ni da dukkan karfin sa ya buga kaina a jikin bango. Kara na sa na razana da kuma na ceto naji ya shake wuyana kaman mai neman ciren numfashi. Wasu abubuwan da bakina ba zai iya furta wa ba ya fara kokarin yi min ina fus fusgewa, gashi ya shake min wuya ba daman anji ihun da na ke ta faman afkawa. Idanuna duk sun firfito waje tsabagen tsafin shakan da ya min. Gashi na ya jawo da dukkan kokarin shi ya wulla ni kasa baya na ya bugu da kujere. Ratsanan kara na saki, ko a jikin shi ya bini ya hau danne ya ja kokarin cimman burin shi. Sai dai fisge fisgen da na keyi ya kasa bashi daman hakan. Cikin wani dasheshiyar murya ya fara magana "ke wlh ba ki isa ki hanani abinda na ke muradi ko ki tsaya salin alin ko kuma kici dukkan banza" kara tsorata ni yayi sai dai hakan bai sa na saduda. Kwalban da ke gefen Wanda na ke da tabbacin na giya ne na fara kokarin daukowa zan kwada masa. Gane hakan yayi, saurin da ke yayi yana fadin "ke don uwarki ni za ki bugawa kwalba? Duka ya fara kai min ko ta ina tun ina ihu ina kuka har na kasa tsinana komai. Ganin hakan ya sa ya fara komawa abinda ya ke hari tun farko, duk fisge fisge na wannan karon bai hana shi ba, gab ya ke da cin wa burin shi.

Ban san Sanda wani karfi ya zo min ba na hankade shi ya fadi kasa. " lafiya, me ke faruwa a nan?" Umar Sanda ya fada tare da karaso wa ciki, ido hudu mu kayi dashi ina kokarin mikewa sai dai na kasa. Wani kallo ya bi Yaya baba dashi. Idanun shi nan ta ke su ka kada su kayi ja, har jijiyoyin kanshi sai da su ka fito. "Adams ashe daman ba ka daina dabbanci nan naka ba? Dan akuyanci ma ka rasa Wanda za ka far ma sai kanwar ka da kuke Uba daya? Ashe rashin hankalin na ka ya      kai nan, amma wlh kayi asaran rayuwa."

"Faroukh!" Yayi saurin kiran shi "please let this stay between us please" tsaki Umar Sanda ya ja sannan ya maido hankalin shi kai na, numfashi na na ke kokarin saisaitawa, nayi kokarin mikewa gabadaya na kasa, saboda bugun da nayi a baya. Hannu na na kai baya na fara kokarin jan zip ina, na jawo ribbon ina da ke gefe na daure gashi na. Kaman kujeran nayi duk da jirin da azaban da na keji bai hana ni mikewa ba da taimakon kujeran da na kama. Yagegen hijab ina Umar Sanda ya dauko ya mika min, nayi saurin amsa ina dafe bango na sa. Da jajayen idanu da za ka iya hango tashin hankali kwance a ciki yace "Sannu Suhaima bai taba ki ba ko?" Nayi dan mintuna kafin na gano abinda yake nufi. Girgiza mishi kai nayi don ba zan iya magana ba. "Alhamdulillah Allah zai saka miki" ban ce mishi komai ba na cigaba da dafa bango na fita a haka na karasa cikin gidan. Nayi zaton komin rashin imanin mutum ya ga halin da na ke ciki sai ya tausaya min. Ina shiga falon Anty Yana ta kafa min ido "ke fa tsiya ta da ke rashin ji hala laifi kika yi wa baban ya miki wannan bugun?

