CHAPTER 9
Sarki kuwa abin ya burgesa hakan yasa yace idan har gidan su munira ne suka ci toh zai bawa Adam din mashin sa.
Rigijib gabji toh yanzu ne fa ido zai raina fata domin mahaifiyar Adam bata San ana yi ba tana can ana kokarin yanda za'ayi hamdama a kwashi na banza yayinda sarauniyar ke zaune a gefen sarki da yaran nasu a gefen su sai mai martaba baban Umar ta dayan bangaren. Share fili akayi kowa ya fita nan aka fara.
Ka'idar wasan an ajiye wani Abu mai kama da gora amma yana da tsayi sannan yana da kunnuwa biyu. Idan ka wulla ya fada cikin gorar toh kana da maki ko points 2 in ya fada ko wani daya daga cikin kunnan maki 4 ne.
Saide abin yana da aljihu ta baya Dan haka idan saitin ka ya kai saiti ka iya wullawa ma aljihun baya Wanda baka gani kana da maki 10. Durmemen gangan su aka buga sannan San Kira yace an fara!
Yarima Umar ne zai fara wullawa Dan haka wullin farko ta fada cikin ramin cikin normal rami aka rubuta masa 2. Yaba shi mutanen sarki sukayi aka rubuta masa biyun sa a babban allo.
Yarima Adam ne ya wulla nasa saide kashi daidai kusa da abin ta fadi.kirjin sarauniya ne ya fadi Dan kuwa auren yar ta ake kuma sadakin yarta aka sa a matsayin kyauta. Kwantawa tayi kadan ta radawa sarki kuma mijin ta wato baban munira ya Nemo uwar yaron nan wato marka tazo ta dauke danta.
Dan ita wallahi bazata yarda a salwantar da sadaki yar ta ba. Da hannu sarki yayi Mata alamun ta rage murya kar sarki baban Umar ya ji ta. Shi kam mai martaba bai ma San ana yi ba sai gyada kai yake cikin alfahari da dansa.
Kamin kace me yarima Umar yana da maki 10 yayinda yarima Adam ke da 6. Munira da ke cinyan baban ta tanajin me ake cewa tayi luf sauka tayi baban ta yace yarinyar arziki ina zakije ? Bata ko kulashi ba sai ma washe masa baki da tayi ta fita da gudu zuwa filin.
Fadawa be sukayi kokarin rikota amma ina sama tayi wa yaro nisa zuwa tayi ta rike hannun Adam tace yaya bani kamar wawa ya mika Mata ya fita daga filin yana kuka. Juyowa yarima Umar yayi ya kalleta yaga wani Abu dan dunkul a gefensa bai San sands murmushi mai sauti ta kufce mai ba Dan abin ya bashi dariya.
Kato ma ya kasa cin sa sai wannan yar tsamurmurar? Sarauniya batasan sanda ta sauko daga kujeran ta ba tana Dan dariyar karya saboda idon sarki tace haba ke kuwa munira ina abin yaro ba ko alkalami baki iya rikewa ba ina ke ina yin wasan mashi. Zo muje na baki cumui kici kar ki jiwa kanji ciwo.
Da sauri sarki ya jinjina kai shima yana murmushi yace kar kiyi taurin kai munira zaki ji ciwo maza zo ki zauna a cinya na kinji? Make kafada tayi tace ko ba Dan kyauta ba ni bazan zauna ina gani martaban gidan mu ya fadi a a hannun wannan katon banzan b..... da sauri sadiya ta rufe Mata baki tace kar kiyi taurin kai munira zo mu tafi.
Warcewa tayi tana kokarin magana sadiya ta ciccibe ta. Mai martaba baban Umar abin ya burgesa Dan yarinyar bata tuna masa da kowa sai marigayiya Fatima. Cikin fara'a yace ah ah sarkin banty ya haka? ku barta mana ba wasa bane kunsan yara da kiriniya. Ku bata mana ta nuna mana baiwarta.
Ba Dan ransu ya so ba haka barta kuma dole mutum yayi fara'a da yake jefawan Adam ne kuma yanzu ana zagaye na biyar wato round. Kuma dama sau 7 ake wullawa yarima ya wulla nashi na 5 ko wanne yana ci. Yayinda Adam yaci 3 ya fadi 1 anan ya samu maki 6. Na biyar din ne munira zata wulla. Kallon abun tayi da saiti daidai kunnan nan ta wulla AI kuwa ya fada. Da mamaki yarima ya juyo ya kalleta.
