CHAPTER 6

Bugawa kirjinsa yayi a take ya dafe saboda zafin da ya sake yi masa.....
Matsowa tayi a hankali tana Dan leka fuskan sa sannan tace masa me wai kake dafe kirji? Da hannu ya Mata alamun kar ta karaso tunda shi ba gane abinda take cewa yayi ba.

Juyawa tayi ta kama kunkumi tare da fadin tunda naga bazaku iya babu ni ba sai kun biyo ni ku zo in Baku kariya sannan ta fara taku kamar wata sarauniya. Dariya yimla yayi Dan yasan da gyara a maganan.

Tafiya suka ci gaba da yi yarima yace ke kin wani shige gaba kamar jakadiya ki dawo baya mana bakisan mace a baya ya kamata tayi tafiya ba? Tace dokar waye ? Yace me kika ce? Dafe kai tayi kawai tayi masa NUNI da suci gaba da tafiya. Yace ki dawo baya ni in shiga gaba. Make kafada yayi a ransa yace ni da na damu da ke ma kenan da alamun banason dogon magana baki na har ya fara ciwo.

Kukan zaki sukaji yarima bai San me ya faru ba kawai de ya ga mutum ta makale masa ne ta bare baki tana kuka yadda jarirai ke yi sannan tana nuna inda ta jiyo kukan zakin da yatsa.

Dariya ya fashe da shi kuma a lokaci daya ya yatsine fuska tare da dafe kirji sannan yace sauka. Girgiza kai tayi tare da kara kankameshi sannan ta kara murya. Zul ne yace shugaba waye wannan dace ki akayi ko  ari mu kashe shi. Da sauri ta diro tace karku tabashi. Sannan ta rungume zul wato dilanta cikin Muryan kuka tace zul Dina.

Yarima kuwa zama yayi a gefe ya rintse ido gumi na tsattsafo masa ya rasa dalilin da yasa kirjin sa ke masa suka daga tazo kusa da shi kamar ana daba masa mashi haka yake ji. Zul yace su waye wannan? Tace oh sabin ahalin mu ne. Muje gida zan fada muku.

Bayan yimla yarima ya hau suna tafiya tana basu labari suna ta dariya tare da yi Mata tambayoyi zul yace toh yanzu ya zaki yi da su tace mutumin de cikin gari zan kaishi. Amma yimla na kam zan rike shi ko yimla? Kallon kallo yimla da zul sukayi kowa ya dauke kai irin kishin nan.

Bayan sun iso ne tace kai yunwa nake ji nan dai suka cicci abinci sannan ta shirya tace bari tace wa yariman ya jirata zata hada wani abu. Tsimmokara yaga ta hada sannan ta saka fata ta kasa ta saka a jikin ta kamar bante ko Dan kamfai yace menene wannan? Da kafada kawai tayi masa alamun ita ma bata sani ba.

Sannan ta dauka zata saka a jikin ta domin tare al'adar ta ganin ya kure ta idanu ta nuna masa ya juya Tabe baki yayi yace ko baki fada ba. Juyawa yayi abinsa yana fatan kar Allah yasa zuciyar sa ta sake yi masa wannan ciwon sannan daga ya shiga cikin mutane zai nemi magani.

Kama hanya sukayi suka shiga cikin gari saide ba kamar kullum ba yau bata yi shigan maza ba Dan haka anan ganin ta tare da namiji Wanda shine ya rufe fuska akayi caraf aka danke su sai gidan sarki yayin da aka buga hangar dake wajen gari Wanda ana biyashi ne idan an kama mai laifi domin sarki ya zarar da hukunci.

Sarkin garin banty ne ya shigo fadawa na ta faduwa suna kwasar zunubin su 😂. Allah ya ja zamanin sarki, a cikin wannan gari mai tsarki wannan gari naka yau aka kama wannan maiyar da namiji sun shigo mana gari da tsakiyar rana kuma kamar de yadda muka sani wannan matashi ba muharramin ta bane.

