51

Ta zana jarrabawan, Kuma Alhmdlh komai yazo mata cikin sauki. Sai dai godiyan Ubangiji, don haka suna tsammani sosai a cikin lamarin ga dukkan Wanda ya maida lamuran shi ga Ubangiji. Tana hanyan komawa gida, Kira ya shigo wayan ta. Kai tsaye taji ance mata "Na shigo Kano kina ina ne?" Dif! Natsuwan ta ya dauke, in har kunnen ta ba karya ya mata, to kuwa muryan Zayd taji Yana mata kunnen.

Kai tsaye ta fada mishi inda take jiki a snayaye. Cikin yan mintuna kalilan ya iso wurin, dake shagari quarters zata to akan zoo road su ka hadu. "Bismillah" yace mata, ta bude motan ta shiga. Closest, wurin da zasu iya zama suyi magana in public shine gidan Zoo. Dukkan su basu taba zuwa wurin ba, Amma hakanan suka dukufa wurin.

"Suhaima, Ina neman afuwa a wurin..." Bata bari ya karasa ba tayi saurin katse shi. "Ina zan nemi gafara a wurin ku, tunda nine na zauna daku da wata manufa ta daban" girgiza Kai yayi, yace "Duk da haka Suhaima, zuciyan ki na da kyau. Da badan haka ba, irin wannan Daman da kika samu ba abunda zai hana kiyi amfani dashi ki cutar damu Amma Baki yi hakan ba" ba wai don ta amince ba tayi shiru kawai.

"Tell me about Amal, meya faru da ita?"

"Ba suicide bane" kalman nan da ya fada kadai yayi nasarar sauke wani babban Miki a zuciyan ta, hakan bai boyu ba har Sai da ta saki wani ajiyan zuciya mai nauyi. "Alhmdlh Alhmdlh" ta furta sau biyu a bayyane.

"Me ya same ta?" Ta kara tmbyn shi.

"Cancer ne, bai yi showing kanshi bane Sai da ya fara Kai last stage. Brain turmor ne, in Zaki tuna tana yawan ciwon Kai, Sai Kuma ya hade mata da yawan faduwan da take yi ta sanadiyyan abinda take Sha. To abun ya hade mata ne, harda fatty liver saboda irin nauyin abubuwan da take Sha. Alhmdlh, ta bani sakon da ya min dadi har yanzu nake farin ciki dashi, domin nafi ganin hannu dumu dumu akan mutuwan Amal fiye dake. Ke kam ma ban ganin akwai naki kason ko kadan."

"Taya kenan?" Ta tmby. Dan Kara gyara zaman shi yayi, Yana gyaran murya. "Ta fada min in Miki godiya, domin bayan kun rabu da farko, abubuwan ta cigaba da Sha domin neman gushewan danuwa da bakin ciki. Sai daga baya, da taga sabanin hakan kawai take ta gani, Sai ta fara gwada hanyan da kika daura ta a Kai. In ta daina, Sai ta kasa samun sauki a wancan hanyan nata in ta koma wancan kuma Sai abun ya ragu. Cikin ikon Allah, nakin sai yafi tsaya mata a rai, Kuma Sai ta fi ganin nasara a nan in. Kuma tana kan wannan hanya har lokacin da mutuwa ya riske ta, tace min bata rike ki da komai ba har zuciyan ki, Kuma ita tsakani da Allah take son ki don tana neman afuwa a gunki in ta Miki wani abun" zuwa lokacin, hawaye ne ke yawo kaca kaca akan fuskan Suhaima, hakika tayi rashin Aminiya irin Wanda samun irin ta ke da matukar wuya.

"Lokacin da abun nan ya faru kuwa" Ya cigaba "Lokacin ne farkon da ciwon bata ya fara nuna kanshi. A gaban apartment in gidan su ne, tazo fita ta yanke jiki ta fadi. Shikenan Sai news ya dauka daga saman gidan ta fada saboda Karan faduwan da aka ji da yanayin yanda ta fadin a kife. A daren ranar aka Kira likitan su, ya duba ta Kuma a daren suka bar Nigeria a private jet, kinji dalilin da yasa mu kaje bamu same su ba. Ina Miki albishir da cewa muna kyautata mata samun rahama wurin Ubangiji, don haka addu'an mu take nema a yanzu"

"Allah ya mata Rahma, yasa karshen wahalan ta a nan duniyan ya Kare" Cikin kuka tayi maganan, baki ya dan bata sannan suka cigaba da magana.