Toh yanzu kam ya gane ba abokiyar wasar renawa bace gashi yana zagaye na 6 amma shi gwani ne Dan haka ya saisaci kunne shima ya wulla ya zamto yanada 14 ita kuma Goma kunne ta sake jefawa ya zamto tana da 14 itama toh fa yarima daga wannan yin ko yaci ko ya fadi ne kuma ba taba faduwa a wani gasa ba tunda yake.
Dan haka dauko guda 2 yayi a lokaci daya ya saisaci kunnuwa biyu ya wulla inda ya Sami 8 Dan haka yanada 22. Sarauniya fa guiwar ta yayi sanyi dan haka ta sanar da baiwa tace wa munira ta wulla biyu ita ma Dan idan ta kuskura ta fadi sai ta sata sharan filin nan na kwana 3. Kuma filin ya kai stadium girma dukda ko ta fada ne Dan ta bata tsoro.
A kunne baiwar ta ce wa sanar da munira kamin ta koma ta tsaya a inda take. Rufe ido munira tayi tana tunani ita bata iya biyu a lokaci daya ba mahaifiyar ta bata koya Mata ba amna idan ta bari ta fadi ta ina zata fara share wannan fili? Sannan idan sarauniya ta tsaneta AI sun kade Dan sarauniyar baza'a ce tana son su ba amma bata tsanesu ba.
Sabanin su marka Wanda da ba Dan idon mijin ta ba da tuni ta sayar da ita. Abu data ne ya fado Mata a rai ko kuma idan ta bi wannan abun dayan biyu ne ko ta sha ko kuma a sha da ita. Amma ya zatayi ta bari a sha da ita? AI dama mutum baya nasara sai yayi garaje saga nan zai gane kuskuren sa ya dinga gyara su.
Daukan guda daya tayi sarauniya ta dunkule hannu a ranta fadi take yarinyar nan in ta kuskura aka dauki sadakin diyata sai na saida mahaifiyar ta Dan suna ban tausayi bazan iya dukan ta ba.
Mai martaba kuwa yana baza ido yaga yadda za'ayi yarinyar nan ta samu maki takwas a jifa daya. Daga hannu munira tayi kusan dakina talatin suka tafi bata harba ba wajen kowa yayi shiru ana kallon ikon Allah. Daga kan mashin tayi ta wulla maimakon ta jefa shi a straight dukda ko anyi mashin ne kamar baka.
Rufe ido tayi tana jiran taji yadda za'ayi da ita kawai sai taji an saki shewa ya fada cikin aljihun bayan nan kamar yadda take Hari hakan yasa ta samu 24 tsalle ta daka ta fada cikin yarima Umar tana washe baki bai ture ta ba kawai barinta yayi ita da kanta ta diro tayi masa gwaliyo kamin cikin karamar muryarta irin na yara masu cakwaikwaiwa tayi masa gwaliyo tace nice nayi nasara Dan haka daga yau dole ka Kira yayana yayanka.
Juyowa tayi ta kalli maimartaba cikin iyayi da ba Wanda ya taba ganin tayi tace kai me martaba ina mashin da kace zaka ban? Dariya mai martaba yayi Dan yarinyar ta burgesa. Da kansa ya Mike ya damka Mata mashin. Riko hannunta yarima Umar yayi duwa wani baranda ba kowa a wajen yace ke. Turo baki tayi tace me? Yace tunda nake ba Wanda ya taba sha da ni lallai ke jaruma ce.
In kin girma zaki aureni? Kallonsa take kamar wani shashasha tace me yasa zan aure ka ni nace ma zanyi aure ne? Yace ni de ki yarda zaki aure ni tace toh kana so na ne? Yace eh dariya ta kyalkyale da shi Dan ita Sam bata dauki abin da muhimmanci ba tunda yarinya ce ta dauka wasa ce kawai tace ban yarda ba. Yace me zanyi in tabbatar kalle kalle tayi ta hango wani kwaro daukowa tayi tace sai ka ci wannan kwaron.
Ba musu ya karba ya danna a baki Dan kuwa bayida buri sai ya aureta dan tun suna yara gimbiya hauwa ke damun sa yasan idan ya auri wata toh gimbiya hauwa bazata yadda ta zama kwarkwara ba ai. Saide danika biyar da cin wannan kwaro ya yanki jiki ya fadi warwas a kasa.
TOH FA ME YA SAMU YARIMA HAKA? SHIN KUNJI DADI DA MUNIRA TA CI? DONT FORGET TO VOTE, FOLLOW AND COMMENT
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top