Waziri yace ayi hattara de Dan talakawa. Kowa dai yasan wacece wannan maiyar. Sarki ne yayi gyaran murya yace waziri bana son shiririta. Waziri yace tuba nake mai martaba.

Sarki yace a shigo da su. A cikin buhu guda biyu aka shigo da su aka ware dayan yarinyar ce a ciki. Tana fitowa ta turo baki tana shirin fashewa da kuka. Hankadata akayi ta fada gaban sarki yayi da sarkin tunda ya Mata kallo daya bai kara kallonta ba. Fito da yarima akayi fadawa suka sa hannu suka ware Nadin da ke fuskar sa.

A take suka rissina tare da fadin Allah ya kara wa yarima nisan kwana sarkin garin banty da kansa sanda ya Mike ya tsaya Dan basu tsammaci su ga yarima ba. Yarima yace yarima kuma? Wani ciwo yaji ya sari kansa a take ya bude idanun sa ya Mike ya tsaya tare da hade rai domin kuwa ya Tina komai.

Hakan yasa ya gyara zaman rigansa sa yayi kananu da ido. Sarki baki na rawa ya bada umarni a kawo wa yarima kujera. Zama yayi akace jama'a da suka taru domin a jefe mazinatan duk su watse.

Sarki yace Allah ya ja zamanin yarima ya kare ka daga sharrin mutum da aljan lallai bamu tsammaci Kaine zaka kasance a wannan wajen ba. Saide my a ka'idar mu da al'adar mu idan muka kama irin wannan abun hukuncin kisa muke yi shiyasa ko da wasa ba'a zina a kauyen mu.

Yarima yace haka addini yace? Ko kun kamata tana zina ne? Daga ganin mace da namiji ba bincike ba shedu Luce zaku kashe su? Ta taba yin aure ne da zaku kasheta? Sarki yace tuba nake yarima ayi min afuwa bisa kuskure na.

Yarima yace wacece ita kuma me yasa bata zaune a cikin al'umma?kallon kalli kowa yayi domin an kafa doka duk Wanda ya kuskura ya dago maganar ta toh lallai za'a koreshi a garin. Yarima yace bana son na maimata kaina. Sarki yace yarima duk bazasu amsa maka ba ni daya ne zan iya amsa maka. Mu shiga daga ciki.....

......

Masarautar unto kuwa mai martaba bavan yarima a take ya tashi mutane domin a tafi neman kafadan da ake tunanin ya fada ruwa saide ko da suka je basu samu kowa ba sai alkyabban yarima. Koda aka kawo wa sarki labari cewa alkyabban yarima aka samu hankalinshi ya Dan kwanta kuma ya sake tashi.

Domin koda shi ya fada ruwan ai ba'a samu gawan sa ba saide akwai yuwuwar yana raye. Da daddare sarauniya kuma mahaifiyar su kabir ta shigo bangaren mai martaba murmushi yayi da ganin ywar gidan sa itama murmushi tayi masa da ka ganta ka ga mai wakiltar shedan a doron kasa. Zam tayi a gefen sa tare da riko hannun sa yace mai martaba karka damu komai zaiyi daidai insha  Allah tunda aka samu rigar sa shima za'a sameshi.

Murmushi sarkin ya kara yi Mata yace insha Allah na gode Mata ta lallai ina alfahari da ke saboda yadda kike son yaron nan kamar ke kika haifeshi. Murmushin yake kawai tayi amma ita ko sunan yarima aka Kira sai ranta yayi suya balle ta kalle sa ji take kamar ta cinnawa duka masarautar wuta. Domin its fa hatta ya yan ta so take taga bayansu a cewar ta tana son ta kafa tarihi ta zama mace ta farko da tayi mulki a masarautar.

HMM TOH FA LALLAI ABIN NATA YA KAI... KU BIYO NI DON JIN WACECE YARINYAR SANNAN ZA'A KASHETA KO DE YARIMA ZAI CETO TA? ZATA SHIGO MASARAUTAR YANZU KO DA SAURA?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top