Wayan Umar Faroukh ne ya shigo, da sauri ta dauka "An tashi jarrabawa, why are you not at home"

"Ina gidan Zoo" kawai ta fada ya kashe wayan. Da alaman nan in zai zo.

"Shi Zaki aura?" Zayd in ya bukata. Murmushi tayi sannan tace "In Sha Allahu"

"Allah ya yardan mana, Ina Miki fatan Alkhairi Suhaima. Hakika nima yanzu na gane kuskure na, ga hakkin matan da na tabbata Yana bina. Kullum a rayuwata wani sabon jarrabawa nake cin karo dashi. Ina fatan cinye su duka, naga canji wurin Nainerh Kuma nasan daga wurin ki ne, don haka muna godiya"

Dai dai lokacin Umar Faroukh ya iso, Sai da ya dan girgiza ganin su a tare. Wannan karon ma Zayd in ne ya fara bashi hannu suka gaisa. Yanzu sam bai da wani gadara duk da can inma ba kowa ya ke ma wa ba.

A hanya ta fada mishi komai ba tare da ya tmbyn ta ba. Ya jinjina mata sannan Kuma yyi fatan rahma ga Amal in. A ranar ya sa ta hado kayan ta. Ta ma dauka Abuja zasu koma Sai ta ga ya dau hanyan cikin unguwa. Badawa lay-out suka tsaya a bakin wani gandamemen gida. Bin shi dai kawai tayi ba wai don ta San asalin abinda za ayi ba.

Yana bude mota ita ma ta bude ta biyo shi. Booth ya bude ya dauko trolley inta sannan ya mata jagora zuwa cikin gidan.  Tun daga Sallaman ta, taji hayaniyan kaman da mutane a cikin gida. Kafin ta gama tunani taga Aseem da Afra sun fito da gudu suna wasa, suna ganin ta suka canja hanya zuwa Inda suke. Zabagen mamaki shiru kawai tayi, ba abun fadi. She can't remember daya daga cikin su ya fada mata sun zo Nigeria. No wonder, jiya tayi ta neman numban Hajjah ba ta samu ba.

Taji dadin ganin su sosai, musamman Ummin ta. Zama take a wurin ta tayi ta mata shagwaba. Ummin Sai dai tayi dariya, tasan Wanda ba ta samu tayi da bane take ramawa. Ummin ce ta zauna da ita tana sanar da ita maganan zuwa Damaturu, an gaya Mata sun dade da dawowa daga Jigawan dake yanzun gari an samu lfy. Taji dadin zancen, Sai dai Kuma hakan bai hana gaban ta faduwa ba.

Daga Ummi, Jiddah, Baffah, Suhaima Sai Umar Sanda ne suka tafi yoben. Su Jiddah da Baffah Kam da basu wani sanin Yan uwan nasu ba, hankalin su kwance sabanin ita da kana ganin ta kasan tana cikin rudani.

A gidan wata yar uwar Ummin suka sauka, in ka cire Umar kenan. Sai Washegari da suka shirya tukunna suka nufi gidan. Abbah ne kadai yasan da zuwan su, shi inma bai San cewa da Suhaima a cikin su ba. Illa ma tunanin da yasa ma kanshi, in Ummi tazo mai zai dube ta ya fada mata? Yar ta, ta bata? Ko da ya tashi gaya ma Anty Yana za ayi Baki, bai fada mata su waye zasu in ba.

Sai bayan sallan Azhar suka nufi gidan. Suhaima da dogon hijab a iikin ta, ta saukar da kanta kasa suka shiga cikin gidan. Abbah ya dan fita, so Anty Yana be kawai da yaran ta su sadiya. Tana ganin Ummi ta mike da sauri tana Binta da kallon mamaki. Da kyar bakin ta ya iya furta "Aeey" murmushi Ummin tayi, suka gaisa faran faran. Su Jiddah ma duk suka gaisheta, ita dai Suhaima kanta a kasa ba ta iya dagawa ba. Musamman a gidan da yake da bad memories akan ta.