"Ai Anty Yana tun dazu na ke jin ihun ta ba karamin bugu ya mata, daman duk Wanda yace shi rashin ji zai yi lallai yana tattare fa wahala" Adda Falmata ce tayi maganan. Tsabagen yanda raina bushe, idanuna ma bushe su ke karara sai tashin hankalin da ke cikin su. Wani irin Kallo na ashe baki da hankali nabi Adda falmata tashi sannan naja tsaki nayi daki. Adda falmata ce ta biyo ni tana fadin "dan uwarki ni zaki wa tsaki?" Ko kallo ba ta ishe ni na hau hada kayana Wanda yace daga Goggo ne sai na Abbah. "Ni zaki share ina miki magana?" Hannu ta kai za ta buge ni nayi saurin rike hannun, ko kallon da na mata ne ya tsorata tayi saurin jan hannun ta tana ja baya. "Ban son iskanci shegiya wacce uwarta ta tafi gantali" dariya nayi, a raina nace "ko me zaki fada ki fada amma kin gama buguna a duniya" haka na hada kayana tana ta banbami ta wuce tana fadawa Anty Yana. "Bar ta mana Abban in ya dawo ta mishi bayanin inda ta je. Kila uwar ta ta zata bi" ban tanka ba naja akwati da hijabi a jikina na fita. Ko kudi banda shi na nufi nemen machine. Motan da na shaida ta da na Umar Sanda ne ya tsaya a gabana "ina zaki Suhaima" tabe baki nayi don ko har yanzu bai gama goge laifin da ya min ba, ban son jan maganan don haka nace "ajeyari gidan Goggo"

"Mu je in sauke ki" girgiza kai nayi na juya ina kokarin tare machine. "To ga kudin mota" ko kallon shi banyi ba na hau machine in da ya tsaya a gabana mu ka tafi. Ina sauka na hango  Ajiddah ta fito daga gida, ita na kira ta biya min kudin machine, mu ka shiga gidan tana tmbyn meya faru. Ban ce mata kala ba saboda duk Wanda ya ganni ya san ba lfy ba. Ban shiga wurin Goggo ba sanin halin da ta ke ciki.

Direct side in Anty Amarya na nufa Ajiddah na bina a baya. Muna ido hudu da ita, na rungume ta na fashe da kuka. Ba ta hanani ba, bari na tayi nayi ma ishi domin wanin lokacin ka na bukatan ka fidda damuwan ka ko da ta hanyan kuka ne. Ajiddah ma ba ta bani hakuri saboda zuwa yanzu ta san duk wani abu da ke faruwa a rayuwa ta. Sai da lokacin Sallah yayi na hakura na tashi yin Sallahn, nayi karatun qur'ani. Alhmdlh hakan ya haifa min saukin kunan da na ke ji. Lallaba ni Anty Amarya tayi in ci abincin, duk da Ajiddah ne kwata kwata na kasa cin abun kirki. "Me ya faru Suhaima?"

Shiru nayi ina tunanin ta ya zan fara sanar da Anty Amarya bakin labarin abinda ya same ni. Shin za ma ta yarda dani? It was so unbelievable! Ganin ta zuba min idanu ya sa na fara magana. Ko da na gama basu lbrn gabadaya fuskar rudani ne kwance akan fuskan su. Ajiyan zuciya Anty Amarya ta saki hade da girgiza "Tura ta kai bango Suhaima, lokaci yayi da dole ki bar gidan mahaifinki tunda har abu ya kai da haka, Wannan wani irin dabbanci ne daga uwar har yaranta. Ya za ayi suna jin ihun ki amma ba su damu su san me ke faruwa ba? Mutanen nan ba su damu da duk abinda zai faru da ke komin tsanin shi kuwa ba zasu ji kan ki ba." Sabbin hawaye ne su ka taru a idanuwana. Tabbas duk abinda Anty Amarya ta fada gsky ne, shin amman menene mafita? "Ta ya zan cewa Abbah ba zan koma gidan shi ba?"

Ajiddah da idanuwan ta su kada su canja launi ta juyo tana min kallon lfyn ki "Suhaima ki fadawa Abbah abinda ke faruwa kawai shine mafita"

"Karyata ni za suyi Ajiddah"

"Ki fadawa Goggo toh ko sun karyata na tabbatar ba za ta barki ki koma ba in kika nace" Anty Amarya ce tayi maganan. Nan ta ke ko naji zuciya ta ta amince da shawaran ta amma kuma inda gizo ke sakan ta ina zan fara duban Goggon da wannan magana a irin halin nan da take ciki?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top