Ruwa tasa Sadiya ta kawo musu, ba wanda ya taba cikin su. Sai can Anty Yana tace "To wacece Maijiddan a cikin su?" Murmushi kawai Ummi tayi, ba dai ta gane sauran ba. Nuna mata maijiddah Ummi tayi. Ba yabo ba fallasa fuskan ta ta kalli Maijiddah "Ma Sha Allah an girma"

"Ina Falmata fa dasu Al-lawan?" Ummi ta tmby. Dai dai lokacin kuwa Sai ga Al-lawan ya shigo gidan. Da farko bai gane su waye bane, Sai da Anty Yanan ta fada mishi. Da saurin shi kuwa yazo ya kara gaishe da Ummin da kyau, daman tun can shine dan gidan ta. Ya gaisa da Maijiddah da Baffah ma, sannan Suhaima. Yana jin muryan ta yayi saurin mikewa yana Kiran "Suhaima?" Lokacin ta dago, ya kara tabbatarwa ita ince. Domin Yana jin muryan ta ya San itace, Sai dai sauran doubt dake fuskan shi.

Har Anty Yana Sai da ta girgiza ganin tabbas Suhaiman ce. "Suhaima kece?" Ta ambata domin Kara tabbatar wa. Murmushi Mai ciwo kawai Suhaiman tayi, tana Kara kallon Anty Yana.

Sun Sha mamaki Kam, domin bakin su dai yaki rufuwa. Su Kuma su Suhaima, suma dai gasu nan ne dai kawai zaune ba wai suna jin dadin zaman gidan bane. Musamman Ummi, da zaman gida ke kara taso mata da abubuwa da dama. Duk dai ba zata ce Anty Yana ta Mata komai a iya zaman ta, matsalan ta daman Falmata ce yawanci. Amma wani abu na mugunta ba ta Mata, illa yarta Suhaima da bata damu da rayuwar ta ba. Bata wani ga laifin su ba, duba da cewa ba yar ta ba. Kuma daman ance yar wani da uwar wani Sai Allah. In akwai mai laifi ma tafi ba wa kanta da Kuma shi mahaifin Suhaiman.

A nan Abbah yazo ya same su, cikin kwanciyar hankali suka gaisa da Ummi. Tace mishi "To ga dai yaranka nan, nazo dasu ka gansu" daga jin maganan ya San magana ta fada mishi. Don Kuma ga kamannin shi nan kiri kiri ya bayyan a fuskan Jiddah, yanayin maganan su ma daya ne. Sai dai har yanzu tafi kama da Ummin.

Da kunya ya ke kallon su. Ya gane Maijiddan, ita kanta yarinyar Sai ya tsince da jin nauyin ta balle Kuma uwar. Ganin Baffah ne ya bashi mamaki "Baffah Kai ne?" Daga Kai yake, ganin he is still confuse yasa Ummin ta warware mishi tsakanin su da Jamila. Har ga Allah, Sai da yaji wani nauyi ya saukan mishi, at least bai yi sanadiyyan raba uwa da dan ta ba. Sai dai har yanzu Yana jin nauyin abinda zai fada mata akan Suhaima.

"Abbah ba kaga Suhaima ba?" Shi inma a firgice ya dago yana kallon ta. Four eyes su kayi dashi, nan da nan idanun ta suka ciko da kwalla. Bata San Sanda ta mike da sauri ta durkusa gaban shi tana mai neman gafaran shi aka bin umurnin shi da tayi lokacin da yace mata ta same shi a Jigawa. Har lokacin tana jin hakkin shi ne ke bibiyan ta, domin kuwa yayi kokarin tsare mata komai a matsayin shi na mahaifi.

Saurin dakatar da ita yayi, Yana fadin shine ma zai nemi gafarar ta ita da Yan uwan ta da Kuma mahaifiyan ta. A lokacin dai duk aka yi kokarin sulhunta komai. Ba a dade Sai ga Falmata ta shigo, ita Ummi har ga Allah da bata ganta ba ta dauka aure tayi, har tana Shirin tmbyn Anty Yana ina take da zama. Duk ta rame tayi wani iri, da ta gansu ma sarai ta gane su Amma sama sama ta gaishe su. Baba ne dai basu gani ba, ko da suka tmby murmushi Mai ciwo kawai maman tayi. Sai daga baya suke jin ashe ya shiga cikin Boko Haram ne daga baya. Yanzu haka ba a San inda yake ba, Kuma sojoji neman shi suke Ido rufe. Dashi da dayawa daga cikin abokanan shi Wanda Suhaima ta gane tare su ka keta mata mutunci. Falmata kuwa har lokacin ba mijin aure, ashe har Sanda Anty Yana tayi ma magana akan Falmatan ta dade tana son shi, murmushi kawai yayi yace suyi Hakuri Yana da wacce zai aure. Sai mutum yazo kaman za ayi auren daga baya a nemi shi kawai a rasa, haka dai abun ya cigaba da tafiya. Daga karshe tsabagen damuwa ya Mata yawa, shine har ya kaita da fara shaye shaye. Duk da dai yanzu an dakatar da abun da kyar, shine baki daya ta lalace ta koma wani abun. Karshe dai, Yan lesbian in da ta taba ma Suhaima gorin tana bi, su yanzu ta fara bi Kuma. Don ma Abbah, na da zafi shiyasa wani iskancin bai yiwu ba. Su baba ne dai sun riga da sun fi karfin shi.

Al-lawan ne dai yanzu haka ana maganan auren shi, saboda ya samu aiki mai kyau a university yake lecturing Amma a can Gombe.

Abbah Kam duk jikin shi yayi sanyi da yaji labarin irin rayuwan wahalan da Suhaima ta shiga, har kwalla Sai da yayi. Ga kuma daman yanzu ya gane duk wani kulla kulla yayan shi ne yayi. Shi da kanshi yazo Yana neman gafaran shi, Daman ance ramin karya kurarre ne.

Washegari, musamman su kaje gidan su Adama, inda Goggon yanzu take da zama baki daya. Godiya Ummi ta dinga Mata, duk ta gane Goggon ba ta gama fushi da ita ba, daga ita har Suhaima. Sun dai bata Hakuri, ta kuwa ji dadin ganin su dukkan su. A nan Suhaima taji cewa kawar ta na garin Kaduna, tunda dadewa suka koma can. Nan fa Goggon tasa Ummin a gaba dole sai da taje kollere, suka daidai ta da Yan uwan ta. Sunji dadin ganin ta, musamman yayan ta da yake fama da rashin lafiya. Ta kuwa taimaka mishi sosai, domin har asibiti tasa aka Kai shi a Kano.

Basu bar Damaturu ba, Sai da Alh Umar Machina yaje neman ma danshi Umar Faroukh (Sanda) auren Suhaima. Abban yaji dadi kuwa sosai, domin dai an San waye Sandan. Dan ma tun rabuwan su da Baba, zumunci nasu ya Dan ja baya. Duk da musamman yana zuwa gaida Abban.

Ba a tsaya wani dogon bincike ba, Abban yayi magana da yan uwan shi aka bada auren. Musamman Abban ya Kira Ummin akan yaushe za a sa auren. Duka duka dai karshe wata biyu aka sa. Ita dai Suhaima jin abun take banbarakwai, don har yanzu ba wani hira sosai suke a tsakanin su ba. A dai kwai sabo ba laifi, kafin su koma Egypt.

Baffah da Abdallah dai sun koma Egypt, Amman Ummi musamman taje ita da Hajjah dasu Suhaiman gidan Su Anisa domin yi musu godiya. Antyn ma taji dadin ganin su, nan Kuma ta kara tabbatarwa Suhaima daga gidan mutunci ta fito. A nan take jin ansa auren Faroukh da Zahra, ta musu fatan zaman alkhairi.

Har gidan Dr Fahad Sai da suka je da Barr. Coincidentally, a gidan suka hadu da Ummin Dr in, tazo garin ranar zata koma dasu Zahra da laylah.  Tana ganin Ummin ashe sun San juna, Daman ita Suhaima tana expecting haka. Ashe kawaye ne sosai tun suna yara, duk da akwai zumunci ma Amma ba wani mai karfi bane tunda aure ne ma ya hada. Sun ji dadin ganin juna, nan suka you exchanging contact tare da alkawarin keeping in touch. Ba laifi domin kuwa dai lamarin ya daidaitu tsakanin su da Rufaidan, musamman ma da ta kasance Mai biyayya a gare ta sosai kaman zata bauta Mata. Ga kuma kyautatawa da yaran ta duk ta hada tana mawa. To daman yara in kana kyautata ma uwarsu Kuma suma kana jan su a jiki, tuni zasu soka. To uwa Kuma baya da abokan shawara kaman yarana ta yan Mata, don haka su zasu tusa Mata son ka ko akasin haka, musamman da ta kasance surukar ta. Sun ma Zahra fatan alkhairi tare da alkawarin zuwa bikin, tunda bayan bikin ne.

Maryam kuwa, ga mamakin Suhaima faran faran ta tarbe su, ga gidan ta tsaf tsaf Sai kamshi yake haka ma Kuma dan ta. Cikin ta kuwa har ya fito. Ashe ashe dai Barr mustapha maganan aure ya dago gadan gadan, Kuma daga daya daga cikin kawayen ta da suke zuga ta, daga Anty har daddy suka goyi bayan shi, shine fa ta saitu data gane amanan ta kawayen nata ke neman ci. Abinda ba ta sani ba plan ne, ita ma kawan abokin shine ya kawo ta aka biya ta. Maryam ta gama haukan ta, ta hakura tilas daga baya ta shiga taitayin ta suka dawo kan hanya. Ana dai fatan abun ya daure, saukin ma mijin ta na son kayan shi.

Bayan nan ne ita Suhaima da Jiddah, Umar ya Kai su gidan Adama. Yaran ta biyu, duka Mata. Kyawawa dasu, har Sai da su kayi kukan murnan ganin juna. Gidan ta babba, gashi tayi jiki tayi kyau. Da alaman dai tana jin dadin zaman auren. Sun dade a gidan, daga baya Adama daru tasa dole suka zauna suka kwana. Haka Jiddah ma ta dinga Jan ta a jiki, ranar da kyar suka yi bacci. Ta taya kawar ta murna sosai.

Haka Bauchi ma suka je gidan Anty Amarya, domin ita ma ta taka rawan gani sosai cikin rayuwan ta. Ta kuwa ji dadi, daman tsakani da Allah take son Suhaiman. Sai Kuma Kano da suka je, ta nemi Ajiddah. Ita dai Sai dai godiyan Allah, duk kudin da take buri babu wani su Amma da ke tana business akwai na rufin asiri. Ita ma kaman tayi me data ga Suhaiman tsabar dadi rasa inda zata sa kanta tayi.

Duk sunma Suhaima fatan alkhairi, sannan Kuma duk suna Shirin halarta auren. Kafin ta koma Egypt Exams inta ya fita, Kuma Alhmdlh ta samu. Don haka koda suka koma, gadan gadan hidiman auren aka hau. Banda tsokanan ta ba abinda Umar yake yi, ita Kam ma kunyan shi take ji.

Jarrabawan ta ya fito ta samu, don haka ko da suka koma Egypt hidiman auren suka fara kawai gadan gadan. Ga Umar Sai wani rawan kafan da bata San dalili ba take yi, ita kunya ma yake bata. Da ya zauna ya bata labarin yanda ya sota a lokacin da ta dinga mishi kwana kwana Sai da ta dinga jin wani iri. Bai fada bane kawai saboda Kar hakan yayi sanadiyyan rabuwan su.

A Damaturu aka daura auren, ba ayi wani bikin ba. Abbah da kanshi ya kaita Abuja har cikin gidan da Umar in ya gina zai ajiye ta, Ummi ta mata wa'azi Mai shiga rai haka Hajjah. Kaya kuwa da aka hada Mata har ba a magana. Daga Abbah har Ummi dasu Hajja ba a bar su a baya ba. Shi ma gogon ya taka rawan gani sosai. Haka aka kaita gidan ta, inda ake fatan ta samu rayuwa mai albarka Kuma Mai dorewa.

Shi kadai ya shigo ba tare da wani dan rakiya ba. A daki inda aka barta, nan ya same ta. Yayi Sallama ta amsa. Kallon ta yayi yaga duk ta wani takura kanta. Murmushi yayi ya sa hannun ya dago kanta dake kasa, sannan ya ajiye gyalen da ke jikin ta a gefe. Hura mata iska yayi akan fuskan, tilas ta dago tana kallon shi.

"Kinyi kyau Amarya, sai walkiya kike abun ki" bata iya amsa wa ba. Ya cigaba da cewa "da kinsan shekarun da na deba ina jiran isowan wannan ranar da baki tsaya min wani noke noke ba" kallon shi ta danyi tana smiling.

Wani irin runguma ya mata, harda sakin wani nannauyar ajiyan zuciya. "God i've been waiting for this opportunity tunda dadewa. Ina sonki Suhaima, wannan kalman ba ta dade adane a cikin zuciya ta. Ina fatan zaki samar mana farin ciki mai dorewa"

"Allah ya bamu zaman lfy" cikin siririyan murya tayi maganan.

"Ameen Amaryata, won't you tell me you love me?"

Dan sunne kai tayi "Ina sonka nima sosai" da sauri kuma ta boye kanta a cikin kirjin shi.

Hannu yasa yana jin wani annashuwa na mamaye shi. Ya wani shafo fuskan ta "Tashi muyi Sallah kinji, yau akwai labari dayawa" wani kallo ya mata, ya kashe mata ido daya. Murmushi tayi kawai ta sauko, da alamun dai angon nata dan soyayya ne.

Tammat Bihamdillah.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top